← Book details Akidata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 82

Sashe 41

Akidata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Alhamdilillah, ya ka baro mutan gidan?"

"Lafiya ƙalau Alhamdilillah, ina Yusuf kuwa?"
Isa ya taɓa baki yace "Yana nan yanzun nan ya shiga cikin gida, gimbiyar masu gida tana kiransa"
"Allah sarki, ina fatan yana aikin sa babu matsala?"
"Eh to yana yi, se shishshigi da zaƙewa, yaga ya samu gurin zama a gurin masu gidan, shine yake ta Wulaƙanta mu gamu gashi amma se yaga dama ze kula mu"

"Hmm ni kaina wannan baƙin halin nasa yana ƙular dani, dama haka yake se kunyi a hankali wasu lokutan bashi da kirki sam wallahi".

Yusuf seda ya É—an tsorata, ganin Widad ta rame daga jiya zuwa yau, idanunta a kumbure da alama kuka tayi sosai, gaba É—aya se yaji tausayin ta ya kama shi.

"Gurin Bulama zaka kaini yanzun nan"

Jinjina mata kai yayi, ta miƙa masa jakarta ya karɓa sannan suka fito.

Tunda suka fito Abbas ya ƙura musu ido, se kace mata da miji, tabbas Yusuf ya samu gindin zama yadda yakamata a gidan nan.

Yusuf na ganin Abbas tun daga nesa ya fara murmushi, suna isowa inda su Abbas suke kafin Yusuf yayi magana, Widad ta ƙurawa Abbas ido, shikansa Abbas seda yasha jinin jikin sa.

"Waye wannan?" Widad ta tambayi Isa megadi"

Cikin inda inda Isa yace "Amm... Am. Dama abokina ne, kuma shine wanda ya kawo Yusuf aiki a gidan nan, ina tunanin ma É—an uwansa ne"

"Kar in ƙara ganin sa a gidan nan, ko a harabar area nan na sake ganinsa zan ɗau matakin da ya dace"

Binta sukayi da kallo, inda sabo Yusuf ya saba da wannan halin nata, dan haja yayiwa Abbas Alama da zasu yi waya.

Abbas ya miƙe cikin mamaki ya bar gidan.

Yusuf dama beyi zaton zata gaya masa dalilin ta na korar Abbas ba, amma abun ya bashi mamaki, seya barshi a matsayin kawai duk cikin hakinta ne na rashin yarda da mutane.

Koda suka iso gidan Bulama, kafin su shiga megadi ya sanar dasu cewar Bulama da shi da iyalansa basa nan sun fita.

Haka Yusuf ya juya akalar motar suka koma gida.

Abbas ba ƙaramin mamaki yayi ba, yaga dai farkon zuwansa gidan daya kawo Yusuf tare suka je, amma yau ta nuna bata sanshi ba wai kar ya ƙara, zuwa gidan.

Kai tsaye Abbas ya É—akko wayarsa ya kira layin Saleh.

"Hello Saleh kana ina ne?"

"ina gidan gona bakin aiki, meyafaru?"

"ina son ganinka ne"

"ka bari zanzo in same ka a gidanka, karka zo nan babu security"

"shikenan sekazo"

Yusuf Alla Alla yake ya kai Widad gida ya tafi gurin Abbas.

Seda suka je gida yay parking, Widad ta kalle shi tace "Karka bar gidan nan se bayan sallar isha'i"

"Saboda me?" ya tambaye ta

Bata bashi Amsa ba ta fice daga motar ta barshi a gurin, ba ƙaramin haushi yaji ba, yasan dai duk abu ba wani gurin ze kuma kaita ba, Amma tace baze tafi ba, da niyyarsa yayi tafiyar sa amma se ya fasa, haka ya cigaba da zama har se lokacin da tace ya tafi.

Saleh ne zaune shida Abbas a wani É—an madaidaicin falo, Saleh yace
"Neman me kake min ne haka?"

Abbas yace "dole in neme ka ai, Yusuf se alheri yake samu a wannan aikin da yake, ta sakarmasa kuÉ—i kawai take sakarmasa, seda nayi dana sanin rashin yin aikin nan da kaina"

Saleh yai murmushi yace "tabbas Widad akwai kyauta ta ban mamaki, Sedai kasan aikin da yake a rayuwar sa a hatsari take ko?"

"Nasani amma babban abunda ya ɗauremin kai shine yau naje gidan gurin sa, Amma tana ganina tace kar in ƙara zuwa ko area gidan"

"zata aikata saboda bata da yadda sam, dan haka bata son baƙuwar fuska, gani take kowa ma cutar da ita zeyi, yanzu ya ake ciki game da binciken da yake yi, naga alamar yaron yasan aikin sa, duk yadda kaso ka daki cikin sa ba ze gaya maka komai ba, na jarraba shi rannan da suka zo tare, Amma naga yana da wayo "

Abbas yace " Hmmm, aiki kam yasan kan aikin sa sosai, dan ina tabbatar maka da yana aikin yadda ya kamata yana tattara abubuwa masu mahimmanci sedai har yanzu ban san meye sakamakon binciken nasa ba"

Saleh ya numfasa yace "yanzu abunda nake so da kai shine, ka kawomin rahoton duk binciken da yayi, ka kawomin file ɗin zan miƙa shi ga wannan mutanen dan su sakarmin ɗan uwana dan ina zargin su suka yi poisoning ɗinsa yake kwance ba lafiya"

Abbas yace "yana na'aikaci ina ma'aikaci tayaya kake tunanin ze yadda ya bani kundin binciken sa?"

"wannan ya rage naka kuma Abbas, ni na gama magana kuma ka saka ido ka cigaba da bibiyar sa dan jin yanayin kusancinsa da ita"

"Shikenan zanyi iya abunda zan iya, Insha Allah zan kawo maka abunda ka buƙata.

Ba ƙaramin haushi Yusuf yaji ba da Widad ta hana shi tafiya da wuri, dan haka se bayan isha'i sannan ya tafi gida, bayan yaje gida yaci Abinci yana shirin kwanciya message ya shigo wayarsa

"HAR YANZU MUNA SANE DA KAI, KUMA ZAMU CIGABA DA BIBIYAR KA HAR SEKA BAMU ABUNDA MUKE SO A HANNUN WIDAD"

Tsaki Yusuf yayai ya ɗanyi shiru yana tunanin wai wani abubne wannan haka da'ake son karɓa a gurin Widad, da har ake masa barazana haka?
Ganin bashi da amsa yasa yai kwanciyarsa.

************************************
"Fahad kasan meyasa na kiraka muyi magana a daidai wannan lokacin?"

Fahad ya girgiza kai yace "a'a Daddy"

Bulama yace "Yawwa, na yanke wani hukunci ne kafin ka dawo, shine nake so ka baani aron hankalin ka da kunnuwan ka da kyau ka saurareni"

"To Daddy ina jinka"

"Kasan Widad ai ko? 'yar gidan Alhaji Nasir daula"?

"Eh Daddy nasani"

"Kasan alaƙar dake tsakanina da mahaifinta ko?"

"Nasani Daddy" Fahad ya bashi amsa

"Masha Allah, Kasancewar ka yaro me biyayya shiyasa na yanke wani hukunci wanda nasan ba zaka bijiremin ba Insha Allah"

"Ina jinka Daddy".

"Kamar yadda kasani, yarinyar nan ta gamu da larurar Ƙwaƙwalwa, ta ɗau wata AƘIDA da wata irin rayuwa ta nayi, ta zaɓi rayuwar kaɗaici wanda hakan ke barazana ga lafiyar ƙwaƙwalrwata, shine muka yabke hukuncin yi mata Aure nida mahaifinta, koda Allah zesa a dace a samo kan hankalin ta"

Fahad yace "to ai Daddy ni banga meye nawa a ciki ba"

"Fahad kai muka yanke shawarar zaka auri Widad"

A razane Fahad ya kalli Mahaifinsa yace "Kamar ya ni Daddy, kawai se in auri mahaukaciya kaifa kace bata da hankali ta yaya zan Aure ta?"

"ta yadda na gaya maka mana, aiba hauka take tuburan ba se lokaci lokaci yake tashi, dan haka umarni nake baka ba shawara ba, idan bamu haÉ—u an temaki yarinyar nan ba waze aure ta da wannan larurar?"

"Amma Daddy a rasa wanda za'a bawa seni? Ina da wadda nake so meyasa za'amin haka? Ta yaya za'a yanke min hukuncin yarinyar da zan aura ba tare da izinina ba"

Cikin tsawa Bulama yace "rufemin baki, na gaya maka wannan umarnina ne, kuma dole kabi gobe in Allah ya kaimu zakaje ku gaisa da ita, kuma wallahi naji wani abu daga gareka wanda be gamshe ni ba, kasan halina sakarai kawai"

A hasale Fahad ya tashi ya bar falon mahaifinsa, É—akin mahaifiyarsa ya tafi yana kumbura fuska.

"lafiya ka shigomin ɗaki ba ko sallama kana ta haɗe rai kamar tsohon raƙumi?"

"Mumsy kina gidan nan, kina raye za'ayi min Auren dole? Kamarni ta yaya za'a auramin mahaukaciya?"

Ajiyar zuciya tayi tace "Fahad this is out of my control, I did my best to destroy this matter but is beyond my control, ba yadda banyi da mahaifinka ba amma fafur yaƙi, ya zanyi sedai kayi haƙuri"

"Au Hakama zaki ce? Wallahi se yarinyar nan tayi dana sanin Aure na, sena mata wulaƙancin daba'a taɓa yi mata ba se naci mutuncin ta, zata gane kuskurenta"

"Kai Fahad ka shiga hankalin ka, 'yar gidan Daula ce fa, ita zaka ciwa mutuncin? Amma kasan me ci mata mutunci ke nufi ko?"

"ko' yar gidan bushashace ba Daula ba ba ruwana wallahi"

"shikenan kaje kayi abunda ka ga dama kaida ubanka ba me É—agamin hankali wallahi"

Fuuuu Fahad ya fice ya bar É—akin yana tsaki

Da safe Yusuf yanata shiri, dan yau gurin aiki yake son zuwa dole yana son ganin Yallaɓai Suleiman, Amma message ya shigo wayar sa.

"ka tabattar ƙarfe takwas tayi maka a gidanmu, zakamin aiki yau"

Yana ganin message É—in yasan daga Widad ne, haushi ne ya kama shi gaba É—aya bashi da lokacin kansa sena wannan fitsararriyar yarinyar.

Haka ya shirya a gaggauce ya tafi gidansu Widad, mutan gidan ko tashi daga bacci basu yi ba, tsabar takura irin ta Widad da son nuna isarra yasa take masa wannan ikon.

Wani ɗan ƙaramin lambu dake gidan Yusuf ya tafi yai zaman sa, yana kallon shuke shuke da tsuntsayen dake gurin.

Jin tsayuwar mutum yayi a bayan sa dan haka da sauri ya juyo.
Amal ce tsaye a bakin lambun tana ƙare masa kallo "barka da Safiya Yusuf"

"Yawwa barka" ya faɗa a taƙaice

"Yusuf wai ya naga kana wani baya baya dani? Dan Allah kayi haƙuri da abunda ya faru, wallahi ina matuƙar kishin ka ne"

"Amal dan Allah kiyi haƙuri, ni bana son abunda zesa ki jamin matsala, ki ƙyaleni dan Allah"

"Idan kaga na ƙyaleka to tabbas ɗayan mu ruhinsa ya rabu da gangar jikinsa, ni matsala duk girmanta duk ƙanƙantar ta bana gudun ta, indai akan biyan buƙata tane, kalleni Yusuf me na rasa? Wace tawaye Allah yayimin da ban kai ka kalleni ka karɓi soyayya ta ba, kana ganin irin mazan da suke sintiri a gidan nan da sunan suna sona, Amma na ajiye class ɗina na ajesu a gefe nace kai nake so, me zesa kace baka sona"

"Saboda bana Soyayya, bata gabana babu ita a tsarina, dan Allah ki ƙyaleni"

"ƙarya kake Yusuf kana Soyayya, koma baka yi zaka fara a kaina bazan taɓa ƙyaleka ba, zan cigaba da bibiyar ka sena hanaka jin daɗi muddin baka amince da soyayya ta ba "

"Masoyiyar gaskiya ba zata taɓa faɗar haka ba, ke ba abun yadda bace dan haka bazan taɓa yadda da wannan shirmen ba"
Chapter 41 · 0% Book details