Sashe 28
Akidata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nan fa kallo ya koma sama, nan 'yan sanda suka shiga dube duben su, aka tabattar da mutumin nan shine ya karya doka, nan fa mutanen gurin suka É—au sowa.
Widad taje gaban sa tace " if you are somebody you won't say it yourself, don't ever say you are Somebody when you are nobody, yanzu ka durƙusa ka bawa direba na haƙuri akan cin zarafin da kayi masa"
"Wallahi baki isa ba keɗin banza, in bawa wannan wulaƙantaccen haƙuri, kin san koni waye?"
Ɗaya daga 'yan sandan daya kira ne yaja shi gefe yace "kai wallahi wannan' yar masu ƙasa ce, idan taso zatasa a ɓatar da kai gaba ɗaya wallahi, kayi abunda tace kota sa a ɗaureka"
"wannan ƙaramar yarinyar 'yar cikina?"
"to karkayi cigaba da taurin kai, wannan' yan sandan data kira muma iyayen gidanmu ne"
Mutumin ya dawo a ƙule ya kalli Yusuf yace "Yi haƙuri"
"Akan gwiwowinka zaka durƙusa ka bashi haƙuri" cewar Widad
Cikin tsawa wani É—an sanda yace "ba zakayi bane? Semun tafi da kai?"
A hankali yaja da baya ze durƙusa, Yusuf yayi saurin riƙe shi tare da girgiza kai ya kalli Widad yace "please Madam ina nema masa Alfarma, kiyi haƙuri dan Allah, ni zan durƙusa in baki haƙurin a madadinsa"
Dama Widad tasan Yusuf baze taɓa yadda hakan ta faru ba, tayi ne dan nunawa Mutumin shi ɗin bakomai bane.
"Shikenan tunda ya haƙura, gobe in Allah kaimu, yaje station ɗinka ya karɓi kuɗin motar sa, na ninka maka masa sau uku, Amma ya kiyaye gaba"
Ta juya ta tafi motar su, Izzar Widad da yadda ta tafi da al'amuran cikin isa da izza, da bajinta suka birge mutane, aka dinga sowa, anawa mutumin nan dariya.
Dare yayi musu a gurin nan saboda wannan incident É—in, Yusuf yaja motar cikin nutsuwa suka tafi.
Amma still lokaci lokaci tana goge Hawaye a fuskarta, suka ci gaba da tafiya Yusuf na godewa Allah da Widad bata ga bindigar nan ba, tabbas yasan da Asirinsa ya tonu daya gama kaɗewa, ƙarshen ta seta kulle shi me fitar dashi se Allah.
suna zuwa gida Yusuf yayi horn Isa ya buÉ—e musu gate, Yusuf ya shiga da motar yayi parking, har ya gama abunda zeyi ze buÉ—e motar ya fita, Widad tana zaune ko gezau ba tayi ba, bata da niyyar fita daga motar.
fita yayi ya zagaya ya buɗe mata ƙofar, yace "Munzo fa" ɗaga kai tayi ta kalle shi, a hankali ta zuro ƙafafunta da take jin kamar ba'a jikinta suke ba waje ta yunƙuro ta fito, sedai tana fitowa ta tafi luuu zata faɗi, cikin zafin nama Yusuf zama shamaki da faruwar hakan, ta hanyar riƙeta ta faɗa a jikinsa.
Ƙirjinsa ya dinga bugawa da ƙarfi, saboda jin hakan wani irin abu daban, Isa me gadi ne ya zaro ido ganin abunda yake faruwa, Yusuf kamar me raɗa yace "Are you ok?"
Jinjina masa kai tayi ta sake ƙoƙarin miƙewa, amma still jiri ke kuma ɗibarta, tafiya take tana tangaɗi kamar wadda tasha wani abu, Yusuf yabi bayanta ya mata rakiya har cikin babban falo, hannunsa riƙe da ƙaramar jakarta da kuma wayar ta.
A babban falon ta zauna tana riƙe kai, hawaye nata zarya a fuskar ta, ƙoƙarin cire takalmin ƙafarta take, amma abu ya gagara, se kokawa take da takalmin.
Yusuf ya taka inda take ya durƙusa ya kwance igiyar takalmin nata me tsinin tsiya ya cire mata.
Ta gyara kwanciyar ta sosai ta miƙe ƙafafunta akan doguwar kujerar tare da lumshe idonta, don bawa hawayen idon nata damar gangarowa.
Yusuf a ransa yace 'Ikon Allah, wannan wane irin kuka ne?'
"ko za'a kira likita ne?"
"Ni lafiya ta ƙalau" ta bashi amsa idonta a rufe.
"Jikinki yana rawafa, kamar zazzaɓi ze kamaki fa"
"to ina ruwan ka? Jikin ka ne ko nawa? Ni kaimin kayana É—aki ka tafi ka ban guri"
ÆŠan girgiza kai Yusuf yayi yaje ya ajiye mata kayan ta ya fito, tana nan inda ya barta, yasa kai ya fice.
Yana fitowa ƙofar da zata sa dashi da harabar gidan yaji an riƙo rigarsa, waigawa yayi yaga waye wannan.
Amal ce tsaye tana huci,
"Amal lafiya kuwa?"
"dole kace lafiya mana? Yusuf daga ina kake kai da Widad?, saboda tsabar abu harda cire mata takalmi, Yusuf wai kai wani irin mutum ne dan Allah? Me kake aikatawa ne haka Yusuf? me yasa lallai seka yi abunda zaka birgeta, bayan kullum baka da kima a idon ta? Sau nawa nake gaya maka kusanci da ita tamkar kusanci da mutuwarka ne? "
Yusuf yace " look Amal niba wani abu nake nema a gurin Widad ba, kuma ba neman kusanci nake da ita ba, kawai ina tausayinta ne, kuma ina jin daÉ—in yadda mahaifinta ke mutuntani"
"kace tausayi Yusuf? Yusuf daga tausayi so yake shiga, ban taɓa ganin mutumin daya samu damar da ka samu a gurin ta ba, Yusuf a gidan nan ba kowa keda ikon zuwa inda take ba in bada izinin ta ba, kai kuwa kana iya zuwa gurin ta duk lokacin da kake so a matsayin ka na direbanta, Yusuf ina kishin ka, Yusuf sonka nake wallahi bazan zuba ido abubuwa su cigaba da gudana tsakanin ka da Widad a haka ba"
"Amal, Soyayya tsakanina dake ba zata yuwu ba, Mahaifiyarki bata ƙaunar talaka, kuma ni talaka ne inani ina iya Soyayya dake Amal?Hausawa suka ce ƙwarya tabi ƙwarya, idan tabi akushi zata fashe"
"dakata Yusuf" Amal ta katse shi, hawaye tuni ya fara sintiri a idon ta, tace "bazaka iya Soyayya dani ba, amma zaka iya da Widad ko?"
"Amal ni ba Soyayya nake da Widad ba, inani ina son mace kamar ta, ita a kanta bata yarda da wata soyayya ba, Amal nayi Soyayya a baya, abun da na fuskanta a soyayya bazan ƙara yadda in sake fuskantar sa ba, ke kanki da kin san wayeni bazaki soni ba, ba zaki so kasancewa da mutum kamar ni ba, kiyi hakuri "
"ba abunda ya shafeni, what I know is that ba zan zuba ido ka faɗa soyayya da mahaukaciya mara tarbiyya ba, kuma bari in gaya maka ba zaka taɓa kuɓucemin ba kasa wannan a ranka"
Tana gama faÉ—ar haka ta juya da sauri ciki tana kuka, jikin Yusuf yayi sanyi a haka ya ja jiki ya fito.
Masallaci ya wuce yai sallolinsa, sannan ya zauna yana karatun Al'qur'ani mai girma, ya daɗe yana addu'a sannan ya miƙe ya nufi titi dan samun abun hawa zuwa gida.
Abunka da unguwar masu kuɗi, tuni unguwar tayi tsit se sanyi bishiyoyi dake kaɗawa, yana ta tafiya a ƙasa yana tunanin abubuwa da dama, ya baro layin su Widad sosai inda security suke, ba tsammani se gani yayi ansha gaban
sa da mota, tsayawa yayi cak yaga ikon Allah.
Wasu ƙarti ne suka fito daga motar suka zagaye shi, ɗayan yace "kaine direban 'yar gidan Alhaji Nasir?"
Ba tare da tsoro ko shakka ba Yusuf yace "Eh nine"
"Good labari ya ishemu cewar akwai kusanci tsakanin ka da ita, duk inda zata tare kuke zuwa, an samu mu ɗakkota kwanaki amma ka hana, bari in gaya maka wani abu, zamu ƙyaleka ne saboda zakayi mana amfani, zamu ci gaba da bibiyar ka saboda akwai wani abu da muke so ka karɓo mana a gurin ta" cewar ɗaya daga cikin ƙartin
Yusuf yace "Babu wani kusanci tsakanin mu, aiki nake mata tana biyana, ko meye kuje ku tambaye ta ta baku mana"
ÆŠaya daga cikin sune ya sakarwa Yusuf wani mummunan naushi, da seda jini ya fito daga bakin sa, a zuciye Yusuf ya É—ago yana kallonsu, babban yace
"Wallahi idan baka kawo mana abun nan ba se mun kasheka, akwai wasu mahimman abubuwa da muke so ka karɓo mana a gurinta idan kaƙi semun maka yankan rago"
"Bayan yankan ragon se kuma me?" Yusuf ya faÉ—a babu alamar tsoro
Wani naushin suka ƙara masa a gefen ido,
Maimakon Yusuf ya tsorata, ko ya nuna jin zafin naushin, se yayi murmushi yace
"idan kunmin yankan rago, ku kuma ku zauna a naɗe duniya daku?, babu wani mahaluki daya isa yasa Yusuf yin wani abu dan son zuciya da zalunci, kuje ku gayawa wanda ya aiko ku cewar karya kuskura yayi gangancin cin iyakar gonar da ba tasa ba, idan kuma yaƙi zanwa shukokin feshi in ƙone nawa da nashi, kowa ya rasa, wannan saƙon Yusuf ne ga uban gidanku ko wayeshi"
Wani naushin suka yi niyyar kai masa amma ya riƙe hannun ɗayan.
"Waye kai? Waye ya gaya maka wanine ya turomu?" cewar É—aya daga cikin su
"yadda kuka binciko kuka gano nine direban Widad, haka yakamata ku bincika kusan wayeni, nasani aikoku akayi ku koma ku ƙara tabbatarwa wanda ya aikoku nina ɗauke Widad lokacin da yasa a sace ta, ni aikina tuƙata a mota dan haka ya kiyayi yunƙurin cutar dani"
Hausawa sukace 'sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi, sun daki Yusuf sosai, yaso yayi amfani da bindigar sa, amma yin hakan ze rusa masa da yawa daga shirinsa, dan haka ya fasa ɗaukar bindigar, suka daddake shi, wani yana iya ramawa wani kuma baya iyawa.
"zamu cigaba da bibiyarka, harse ka bamu abunda muke nema, zaka gane baka da wayo, Uban taurin kai, Ubangidanmu yafi ƙarfinka"
haka suka barshi a gurin suka tafi.
Da ƙyar Yusuf yaja jikin sa ya hau Napep ya tafi, hancinsa yana ta zubar da jini, jiri ne yake ta ɗibarsa saboda jinin da yake zubarwa da yawa, da ƙyar yaje gida, Allah ya temake shi Umma tayi bacci.
ya cire kayan jikinsa yana goge jinin fuskarsa, Aljihun wandonsa ya taɓa yaji wayar da Widad ta bashi ɗazu.
Hannu yasa ya ɗakko ta yana jujjuya ta "Ka ɓoye ta kamar yadda zaka ɓoye ranka, wannan wayar tamkar rayuwar ka ce"
Maganar Widad ta dawo masa, kunna wayar yayi, Amma akwai password akai shiru yayi yana nazarin kamar yaya wayar nan tamkar rayuwar sa take? Ajiye wayar yayi ya shiga yayi wanka ya fito, nan ya shiga aikin nasa na tunani dan abubuwa da dama sun faru da suke buƙatar nazari.