← Book details Akidata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 82

Sashe 12

Akidata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"gaskiya ni Mummy zan tattara kaya na in bar gidan nan na gaji, wannan wane irin cin zarafi ne?"

Mummy tace "duk nasan da haka amma kuyi haƙuri ku ƙara wataran se labari da munsamu abunda muke so shikenan fa an wuce gurin"

Amal tace "dan Allah Mummy yaushe wataran É—in nan zata zo, shekara nawa muna zama kaman bayi? Wallahi nagaji kalli cin mutuncin da tayi wa wannan bawan Allah dan kawai ya kaini unguwa"

A fusace Ramlah tace "dallah rufewa mutane baki, dan taci masa mutunci seme ina ruwan wani? Shi ta fara yiwa cin mutunci? Dama naga yadda kike wani zaƙewa a kansa tun wuri ki nutsu dan ni natsane shi wallahi sam ban yadda da shi ba"

Amal tace "Malama ba ruwan ki da abunda nake yi seki ta tsanar tasa ai, seki kashe shi tunda kin tsane shi"

Mummy tace "kunga dan Allah ya isa haka kar kuyi min faÉ—a, ni kaina ban yadda da wannan Yusuf É—in ba, narasa yadda aka yi megidan nan ya wani É—aukake shi haka, ina son sanin daga ina yake"

Haɗe rai Amal tayi ta zumɓura baki

Mummy tace "ku kuke tada hankalinku, Ramlah zancen da kika yi min ranan na tambayi babanta ya tabbatar min da cewa Aurar da ita zeyi"

Da yake Amal bata san zancen ba da sauri ta waigo tace "Aure kuma? A hakan za ai mata Aure? Waze kwashi wannan Jarabar"

Ramlah tace "Mummy dama na gaya miki, Amma wane me tsautsayin za'a liƙawa wannan Mahaukaciyar? Nasan dai bata da saurayi to waze ma kulata taci masa zarafi"

Mummy tace "ba wani bane Fahad  ɗin Alhaji Bulama ne"

Asahar Ramla ta saki tace "Wane Fahad É—in?"

Murmushi Amal tayi tace "Bulama nawa muke da shi? Fahad dai da kika sani, Fahad naki shine me tsautsayin"

Ramlah tace "Taɓɗijan wallahi da sake, baze yuwu ba akan me? Ita Hajiyar sa tana me za'a aura masa wannan tantiriyar ga hauka gashi maybe ta gama watsewa da turawa, shekararta nawa a turai, Allah kaɗai yasan me take acan baze yuwu ba"

Ta miƙe ta bar ɗakin tana masifa.

Yusuf be bar gidan ba ranar se bayan sallar isha'i.
Koda yaje gida ya tarar Umman sa ba taci Abincin dare ba shi take jira, seda sukaci Abinci suka yi hira sannan ya koma É—akin sa.
Ya É—akko laptop É—in sa ya shigar da duk abunda ya faru da date da komai, dukkanin hirar da suka yi da Amla seda ya rubuta sannan ya kwanta.

Tun daga ranar Yusuf yake taka tsantsan gurin bin dokokin Widad, Sannan yana ta ƙara lura da yanayin mutanen gidan da ɗabi'ar kowa daga cikin su.

Widad ta aika Ramla ta kira mata Yusuf.
Ramlah tana zuwa inda suke zama ta kalle shi a wulaƙance tace
"kai wa kake kazo inji waccan yarinyar"

Yauma Yusuf ya shirya tsaf ze kai Widad Store za tayi siyayya bayan fitar su, Hajiya Halima ta aika aka kira mata Isa mai gadi, yaje ya same ta a ya durƙusa ya gaishe ta, ta amsa masa a wulaƙance sannan tace

"kaine ka kawo wa Widad direba ko?"

"Eh nine Ranki ya daÉ—e"

"Good, ina son sanin daga ina yake?"

Isa ya risina sosai sannan yace "Wallahi ranki ya daÉ—e ban san daga inda yake zuwa ba, nima wani abokina ne Sani ya kawomin shi yace É—an uwan sane amma ban daga ina yake ba"

"ka buÉ—e kunnen ka da kyau ka saurareni"

Isa yace "to Hajiya"

"Ina so duk yadda za'ayi in san daga ina yake? Daga ina yake zuwa gidan nan, sannan ina so ka ƙara samun ido akan sa sosai ina tunanin akwai wani ɓoyayyen abu a tare da shi"

"An gama ranki ya daÉ—e insha Allah zanyi yadda kike so"

"sannan wannan maganar ina so ta tsaya daga ni se kaine, bana son wani ya san munyi ta"

"babu me ji ranki ya daÉ—e"

"tashi ka tafi" Isa ya tashi fita.

Yusuf kam wani katafaren shago ya kai Widad, ta siyi kayan da take buƙata, hatta ruwan roba da zata sha seda ta siya abun ta.
Banda kayan ciye2 da sauran kayan ƙyale2

Seda sukaje gurin biyan kuÉ—i ta kalli Yusuf tace "jeka mota ka É—akko jaka ta"

Ba musu yaje ya ɗakko 'yar ƙaramar jakar ta ya kawo mata"

"buÉ—e ka É—akko ATM card É—ina"

Ya ɗakko ya riƙe aka lissafa kuɗi, kuɗi ne masu yawan gaske, ko a jikin ta tace
"basu ATM ɗin" ya miƙa musu suka saka a POS suka miƙo masa yasa ka password ya sa hannu ya karɓa ya miƙo mata domin ta saka lambobin da zasu bada damar cirar kuɗin, a hankali tai ƙasa da muryar ta tace

"7724" Yusuf ya gane me take nufi haka ya danna lambobin ya miƙa musu.
Suka ciri kuÉ—in su yana mamakin me yasa ta gaya masa password É—in cirar kuÉ—in ta.

Sun fito harabar Store ɗin zasu tafi suka wuce ta gefen wani mutum dake ƙoƙarin rufe motar sa yabi Widad da kallo tare da faɗin subhanallah.

Da sauri yabi bayan su Widad, Yusuf yayi gaba yana zuba kaya a mota mutumin ya sha gaban Widad yace

"Ahh excuse me Madam you look so hot"

Zare glashin fuskarta tayi tai masa kallon sama da ƙasa ta mayar da glass ɗin ta, tai gaba abunta.

Sake binta mutumin yayi ya sha gaban ta zeyi magana Widad tace "wai me kake nema ne?"

Yusuf kam ganin ta tsaya ya sashi komawa inda take tsayen dan ganin meke faruwa.

Mutumin yace "Wow ashe bahaushiya ce? Gaskiya beb bazan ɓoye miki ba kin tafi da imanina, kin min ina sonki, ki bani contact ɗinki mana se muyi magana, you look sexy" yai maganar yana wani kashe ido irin na 'yan bariki tare da miƙowa Widad wayar sa

Karɓar rantsatsiyar wayar tayi kaman gaske, ta sake ta a ƙasa ta fashe sannan tace "waya gaya maka samun lamabr mace kamar ni a gurin ƙasƙantattun mutane marasa amfani irinka abu ne me sauƙi, dalla matsa a gabana ko in tsinka maka mari sakarai kawai"

Waro ido mutumin yayi "ni zaki tsinkawa mari? Kin san waye ni kuwa? In baki wayata ki fasa min"

"Waye kai banda banza wofi, matsiyaci mara amfani? Kauce a gaban kafin inyi maganin ka"

Kan Widad mutumin yayo yana kumfar baki "Wallahi sena nuna miki koni waye a garin nan, 'yar uban waye ke da zaki min haka? Sena ci zarafin ki na wulaƙanta ki"

Tuni Attention É—in mutane ya fara yowa kansu kaman ze daki Widad, Yusuf ya shiga tsakanin Widad da mutumin ya kalli mutumin yace

"kana ta mana kumfar bakin ba' a san waye kai ba, ita kasan wacece? Ina ruwan ka da ita da zaka biyo ta kafaɗi maganar banza akan ta, ka kiyaye harshen ka kafin a nuna maka ƙarfin ikon data ke dashi"

"Kaikuma waye kai waye ya sakoka a cikin wannan maganar?" mutumin yasa hannu a aljihu ya miƙowa Yusuf id card ɗinsa, kafin Yusuf ya karɓa Widad tasa hannu ta karɓe ta duba id card ɗin nasa sannan tace

"Ashema matsiyaci ne taƙamarka kaki ko?  Zan iya sawa a keta kakin naka a gaban mutane a wulaƙanta ka, a tozarta min kai, sannan in ɗaure ka, kuɗi sunfi wannan kakin banzar da kake tin ƙaho dashi, Widad Nasir Daula inada Arzikin da zan wulaƙanta ka ka ƙare a gidan yari sakarai kawai "
tayi jifa da ID card É—in nasa ta tofa miyau akai

Ai Sunan ta data faÉ—a yasa mutumin nan wani mummunan zare ido tare da sauke numfashi yana kuma maimaita sunan nata.

Widad ta wuce mota Yusuf ya bita suka tafi, suna tafe tana ƙwafa tareda yin tsaki jefi2 kallon ta kawai Yusuf yake.

Suka isa gida ta buÉ—e murfin motar ta fice abunta, Yusuf ya É—ebo kayan ya bita dasu, matar gidan tana falo tana kallo, Yusuf ya shigo yabi bayan Widad har É—akinta ya ajiye mata kayan, ze juya ya É—ebo sauran tace "É—an tsaya" Yusuf yaja ya tsaya tazo ta duba kayan, ta É—akko wata Jaka da turaruka a ciki ta ajewa Yusuf, cike da iko da kashedi tace

"daga yau karka ƙara saka wannan banzan turaren da kake sawa in zaka zo inda nake, ga wannan turarukan kar in kuma jin kasa wannan turaren dan yana samin tashin zuciya ina fatan ka gane?" jinjina mata kai yayi alamar Eh.

Ya É—au ledar turaruka ya fita ya kwaso mata sauran kayan ya kawo mata, yana zuwa ya tarar ta shiga wanka, dan haka ya haÉ—a da ledar turarukan da ta bashi, ya ajiye mata akan gadonta yai ficewarsa.

Bayan Yusuf yayi sallar Azahar ya nemi guri ya zauna a inda suka saba zama da sauran ma'aikatan gidan, Isa mai gadi yace
"Yusuf manyan ƙasa, gaskiya ka ciri tuta a gidan nan, ina jinjina maka"

Yusuf yace "Mena yi na cancanci jinjina haka"?

"Ahh irin yadda kake jure cin mutuncin wannan yarinyar mana, naga da alama kaman kai bata yi maka wulaƙsncin, amma dukda haka kana haƙuri wallahi yarinya se kace sheɗaniya, zuciyar ta babu Imani se miyagun Aƙidun turawa to aibtama ci uwar turawa wannan"

Yusuf yace "kaga dakata Isa, kana gidan mahaifinta kana cin Arzikin su sannan kuma ka dinga zagin ta? Aiba'a haka a rayuwa, ni duk wannan abubuwan da kuke faɗa akan ta ni bana  gani, danni ba ta yi min ba"

Isa yace "ni na rasa me yasa kullum kake ƙoƙarin kare ta, da anyi magana ka hau kare ta, ina tausayawa ranar da zata maka mugun halin nata, naga yadda zaka yi ai"

"kaga Isa abar wannan maganar dan Allah"

Isa yace "shikenan tunda haka kace, nikam nace ina Sani kuwa? kwana biyu baya zuwa gidan nan ko a waya bana samun sa, nasan kai kuna haÉ—uwa tunda unguwar ku É—aya"

Yusuf yace "waye ya gaya maka unguwar mu É—aya?"

"Ai gani nayi É—an uwanka ne shiya kawo ka gidan nan, dan haka nayi zaton unguwar ku É—aya"

Yusuf ya murmusa yace "A'a ba unguwar mu É—aya ba"

"to kai a wace unguwa kake? Ko ince inane ƙauyen ku? Dukda baka yi kama da 'yan karkara ba, ni mamaki ma nake yadda matashi kamar kai yake aikin direba"
Chapter 12 · 0% Book details