← Book details Akidata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 82

Sashe 48

Akidata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ji tayi kamar ana kallonta ta É—aga kai suka haÉ—a ido da Yusuf, ta tsuke fuska tace "baka iya Sallama bane?"

"Ai idan nayi sallama bakya amsawa" ya bata amsa

"Se yanzu kaga damar zuwa ko?"

"Umma na taya aiki shiyasa banzo da wuri ba"

"shikenan, zamu fita yau ƙarfe tara"

"Amma ai tara ta wuce yanzu, sedai ta gobe in Allah ya kaimu"

"tara na dare" ta bashi amsa

"tara na dare kuma? Ina zamuje haka da daddare? Kuma mu dawo yaushe? "

Ba tare da ta kalli Yusuf ba tace "hmmm akwai ka da ƙwarin gwiwa, ƙarfin hali bin ƙwaƙwƙwafi da sa ido sekace ɗan Sanda ko wani jami'in sirri, za kayi kyau da Aikin ɗan sanda ko kuma fannin shari'a"

Wani abune ya tsarga tun daga kan Yusuf har yatsunsa na ƙafa.......

(INA BUƘATAR JIN SHARHINKU FANS, ME KUKE TUNANI NE AKAN WANNAN TURKA TURKA, INGA COMMENTS ƊINKU KO IN KOMA POSTING DA TSALLAKEN KWANA ƊAYA)

Share and share please
domin sharhi, gyara ko shawara
Ayshercool
07063065680

                      _*AƘIDATA*_
       

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *

I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum

Haƙƙin Mallaka ⚠ : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

ELEGANT ONLINE WRITER'S

                         PART1
                                Page 20_21

Widad ta cigaba da cewa "da aikin shari'a zakayi zeyi wuya a iya kada kai, yakamata Alhaji Nasir yayiwa yayansa wani abu, yakamata ya nema maka makaranta ko dai horarwa akan aikin tsaro kokuma a nema maka aikin shari'a" ta ƙarasa maganar da wani ɗan guntun murmushi

Yusuf ya daskare ya kasa ko motsa É—an yatsansa 'Widad ta gano shine kokuwa?'

"Jeka in lokacin yayi kazo mu tafi"

Kasa motsawa Yusuf yayi, ya tasaya yana kallon Widad, ta É—ago ta kalle shi tace "ya dai naga ka tsaya? Meyafaru?"

Girgiza kai yayi ya juya ze fita, beji takuma cewa komai ba.

Tunani ne ya shiga zarya a zuciyarsa, kodai Widad tasan waye shine? Amma ya tuna da sharaɗinta bata yafewa wanda yayi mata ƙarya, a rashin yarda nan tata tabbas da tasan waye shi da tuni tayi maganinsa ta ɗau mataki akansa.
A hankali ya furta "Ubangiji Allah ka shiga lamarina, Allah yasa har in kammala aikin nan yarinyar nan ba zata ganoni ba"

*****************************

"Amma ni tabbas ba'ayimin Adalci a wannan lamarin ba, nida É—an uwana ku kusan halaka shi sannan ace bazan ganshi ba, wannan wane irin zalunci ne"

"zaka iya kiransa da duka abunda kaga dama, amma tabbas ba zaka ganshi ba, zamu ci gaba da ajiye shi a ɓoyayyen guri har se sakamakon binciken nan yazo hannun mu"

Saleh yace  "binciken nan bani na yake yi ba, kun san hukumar da sukeyi meze sa ku cigaba da azabtar min da ɗan uwa"

"saboda shi kaÉ—ai ne hujjar daze fallasa komai a kotu, kuma yana nan shirin tona mana Asiri dan haka gara muyi maganinsa"

Cike da damuwa Saleh yace  "to ai wanda yake ƙoƙarin samo min sakamakon anyi masa transfer ya kuke so inyi, ni ko ganinsa inyi shikenan"

Alhaji Musa yace  "baja da wannan damar Saleh, kayi abunda muka ce kawai"

A fusace Saleh ya miƙe ya bar gurin zuciyarsa na masa zugi, tabbas su Alhaji Musa masifa ne a rayuwarsa da ɗan uwansa.

Anwar a cikin ɓacin rai yaje ya samu Fahad a gida, Fahad na ganinsa yace  "Ohh God, Anwar ai namanta gaba ɗaya jiya zaka dawo am so sorry brother"

Jiki a sanyaye Anwar ya kalli Fahad yace "Am disappointed Fahad, dole kace ka manta jiya zan dawo, yanzu Fahad yarinyar dana daÉ—e ina mafarkin aura ita zaka aura?"

Ajiyar zuciya Fahad yayi yace "am sorry, nima bani nace ina son ta ba cusa min ita akayi akace sena Aureta dan anga tana da taɓun hankali"

"Fahad, Widad ba irin matan da za'a cusawa mutum bane, sannan idan har cusa maka ita akayi saboda taɓin hankali, ni ka barmin ita in aura tunda ni ina son ta"

"nice maka akayi bana sonta? Ko kuma so kake in kalli mahaifina ince zan bijirewa umarninsa"

Anwar yace "ni bahaka nake nufi ba amma nasani ka sani Baka dace da Widad ba, nasan halinka gaba da baya"

"kasan halina amma ka barni nake soyayya da ƙanwarka? Ko abun naka son zuciya ne?"

"son zuciya be wuce wanda ake shirin yiwa Widad ba, Ramla tasan dai dai tasan abunda take yi dan haka idan ta zaɓeka a matsayin miji ita taso hakan, Amma Widad fa Yarinya ce sannan...

"kaga Anwar ya isheni haka" Fahad yai maganar a tsawace

"Idan har ba so kake abotarmu ta samu matsala ba ka ƙyaleni, ka fita daga batun Auren nan"

"Idan kuma naƙifa?"

"Komai ze iya faruwa"

Anwar yace  "to sonake koman ya fary Fahad, naga baka gane rarrashi zan ɓullo maka ta inda ya dace"

Fahad yace  "Anwar karka kuskura kaje ka faɗi wani mummunan abu a kaina a gurin mahaifin Widad"

"Fahad dani da kai a ƙarƙashin kulawarsa mukayi karatu, ba abunda be mana na gata a rayuwa ba, bana jin Widad kanta ta moreshi kamar yadda muka moreshi, idan har aka lulluɓe kura da fatar Akuya ba muyiwa Alhaji Nasir Adalci ba, kaima kasan baka dace sa Auren 'yarsa ba"

"Amma Anwar kasan taimakawa zan in Aureta tunda mahaukaciya ce?"

"kabar taimakon naka mana, kaje ka auri Ramlah"

"Amma Anwar meyasa kake fifita Bare akan ƙanwarka? Idan har dagaske kake Ramla yakamata kace bazan Aura ba"

"Fahad ba goyon bayan bare nake ba, goyon bayan gaskiya nake kuma kaima ka sani"

Yana gama maganar ya fice a fusace cikin sauri.

**********************************
Ɓangarren Nurat kam lamarin mahaifinta yana bata mamaki, gaba ɗaya babu wanda ya gane inda yasa gaba daga ita har mahaifiyarta, ga ta'amali da wasu irin ƙarti da yakeyi wanda daka gansu zaka san ba mutanen kirki bane, suyita musu zirga zirga a gida, babu me ikon cewa uffan saboda duk tsoronsa suke ji.

Gefe guda kam tunanin Abokinta ya cika mata zuciya, zuciyar ta na matuƙar begen ta ganshi amma abu ya gagara, tasan ko giyar wake tasha bata isa taje gidansu Widad ba, tunda ta dena ɗaga wayarta tasan akwai wata a ƙasa haɗuwarta sa Widad ze iya haifar mata da matsala ne kawai.

Ba zata iya ƙirga adadin saƙonni da kuma kiran da tayiwa Yusuf ba, gefe guda kuma dai zuciyar ta na kwaɗai mata son sanin me mahaifinta ke ƙullawa wanda yasa shi yin mu'amala da wannan mutanen haka, suke ta musu sintiri a gida.

************************************

Anwar ne ya shiga É—akin Alhaji Nasir da Sallama, cikin sakin fuska ya amsa masa, sedai mahaifiyarsa tana tare da Alhaji Nasir É—in a wannan lokacin, fuskarsa ta nuna yana cikin damuwa kuma yana son yin magana ne.

Alhaji Nasir yace "shigo mana Anwar"

Anwar ya ƙarasa ya zauna a ƙasan carfet yana sunkuyar da kai, can yace
"Daddy, naji ka yanke wani hukunci, wai dagaske nan da ƙarshen wata zaka aurar da Widad?"

"eh hakane Anwar, halin ƙanwar taka ne se ita, gashi har yanzu ciwon ta yakan tashi, bekamata ace mamanku ta cigaba da ɗawainiya da ita ba, akwai buƙatar itama tayi Aure tunda ta girma"

"Amma Daddy kayi bincike akan wanda zaka bawan kuwa?"

Alhaji Nasir yace  "bafa wani ne ba, Fahad ne ba wai wani guri aka samo mata mijin ba, Fahad ne Abokin ka ɗan gidan Bulama"

Irin mugun kallon da mahaifiyarsa ke jifansa dashi ne yasa ya kasa cewa komai yace  "shikenan Daddy, Allah ya Sanya alkhairi ya kaimu lokacin"

Ya tashi gwiwa a saɓule yana kallon mahaifiyarsa ya bar ɗakina.

Alhaji Nasir yace  "Halima kaman akwai abunda yake damun Anwar amma ya kasa faɗa"

"ba abunda yake damunsa, naga dai kamar ya É—an damu ne da batun Auren Widad"

"ko dai yana sonta ne?"

Da sauri tace  "A'a kasan halinsa dai da tausayi, da yana son ta ai da tuntuni ya faɗa"

"hakane, aikam da ban bawa Fahad ba da Anwar zan bawa, dukda gaba É—ayansu 'ya' yana ne, amma wata kusan ai tafi wata"

"hakane kam, Allah ya wuce mana gaba"

Bayan ta sallami Alhaji Nasir, ta fito ta tafi É—akin Anwar, yana zaune a bakin gado ya dafe kai yana tunani, jin motsin shigowarta ne yasa shi É—agowa ya kalleta, Hajiya Halima tace
 
"kaga Anwar zuwa nayi in sake yi maka kashedi, wallahi tun wuri ka fita daga harkar Auren nan, wai ƙanwar uwarkace ita kota ubanka? Ka shiga hankalin ka na gaya maka"

Fahad yace "Allah ya baki haƙuri, Insha Allah zan kiyaye, amma dai Fahad be dace da Aurenta ba"

"da anyi magana ka iya bada haƙuri ai, ko waze aurawa ina ruwanka, shi ya haifeta ba in ya ga dama yaje ya aurawa kare ita mana ina ruwan wani?"

"Amma Mummy ya zakiyi da Ramla da take mutuwar son Fahad?"

"Ai magana ta ƙare tunda Fahad ze auri mahaukaciya, Allah ya bata wanda ya fishi seta haƙura"

"Amma ba kya tunanin yadda take son shi hakan ya haifar da matsala?"

"Kai rufemin baki, Allah ya tsaremu da matsala ina sake jan kunnenka ka fita daga sabgar yarinyar nan, in kuma kaƙi ji baka ƙi gani ba"

Anwar ya bita da kallo yayin da ta bar É—akin, ya girgiza kai tare da sauke ajiyar zuciya.
Chapter 48 · 0% Book details