Sashe 29
Akidata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Me Widad taje yi Hotel? Me ta gani ya sata kuka? Waye ya turo mutanen nan? Ko waye akwai sa hannun wani a gidan su Widad? Amma dagaske Tausayin Widad zesa ya fara sonta? Me yasa tasa a durƙusa a bashi haƙuri yau? Tabbas zata iya yuwuwa akwai Alaƙa tsakanin wani a gidansu Widad da mahaifin Nurat"
Ji yayi kansa kamar ze fashe, dan haka ya rintse idon sa yana addu'a da fatan bacci ya ɗauke shi koze ɗan samu nutsuwa, Amal ta faɗo masa a rai itama, wai ita bilhaƙƙi son shi take.
Wani tunani ya shigayi watanni shida da suka gabata, da yanzu yana nan da Auren sa, katsam a dalilin irin tasa ƙaddarar aka fasa wannan Aure, bayan cin zarafi da wulaƙanci daya fuskanta daga iyayen matar daze Aura, bacci dai se ɓarawo ne ya ɗauke shi.
*******************************
Da safe Yusuf ya tashi da matsanancin zazzabi, kansa har sarawa yake sosai saboda dukan da yasha jiya, juyi kawai yake akan gadon gaba ɗaya jikin sa ciwo yake masa, ganin har kusan ƙarfe tara be fito ba yasa Umma leƙawa ɗakin sa, ta tarar da shi kwance a kan gadon sa, ƙarasawa tayi ta taɓa jikin sa tace "Yusuf lafiya kuwa? Naga har ƙarfe tara baka fito ba?"
"Bana jin daÉ—i ne Umma"
"dan baka jin daÉ—i seka zo ka kwanta kana juyi, ka tashi ka watsa ruwa, ka karya seka sha magani"
"to Umma"
Yusuf ya miÆ™e ya shiga yai wanka, kayan breakfast É—in ta kawo masa É—aki, ta kalle shi taceÂ
"Yusuf kamar kumburi nake gani a gefen idonka da bakin ka"
Yusuf yace "Mun faɗi akan babur ne jiya da daddare"
"Amma ka kasa gayamin? Meye amfanin hakan, haba Yusuf"
Yusuf yace "Yi haƙuri Umma, bana son ɗaga miki hankali ne"
"Amma ina fatan ba wani mummunan ciwo daka ji?" tai maganar cike da damuwa
"Eh banji ciwo me yawa ba"
Da kanta ta zauna tana bashi Abinci a baki, ta É—akko masa first aid box É—insa ya É—au magani ya sha, ya koma ya kwanta.
Kwanciyar sa ba daɗewa Abbas ya kira shi, da ƙyar Yusuf ya ɗaga wayar, Abbas yace "Mutumina kana ina ne? Ina son ganin ka"
"Ina gida bana jin daÉ—i ne"
"Subhanallah, meya sameka?"
"Zazzabi ne" Yusuf ya bashi amsa
"Shikenan gani nan zuwa"
Su kayi sallama
**************************
Hajiya Halima na zaune falon ta tana shan tea, Isa mai gadi yazo yana kwaɗa sallama a ƙofar falon ta, A fusace tace "wai meye hakane? Lafiya kame do kamin wannan sallama kamar kana bina bashi?"
"Hajiya nine, Isa ne"
"to ya a kayi?"
"Hajiya gurin ki nazo"
Ta ɗanyi tsaki sannan tace "shigo"
Ya shiga falon ya durÆ™usa yaceÂ
"Ina kwana?"
"Kai bana son doguwar gaisuwar nan meke tafe da kai?"
"to Hajiya kin san shi sha'ani na rayuwa kiwon mutum ake ba dabba ba koba haka ba?"
"kai nifa bana son wannan surutam banzae, ka faÉ—amin kanka tsaye meke tafe da kai"
Isa ya gyara zama yace "game da sabon direban nan ne Yusuf, gaskiya Hajiya akwai buƙatar kisa ido, jiya yadda na gansu Allah ya nuna min Annabi salallahu alaihi wassalam, kin san dai irin shigar da take yi, bayan kin fita ita dashi suka fita, basu dawo ba se ƙarfe tara na dare, bayan sun dawo a gabana da idanun nan nawa" yai maganar yana gwalo idon nasa ya cigaba da cewa
"da idanu na naga suna rungume juna, Hajiya a saka ido, kina gani idan ba kiranmu akayi ba bamu da damar shigowa kiga yadda take hantarar mu, Amma shi ba yau ba gobe cikin sintiri yake har cikin É—akin kwanan ta, Allah kaÉ—ai yasan me suke yi, gaki da 'yan mata kema kyawawa bekamata yana gardi baligi ya dinga wucewa yana kalle miki su ba, shiyasa nace bari inzo in sanar dake abunda ake ciki "
Dire kofin hannun ta tayi, taja wata nannauyar Ajiyar zuciya tace " Hmm naji maganganun ka, kuma kazo da magana abun dubawa, tashi kaje zan san abunda zanyi "
Isa ya miƙe yana murna yace
"shikenan Hajiya na barki lafiya "
Shiru Hajiya Halima tayi tana zake nazartar kalaman Isa megadi, tabbas Widad bata yadda wani ya Wulaƙanta Yusuf ba, lokacin da ciwon ta ya tashi taƙi yadda da kowa se Yusuf, idan har dagaske wani abu na faruwa a tsakanin su to tabbas akwai yuwuwar ta gayawa Yusuf inda abunda suke nema yake.
**************************
Widad kwana tayi da zazzabi da ciwon kai, da ƙyar ta samu tayi bacci.
Jikin ta sam babu ƙwari ta miƙe domin haɗawa magen ta abunda zeci.
Widad na matuƙar son dabbobi, tana tausayin su fiye da yadda take tausayin mutane, akwai shaƙuwa me ƙarfi tsakaninta da dabbobinta, mussman ma wannan magen nata pita, da kuma karen ta dake gidan gona, tana jin daɗin kasancewa da su, dan ba ƙaramin ɗebe mata kewa sukeyi ba.
Ta samu container ta zuba masa madara, ta samo wani ta zuba masa gugguru, ta koma gefe tana kallon magen, maimakon magen yaci seya koma jikin ta ya kwanta, dan ya saba idan lokacin cin Abinci yayi, ta zuba masa nasa yana ci itama tana cin nata
**********************************
Abbas ne yayi Sallama ɗakin Yusuf, da ƙyar Yusuf ya iya amsawa, ya miƙe zaune suka gaisa da Abbas.
"Sannu Yusuf, ko Asibiti za muje in sauke ka"
Yusuf ya girgiza kai yace "A'a na sha magani kawai, ya kake ya aikin?"
"Alhamdilillah, jiya Oga Suleiman yake neman ka, shine kiran da nayi maka, kuma se kace baka jin daÉ—i, yanzu yau ba zaka gidan su mutuniyar taka ba?"
Yusuf yace "bazani ba gaskiya, sedai zuwa gobe in Allah ya kaimu idan naji sauƙi"
Abbas yayi Æ™asa da murya yaceÂ
"Ya kuÉ—in nan waye ya turo dasu kuwa?"
"itace wai Albashi na ne na watanni uku da bata bani ba, nace mata yayi yawa ta rage taƙi"
"Taɓɗijan kaima Yusuf da wani abu, kamarya ta rage? Malam kawai kaci kuɗi, meye labari kuma?"
Yusuf ya gaya masa Hotel da suka je, da yadda suka dawo tana kuka, Amma be gaya masa zancen wayar nan ba data bashi.
Nan suka cigaba da tattaunawa zuwa wani lokaci Abbas yace ze tafi, Naira dubu É—ari Yusuf yayi masa transfer a cikin kuÉ—in, Abbas yaita murna yana godiya suka yi sallama.
Amma ƙasan zuciyar Abbas kamar ya fasa ihu
'dana san wannan alherin Yusuf zeje ya dinga samu da tun farko nina karɓi aikin nan, ya samu dubu ɗari biyar amma ya bani wata shegiyar dubu ɗari, ga danƙareriyar waya ya samu, na tura shi dan ina gudun wulaƙanci amma yaje yana samo abun Arziki, dole in san yadda zanyi a cire shi daga kan aika ni maye ni"
'Amma hatsari da kasadar dake cikin aikin fa?' wata zuciyar ta tambaye shi, tsaki yayi yana ci gaba da surutai.
*******************************
Shafa jikin magen take a hankali tana lallaɓashi yaci Abinci, wayarta ce ta fara ringing, muzurun nan ya kasa a guje yaje ya ɗakko ta a bakin sa ya kawo mata, shafa kan muzurun tayi tace "thank you Roux"
Ta amsa wayar tasa a kunnen ta
"Ranki ya daÉ—e Bala fa babu lafiya, an É—auke shi rai a hannun Allah an kai shi Babban Asibitin cikin gari, dan besan waye a kansa ba"
Miƙewa tayi tsaye tace "what? How comes? Wace irin rashin lafiya ce wannan?"
"Nima ban sani ba gaskiya, Amma an fita da shi daga Asibitin cikin kurkukun gaba É—aya"
Bata kashe wayar ba ta miƙe, da sauri ta shiga bedroom ɗinta ta canza kaya, dukda yanayi na rashin lafiya da take ciki, wayar ta ta koma ta ɗakko ta fara daddanawa sannan tasa a kunnen ta.
Yusuf yana jin wayarsa tana ringing ya ƙi ɗagawa yasa ta a silent, ya ajiye wayar ya cigaba da kwanciyar sa.
Jifa tayi da wayar akan kujera ta fice harabar gidan, gurin su Nura ta nufa, tana zuwa suna gaishe ta amma bata kula suba taceÂ
"Ku kiramin driver yanzu"
Jiki na rawa suja shiga kiran Yusuf babu ƙaƙƙautawa, Amma be ɗaga ba.
Ta kalli Nura tace "É—akko mota da sauri, zaka fita dani"
Cike da washe baki yaje ya ɗakko mota, ta shiga Nura yaja motar suka fita, gaba ɗaya ji take kamar tayi Amai, dukda a bayan motar ta zauna amma warin hammatar Nura ya cika motar, se tsaki take yi badan ya zama urgent ta fita ba babu yadda za'ayi ta yadda wannan ƙazamin ya jata a mota, suna tafe tana masa tsawa gami da hantararsa, Amma Yusuf ze gane kurensa na ƙin zuwa da yayi yau sannan yaƙi ɗaga waya.
Prison tasa ya kaita, suna zuwa ta fita ta shiga, kai tsaye ofishin Hisham ta wuce.
Yana ganin ta yai murmushi ya sallami kowa daga office ɗin sannan yace "barka da zuwa lady boss, Ashe kin dawo Nigeria?"
"Ya aka yi Bala ya kamu da rashin lafiya da har ta kai shi ga kwanciya, seda aka fita da shi daga gidan nan?"
"Ranki ya daÉ—e gaskiya dama yana É—anyin rashin lafiyar a tsai tsaye, Kawai se É—an uwansa ya kawo masa ziyara, bayan ya tafi jikin sa ya rikice"
"yanzu kana nufin kace min ÆŠan uwansa ne ya kawo masa abunda yaci, jikin sa ya rikice kenan? Saboda sakaci da rashin sanin aikin ku?"
"A'a ranki ya daÉ—e kin san?...
"Yimin shiru malam, saura sati É—aya tal a koma kotu, kawai se inji wannan banzar maganar mara tushe, shikenan amma kasani idan har rashin lafiyar Bala haÉ—in baki ne, duk wanda yake da hannu a ciki shima abunda ya samu bala ze sameshi. "
Ta miƙe a fusace ta fito, Hashim ya biyo ta da sauri amma ta shiga mota da niyyar ta ta wuce gurin lawyern Daddy, amma ba zata iya jure wannan tsamin da Nura yake ba, dan haka tace ya nsida ita gida, tana mamakin ƙoƙari irin na Daddy da yake iya shaƙe wannan warin hammatar, Yusuf kullum tsaf dashi cikin ƙamshi, amma wannan ƙazamin kamar baya jin yadda yake wari, seda ta bari sun koma gida, sannan tayi wa Nura ta tas akan ƙazanta da warin da yake yi a gaban sauran ma'aikatam.