← Book details Akidata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 82

Sashe 25

Akidata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"haka kace ko, to shikenan zakaga abunda bijirewa buƙata ta ze haifar maka, ba dai shishshigewa wannan mahaukaciyar ka zaɓa ba, a haka zata ƙare a hauka, kuma death contract data gaya maka zaka ganshi dan kusancinka da ita tamkar kusancinka da mutuwar Kane, Akwai mutanen dake farautar mutane irin ka, wanda suka raɓeta, zasu cigaba da farautarka da bibiyar ka, zasu nemi wani abu a gurin ka, muddin ka gaza yi musu zaka ga abunda ze biyo ba, ka rubuta ka ajiye zaka ce na gaya maka, sakarai mara rabo kawai "

"Ke rabon ne yasa kike zaune a gidan mutane kina harin yin zamba cikin Aminci ai, dukda irin gata da sutura da akai muku"

Wani murmushi tayi me ciwo, badan Widad tana Wulaƙanta su a gaban Yusuf ba ya isa ya kalli idon ta ya gaya mata wannan maganganun, ta ɗaga ido ta kalle shi tace  "ka faɗi abunda kake so a yanzu, amma ka saurari ƙalubalen dake fuskantar ka" ta shige ta kunna motarta ta bar gurin a guje.

SHARE PLEASE 🙏

Please pray for my Dad, he is sick

Ayshercool
07063065680

.                   

                      _*AƘIDA TA*_

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *

I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum

Special thanks to all members of my Association
Perfect writers Association may Allah subhanahu wata'ala bless our pens and grant us wisdom to write what will bring positive changes to our Community.

                

                           PART1
                                  Page 11

Bin motar Yusuf yayi da kallo harta ƙure, sannan a sannu yaja ƙafar sa ya ci gaba da tafiya abubuwa daban daban na yawo a kwanyarsa.

Maimakon ya tafi gida seya tsaya yayi sallar azahar ya wuce gurin aiki, office ɗin Abbas ya tafi yaje ya tarar da shi yana tsaka da wani aiki, Abbas na ganin Yusuf  yai murmushi suka gaisa sannan yace 
"Yane mutmina? Akwai wani latest update ne?"

Yusuf ya ɗan ɓata rai yace "na baka abu kayi assisting ɗina kaƙi, seni nayi abuna bakomai nagode"

"wane abu kace inyi assisting ɗin naka naƙi?"  Abbas ya tambaya

"Akan mahaifin yarinyar nan Nurat mana, Nace ka tayani bincike akansa amma ƙarshe ni nayi abina"

Dafe kai Abbas yayi yace  "Sorry my man, wallahi aiki yayi min yawa na manta shaf"

"Shikenan amma ina tafe da Labari ne"

Abbas ya tattara hankalin sa yace  "ina jinka, dama kamar kasan jiya Oga Suleiman yayi min maganarka"

Yusuf yace "Abbas ina kyautata zaton akwai sa hannun matar Mahaifin Widad a farmakin da'ake kai musu"

Abbas ya ture System ɗin gabanshi ya sake tattara hankalinsa yace  "ta yaya kenan? Meka gano?"

Nan Yusuf ya gaya masa abubuwan da Su Hajiya Halima keyi, da kuma Yadda suka yi da Ramla"

Jinjina kai Abbas ya shiga yi yace  "Lallai biri yayi kama da mutum, amma kaga Oga yana Abuja akan wani case, Amma idan hakane meye alaƙar iyalan Alhaji Nasir da Mahaifin Nurat?"

Yusuf yace  "Abunda zan ɗora da bincike na akai kenan"

Waya ce ta fara ringing, Abbas da Yusuf suka shiga waige waigen wayar da take ringing ɗin, Abbas yace  "kamar daga jikin ka ringing ɗin ke tashi fa"
Se yanzu Yusuf ya tuna an bashi sabuwar waya, hannu yasa ya É—akko wayar ya É—aga, suka gama magana Umma ce ta kira shi.
ssebayan Yusuf ya gama Abbas yace 

"jar uba mutumina wannan latest phone ɗinfa? Miƙomin in ganta, yaushe ka siyi waya haka, kaida manyan wayoyi basu dame ka ba?"

Yusuf ya miƙa masa wayar yace  "Widad ce ta aikeni na siyo mata wayoyi masu tsada guda biyu, ina kai mata ta bani wannan"

Abbas ya dinga jinjina kai yana jujjuya wayar yace  "Lallai ka faso gari, amma kamata yayi ka siyar da ita kai sabgar gabanka da kuɗin"

"Idan kuma ta tambayeni wayar nace na siyar taji daɗin Yimin wulaƙanci ko?"

Abbas yace  "A'a ba haka nake nufi ba, Ashe dai har yanzu halin nata na nan, ai kwanan nan Insha Allah zan ɓullo gurin naku"

"to nidai in kazo ka kula, karka sake ka gaya wa wani unguwar da nake, haka kurun sun matsa da son sanin daga inda nake zuwa, dan nima kaina ban yadda da mutanen gidan ba"

Abbas ya kwashe da dariya yace  "ashe dai ta koya maka halin nata"

Alert ne ya shigo sabuwar wayar Yusuf  dake hannun Abbas, zare ido Abbas yayi yace "Yusuf an turo maka kuɗi"

Yusuf yace "waye ze turomin kuÉ—i tsakiyar wata haka?"

"wallahi dagaske nake, dubu É—ari shida"

Miƙewa tsaye Yusuf yayi yace "ni a wa? Waze turomin kuɗi haka?tabbas anyi kuskuren lambar account"

Abbas yace "dakata, kuma ba uwaÉ—akinka bace?"

Shiru Yusuf yayi yace  "to aini bata da Account number ɗina, sedai idan naje gobe in Allah ya kaimu in tambaye ta, Amma inma itace gaskiya kuskurene, Kaga Abbas se anjima akwai inda nake son zuwa"

Gaba É—aya Yusuf ya ruÉ—e, mamaki ya cika zuciyarsa yafi tunanin ko Ramla ce, dan tana son ta siye shi yayi mata aikin data keso? Amma daga rabuwarsu ta ina zata samu Account number É—insa?.

***********************

A mugun fusace Ramla ta koma gida, tana zuwa bata tsaya ko ina bs se É—akin mahaifiyar su, taje ta tarar da ita suna magana da Amal.

"Mummy akwai matsala fa"

"matsalar me?"

"Mummy this guy is very rude, we have to exact power over him, how dare will he look into my eyes and tells me that he won't do what i ask him to do?" ta ƙarasa maganar tana ta gauraya Numfashi.

"Kinga nutsu kiyi min bayani ya kukayi dashi?"

Ramla ta warware mata komai, Amal tace  "da anyi shawara dani da baza'a tun kare shi ba saboda nasan ba zeyi ba, Mutum ne me kafiya da dagewa akan gaskiyar sa"

Cikin fushi Ramla tace "A beg shut up Malama, wayafi kafiya talakan banza mara amfani, ni ya tsaya ya kalli cikin idanuna ya cimin mutunci, shikenan dani yake zancen wallahi se nasa zaman garin nan ya gagare shi banza da kansa kamar lemo"

Amal tace  "Wai kansa kamar lemo, kekuma naki fa"?

"dan Allah kuyi min shiru karku yi min faɗa anan, mafita ya kamata munema ba surutu ba, sannan Amal wallahi idan baki kiyayeni akan yaron nan ba sena saɓa miki fiye da tunanin ki wallahi, bazan taɓa aurawa maƙasaƙancin mutum ɗana ba, dan haka ki shiga hankalin ki, zaƙewar da kike masa tayi yawa "

Zumɓura baki Amal tayi ta bar ɗakin.

"Mummy inaga mubi Amal a hankali, tabbas son gayen nan take, Amma cikin hikima zata iya samo mana abunda muke so, ki dena yawan hantarar ta a kansa, karta zo ta bijire mana daga baya fa"

"Bazan bari alaƙar tasu tayi nisa ba, saboda yaron kalar mayaudaran mazane, yana da mu'amala me kyau, daɗin Soyayya ze iya sa Amal ta tona komai, kin san bata da hankali, Amma zan sanar dake mataki na gaba da zan ɗauka.

**************************

Safa da marwa yake yana kaiwa yana komowa a cikin wani matsakaicin Office, yana ta sake nanata maganganun da Oga ya gaya masa game da poisoning É—in Bala a prison, wani mutum ne yayi Sallama a office É—in yace
"Yallaɓai Hisham lafiya kake nemana?"
Hisham yayi ajiyar zuciya yace  "Oga Bukar ne ya bada wani aiki, kuma muddin aka samu kuskure bamuyi ba ze halaka mu"

"Kamar Yaya? Wai shi meyasa be maida kisan kai komai ba saboda buƙatunsa? Wallahi nayi dana sanin sabga dashi"

"Kwantar da hankalin ka Bashir, mu lallaɓa muyi masa wannan aikin bisa Yarjejeniyar shine na ƙarshe, idan ya cigaba da takuramu, semu ma mu ɗana masa tarko"

Tsaki Bashir yayi yace  "ina jinka, me kuma zamuyi masa?"

"yace so yake ayi poisoning ɗin Bala, yadda ze fara rashin lafiya, da an kai shi Asibiti kuma zesa a ƙarasa shi, saboda Balan yayi barazanar tona Musu Asiri, sun barshi a gidan yari tsawon shekaru takwas, sunƙi fitar da shi"

"wallahi Hashim mutanen nan basu da Imani, tsaf muma zasu iyayi mana abunda suka yi wa Bala, amma salin alin muyi abunda suke so, muna dafe kan madarar kawai zan ajiye aikin gidan nan in fece"

Hisham yace  "shikenan but you have to focus"

Bashir ya jinjina kai ya fice daga office É—in.

*********************************
Dogayen kaya ne a jikin Yusuf, yayi kyau sosai ya shiga falon da sallama, ba'a amsa ba kasancewar ba kowa a ciki, ɓangaren Widad ya nufa kansa tsaye, yaje ƙofara falonta ya tsaya, tare da yin knocking.

Ƙasa ƙasa ya jiyo muryar ta tace  "Come in" da Sallama ya shiga falon, tana zaune tana shan tea, ya kalleta yace  "barka da Safiya ranki ya daɗe" jinjina masa kai tayi ba tare da ta amsa ba, ta cigaba da abunda take ba tare da tace uffan ba.

Haka ya shuÉ—e tsayin wasu lokuta yana zaune yana jiranta, ga shan tea É—in take kamar tana shan magani.

Yusuf ya gyara zama yace 
"Ranki ya daÉ—e jiya naga an turomin kuÉ—i a account É—ina masu yawan gaske, ban sani ba koke ce, shine nace bari in tambaye ki"

"Kana expecting É—in kuÉ—i daga gurin wani ne?" tai maganar tana ajiye cup É—in hannunta

"A'a, bana yi" ya bata amsa

"Anyway salary É—inka ne na 3 months da ban baka ba"

Zare ido Yusuf yayi yace 
"Amma sunyi yawa fa, ya zanyi da wannan maƙudan kuɗaɗen?"

"Zaka iya zubarwa, wannan kai ta shafa"

"A'a Madam, banyi aikin da zan karɓi wannan kuɗaɗen ba, sun yi yawa ban san....
Chapter 25 · 0% Book details