← Book details Akidata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 82

Sashe 75

Akidata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yusuf yace "Shikenan, Insha Allah zan san abunyi"

"Sannan kuma..." se kuma tayi shiru

"sannan kuma me?" Yusuf ya tambaya

"Nasan baza'a samu shaving cream ko powder ba, a siyomin shaver please"

Cike da son ya kunnata Yusuf yace "shaver kuma, me zakiyi da shaver?"

"Abunda kake yi da ita" ta bashi amsa cike da tsiwa

Yayi murmushi yace "Aini gemuna nake askewa da ita"

Ta kalle shi ta É—an tsuke baki tace "Nima nawa gemun zan aske"

Aikuwa Yusuf ya kwashe da dariya, sosai yadda tayi magana da abunda ta faÉ—a É—in ya bashi dariya, kallonsa take yi yadda dariyar tayi masa kyau.

"wallahi idan ka ƙware ba ruwana"

Tai maganar tana shirin Miƙewa, ya kalleta yace "Ina zaki?"

"tsakar gida nake son fita"

"Amma kin manta halin da kike ciki ne?"

"To zama zan tayi ina kallonka, ni na gaji da kwanciyar ma, zan kula sosai"

Yusuf yace "Aini bana gajiya da kallon kyakkyawar fuskar nan taki, muyi zamanmu a É—aki nima na iya hirar se in miki, kuma baki ci Abinci ba, ko kin manta?"

'ƙyale Abincin nan, ni idan ina period bana son Abinci sosai "

Yusuf yace " dama can haka kike, ina lura dake tarkace kawai kike ci ba Abinci ba, so nake ki ƙara Ƙiba ki daure kici ko kaɗan ne mana"

"Ni gaskiya, ba irin wannan nake so ba"

"wanne kike so" ya faÉ—a cike da kulawa.

ÆŠan tsura masa ido tayi, sannan tace
"Bari dai inci kaÉ—an"

Ya É—akko kwanon dambun ya ajiye mata, tasa cokali ta fara ci, dambun tsaki ne amma yaji gyaÉ—a da zogale yayi daÉ—i Sosai.

Widad tace "tunda nazo ƙauyen nan, ban taɓa cin Abinci me daɗin wannan ba"

Yusuf yayi murmushi yace  "harda bredin jiya?"

Widad tace "hmm dan dai kar kaji haushi ne, amma gaskiya bredin nan ya daÉ—e a ajiye, se marmashewa yake ba daÉ—i"

Yusuf yace "dagaske ba kya son inji haushi?"

ÆŠan kallonsa tayi tace "No i mean banyi niyyar magana ba lokacin shine kawai, ka É—akko spoon muci Abinci mana"

Yusuf ya girgiza kai yace "A'a kici kawai, idan kin rage se inci"

Widad tace "meyasa? Ai ze ishemu"

Yusuf yace "bana son in samiki yawuna a jiki, naga bakya son hakan"

Ɗan tura baki tayi, cikin ƙunƙuni tace "na nawa kuma, ƙarewa ma ai Yawun naka ka samun a bakina jiya"

Yusuf yace "ai bazan manta wannan moment É—inba, nayi kissing É—in gimbiyata the most memorable moment in my life"

Widad tace "tabbas kam, ka kafa tarihi, kayi abunda wani mahaluki be taɓa gangancin gwadawa ba, kayi min abunda ban taɓa zaton wani zemin in ƙyaleshi ba, hmm ban san meyasa kake min abubuwa son ranka ba, ƙyaleka kawai nake"

"Are you sure babu wanda ya taɓa kissing ɗinki seni?"

Watsa dambu tayi a bakinta, ta ja wasu seconds sannan tace "Idan an taɓayi kana tunanin zanji tsoron ka ne? Ban taɓa shan yawun Ƙato ba se a kanka, kuma bashi ka ɗauka, tunda kasa na haɗiye yawunka"

Murmushi Yusuf yayi yace "Yaushe ne ranar biyan bashin?"

Banza tayi masa taƙi ko kallon inda yake, can Yusuf yace "Amma meyasa kike zuwa Clubs da kuma Hotel?"

Jin tambayar tayi a bazata, take taji tana kokawa da dambun dake bakinta, gaba É—aya Mood É—inta ya canza a hankali tace

"ai tun a lokacin na gaya maka me nake zuwa yi, na gaya maka ni karuwa ce kamar yadda matan gurin suke"

Haɗe rai Yusuf yayi yace "Kamar yadda bakya son ƙarya, na tabbata kema bakya aikata ta se bisa kuskure, meyasa zaki gayamin haka? Ko kina son zuciya ta ta buga ne?".

"Tunda baka yarda ba shikenan, amma kasan dai bazan zauna ina rantse maka dan ka yarda dani bako?"

Ta ajiye spoon É—in Abincin ta je ta sha ruwa, tayi waje abunta ta bar Yusuf a gurin a zaune.

Roƙon Allah ya shiga yi akan Allah yasa abunda Widad ta faɗa ƙaryane, dan ba ƙaramin kishi yaji ba, kuma yasan halin ta ko meye zata yi ƙoƙarin gaya maka gaskiya, ko ta maka daɗi ko akasin hakan'

Tana fitowa Gwaggo tace "Amarya kin ware kenan?"

Widad tace "eh Alhamdilillah"

"Masha Allah, haka nake son ji"

Hari tace "Wai meya same ki ne?"

Widad tace "Kaji Baba Harin nan, sekace kin damu dani, bayan ko gani kika yi zan mutu murna zaki yi, to ciwon yara nake bana tsofaffi ba dan haka base kinji ba"

Aikuwa a fusace Hari tace "karki ƙara cemin tsohuwa, ta ina nayi miki kama da tsohuwa? Da ƙuruciyata dudu shekarun nawa ba zasu gaza Ashirin da shida ba, amma kike kiramin tsufa"

Ai gaba ɗaya wanda ke tsakar gidan ba wanda be dariya ba, Widad tace "A'a kin manta a zanin goyo kike ma ƙarewar yarinta, harfa jikokine dake amma kice shekarar ki Ashirin da shida, shekarar ki biyar akamiki Aure kenan"

Hari tace "koma yane dai, niba tsohuwa bace ba ehee, dan jina nake garas kamar 'yar shekara goma sha shida"

Widad tayi dariya tace "dama zaki dinga gayune, za kiga yadda zaki koma yarinya sharaf, amma indai baki dena ƙazanta ba, to tabbas wataran za' a kalle ki ace shekararki sittin da 'yan kai"

Hari tayi kicin kicin da Fuska, dan Widad ta fara kaita bango, idan ta cigaba da biye mata to tabbas za suyi ba daÉ—i, dan haka tayiwa Widad banza.

Widad ta ƙarasa inda Hindu ke tsinke zogale ta zauna tace "Hindatu, ya ki keyi? bari in tayaki"

Hindu Ta gwadawa Widad yadda ake tsintar zogale, ta zauna suna yi tare.

Can Widad tace "Hindu, wai kuma idan kuna period bakwa amfani da pad ne? Se tsimma"

Hindu tace "meye kuma firiyios?"

Widad tace "A'a ba kije makaranta bane? Me yasa Common things idan na faÉ—a, seki ce baki sani ba?"

Hindu tace "bari Amarya wallahi muna son karatun nan, amma ba yadda muka iya ne, kinga inda muke zuwa makarantar furamarai can wani ƙauye ne, kusan ƙauyuka biyar duk ita muke zuwa, to guri ba kusa ba nisa kafin kaje duk anyi wani abu baka nan, lokacin damuna kuwa bama samun zuwa, sannan akayi ruwan Sama me ƙarfi ya kwashe kwanon da'aka rufa azuzuwa, ai kuwa akace mu dena zuwa se an gyara, dan haka tun aji huɗu furamarai nidai na dena zuwa har yanzu "

Widad tayi shiru, ita ko a tatsuniya bata taɓa jin wannan al'amarin ba, ace a Nigeria akwai 'yan ƙasa wanda basa samun ilimi, ina wakilansu? Meye amfanin shugabannin da suka zaɓa suka wakilta dan suyi musu aiki? Ace ƙauyuka huɗu su dogara da primary ɗaya, kuma shima se sun sha baƙar wahala kafin suje, dole abun ya fita daga ransu'

Widad tace "gaskiya banji daɗi ba Hindu, ai Ilimi shine mutum, tabbas da'a bakin wani naji cewa zanyi ƙarya ne labarine kawai"

Hindu tace "aikuwa gashi a zahiri kinji, shiyasa duk muka haƙura wasu suka kama talla har zuwa lokacin da mace zata samu miji tayi Aure, dama idan kana karatun wasu kallon ɗan iska suke maka, muka koma zuwa ta Allo ta Allonma gata nan dai nidai na samu nayi izu biyar na haddace itama munyi yawa, babu wata kulawa yadda yakamata, dan anan wajejenmu makarantar Allo ɗaya ce"

Widad ta jinjina kai tace" to sauran litattaafai fa, kamar Ahlari, fiqhu hadisan manzon Allah salallahu alaihi wassalam, suma ana koya muku? "

Hindu tace" Taɓɗijan, Al'qur'ani kawai ake koya mana a makarantar Allo, kuma shima mun dena zuwa, se Baffanmu ne dai da yana koya mana Alhadisin Auwwalu, shima yace mana Babansa ne ya koya masa, kuma ma yanzu duk mun manta tunda shekarun da yawa "

Widad kawai tayi tagumi tana sauraren Hindu, tana jin kwamacalar da ko a Film bata taɓa ganin irinta ba, yanzu dama da irin wannan mutanen suna rayuwa a haka, amma ake samun mutanen da suke wawashe dukiyar al'umma, a 'ya' yan sanatoci akwai wanda tasan ana biya musu ku&in makaranta na secondary naira milyan uku, duk term miliyan ɗaya, iya 'yan tsirarin' ya'yansa, amma ga dubunnai zaune a gida babu arabi babu boko, irin wannan ne idan suka faɗa harkar ta'addanci basa imani sam.

Hindu ta kalli Widad tace "ya naga kinyi shiru ne?"

Widad tace "Mhmm bakomai"

Hindu tace "Yawwa, dan Allah meye Firiyas É—in da kika ce?"

Widad tace "Period nace, ina nufin jinin Al'ada"

Hindu tace "Auho ai ban gane ba, seki cemin baƙon wata, ai mu da tsumma mukeyi, mu yayyanka tsumma semu dinga amfani dashi, duk wanda muka cire se mu wanke mu ninke"

Widad ta kalleta da sauri tace "ku wanke me?"

"tsimmar mana, idan É—an kamfan mutum É—aya ma haka ze haÉ—a duk ya wanke, ya É—an jira ya bushe seya sake mayarwa"

Dafe kai Widad tayi, tayi shiru ta shiga duniyar tunani, ta tuna yadda take fantamawa a cikin kuÉ—i, babu abunda ta nema ta rasa a rayuwar ta, Kama daga Abinci, sutura abun hawa gurin kwana, har wasu kuÉ—i ne da ita na musamman wanda take kula da dabbobinta kawai, tayi kyautar mota, tayi kyautar gida ta bada kuÉ—i kamar aikin banza, ashe akwai bayin Allahn da sun fidda rai da samun wani jin daÉ—i.

Hindu tace "Amarya, Allah yasa ba wani abun na miki ba, naga kin ɓata rai?"

Widad tace "bakomai Hindu, mu cigaba da aikin kawai"

Widad bata iya tsinkar zogalen ba, dan haka wani yanayi wani kuma harda kararen jiki take zubawa, Hindu bata damu idan Widad ta zuba a haka se tabi tana gyarawa.

Hanne ce ta taho a fusace tasa hannu ta ɗauke robar da suke tara zogalen tace "Aikin banza, ke Hindu kin san ba abunda ta iya kawai kin ɗauki abu kin bata kinsa se ɓatawa mutane take, tana mayar mana da aiki baya kin zauna se surutan shirme ki keyi, da yanzu an wanke an ɗora amma duk ta ɓata mana"

Hindu tace "Haba Hanne, to ba a hankali zata iya ba, kuma ai tayani take tana yi ina gyarawa, meye a ciki dan munyi tare"

Tsaki Hanne Tayi, tai gaba da robar zogalen, Widad ko É—aga kai ba tayi ba balle ta kalli Hanne, tayi shiru ba tace komai ba.
Chapter 75 · 0% Book details