← Book details Akidata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 82

Sashe 10

Akidata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yusuf ya kalli kayan dake jikin Widad, da kuma abunda Ramadan yace kawai ya girgiza kai

Ramadan yace "yeah yana nan"

Ƙoƙarin hawa bene Widad take yi, budurwar tace

"hey Baby who is this gentleman with you?"

Aiko tsaya ba tayi ba balle bada amsa, ta haye saman benen da sauri, Yusuf bashi da zaɓin daya fi yabi bayan ta.

Wata ƙatuwar ƙofa ta buɗe, ta kutsa kai Yusuf yabi bayan ta, shima wani haɗaɗɗen falo ne me girman gaske, sanyi Ac ke rasa ko ina na ɗakin.

Alhaji Bulama ne ke zaune akan É—aya daga cikin kujerun falon, yana shan tea tareda dannan system, Yusuf ne yayi sallama, Alhaji Bulama ya É—ago ya kalle su.

Murmushi yayi ya amsa sallamar Yusuf, yana ƙarewa Widad kallo, guri ta nema ta zauna tana fuskantar Bulama.

Bulama yace "Daughter wai shi wannan duk inda zaki se tare da shine? Ina direba ne kawai? Kodai Allah ya karɓi Addu'armu kin fara sakin jiki da mutane?"

HaÉ—e rai tayi tace "my policies remain constant, babu abunda ya canza, babu ruwan ka da dalilin da yasa duk inda zani yake bina"

Alhaji Bulama ya murmusa yace "shikenan Allah ya baki haƙuri"

Ya kalli Yusuf yace "Sannu ɗan Samari, daughter ɗin tamu seka na haƙuri, muma lallaɓata muke"

Da ido ta kalli Yusuf, dan haka Yusuf bece komai ba se É—an murmusawa da yayi.

Alhaji Bulama ya maida kallon sa ga Widad yace "ina jinki?"

"Meyasa ka turawa Daddy na ra'ayin ayimin Aure?"

ÆŠan girgiza kai Bulama yayi tareda murmushi "yaro yaro ne, Widad Aure shine ya dace dake, domin shine ze gusar miki da wannan larurar ki zama kaman sauran mutane"

"na taɓa ce maka ina son Aure ne? Ko kuma akwai shi a cikin tsarin Rayuwa ta?"

"look daughter, Aure shi ze gusar miki da dukkanin wannan halin da kike ciki, babu yadda za'ayi lafiyayyen mutum ya rayu ba tare da mutane a cikin Rayuwar sa ba, shi yasa muka yanke shawarar Aurar dake"

"ka dai yanke shawara sannan ka cusawa Daddy na ra'ayin hakan, ace har Daddy yamin laifi sannan ya fita harka ta dan naƙi yadda da batun Auren nan, duk kai ka jamin, sannan nida ban yadda da soyayya ba balle inyi ta har in samu mijin Aure, wazaku aura min?"

Gyara Zama Bulama yayi yace
"Fuhad mana first born É—ina, kun dace sosai, ze soki tsakani da Allah ya zauna dake, tunda ke 'yar uwassa ce"

Shiru tayi ta kalli Bulama sannan tace "what the fucking shit are you talking about? meye wani ze soni tsakani da Allah? Let me tell you something, i don't believe in Love talk less of true love, Love is just an imagination full of bull shits and stupidity, so ke sa ayi aure ko? To ban yadda yayi existing ba, dan haka ka gaggauta warware wannan maganar, dan ko aure zanyi bazan auri namiji bahaushe ba, you people that are not romantic at all, babu abunda kuka iya banda iko da ɗaukar matayen ku tamkar bayinku, baku damu da halin da zasu shiga ba idan har taku buƙatar zata biya, baku iya komai ba se masifa da hantara, don't you see how women are complaining about you? How Hausa women's are suffering because of your poor marital life? Women's are always complaining about marriage issues, this is type of life you want me to do? Do you think I can live with someone that will be shouting at me?"

Shiru Bulama yayi yana kallon ta, Ta gyara zama ta kalli cikin idon Bulama tace
" idan baso kuke ku ƙara tunzura haukan nawa ba kaman yadda kuke iƙrari ba, ya kamata ku ƙyaleni da maganar nan"

Numfasawa Bulama yayi yace "Amma kin san mahaifinki ma bahaushe ne, kike wannan maganganun akan mazan hausawa"

"da nace ban dashi a ciki ne? Shima badan yayi rayuwar Turai ba he will have the same negative habits on his wife, it seems it is in your genes, Alhaji Bulama daga yarin tata sanina da kai mata nawa ka aura bakwa tare yanzu? Go back to your senses Sir, Am not ready to ruin mad, i don't have interest of getting marriage, i don't know maybe later, but I can't married a man from hausa people, they don't value their wives "

Ba Bulama ba, Yusuf kansa yaji haushin cin mutuncin da Widad tayi wa ƙabilar Hausawa, duk lalacewar Al'umma akwai mutanen kirki ai, Amma ba shida ta cewa, tunda shi ɗan karere ne.

Ta miƙe tsaye tayi gaba abun ta, Yusuf ya rufa mata Baya, yauma har suka je gida ba wanda ya kula wani, sedai da suka koma gidan, a mota ta bar jakarta da wayarta, dole Yusuf ya ɗauka ya bita da su ba dan yana so ba, dan sam baya son shiga cikin gidan, ba ƙaramin tsarguwa yake da irin kallon da mutan gidan ke masa yake ba.

Yanzu kam ba 'a hankali take tafiya ba cikin gaggawa take tafiya, kaman tana son tayi wani abune, ta falon da zata bi ta wuce ta tarar da Mahaifinta a zaune da shi da matarsa, ko kallon su batayi ba tasa kai zata wuce.

"Widad" Mahaifinta ya kira sunan ta ba tare da juyo ba ta tsaya cak, be damu ba ya É—ora da cewa
"Munyi waya da Bulama ya gayamin abunda kika je kika ce masa, ki sani wannan karon dole kibi abunda nake so, bani zan biki ba, am doing all this for your benefit, in the next two Months insha Allah Fahad zezo ƙasar nan, ina son ayi Auren ku kafin ya koma"
Cigaba tayi da tafiyar ta ba tare da cewa Mahaifinta komai ba. Yusuf dake tsaye yana jinsu ya ƙarasa ya gaida mahaifin Widad da matarsa Hajiya Halima.
Ya amsa masa cikin, yayin da Hajiya Halima ta Amsa masa a ciki.

Yusuf ya miƙa wa Mahaifin Widad jakar ta da keys ɗin motar ta, yayi musu Sallama ya fice.

"Yaya Yusuf" yaji an kira sunan sa, tsayawa yayi ya waigo, Amal ce take tahowa da sauri hada É—an haÉ—awa da gudu.

"Sannu ashe kun dawo?"
"Eh mun dawo, akwai wani abu ne?"

ÆŠan sosa kai tayi tace "dan Allah in babu damuwa so nake ka raka ni Shopping"
"Shopping kuma? NiÉ—in?"
"Eh amma idan ban takura maka ba"
"ina batun takura ni da nake muku aiki, idan kin shirya kimin magana"
Murmushi tayi tace "nagode sosai Yaya Yusuf"
Shima murmushi ya mayar mata yai gaba abun sa.

(WASA FARIN GIRKI)

Share please 🙏 🙏 🙏

Comment nake so ba sticker ba ko kuma thanks ba, inda suka fi Comment su zasu dinga fara samun posting
Domin gyara, sharhi, kokuma ƙorafi a tuntube ni akan wannan lambar
07063065680
Watpad Ayshercool7724

_*AƘIDA TA*_

*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *

Haƙƙin Mallaka ⚠ : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode

ELEGANT ONLINE WRITER'S

                            PART1
                                  Page 5

Yusuf ya fita yaje yai alwala yai salla saboda lokacin salla yayi.

Widad kam tana zuwa É—akin ta ta jefar da Jakarta da wayar ta akan gado ta fara safa da marwa a É—akin ta

"Bulama ina ganin girman ka, ina maka kallon uba amma kana ƙoƙarin ƙetare gona da iri, kana ƙoƙarin tsallake iyakokinka, a tunanin ka yin Aure ze sa in canza ra'ayina? Daddy kunyi kuskure daga kai har Bulama, kuma bazan taɓa bari wannan kuskuren naku yayi tasiri a kaina ba, dole inyi wani abu" haka ta cigaba da surutai ita kaɗai.

Hajiya Halima ta kalli maigidan ta tace "Nikam wai Alhaji dagaske Widad zakayi wa Aure ko kuma yaya? Na kasa gane kan lamarin"

ÆŠan shiru yayi sannan yace "Eh hakane, Bulama ya bani shawarar akan cewa muyi mata Aure hakan ne kawai zesa ta canza wannan halin nata, Amma yarinyar nan kin san halin ta da kafiya da taurin kai, ta tirje tace sam bata san zancen ba, Amma a wannan karon bazan canza ra'ayi ba, ina son inga ta dawo da walwalarta, wannan karon dole tayi biyayya ga umarni na"

"Amma Alhaji baka ganin yin hakan tamkar ze ƙara tunzura rashin lafiyar ta ne, zaka ƙara sawa rashin lafiyar ta ya tsanan ta, ko ka manta sharuɗan da likitoci suka gindaya ne akanta?"

Alhaji Nasir Ya numfasa sannan yace

"Shima zaman ta a hakan bakomai ze ƙara mata ba face cigaba da dawwama a cikin damuwa da rashin walwala, akwai buƙatar ko bayan raina Widad ya zama na tana da kafaɗar da zata tada kai, ya zamana tana da wanda ze kula da rayuwar ta"

"Amma Alhaji wa zaku bawa Auren ta? ina fatan wanda zaku bawa yasan yanayin larurar ta? Tunda kaga ba shiga mutane take ba balle a ce tana da wanda take so, kar a bawa wanda besan ya take ba abu yazo ya ɓaci"

Alhaji Nasir yace "Ai ba wani bane za'a aura matan, fahad ɗin Bulama ne, itace dai batayi wayon saninshi sosai ba, rabon da su haɗu tun tana yarinya ƙarama, Amma shi ya santa kuma nasan baze bamu kunya ba Insha Allah, tunda itama tamkar ƙanwa take a gurin sa"

Jinjina kai kawai tayi ba tare da ta kuma cewa komai ba.

Wajejen la'asar Amal ta shiryo cikin wata irin doguwar riga wadda ta kama jikin ta matuƙa, se zuba ƙamshin turare take wanda turaren har hawa ka yake yi saboda ƙarfin sa ta hau kan wani takalmi me uban tsini, duwatsun jikin rigarta se ƙyalli suke suna rawa.

Cikin iyayi ta ƙarasa inda Yusuf yake zaune da su Nura da sauran ma'aikatan gidan tace "Yaya Yusuf mu tafi ko na shirya"
Ba musu Yusuf ya miƙe yayi wa su Isa sallama.

Ya karɓi mukullin Motar Amal, suka shiga mota suka fice.
Chapter 10 · 0% Book details