Sashe 14
Akidata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yusuf na bakin gate ya bada hankalin sa akan wayar sa, Amal ta fito yana ganin ta yai murmushi tace "Sannu da hutawa"
"Yawwa ranki ya daÉ—e ya gidan?"
"lafiya ƙalau, Widad na nemanka"
"to shikenan muje" ya tashi ya bita har part ɗin Widad, suna shiga Widad ta tsira musu ido, ta sauke idon ta akan Amal ta ƙura mata ido ko ƙyaftawa ba tayi, Sum sum Amal ta fita ta basu guri, zuciyar ta ɗauke da zazzafan kishin barin Yusuf daga shi se Widad a ɗaki.
Widad ta ƙare Yusuf kallo kaman bata sanshi ba kallo ɗaya yayi mata ya ɗauke kai, dogon wando ne a jikin ta da vest ko kunya ba taji a irin shigar data keyi Widad tace "zan fita anjima ƙarfe huɗu zanje gurin birthday, ƙarfe huɗu, in kaga dama ka tafi yawon ka"
Ya jinjina mata kai yace
"Insha Allah zan kiyaye lokacin" daga nan ya fice.
Ƙarfe huɗu saura kwata akayi sallar la'asar, Yusuf ya gabatar da sallar la'asar, sannan ya shiga cikin gidan.
Yana zuwa ya tarar da Alhaji Nasir da iyalan gidan, gefen sa ga trolley alamun tafiya zeyi.
Yusuf yace "barka da rana Yallaɓai"
Alhaji Nasir yace "Yawwa Yusuf ya aikin, ya haƙuri da Daughter"?
Murmushi Yusuf yayi yace "ai mune take haƙuri damu, Aiki kuma Alhamdilillah, mungode Allah"
Alhaji Nasir ya jinjina kai yace "tafiya ta kamani zani Paris, se shagwaba take wai bazan tafi ba, Yusuf ga amana ta nan, na bar amanar daughter na a hannun ka, har inje in dawo kar a bari tayi kuka, idan tana buƙatar wani abun akula ayi mata dan Allah"
Widad da sauri ta kalli mahaifin ta sannan ta kalli Yusuf a wulaƙance tace
"Allah ya kiyaye Ina da komai da nake buƙata, dan haka bana buƙatar taimako daga gurin kowa balle talaka kaman direba na"
Gaba É—aya suka É—auke wuta, shi kansa Alhaji beji daÉ—in abunda Widad É—in ta faÉ—a ba.
Yusuf kuwa yai murmushi yace "indai wannan Amanar ce Alhaji na yadda na karɓa, Insha Allah zaka je lafiya ka dawo ka tarar da ita, Allah ya bani ikon kula da ita"
Alhaji Nasir yace "Ai dama nasani duk me sunan Yaya na mutumin kirki ne, ban taɓa ganin Yusuf wanda ba shi da kirki ba, Allah yayi wa Rayuwar ka Albarka"
Yusuf ya amsa da Ameen
Ita kuwa Maman su Ramla tamkar ta haÉ—iye zuciya, wai direba ake bawa amanar 'yar masu gida, tunda ita cinye ta zata yi ai dole a ce direba ya kula da ita, shikenan direba ya kula da ita in yasan wata ai be san wata ba.
Ba ƙaramin haushi take ji yadda Alhaji Nasir ke nuna wa Yusuf kulawa ba.
Yusuf ya É—aukar wa Alhaji Nasir trolley É—in sa suka fito harabar gidan, Nura ya taho jiki na rawa ya buÉ—ewa Alhaji Nasir bayan mota ya shiga.
Ramlah ce ta taho da nufin itama ta shiga motar ayi rakiyar Alhaji Nasir da ita.
Widad ta kalli Ramlah tace "ba gurin ki a motar nan, dan bama buƙatar rakiyar ki" ta kalli Yusuf tace "shiga gaban motar" .
Nura ya tsaya ya kalli Widad ya kalli Yusuf, Yusuf ma saroro yayi yana kallon Widad, Waidad tace
"ba kaji ba? ko sena maimaita"
Yusuf ya buɗe gaban mota ya zauna, yayin da ita da mahaifin ta suka shiga baya suka zauna.
Nura ya ja mota suka tafi, Ramlah ta rasa me zata yi ne, Mummy tace
"yi haƙuri ƙyalesu, in sun san wata basu san wata ba"
Haka ta rarrashi Ramlah suka wuce cikin gida.
Jefi2 Alhaji Nasir da Widad suke hira, yayin da Yusuf da Nura suka yi shiru kowa da abunda yake saƙawa a ransa
Suna cikin tafiyar ne, Alhaji Nasir yace "daughter na dan Allah ina sake roƙon ki, karki watsamin ƙasa a ido, idan fahad ya dawo ku daidaita, ina son ganin ki cikin farin ciki ne daughter bana son irin wannan rayuwar takura kan da kike yi"
Banza tayi da Daddyn, seda aka ja lokaci sannan tace "Daddy na fara tunanin ka dena sona, idan har kana tunanin yi mun aure ne ze sani farinciki, to tabbas zaka sake jefani ne cikin wata damuwar, kafi kowa sanin meye buri na, Aure ze zama tamkar barrier ne a cimma buri na"
"Daughter yanzu abun nan baze wuce a gurin ki ba? Ba zamuyi haƙuri ba mu barwa Allah, ba zamu yadda komai ya faru damu muƙaddari ne daga Allah ba?"
"Daddy bazan taɓa mantawa ba, kuma bazan yafe ba sena cika buri na, kuma ka dena min batun Auren nan bana so, bazan iya zama a ƙarƙashin wani ba inyi masa biyayya ko waye shi, ku ƙyaleni da zancen Auren nan please bana so"
Ta mirror Yusuf yake ganin Widad yadda Hawaye ya wanke mata fuska, ta rintse ido tana magana cikin kuka.
Alhaji Nasir ya rungume ta a jikin, sa cikin sigar rarrashi yace
"Am sorry my dear, i don't mean to hurt you, nasan tamkar na fama miki wani ciwo ne dake cin zuciyar ki, amma kiyi haƙuri ina ƙoƙarin wanke miki wannan damuwar ne, ina son komai ya wuce kema ki fuskanci rayuwar ki"
"No Daddy i can't, ta yaya zan manta da abunda ya faru, Daddy bazan ƙara yadda da kowa ba, yin aure na tamkar ƙara kusanto da maƙiya jikin mune, ni bazan yadda da kowa ba balle a sake cutar dani a karo na biyu ba, Daddy i repeat my self bana son kowa a kusa dani, bana so" sosai kukan nata yake ƙara ƙarfi harda sheshsheƙa.
"yi haƙuri daughter na, Amma ina sa ran Insha Allah zakiyi alfahari da auren fahad, yana da kirki sosai ɗan uwanki ne, tunda jinin Alhaji Bulama ne, bana tunanin akwai wata cutarwa da Alhaji Bulama ze mana"
Haka nan Yusuf yaji ta bashi tausayi, duk abunda zesa Widad ta sauke wannan izzarta ta, ta dinga irin wannan kukan lallai ba abune ƙarami ba.
Har suka je airport Widad kuka take, har kyawawan idanuwan ta sunyi ja, haka suka yi Sallama da mahaifin ta.
Alhaji Nasir ya dubi Yusuf yace "Yaya na a kulamin da amana ta"
A fusace Widad tace "Daddy karka ƙara cewa ka bar amana ta a hannun wani , ka barni a hannun Allah zaka je ka dawo ka tarar dani lafiya Insha Allah, amma zuwa yanzu yaci ace kayi darasin da bazaka ƙara bawa mutum yadda da Amana ba, narasa me yasa Daddy ka kasa fahimta ta"
Alhaji Nasir yai murmushi ya riƙo hannayen ta yai mata raɗa a kunnen ta, sannan a fili yace "ina da surprise a gare ki idan na dawo, ku koma karku yi dare my lovely"
Haka Widad suka juya zuwa mota, yanzu ma Nura ne ke jan Motar
Widad tace "yi parking anan" Nura ya tsaida motar, tace masa
"gaya masa inda farm house yake"
Nura ya gane abunda take nufi, dan haka yaiwa Yusuf kwatancen inda tace.
Daga nan ta ɗaga idon ta wanda suka jiƙe da hawaye tacewa Nura
"fita ka bar motar nan ka hau ta haya ka koma gida, Kaikuma ka karɓi tuƙin mu tafi"
Nura yace "Amma ranki ya daÉ—e motar Alhaji ce kuma....
"motar Alhaji ta ubanka ce? Ko ta Ubana?" ta jefo masa tambayar
"A'a amma ban fito da kuÉ—i ba"
"Idan ka bari na sake magana, zan ɓata maka rai fiye da tunanin ka, fita daga motar nan nace, idan ba tare muka haɗa kuɗi muka siya ba"
Haka Nura ya fice daga motar, Yusuf ya karɓi tuƙin.
Yusuf ya dinga bin kwatancen da Nura yayi masa, har sukaje gidan gonar Widad bata dena kuka ba, Sam Yusuf yaji beji daÉ—in yadda take kukan ba, gashi ita ba'a iya mata balle ya rarrashe ta
Wani irin tangamemen gida ne har yaso yafi gidan da su Widad ke Rayuwa a ciki girma, Yusuf ya fara tunanin anya wannan gidan gona ne? Horn Yayi aka buɗe masa wani jibgegen gate me matuƙar nauyi ya shiga da Motar cikin gidan.
Ma'aikatan gidan ne suka dinga tahowa cikin matuƙar sauri inda motar su Widad take, Kallon gurin Yusuf yake yi, dabbobi kala kala a ɓangarori daban daban wanda idon sa yake iya gani, gefe kuma gida ne sosai ginanne a ciki, cikin zafin Nama ta fito daga motar tana ta Hawaye, cikin girmamawa ma'aikatan ke zubewa suna gaishe ta, babu wanda ya samu Arziƙin kallo balle ta kula shi.
Cikin matuƙar sauri ta nufi ɓangaren da yake gida ne a cikin gurin, Yusuf ya bita shima cikin sauri, binsu ma'aikatan suka yi da kallo mussman Yusuf, Wani irin murgujejen kare ne fari da baƙi a jikin sa ya nufo inda Widad take yana wani irin gurnani gami da sufa.
Durƙusawa tayi ƙasa Karen yazo yana zagaye Widad yana shanshana jikin ta, shafa gashin karen tayi tana kuka tace "I miss you Miz"
Karen ya kwantar da kansa a jikin Widad yana zaro harshe, ko tsoron sa bataji balle ƙyama.
Haka karen yai lamo a jikin ta tareda ƙurawa Yusuf ido, ita kuma tana cigaba da kuka, can kuma ta shafa kan karen tace
"Excuse me Miz, I will see you later"
Ta miƙe zata yi gaba Yusuf ya bita, Karen nan ya bishi yana masa wani irin haushi da gurnani yana zubar da yawu, Yusuf a ransa yace
"Wane irin jarababben kare ne wannan se kace zaki?"
Widad ta juyo ta kalli karen tace
"don't Worry, I trust him Miz"
Daga nan ta miƙe ta ci gaba da tafiya, Aikuwa tana faɗar hakan karen ya dena bin Yusuf.
Sunyi doguwar tafiya sosai a cikin gidan, dabbobi daban daban wasu daka gansu kasan sun sha banban da kalar namu na Nigeria.
Gida ne sosai a ciki ginanne me matukar kyau, ya tsaru sosai sedai da alama babu mutane a ciki.
Wani ɗaki Widad ta nufa ya bita, suna shiga ɗakin Widad ta ƙara sautin Kukan ta, wani katafaren gado ta nufa ta zube a gaban gadon ta ci gaba da rera kukan ta, daga jin yadda take fidda sautin kukan kasan kuka ne me taɓa zuciya.