← Book details Akidata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 82

Sashe 68

Akidata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallonsa take taji meze ƙarasa, maimakon ya ƙarasa se yayi murmushi yace "tashi kije kiyi brush, muci Abinci "

Ta miƙe ta ɗau brush tayi waje, Yusuf ya gyara mata shimfiɗa, ya gyara ɗakin.

Widad ta fita tsakar gida, gwaggo tace "Amarya ina kwana"

Widad tace "lafiya ƙalau"

Gwaggo tace "Alhamdilillah ya ƙarfin jiki?"

"Naji sauƙi"

Gwaggo tace  "to madalla"

Hari ta ƙurowa Widad ido tana so tayi magana, Widad tace 

"idan baki dena kallona ba, sena saka butar hannuna na  ɓallo miki wannan haƙorin da yake leƙowa idan kina magana"

Hari tace "ke hudas kike ko wudas, yau dai ban kulaki ba balle ace na shiga harkarki"

Widad ta Harareta ta wuce banÉ—akinta.

Data fito ta manta da batun Yusuf dake jiranta, ta tsaya gurin da take leƙen zomaye.

Seda tayi me isarta, sannan ta koma É—aki.
seda taga Yusuf sannan ta tuna ashe ita yake jira suci Abinci, yace  "naga kin daɗe?"

Kai tsaye tace "kallon zomaye nayi" , ta ajiye kayan brush ɗinta, tazo ta zauna ta buɗe kwanon farko, dakakken ƙuli ƙuli ne a ciki, ta rufe ta buɗe ɗayan dafaffen dankalin hausa ne a ciki da ɓawonsa da komai manya guda uku.

Ta kalli Yusuf tace "meye wannan?"

"Dankali" ya bata amsa

"kuma a haka? Ta yaya za'aci"

Yusuf yace "ga mahaɗin nan ƙuliƙuli a wannan kwanon"

Widad tace "ta yaya za'aci wannan abun ba tea?"

Yusuf yace  "seki kora da ruwa" yai maganar tare da fara ɓare dankalin.

ta zuba masa ido, ya ɓare tsaf ya yayyanka shi a kwano, ya ɗebo ruwa ya ajiye mata yace  "bismillah"

Tsayawa tayi tana kallonsa kamar wata sokuwa, ya ɗakko ɗaya ya dangwala da ƙuli ƙuli ya kai bakinta, ɗauke kanta tayi tasa hannu ta karɓa tasa a bakinta.

Ba zata ce babu daɗi ba, sedai gurin haɗiyewa ne daƙyar take yi, dan kasa haɗiyewa tayi seda ta haɗa da ruwa.

Dan haka shima ba taci dayawa ba tace ita bazata iya cin wannan abun ba, shaƙe mata wuya yake.

Yusuf ne yaci sauran, sannan yayi mata sallama ya tafi.

Sufyan abun duniya ya dameshi, ya rasa inda ze saka ransa, ba ƙaramin hatsari bane kashe shahararren mutum kamar Daula, amma kowa se saka rayuwarsa yake a hatsari saboda suna taƙamar suna da kuɗi, shiba abun ya kaisu gurin 'yan sanda ba, shi ze kwana a ciki.

Gaba ɗaya daren nan yakasa bacci, sedai juyi dafa da Asuba aka kuma sake kiransa, bashi da zaɓin daya wuce ya amsa wayar.

"baka da isasheshen lokacin ɓatawa gurin aiwatar sa wannan aikin, kana da yau zuwa gobe in Allah ya kaimu ne kawai, idan baka yi ba ni zan aikata maka abunda nace"

Aka katse layin, Doctor Sufyan yayi jifa da wayar ya dafe kai, matarsa ta lura da yana cikin damuwa ta tambaye shi ko lafiya, yace mata babu komai.

Widad bata taɓa shiga damuwa ba, tsawon lokacin data ɗauka tana rayuwar kaɗaici a rayuwarta se wannan karon, tunda Yusuf ya fita be dawo ba taji gaba ɗaya duniyar ta mata faɗi, gashi ita bata saba da kowa ba se shi, seta ji ta wani iri kamar ita kaɗaice a duniyar, koba komai ganin motsinsa yana rage mata damuwa.

Yau wuni guda tana É—aki, ba wanda yake shigowa inda take, saboda bata da fuskar daza'ayi mata hakan, bayan tayi sallar la'asar yunwa ta isheta ta fito tsakar gida.

Gwaggo tace "Amarya lafiya dai ko?"

Widad tace "Naga har yanzu Yusuf be dawo ba kuma ni yunwa nakeji"

Gwaggo tace  "Allah sarki, yau Harice da girki bata aiko miki da Abinci ba kenan"

Widad tace  "kota aiko ba zanci ba, dan ƙazama ce"

Hari dake salla a tsakar gida ko sallamewa ba tayi ba tace "jar'uba kekam anyi mara albarka, nice ƙazamar?"

"Eh kece ƙazama, kalli zanin jikinki kalli faratanki, hijjabin jikinki ma me datti ne, sekiyi abu ki bani inci, an gaya miki komai nake ci?"

Wato Widad sam ta dena ragawa Hari, gwaggo tayi murmushi tace "Yanzu to me zakici?

Widad tayi shiru ba tace komai ba, gwaggo tace  "Akwai Furar megari dana dama, bari in ɗebar miki"

Widad tace "Nagode"

Hari tace "Furar malam É—in zaki É—iba ki bata? Lallai Yaya akwaiki da neman gindin zama"

Widad tace "Eh ita za'a ban, ba zanci Abincinki ba"

Gwaggo dai ba tace komai ba, ta É—ebowa Widad fura a kofin silba ta bata, ta samu guri ta zauna tana sha.

Furar tayi zaƙi zau da zumar da'aka zuba a ciki, tana cikin shan furar can seta miƙe tsaye, gwaggo tace  "kin ƙoshi ne?"

Widad tace  "A'a Yusuf na ragewa"

Hari tace "Ohh ni jikar Hama, ji wata fitsara take cewa ta ragewa mijinta abu"

Wasu matane suka shigo su Uku, É—aya 'yar babba biyu kuma 'yan mata da sallama suka shigo, Hari tace
"Ahh marabanku da dawowa, wai an sha suna"

Ɗayace ta kalli Widad tace  "Hari wace wannan?"

Hari tace  "wasu baƙine mukayi"

Ɗayar tace  "kalleta kamar balarabiya"

Widad bata tanka musu ba ta koma É—akinta.

Sukam bajewa sukayi a tsakar gida, ɗayar itama matar megari ce hansai, se 'yan matan Hindu da Hanne, suma' ya'yansa ne sunje wani ƙauyene, inda 'yar megari take Aure ta haihu.

Se bayan la'asar Yusuf ya dawo gida, kallo É—aya zakayi masa kasan a gajiye yake, ya gaisa da mutanen gidan ya shiga É—akinsu.

Ba sannu da zuwa bakomai Widad tace "Shine kaƙi dawowa se yanzu?"

Yusuf yace yanzun ma tun É—azu na taho, akwai nisane sosai.

Ya ajiye kayan hannunsa, yaje yayi wanka, a É—aki yayi salla saboda gajiya ya nemi guri ya kwanta yayi shiru.

Widad tace  "to ni dai gaskiya ka dinga dawowa da wuri, kawai seka tafi ka barni nikaɗai, gaba ɗaya nagaji"

Yusuf ya kalleta yace "Aikin me kikayi kika gaji?"

"Aikin zama ba abunda nake, ba kowa a É—akin nan seni kaÉ—ai"

"Amma ai da mutane a gidan, seki fita kuyi hira"

"Ni gaskiya dana fita wannan me haƙoran take min rashin mutunci, nikuma ramawa nake"

Yusuf yace  "Kidinga ƙyaleta, kinga babbace ba sa'arki bace ta girmeki"

"da alama ka manta Widad Nasir Daula ce ko?"

Yusuf yace "ya za'ayi na manta nina isa? Yau ba'a kawo komai bane yunwa nake ji"

Widad ta taɓe baki tace "wannan ƙazamarce tayi girki, ni kuma nace ba zamu ciba, shine Mama ta bani furar mijinta"

Buɗe baki Yusuf yayi yace "ba dai ce mata kikayi ƙazama a gabanta ba?"

"idan na gaya mata zata cinye nine?"

Yusuf ya dafe kai, ita Widad a rayuwar ta bata san kara ko alkunya ba sam.

Ta ɗakko kofin furar nan tace  "gashi nasha na rage maka"

Yusuf yace "dagaske ragemin kikayi?"

"is there anything special, dan na rage maka?"

Yusuf yace a"a a ransa kuma yace "lallai kin damu dani"

Yusuf yace  "Naje kasuwa, naga abubuwa ana saye da siyarwa ba laifi, ɗan megari ze aran kuɗi, inga me zan fara siyarwa, ranar daba kasuwa kuma naje wani gurin inga me zanyi"

"to duk meye na wannan wahalar?, naga dai barin gurin nan zamuyi"

"A'a yakamata in koma ciyar dake da kaina, da duk buƙatunki be kamata mucigaba da ɗora musu ɗawainiya ba, nauyinki a kaina yake yanzu"

Kallonsa tayi tace "don't bother yourself, wannan fa ba Aure neba"

"meye inba Aure ba?"

Tace "Shiri mana"

Yace "Ba ruwan Allah da shiri, kuma koda shirin ne aini yakamata in kula da Gimbiya ta"

"karka ƙara cemin gimbiyarka"

Yusuf yayi murmushi yace "Lokacin da muna gida gimbiyar Daddy ce, yanzu kuma da muke nan ba wanda kika sani seni, dan haka gimbiyata ce"

Tsaki tayi ta miƙe daga inda take zaune, Yusuf yace  "Komai naki me kyau ne Widad"

Ko Kallonsa ba tayi ba tayi masa shiru, yace  "ga Alƙawarin da nayi miki, na samo comb da ƙyar a kasuwa, yaushe zamu gyara gashin namu?"

Ficewa tayi daga É—akin ta barshi, shi kuma ya dinga murmushi ganin takaici ya hana ta magana, Yusuf yace da haka da haka gimbiya"

Sufyan fa hankalinsa gaba É—aya ya gama tashi, ya hanga yaga bashi da wata mafita data rage masa banda ya aikata abunda akace, ya haÉ—a allurai a cikin syringe ya zauna ya zuba musu ido, gabansa nata dukan biyar biyar, kiransa akayi a waya, hannun narawa ya É—auka

"Ka shirya aiwatar da aikinne ko kuwa?"

Cikin jan numfashi Sufyan yace  "Eh na shirya"

"shikenan, ina jiran sakamako a yau, ka duba wayarka zakaga Alert É—in kuÉ—i"
Sufyan bece komai ba ya ajiye wayar yana yakice gumi.

Zuwa yanzu Widad ta fara dangana, ta É—an fara sabawa da halin data tsinci kanta a ciki, Cikin dare Widad tana bacci tayi juyi, hasken farin wata ya hasake É—akin, ta hangi Yusuf a zaune akan shimfiÉ—arsa yayi tagumi,
Da alama tunani yake.

A ranta tace  'Ashe shima yana damuwa, amma ya dinga basarwa yace nize hanani kuka'

"wai tunanin mekake?"

Firgigit ya dawo hayyacinsa, yace "idonki biyune?"

"A'a mafarki nake na maka magana"

Yusuf yace "hmm ba tunani nake bafa, cinnaka ne ya cijeni na kasa bacci"

"yaushe ka fara ƙarya?"

"dagaske nake" yai maganar tare da miƙewa ya fita waje, Alwala yaje ya ɗauro yazo ya tada salla, Widad kam baccinta ta koma.

Yusuf yana cikin sallar ne yaji A gigice Widad tace  "Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, wayyo Allah Daddyna"

Ta miƙe da gudu tayi hanyar waje

(Up Up masoya littafin AƘIDATA, Comments ɗinku na matukar ƙayatar dani, shike bani ƙwarin gwiwa nayin posting, Allah ya bar ƙauna 😍 😍 😍)

Share, share and share please 🙏 🙏 🙏
Domin gyara, sharhi ko shawara
Ayshercool
07063065680

         _*AƘIDATA*_
       

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA _
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *

I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum

Haƙƙin Mallaka ⚠ : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

NOT EDITED

ELEGANT ONLINE WRITER'S
Chapter 68 · 0% Book details