← Book details Akidata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 82

Sashe 8

Akidata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wallahi sena masa wulaƙancin da babu wata halitta data taɓa yi masa, sena sauke dukkan baƙin cikin da nake ciki akansa, waye ubansa? Yana ƙasƙantacce zeyi watsi da dokokin da shi yasa hannu da kansa, Matsiyatan banza marasa Alƙawari, shiyasa wani talakan har ya mutu baze Arziki ba saboda rashin sanin mahimmancin Alƙawari da Amana, ya shirya karɓar hukuncin da ba'a taɓa masa makamancin sa ba"

(Nikam nace masu kuɗi ne kawai suka san Alƙawari da Amana? Ko kuwa Alƙawari da Amana ce tasa suka yi Arziki? Shikenan idan mutum yana aiki a ƙarƙashin wani me kuɗi se ya zama kaman Bawa? Shi besan jin daɗi ba se Bauta? Bashi da wani 'yanci na walwala da jin daɗi kenan? Tabbas da ba talaka ƙaryar me kuɗi yaji daɗin Rayuwar sa komai Arziƙin sa kuwa, Naga kowane ɗan Adam dai ajizine babu wanda baya kuskure, ke Widad ba kya kuskure ne ko kuwa? A ce mutum ya zabi Rayuwa shi kaɗai ƙwal ba mutane? Kowa be iya komai ba ciki hada mahaifinki, Gaskiya kin zafafa Aƙidojin ki, wata sabuwa kuma Widad tace "Love doesn't exist, is just an imagination talk less of getting true love" masu karatu wannan kaɗanne daga Aƙidojin Widad

TIRƘASHI!!!

Yaseen Akwai cakwakiya, Hassada, Munafunci, tsantsar Soyayya, Fuska biyu, kutsen ƙaddara me sauya rayuwar bawa ko be shirya mata ba, da sarƙaƙiyar gaske a cikin wannan littafin kar ku bari a baku labari dan ya haɗu.

Insha Allah ze cigaba da zuwar muku 1 ga watan September

Domin sharhi, gyara, ƙorafi ko makamancin haka ku tuntuɓeni akan
Wannan lambar ta what's app kawai
07063065680

Masu bina private akan in tura musu ABDUL JALAL dan Allah kumin afuwa, Abubuwa sunmin Yawa na kammala part two a document na sake shima, idan baku samu ba ku duba manhajar watpad a account É—ina
Ayshercool7724 insha Allah zaku samu dama sauran litattaafai na.

Masoya a cigaba da haƙuri dani, sakamakon harkar makaranta da wasu abubuwan da suka sani gaba Insha Allah wannan littafi ze fara zuwar muku 1 ga watan September, a what's App, da  telegram groups ɗina, da kuma Facebook a shafin mu na perfect writers Association, ko kuma YouTube channel dinmu

Ina godiya da Adduoin ku.

_*AƘIDA TA*_

*PERFECT WRITERS' ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *

And now *AƘIDA TA *

I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum

Special thanks to all members of my Association
Perfect writers Association may Allah subhanahu wata'ala bless our pens and grant us wisdom to write what will bring positive changes to our Community.

I won't forget you my fans 😍😍😍 you are always in my heart, my love to you is endless, especially those that shows me love support and follow me with prayers since my first Novel to date, i can't mentioned you all but am proud of you all 😍

HAUSAWA SUKACE KYAN ALƘAWARI CIKAWA, KAMAR YADDA YAKE KOYAR WAR ADDININ MU CIKA ALƘAWARI ABU NE ME MATUƘAR MAHIMMANCI, NAZO DOMIN CIKA MUKU ALƘAWARI, A BAYA NASAKA RAN KAMMALAWA DA MAKARANTA A AUGUST, KATSAM AKA ƊAGA JARRABAWA AKA MAIDA ITA 20 GA WATAN SATUMBA, AMMA TUNDA NI NAYI MUKU ALƘAWARIN CIGABA DA KAWO MUKU WANNAN LITTAFI A WANNAN WATA, NA SHIRYA TSAF DAN CIKA ALƘAWARIN KU 'YAN AMANA, WATTANI HUƊU KUNA SAURARE NA, INSHA ALLAH BAZAN BAKU KUNYA BA, KU SHIRYA DOMIN SALON NA DABAN NE, AKWAI TUFKA DA WARWARARA ME MATUƘAR SARƘAƘIYA A WANNAN LITTAFI DA KUKA DAƊE KUNA JIRA.
KARA ÆŠAYA ZAKUYI MIN, SHINE NUNAMIN JIN DAÆŠIN KU TA HANYAR YIMIN COMMENT TARE DA SHARE, LITTAFIN NAN KYAUTA NE DOMIN JIN DAÆŠIN KU MASOYA NA, AMMA A DALILIN RASHIN COMMENT ÆŠINKU KOMAI NA IYA CANZAWA, GA MASU MANHAJAR WATPAD KU GARZAYA KU NEMENI
@AYSHERCOOL7724
KU NEMI LITTAFIN A FACEBOOK A
GROUP ÆŠIN PERFECT WRITERS ASSOCIATION
ƘOFA TA A BUƊE TAKE DOMIN GYARA SHARHI KOKUMA SHAWARA
AYSHERCOOL
07063065680

YADDA NA FARA LAFIYA ALLAH YASA IN KAMMALA LAFIYA

Haƙƙin Mallaka ⚠ : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode

BISMILLAHIRAHMANIRRAHIM

ELEGANT ONLINE WRITER'S

                         *PART1*
                      
                                  _Page 4_

Babu alamar sassauci fuskar Widad, yanayin fuskarta ze tabattar maka da gaske har cikin zuciyar ta zata aikata abunda ta faÉ—a, ta juya ta koma cikin gidan da hanzari.

Jinjina kai Isa ya dinga yi yana kuma sake shafa kumatunsa yadda yske masa raɗaɗi, tare da tausayawa wulaƙancin da Yusuf ze fuskanta.

Ramla kam cikin sassarfa ta nufi É—akin mahaifiyar ta, tun daga waje take kiran "Mummy"

Hajiya Halima tace "Ramla wannan wane irin kira ne haka? Ke kam bakya girma"

Ramla ta ƙarasa kusa da mahaifiyar ta ta zauna tace "wai nikam nace me akayiwa 'yar gwal ne? Naga kaman ciwon nata na ƙoƙarin tashi fa? Kuma ga dukkanin alamu yau ta kwaɓe mata itada uban tane"

ÆŠan tsaki Mummy tayi tace
"sakani yake cikin sha' aninsa shida 'yar sa ne? Ai sedai inga suna lamauran su ta yaya zan san meya sameta?"

Ramla ta sake gyara zama "hmm kinsan dai halin ciwon ta, a corridor ɗin ƙasa na haɗu da ita, tana ta surutai, wai Daddy Aure zeyi mata, se safa da marwa take tana zufa"

Zaro ido Mummy tayi tace "Aure kuma? Wane irin Aure ana zaman lafiya? Waye ze Auri mahaukaciya mara tarbiyya kamar wannan Yarinyar? Shi mijin da haukan zeji ko kuma da rashin tarbiyya?"

Ramla tace "waya sani musu?, sedai ki jiyo mana kanun Labaran muma ki fesa mana, Amma ina tunanin wanda ze kwashi wannan Mahaukaciyar"

"To nidai a iya sanina bata yadda da mutane ma, to ta yaya ta samo wanda ze Aure ta?"

Ramlah tace "Ai samun miji ba wuya ze mata ba, ko dan wannan haÉ—aÉ—iyar Daular, dan haka ko'a turu take dan hauka, za'a iya samun me sonta yace ze aureta a haka"

Mummy tace "hakane, Amma ya zama dole musan waye ze Aureta, dole in gano"
Haka Suka ci gaba da tattauna wa akan lamarin.

Yusuf kam kashe wayoyin sa yayi ya shiga sabgoginsa, duk yadda Isa yaso kiran Yusuf a waya ya gaya masa Saƙon Widad abu ya gagara wayar sa taƙi shiga, ƙarshe se haƙura Isa yayi.

Widad kam baranda ta samu ta kwanta, akan tiles ga sanyin tiles na ratsa ta amma sam bata ji, tayi ruf da ciki tana jin yadda zuciyar ta take mata raɗaɗi, kamar ta tsaga ƙirjinta ta fito, Babban Abunda ya ƙara bata mamaki shine yadda mahaifin nata be biyo sahunta ba balle ya rarrashe ta kaman yadda yake yi abaya, shima kamar yayi fushi da ita karon farko ya barta cikin damuwa, lallai wannan karon mahaifin nata dagaske yake.

Washegari Yusuf ba shida Niyyar zuwa gidan su Widad Sam, da ya tashi da safe ma shirin tafiya Office yayi abun sa, ya shirya ya fito Umman sa ta kalle shi tace
"Ya haka kuma? Yau ina zakane?"

Murmushi yayi yace "Yau Office zanje Umma"

"Kacemin kuma, an turaka aiki gidan Alhaji Nasir Daula, yanzu kuma kace min zaka gurin aiki ya haka?"

Yusuf yace "hakane Umma, an turani aiki gidan Alhaji Nasir Daula, Amma dole zan dinga leƙawa Office, ina documenting findings ɗina sannan indinga presenting sakamakon bincike na"

"shikenan a sauka lafiya, Allah ya tsare ya kiyaye hanya"

"Allah yasa Umma, dan Allah yau ki mana dambu kinji Umma na"

Umma tace "banyi Alƙawari ba, ka bari ranar da kake nan se kayi"

Noƙe kafaɗa Yusuf yayi yace "dan Allah Umma, ni gaskiya idan ba dambu kika yi yau ba bana cin Abincin"

"kar kaci É—in, ai cikin ka ba nawa ba"

Haka yaita zolayar umman nasa sannan yai mata sallama ya tafi.

Da yaje Office ɗin ma Ayyuka sun ɗanyi masa Yawa, ya duƙufa sosai yana ta shigar da ayyukan sa cikin system.

Sallamar da'akayi a office É—in ne ya sashi É—agowa yaga me Sallamar, kamar yadda ya zata sakine ce ta shigo.

Kallo É—aya yayi mata, ya Amsa sallamar ya maida kansa ya cigaba da danna system É—in shi.
Yauma cikin baƙaƙen suit Sakina take, amma skirt ga ƙaramin hijjabi da ta saka, gaba ɗaya kayan sun bayyanar da surar jikin ta.
Kujera ta ja ta zauna tana facing É—in sa.

"Yusuf sannu da Aiki"
Ba tare da ya kalle ta ba yace "lafiya kalau Alhamdilillah"

"kwana biyu baka shigowa Aiki, lafiya dai ko?"

ÆŠan É—agowa yayi yace "Eh an bani wani Assignment ne"

Cikin iyayi da lumshe ido tace "to Allah yaba da sa'a"

Ya amsa da "Ameen"

"Can i offer you something to eat?"

Ba tare da yace komai ba ya girgiza mata kai, Alamar A'a.

Miƙewa tayi ta zagayo inda yake tace
"ko Akwai abunda zan taya ka ne?"

ÆŠagowa yayi ya kalleta a hankali yace "dan Allah ki fitar min daga Office inada Ayyuka da yawa kina takuramin fa"

A Shagwaɓe tace "Yusuf meyasa kake son yi mun wulaƙanci ne?"

"ba wulaƙanci bane, gaskiya ce, Aikine ya kawo ni gurin nan ki barni inyi aikina mana"

"Amma Yusuf meyasa zaka maida Soyayya ƙiyayya, tunda na nuna ina sonka kake wulaƙantani haba Yusuf"

"Sakina niba wulaƙantaki nake ba, yanzu lokacin aiki nane, dan Allah ki tashi ki tafi, bearable in shiga lokacin aiki ba"

"Yusuf" ta kira sunansa, É—aga mata Hannu yayi ya dakatar da ita tare da faÉ—in

"Sakina dan Allah ki barmin office, kalli shigar jikin ki, kuma kinzo kin sani gaba, dan Allah ki tafi"

Suna cikin Jayayyar ne Abbas ya shigo, Sakina ta miƙe ta bar office ɗin a fusace.

Abbas ya kalli Yusuf yace

"Anya Sakina bata fara kama zuciyar ka ba Yusuf?"

ÆŠan girgiza kai Yusuf yayi yace
Chapter 8 · 0% Book details