← Book details Akidata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 82

Sashe 64

Akidata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jiki babu ƙwari ya ƙarasa ɗakin nasu, kayan ɗaurin Auren suna nan a inda suke, da kuɗin sadakin nata, tana zaune ta haɗe kai da gwiwa se rusar uban kuka take.

Dole Widad tayi kuka, rayuwar ta cike take da ƙaddara daban daban, a hankali ya ƙaraso bakin katifar ya zauna, sam bataji zuwansa ba seji tayi ya taɓa ta, a ɗan razane ta ɗago ta kalleshi, ganin Yusuf ne yasa ta maida kanta kan gwiwarta ta cigaba da kukanta.

Yusuf yasa hannu ya É—agota yana kallon yadda farar fatarta ta koma ja saboda kuka da wahala.
Girgiza mata kai yayi amma yakasa ce mata komai, dan bema san ta'ina ze fara ba, Widad ta cancanci tayi kuka.

A hankali tasa hannu ta ture nasa hannun ta kwanta, tare da É—ora hannunta akan fuskarta tana ci gaba da kukan, A hankali take furta
"Ya Allah, aslihli sha'ani kullahu, wala takilni ila Nafsi, É—arfatu ainun"

(wuya koda magani ba daɗi, ashe Widad ta iya Addu'a haka 🙄)

Yusuf ya zauna ya zuba mata ido wai a hakama bata san halin da mahaifinta ke cikiba kenan, inaga inta sani.

Yarone yayi Sallama É—akinsu Yusuf, Yusuf ya amsa, yaron yace "Wai gashi inji gwaggo"

Yusuf ya karɓi ƙwaryar da'aka rufeya da faifai, yace "Masha Allah, kace mata mungode"

Yaron yace to ya fita, Yusuf ya ajiye Ƙwaryar yayi shiru yana kallon Widad da jikinta har rawa yake saboda tsabar kuka.

Yusuf yayi shiru, abubuwa suka cinkushe masa kai, nan da nan kansa ya fara sarawa, ya jingina da jikin bango ya rasa abunda yake masa daÉ—i.

A hankali Widad ta buÉ—e idonta, ta kalli inda Yusuf ke zaune yayi shiru, jijiyoyin kansa duk sun tashi, ga idonsa yayi ja kallo É—aya zaka masa kasan a cikin damuwa yake.

Ta miƙe zaune a hankali, yai saurin juyowa yana kallonta, ta goge hawayenta tace
"me'aka kawo? Yunwa nakeji"

Yusuf yace "ban san me'aka kawo ba bari im duba"

Ya ɗakko ƙwaryar ya duba, fura da Nono ne aka dama, tace "bani cokali a can gurin"

Ya duba ya É—akko mata, ya bata. Sosai take jin yunwa ta É—iba ta kai bakinta, ajiye cokalin tayi a gefe ta kafa kai ta dinga sha, tasha ya kai rabi sannan ta ajiye, ta koma gefe ta zauna tana lumshe ido.

Yusuf yace "kin ƙoshi ne?" ta jinjina masa kai ba tare da ta buɗe idonta ba, yasa hannu ya ɗau wadda ta rage ya fara sha, an zuba zuma a cikin furar shiyasa tasha da yawa.

Gaba ɗaya Yusuf tausayi yake bata, beji ba be gani ba ƙaddara ta haɗasj se wahala suke sha tare, duk abunda za'a kawo na Abinci indai zata iya ci, se taci ta rage sannan zeci, kuma seya tabattar ta ƙoshi sannan ko yaya ta rage shima yaci.

Kallonsa take yadda ya duƙa yana shan furar, wadda ba isarsa za tayi ba, ta lura shidai a rayuwarsa be ɗau komai da zafi ba, irin mutanen nan ne da duk yadda rayuwa tazo zasu karɓeta a haka.

Yusuf ji yayi kamar tana kallonsa, ya É—ago kai ba tayi zato ba suka haÉ—a ido, tao saurin É—auke nata idon.

Jiki a sanyaye yace "har yanzu dai kukan baki dena ba? Yakamata ace zuwa yanzu kin sawa zuciyarki haƙuri, kukan nan bashi da amfani, kina ƙaramin damuwa akan wadda nake ciki ne"

"Ni nace ka damu dani ne? Don't try to comfort me when ever am crying, kaji da damuwarka kaima"

Yusuf yace "tun daga lokacin da kika fara kuka saboda damuwa zuwa yanzu, maganin me kuka yayi miki? Kuka baya maganin damuwa wasu lokutan sema dai ya ƙara maka ƙuncin zuciya, ina tare da ke a guri ɗaya ta yaya zan zuba miki ido kiyi ta kuka, kina wahalar da kanki da yawa "

" kowa yaji da kansa malam ka dena damun kanka akaina"

Yusuf yace "Ai bazan iya bane, in dai kina kuka nikuma zuciyata rauni take"

Tsaki tayi tace "Se kai tayi ai"

Yusuf murmushi yayi bece komai ba.

Can tace "yanzu kaga death contract É—in da nake gaya maka muddin zakayi aiki dani ko? Meyasa baka yi tunani akai ba kasa hannu, dukda na gaya maka haka? "

Yusuf yace "saboda shi bawa baya taɓa tsallake ƙaddararsa, Allah ya ƙaddara se haka ta faru"

Shiru tayi ta shiga duniyar tunani, tana cikin tunanin ne bacci ya kwasheta daga nan inda take zaune, ta lanƙwashe wuyanta.

Yusuf ya miƙe yaje da nufin ya gyara mata kwanciya saboda wuyanta, ashe baccin nata ba nisa yayi ba, ta buɗe idonta ta kalle shi, haɗe rai tayi tace "meye haka?"

"yi haƙuri, gani nai kin lanƙwasa wuyanki, kar yayi miki ciwo kuma bana son in tasheki"

"to ina ruwanka inma yayi min ciwon? Dalla cikani kuma karka ƙara taɓani na gaya maka"

(Nikam nace Mamaki 😂 jimin mara kunya, sekace yau aka fara)

Murmushi yayi yace "shikenan Allah ya huci zuciyarki"

Ta kwanta tareda juya masa baya, Yusuf ya ƙura mata ido tare da yin murmushi a ransa yace 'insha Allah sena maye gurbin wannan damuwar taki da farinciki'

Yusuf ji yake kamar bashi ba, wai shine ya Auri Widad, yasan badan ƙaddara ta Ubangiji ba, kamar shi a yadda yake ya Auri mace irin Widad kyakkyawa 'yar me kuɗi haka, sedai wani iko na ubangiji.

Haka nan yake fatan Allah yasa su kasance tare har Abada, Allah yasa idan ta gano waye shi karta guje shi.

Misalin ƙarfe biyu da rabi na dare, Nurat taji motsi a harabar gidansu, ta leƙa ta taga ta hango mahaifinta ya fita shida direbansa, tunani ta shiga yi ina mahaifinta zeje a wannan daren haka? Tashi tayi ta tafi ɗakinsa, ta murɗa ƙofar a hankali ta shiga, ƙarƙashin gadonsa taje ta ɗakko wayarta da ta ajiye ta kunna recording.

Tayi saving ta fito daga ɗakin ta koma nata ɗakin, anan taji wayar da yayi da batun kuɓutar su Widad, da sauri ta miƙe tsaye tana Alhamdilillah, ta dinga kunna recording ɗin tana sake saurara, hankalinta ya koma son sanin me zasu tattauna a meeting ɗin da zasuyi a wannan tsakiyar dare kamar wasu matsafa.

Babban falon Hotel ne suke zaune, sunyi jugum jugum kamar masu jiran tsammani kallo É—aya zaka musu kasan suna cikin damuwa.
Alhaji Haruna yace  "jama'a ayi magana, abubuwa da sun taho kamar abun arziki, amma yanzu komai taɓarɓarwa yake, ta yaya za'ace sun gudu se kace a film, ko wata tatsuniya.

Alhaji Munir yace "nima abun ya ɗauremin kai, ga kuma wannan samu da rashi da muka gani, muna shirya abu amma wai an fasa taron, wannan shegun turawan ne suka ce a ɗaga, na rasa wani baƙin munafukin ne ya gaya musu ba, nifa kaina gaba ɗaya ya kulle"

Alhaji Musa yace  "babu yadda za'ayi ace su kasa jim rashin lafiyarsa ko kun manta shahararsa ne? Dole zasuji ai"

Wayar hannun Alhaji Musace ta fara ringing, ya fito da ita ya É—aga .

"ban samu halartar zaman da kuke a daren yauba, hakanma duk yana cikin shirina ne, yakamata ku maida hankali gurin gane cewar wani yana muku zagon ƙasa, akwai na jikinku wanda yasan siriinku shine yake ta dagula muku lissafi, ku maida hankali gurin gano waye, sannan kusam duk yadda zakuyi ku kama wanda sukayi garkuwa da 'yar gidan Daula ku kashe su, in bahaka ba akwai gagarumar matsala, sannan ko a mace ko a raye ku tabattar an kama yaran nan an kashesu"  yana gama maganar ya kashe wayarsa.

Nan fa suka sake shiga wani ruɗanin, tabbas inba wanda yake cikinsu ba babu ta yadda za' ayi Su Widad su iya tsira daga inda aka ɓoyesu.

Alhaji Haruna yace "to kun daiji abunda Alhaji Bukar yace, yanzu abunda za'ayi shine, kusa a binciko mana wanda aka bawa bincike hukumar jam'ian tsaro, ayi karɓo mana sakamakon binciken, hakan ze ƙara haska mana wani abun"

Alhaji Munir yace "wannan kuma aikin Saleh ne, shi'aka É—orawa wannan ragamar"

Alhaji Musa yace "Na kira shi sam labarsa bata shiga, inaga zan tura É—an aike a kiramin shi da safe"

Haka suka gama tattaunawa suka tashi ba tare da cimma wata ƙwaƙwarar matsaya ba.

Da safe Hajiya Halima nata safa da marwa, layin Ramlah sam baya shiga, ƙarfe goma na safe sega Ramlah ta dawo, Hajiya Halima tace  "daga ina kike?"

Kafin tayi magana Fahad ya shigo, Yace  'Mummy barka da safiya, mun miki laifi ko? Wallahi bayan mun dawo daga cinema ne naga kwana biyu ba taje gidanmu ba, kawai muka zarce can, daga nan kuma mumsy tace seta kwana tunda bata zumunci "

Hajiya Halima tace " Aida ta kira ta gayamin, hankalina ya tashi ince kaddai kuma an sace mana ku"

Ramlah tace "haba Mummy wani irin sacewa kuma, ai an san wanda ake sata, ina tare da Fahad waye yavisa ya saceni"

Sukayi dariya gaba É—aya, Fahad ya kashe mata ido, sukayi Sallama ya tafi.

Ramlah na zuwa ɗakinta ta jefar da jakarta ta kife akan gado ta cigaba da bacci, saboda har yanzu ƙwayar da ta sha bata saketa ba, kuma ga rashin sabo dama, dan bata taɓa shan kayan maye ba.

Yusuf bayan ya dawo daga sallar Asuba, har ya kwanta ya tashi, ya duba shimfiɗar Widad yaga bata nan, zumbur ya miƙe zaune a gigice yana waige waige, miƙewa yayi ya fito tsakar gidan bakowa, saboda yanayin garin da sanyi kuma gari be gama waye ba, leƙe leƙe ya shiga yi yana nemanta, can ya hangota daga wani ɗan lungu tana tsaye tana leƙa wata taga se murmushi take, hannunta riƙe da brush da toothpaste, kan nan ko ɗan kwali babu, gashinta ko taza babu ta naɗeshi da ribbon ya kwanta a bayanta.

A hankali ya ƙarasa inda take cike da son sanin me takewa wannan murmushi haka?

Jin mutum tayi a tsaye a bayanta, ta juyo a É—an razane, Yusuf ta gani a tsaye a daf da ita.

"meye haka?"
Chapter 64 · 0% Book details