← Book details Akidata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 82

Sashe 52

Akidata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Alhaji Nasir yayi murmushi yace
" karka damu, idan Allah yasa kuka dawo zan gaya maka yanzu dare ya fara yi "

Yusuf a ransa yace" to ko dai Alhaji Nasir yasan maƙiyansa ne? "

A fili kuma yace "Amma yallaɓai kana ganin za' a samu Nasara idan taga wannan likitan?"

"To abun duk lalabune a duhu Yusuf, bamu san inda zamu dace ba"

Suna cikin maganar saƙo ya shigo wayar Alhaji Nasir, ya ɗakko wayar ya duba
Jikin Alhaji Nasir ne ya kama rawa, a É—an gigice yace
"Amm.. Ammm Yusuf jeka ka kwanta dare yayi, saboda ku samu ku fita da wuri gobe in Allah ya kaimu, kabi wannan varrender akwai É—aki yana kallonka acan zaka kwanta"

Yana gama faɗin haka ya shige wani ɗaki ya rufe ƙofa, mamaki ne yakama Yusuf ya miƙe ya nufi inda Alhaji Nasir ya kwatanta masa ya shiga.

Masha Allah, ɗakine tangameme babu abunda babu na jin daɗin rayuwa a ciki, gadon kansa abun kallo ne kamar ka sace ka gudu, hotunan Widad ne ko ina a ɗakin, Yusuf ya dinga ƙare musu kallo, idonsa ya sauke akan haɗaɗɗen hoton Widad.

Tayi kyau sosai tayi murmushi cikin wata jar doguwar riga, ta baje gashin kanta kamar ba ita ba.
Ya daɗe yana kallon hotunan dake jikin bango, sannan ya ajiye jakarsa, yana sake ƙarewa ɗakin kallo.

Ya shiga banÉ—akin yayi alwala ya dawo yayi nafilfili yayi karatun Al'qur'ani da addu'oi sannan ya nemi guri ya kwanta.

Wajen ƙarfe biyu na dare cikin bacci Yusuf yaji muryar Alhaji Nasir na rawa yana kiran sunan Yusuf, a gigice Yusuf ya farka ya tashi zaune.

Alhaji Nasir ya kamo hannun Yusuf yace "taso Yusuf akwai matsala"

"matsalar me Alhaji?"

"Yusuf rayuwar Widad, ni idan tawa ta salwanta bakomai, bana son Widad ta rasa Ranta"

Cike da mamaki haka Yusuf ya biyo bayan Alhaji Nasir,  suka tarar Widad na tsaye a falo tana kuka, gaba ɗaya Yusuf ya rikice yace

"Alhaji meke faruwa ne"

Jiki na tsuma Alhaji Nasir ya miƙawa Yusuf wayarsa

"RANA BA TA ƘARYA SEDAI UWAR ƊIYA TAJI KUNYA, YAU ZAMU KAWO ƘARSHEN WASAN KURAR DA MUKE, KODAI KA YADDA KA BAMU ABUNDA MUKE BUƘATA KA HALARCI TARON KASUWANCI, KO KUMA KA HANAMU KA RASA RANKA DA NA 'YARKA, KOMU KASHE TA AGABANKA MU BAR MAKA MUGUN TABO, WATAƘILA HAKAN YASA KA BAMU ABUNDA MUKESO"

Yusuf yace "to koma mene ka basu mana, saboda rayuwar ka da tata su tsira"

"Yusuf ni kaina abunda suke so in basu ba nawa bane, nayiwa kaina Alƙawarin bawa meshi abunsa, dan haka bazan basau ba"

Yusuf yace  "to ko ka kira jami'an tsaro"

"A' a Yusuf hakanma matsala ne, dan Allah ka É—au Widad ku tafi maza ku tafi yanzu"

Fashewa da kuka Widad tayi tace  "Ni bazan tafi na barka ba Daddy, bana son wani abu ya same ka, Daddy bana son tafiya kai kaɗai ka ragemin"

Dattijon yana zubar da hawaye yace

"Widad bana son rayuwarki ta salwanta, nima ke kaɗaice dani, idan suka kama ki komai ya ɓaci, ki tabbatar kin miƙa amanar nan ga masu ita, karki yards ta salwanta ko a karon banza wasu su karɓa, maza ku tafi"

Ƙanƙame mahaifinta tayi tana kuka tace "Daddy ba inda zanje, kome ze faru ya faru muna tare"

Daddy da kansa yaja hannun Widad ya kaita mota, ya kalli Yusuf yace "Allah ya kiyaye ku Yusufa, na yarda da kai ka kularmin da Amana
ta, ka kula da Widad kayi haƙuri da ita, karku sake ku dawo idan bani na kira ku ba, zaman Widad anan tana cikin hatsari mutanen nan dagaske suke"

Haka Yusuf ya shiga motar yaja, Widad tana wani irin kuka me ban tausayi.

Su kansu ma'aikatan sunyi mamakin fitar su Yusuf a wannan daren.

Saleh ne ya samu Alhaji Nasir yace  "Alhaji lafiya kuwa? Meke faruwane haka?"

Daula yace  "Wata 'yar ƙaramae matsala ce, Amma komai ze daidaita insha Allah"

Alhaji Nasir ya koma cikin gidan yana safa da marwa ya rasa abunyi, wayarsa ya É—akko ya kira Bulama a waya ya sanar dashi halin da yake ciki.

Yusuf kam a besan inda ze nufa ba a wannan tsohon daren, gaba É—aya sahu ya É—auke se abunda ba'a rasa ba,gudu yake yana ratsa tituna ba tare da yasan inda ze dosa ba.

Befi mintuna talatin ba sega Bulama yazo gidan a sukwane, suka haÉ—u da Alhaji Nasir a harabar gidan, Bulama a gigice yace "Daula ina Widad É—in take yanzu?"

A kiÉ—ime Daddyn Widad yace "na haÉ—ata da direbanta nace su tafi"

"su tafi suje ina?"

'Bulama na rasa yadda zanyi ne, ina tsoron rayuwar Widad ta taɓu, nasan yaron baze cutar da ita ba"

A fusace Bulama yace  "kayi hauka ne Nasiru, kamar ya ka haɗata da direba? Kasan daga ina yake ko kuma ina ze kaita, memakon ka kira' yan sanda kawai seka haɗata da direba idan kuma bakinsa ɗaya da mutanen fa"

Girgiza kai Alhaji Nasir yayi yace  "bana tunanin haka Bulama kaina ya gana kullewa ne"

Alhaji Bulama ya É—au waya ya fara kiran 'yan sanda.

Sosai Yusuf yake gudu akan titi, yayin da Widad ta dunƙule tana aikin kuka, Yusuf ya kasa cewa komai se tunanin ya zasu tsira, sedai babu zato yaci karo da wata mota anyi parking ɗinta a tsakiyar titi, wani irin parking na rashin mutunci yanda babu damar Yusuf ya iya wucewa, ga gefe jeji ne, yayi reverse ze juya kan motar wata motar tazo ta ƙara rufe bayan tasu Yusuf aka sasu a tsakiya.

Wasu irin ƙarti ne suka fito daga motocin suka kewaye su Motarsu Widad, gaba ɗaya Widad ta rikice ganin suna tunkaro su, suna zuwa suka buɗe ƙofofin motar, suka sawa Yusuf bindinga aka suka ce Widad ta fito.

Ko motsi ba tayi ba balle ta ɗaga kai ta kalle su, cikin tsawa ɗaya yace  "ba magana ake miki ba"

Sunkuyar da kai tayi taƙi motsawa, ɗaya yasa hannu ze fizgota aikuwa ta riƙe Yusuf gam tana kurma ihu

"Yoseef karka bari su tafi dani"

Yusuf ya riƙe hannun ta yace  "me mu kayi muku kuke ƙoƙarin cin zarafin mu akan titi haka"

"zaka rufe mana baki ko semun fasa kanka da bindiga, dalla ku fizgota ta ƙarfin tsiya suna ɓata mana lokaci"

Ai Widad sekace Mayya ko ƙarfe ta riƙe Yusuf gam, wani gigitaccen mari ɗayan ya kwaɗawa Widad yana ƙoƙarin janyo ta, sedai ga mamakin Yusuf mutumin yana sauke hannun sa Widad ta rama marin, dukda a gigice take tace   "karka ƙara gangancin marina, wallahi ka kuma dukana sena rama"

"Ashar ya saki yace lallai wannan yarinyar akwai ƙarfin hali, yau zamuyi maganinki"

Hannu ya kai ze shaƙota, amma Yusuf ya riƙe hannun mutumin yace  "karka kuskura ka sake marinta"

"Idan aka sake marinta me zakayi? Dan Allah oga ka bani dama in fasa kan gayen nan da bindiga"

Shugabansu yace "babu kisan kai a wannan deal É—in, ban sani ba ko zuwa gaba"

Suka cigaba da jan Widad, Yusuf yaƙi sakin ta, baya son ya zafafa suyi mata illa gashi babu makami a jikinsa.

Yace "idan kunga kun tafi da Widad to tabbas kun kasheni ne, amma ba inda zaku da ita"

Ganin Yusuf na ɓata musu lokaci ga Widad na nema tasa asrinsu ya tonu, bakinta yaƙi rufuwa sunan Yusuf kawai take kira, haka suka haɗa da Yusuf suka sasu a tasu motar.

Suka ƙulle hannayensu, sukayi daji dasu, ihu Widad ta cigaba dayi, gaba ɗaya ta manne a jikin Yusuf sosai tana cewa
"ni ku ƙyalemu, besan komai akai ba, direba nane kawai ku ƙyalemu mu tafi"

Yusuf yace  "kiyi shiru karsu illataki"

Ai be gama rufe bakinsa ba, suka sa ƙyalle suka rufe musu ido.

Widad tasa haƙoranta ta riƙe rigar Yusuf, duk dan kar su raba ta da Yusuf, se haki take tana jin yadda zuciyar Yusuf ke bugawa, Yusuf kam ya yabawa jarumtar Widad yau.

Shikansa Saleh da'aka haɗa baki dashi akayi aikin, ya rikice gaba ɗaya ya shiga damuwa mussman yadda yaga Alhaji Nasir na zubda Hawaye yana kaiwa yana komowa a harabar gidan, Alhaji Bulama nata rarrashinsa amma se kuka yake kamar ƙaramin yaro, zuwan 'yan sanda yayi dai dai da shigowar wani saƙon wayar Alhaji Nasir.

"A ZATONKA KA FIMU WAYO NE, MUN KAMA' YARKA DA DIREBANKA SUNA HANNUNMU, SHAWARA TA RAGE NAKA, ZAMU CIGABA DA AZABTAR DASU, DAN HAKA SEKA KA ZAƁA KO RANSU KOKUMA ABUNDA MUKA NEMA A HANNUNKA"

Yana gama karanta saƙon ya yanke jiki ya faɗi a gurin

In an karanta ayi share please
🙏 🙏 🙏

Gyara, sharhi ko shawara
Ayshercool
07063065680

_*AƘIDATA*_

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *

I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum

Haƙƙin Mallaka ⚠ : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

ELEGANT ONLINE WRITER'S

PART1
Page 24_25

Gaba ɗaya ma'aikatan gidan su kayo kan Alhaji Nasir, sedai jikinsa kamar babu rai, 'yan sanda suka ƙaraso cikin gidan aka kwashi Alhaji Nasir a daren zuwa Asibiti.

Widad kam gajiya tayi da zaman motar, saboda tafiya suke bata wasa ba cikin wani irin azababben gudu, jin tafiyar taƙi ƙarewa ne yasa Widad fara mustu mutsu, tun tana mutsu mutsun har bacci ya kwashe ta, a firgice ta farka ta kurma wani uban ihu tana kiran
"wayyo Allah na Yoseef, karka tafi ka barni"

Yusuf yace "Widad ina nan, muna tare har yanzu Allah ze fitarmu insha Allah, ki dena shouting karsu miki wani abun"

Me tuƙa motar yace gara dai kaja mata kunnen.

Memakon tayi shiru ta cigaba da ihu tana "ku ƙyalemu mu tafi, yoseef na gaji da zaman nan hannuna igiyar nan ta dameni, bayana ciwo na gaji bayana ze karye"

Wata hoda su watsawa Widad, wanda hakan yasa ta baccin dole, ba Widad ba har Yusuf gaba É—aya bacci ya kwashe su.
Chapter 52 · 0% Book details