Sashe 46
Akidata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"waye wannan?" ya nuna mata Bulama
"Alhaji Bulama"
"kin san matsayinsa a gurina?"
"Just a long time business partner to you"
"he is more than that to me, kuma kin sani danme zan baki umarni kiyi fatali dashi? Duk abunda mukeyi munayi ne dan rayuwarki, danme zaki ciwa Fahad mutunci? A gaban Yusuf komai ya faru, daughter nasan duk abunda kike yi, ina ƙyale ki ne saboda nasan halinda kike ciki na maraici, amma kina zarce ƙa'ida wasu lokutan, daughter farincikin ki muke fata shiyasa muke son aurar dake"
Gaba ɗaya Widad ta ɗauke kai daga kallon Daddynta zuwa wani sashin daban, tanajin ɓacin ran saboda wannan daƙiƙin talasurun Fahad ɗin yau Daddynta ke mata faɗa, ze gane bashi da wayo.
"dan haka whether you like it or not, i have took the final decision, ending of this month zuwa farkon wata na gaba zan É—aura Auren ki da Fahad"
Zare ido Ramlah tayi, taji zuciyarta kamar zata faÉ—o.
Fahad ya wani gyara zama ya kalli Alhaji Nasir yace "sannan Daddy gaskiya yakamata ayi mata magana akan tasan yadda zata dinga gayamin magana, ta tauna ta kafin ta faɗeta dan sam bata da ɗa'a"
Miƙewa Widad tayi tsaye a fusace tace "Over my death Body Daddy, wallahi da in auri wannan mara amfanin gara in kashe kaina, kai ka isa ka kalli tsabar idona kace a koyamin yadda zan magana, waye kai"
"Widad!!!" mahaifinta ya kira sunanta tare da Miƙewa kamar ze kai mata duka.
Cikin zafin nama Yusuf ya miƙe ya shiga tsakanin Widad da mahaifinta ya girgiza kai yace "Yallaɓai ayi mata afuwa dan Allah, baka saba yi mata magana haka ba karka fara yanzu karkasa zuciyarta tayi rauni, kowa ya juya mata baya, ka sauraretaba zata rasa dalilinta na ƙinsa ba"
Alhaji Nasir yace "Amma Yusuf yakamata Widad tayi min haka a gaban mutane ta nuna ban isa ba?"
Girgiza kai Yusuf yayi yace "ba tayi haka dan Wulaƙanta kaba, ta tashi a environment ɗin da kowa yana da 'yancin faɗan abunda yake ra' ayinsa, karka ɗau hakan a matsayin ta Wulaƙanta ka, kayi haƙuri dan Allah kasan bata da lafiya"
Tuni hawaye ya wanke fuskar Widad ta kalli Daddynta karo na farko a rayuwar ta da yaƙi bin abunda takeso, hannayenta biyu ta haɗa tareda duƙar da kanta alamar neman afuwa, daga nan ta juya ɗakinta.
Alhaji Nasir ya nemi guri ya zauna, Bulama yace "lamarin daughter se haƙuri, Allah ya shirya mana"
Hajiya Halima ta gyatsine baki tace "wannan direban ne yake hure mata kunne take iskancin data ga dama, na rasa wace irin alaƙace tsakaninsu banda haka ana mata faɗa meye na tsoma baki? Kaima Yallaɓai harda kai da kake saka bare a al'amuran gidanka"
 Alhaji Nasir yace "ba ruwan Yusuf, a irin taurin kai na Widad da irin haƙuri na Yusuf be isa ya hure mata kunne ba, sedai haƙurinsa ne yasa suke tare har yanzu, dan haka karki ƙara aibata shi ko ɗora masa laifi, kaimu Fahad zan shawo kan komai insha Allah"
Yusuf ya miƙe yayi musu sallama ya fice suka cigaba da tattaunawa.
Cakwakiyar gidan nan akwai sarƙaƙiya da ban mamaki, yana nan zaune ya dafe kai yayi shiru Bulama da Fahad suka fito zasu tafi, Bulama ya shiga motarsa direbansa ya ja suka tafi.
Fahad ya tako zuwa gaban Yusuf ya zauna yana fuskantar Yusuf yaceÂ
"kaine direban Widad ko?"
Yusuf yace
"Eh nine"
"Naga kamar matsayinka a gidan nan ya wuce matsayinka na zahiri, zan ja maka kunne ne idan har kana shishshigi da iyayi ka kiyayi Fahad, dan bana barin duk wani abu daze kawomin cikas, matsiyaci kawai kalli rigar wuyanka wai har kaine zaka shiga maganar da bata shafeka ba"
Yusuf yayi murmushi ya miƙawa Fahad hannu yace "Assalamu Alaikum warahmatullah"
Fahad ya kalleshi yace "ni zaka miƙowa hannu kace mu gaisa, kasan koni waye?"
"haka Addini na ya koyamin, ban saniba ko zama a cikin turawa yasa ka manta hakan, rigar wuyana zata iya fin taka daraja in har da gumin halak na sameta, sannan nafi kowa sanin ko kai waye, ɗan adam ne da'aka samar daga Najasa wanda ƙarshena ni da kake kira matsiyaci da kai da kake ganin kanka wani ƙarshen mu ɗaya wato turɓaya kuma Abincin tsutsa, kana fuffukar ban san waye kaiba, kamar ba'a gabana mace ta keta ka ba ta Wulaƙanta ka, wulaƙanci mafi ƙasƙanci shine yadda ake cusa mata kai tana cewa bata sonka "
Galala Fahad yayi yana kallon Yusuf, sam be zaci Yusuf ya iya yanka baƙaƙen magnganu haka ba, Yusuf ya miƙe yace " ka kiyaye gaba, dan idan baki yasan me ze faɗa be san abunda za'a mayar masa ba, bana shkkar kowa se Mahaliccina, kana gayamin abunda beminba zan rama, ni yanzu damuwata be wuce yadda a dalilinka aka samun uwar ɗakina a damuwa ba, damuwarta tafi komai tsayawa a zuciyata"
************************************
"Akan me za'a ayi maka transfer bayan bamu sallami wannan mutanen ba? Waima waye yayi maka transfer ne haka ba shiri? Aknme za'a É—auke ka daga garin nan?"
Abbas yayi ajiyar zuciya yace " wallahi ranka ya daɗe ban san yadda hakan ta faru ba, Suleiman ya cemin daga sama transfer ɗin tazo, abun baƙin ciki aka maye gurbina dana bari da Yusuf, ni ina kyautata zaton shine yaje yasa akamin transfer dan ya gaji muƙamina, kuma da yake munafiki ne ya zo yana nuna damuwarsa akan transfer ɗin da'akayi min"
Saleh ya numfasa yace "Abbas tabbas akwai babbar matsala wannan transfe da'akayi maka ba tare da samun binciken da Yusuf yayi ba, a ɗan ganin da nayi masa beyi kama da mugun mutum ba yana da nutsuwa, dan haka bashi da hannu a cikin transfer ɗin da'akayi maka, ni babban burina in samu binciken da yayi a hannuna in sallami wancan mutanen kafin su shiga target ɗinsu na biyu kuma na ƙarshe akan Widad, wanda target ne me hatsarin gaske"
Abbas yace "nifa takaicina shikenan yanzu ba zan samu kuɗaɗen nan ba? Gaskiya na ƙallafa rai amma karka damu Yallaɓai, dukda zan bar garin nan dole a samu binciken da Yusuf yayi"
Saleh yace "don't stress yourself i know what to do"
"Amma kana ganin rashin bada file É—in akan kari zesa kaima ka shiga cikin matsala?"
"babu wata matsala am also planning something, karka damu ni zan tafi duk yadda ake ciki zamuyi waya"
Daga nan suka yi sallama.
Sam Yusuf ya dena ganin Widad, hakan yasashi shiga damuwa sosai, hakan yaso ya shafi aikin da yake yi, ya damu sosai yaga halin da take ciki, bashi da hujjar shiga cikin gidan tunda ba nemansa akayiba.
Mutanen gidan dama ba wanda yake saurarar Yusuf, dan haka haka yake zuwa ya wuni ya tafi zuciyarsa cike da son sanin halin da take ciki.
Yusuf yana zaune yana tunanin yadda zega Widad dan yasan koba'a gaya masa ba Widad tana cikin damuwa.
Fitowar Alhaji Nasir dasu Hajiya Halima ne ya dawo da Yusuf daga tunanin da yake yi, Fuskar Alhaji Nasir akwai damuwa amma ya danne damuwar tasa yana ta fara'a.
Yayiwa Yusuf alama da yazo, Yusuf ya taso yazo, Alhaji Nasir yace "Babban Yaya, airport za muje zamu ɗakko ɗana Anwar, ya kammala karatun sa"
Yusuf yayi murmushi yace "Masha Allah, shima Yayan uwa ɗakina ne?"
Alhaji Nasir yayi murmushi yace "Yusufa kenan, ai uwaɗakin ka bata da wa ba ƙani, Amma Anwar ma ɗana ne tunda na riƙe shi"
Yusuf yace "ba da ita zamuje bane? Naga ita bata fito ba?" Yusuf yayi maganar cike da son sanin halinda Widad take ciki.
"Kasan tana fushi dani ne, ta dena zuwa inda nake ma, na ɗan ƙyaleta ne ta huta, har seta gane mahimmancin maganata"
Har Yusuf zeyi magana, Hajiya Halima tace "Kaga ka ishemu da surutu, muyi mu tafi kar jirginsu ya sauka yazo yana faman jira"
Alhaji Nasir yace "Bimin shi a hankali Halima, Yaya nane a girmama shi ko dan sunan nasa"
Nura yana gefe ji yake kaman ya shaƙe Yusuf, ba'a taɓa ma'aikacin da Alhaji Nasir ke nunawa soyayya kamae Yusuf ba dukda mutum ne me girmama na ƙasanshi, tsabar abu yanzu Alhaji Nasir be fiye damuwa da Nura yaja shi a mota ba sedai Yusuf.
Gaban Mota Amal ta shige, yayin da su kuma suka shiga baya, Suna tafe a mota iyalan suna hira kamar ba abunda ke damunsu, Alhaji Nasir yana dauriya ne kawai, yayin da Yusuf ko uffan yakasa cewa hankalin sa na kan Widad.
Koda suka je airport sunyi A ƙalla mintuna talatin, sannan wanda suka zo dominsan jirginsu ya sauka, matashin kamarsa ɗaya sak da Amal, kana kallonsa kasan ɗan uwansu ne, da gudu sukaje suka rungume shi cike da farinciki, ya ƙaraso gaban Alhaji Nasir ya durƙusa ya gaishe shi.
Bayan sun gaisa ya kalli Yusuf ya miƙa masa hannu sukayi musabaha, da alama Anwar shi a nutse yake ba kamar 'yan uwansa ba, daga nan suka nufi hanyar gida, suna tafe kamar zasu fasa motar da hayaniya da shewa.
Har sukaje gida hirarsu kawai suke, amma alamu sun nuna Alhaji Nasir biye musu kawai yake, sun Sakkowa sukayi cikin gida yayinda aka bar Yusuf da kwaso akwatunan Anwar.
Suna shiga falo kawai Yusuf yaga Widad a zaune tana shan ruwan roba, sedai idanunta a kumbure suke, alamar kodai bata bacci kokuma kuka take yi, gaba É—aya Yusuf yaji babu daÉ—i.
Anwar yace "Masha Allah, little queen ta girma Amma Daddy sha ka fashe ka bata dan yayi wuri ace tayi wannan girman"
Daddy yayi murmushi yace "gata nan tambaye ta, in da ragiwar sha ka fashe É—in kaima ta sammaka"
Ba tsammani Yusuf yaga Widad ta É—anyi murmushi, yayin da Hajiya Halima ta tsuke fuska tace "kaga muje ka wataa ruwa ka nemi Abinci"
Anwar yace "bari Mummy in gama ganin lovely ɗin Daddyn ta inji dalilin da yasa ba tazo taroni ba"
Yai maganar yana ƙarasawa inda Widad take ya zauna, Alhaji Nasir kam part ɗinsa ya wuce yana murmushi saboda Anwar akwai barkwanci.
Ramla cikin tsawa ta cewa Yusuf "dalla malam ka ajiye kayan na ki fita, uban sa ido kawai"