← Book details Akidata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 82

Sashe 77

Akidata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da ƙyar ta haɗiye wani irin mugun yawu a wuyan ta, ta koma cikin ɗakinsu tana fesar da numfashin baƙin ciki.

Hindu ce ta Kalle ta tace "Hanne lafiya kuwa?"

Hanne tace "wallahi Hindu na tsani matar Yusuf, ji nake kamar in shaƙeta"

Cike da mamaki Hindu ta kalle ta tace "kamar yaya kin tsane ta?"

Hanne tace "Hindu dan Allah kina ganin Yusuf ze iya Aurena?"

Wani mugun kallo Hindu tayi mata tace "Anya kina kallon kanki a mudubi kuwa? Kina ganin mace jawur, kalle ki kice kina son mijinta, matar nan fa tana miki kawaici akan Mijinta, kiyi ta mata wulaƙanci amma tana ƙyale ki, karki kuskura Gwaggo taji wannan maganar da kike"

Hanne tace "ba zaki gane ba Hindu, wallahi Yusuf ɗin nan yana da kirki sosai, ita ba abunda ta iya se rashin kunya, gata bata da tarbiyya sam gata a wani taɓare, ga tsbar iskanci da rainin hankali, komai se tace bata sani ba"

Hindu tace "A'a wallahi tana da kirki, niba abunda tamin da zan zageta, kije kiyi ke kaÉ—ai, Allah ya yaye miki wahala, dan tabbas yana da wannan matar babu abunda ze dake"

Yau kam Widad ta É—an rage yiwa Widad rashin kunya, dan tare suka ci Abinci saboda tana son ya dinga koya mata aikin gida, dan tana jin zafin gorin da'ake mata, wai bata iya komai ba.

Bayan sallar la'asar Widad ta fito daga É—akinsu, dama gyara É—akin baya mata wahala da gyara gado duk wannan ta iya.

Hari ta hanga a inuwar bishiya tana saƙa mafici, Widad ta ɗakko kujera ta zauna a kusa da ita tace  "Uwata ta kaina"

Hari ta harareta tace "Allah ya kiyaye in haifi 'ya irin ki, na haifi fitinanniya kamarki ai se ince ko sa kamun hannu akayi"

Murmushi Widad tayi tace "ba wannan ba, É—an koyamin wannan abun da kike yi mana, idan na iya se in dinga ta yaki"

"Lallai nasan ba iyawa zakiyi ba"

Widad tace "Allah zan iya"

Hari tace "Keɗin ce zaki iya, taɓ"

Widad tace "ni zaki wulaƙanta dan zaki koyamin abu? Shikenan"

Hansai tace "Amarya ba wahala, nima na iya zan koya miki"

Widad tace "Yawwa ummu Sani, thank you very much, May Allah subhanahu wata'ala bless and unite your Family"

Hari tace "kekam wudas akwaiki da tsirfa, meye hakan kuma kika faÉ—a? Ke ba zaki iya magana ba sekinyi yaren Yahudawa, kiyi ta zagin mutane"

Widad tace "aini kona rasa abun zagi, bazan zageki ba"

Hindu tace "Nidai dan Allah amarya ki koyamin turanci, ina son inga na iya"

Widad tace "Shikenan, zan koya miki insha Allah, amma nima zaki dinga koyamin abunda ban iya ba"

Hindu tace "duk abunda kika ce zan koya miki"

Gwaggo na gefe tana jinsu, tana murmushi, sam Widad bata da girman kai idan bata iya abuba, zata yi ta magiya a koya mata.

Da Yamma aka kawo manyan Ayaba daga gonar megari, aka raba aka bawa kowa, Widad se murna take dan tana son Ayaba, ajiyewa taje tayi a É—aki tace, se Yusuf yazo zasu raba.

Yau Yusuf se gefin magariba ya dawo gidan, ya gaji sosai.
Tunda ya samu ya watsa ruwa ya dawo É—aki ya kwanta, salla ma a gida yayi.

Widad tace "Yoseef ga Banana, an bamu daga gonar megari aka cirota, nace in ka dawo semu raba dan idan na fara ci, bazan iya rage maka ba"

Murmushi yayi yace "bani guda É—aya kawai ta isa, kici Abunki"

Ta ɗan ɓata fuska tace "saboda me bakaci? In ajiye maka abu kace ba zaka ci ba"

"i don't have appetite, that's why"

Ta kalle shi tace "kamar yaya?"

Rungume ta yayi a jikinsa, ya kwantar da kansa a kafaÉ—arta yayi shiru.

Widad ta kalle shi da sauri tace "Subhanallah, ai baka da lafiya jikinka yayi zafi sosai fa"

Yusuf yace "karki damu zan warke insha Allah"

Yana nan rungume da ita, yana ta juya kansa a jikin ta, tana jin yadda jikinsa yake tsuma jikinsa na ƙara ɗaukar zafi.

Widad cike da damuwa tace "Yoseef jikinka zafi yake sake É—auka fa"

Kasa magana yayi, sosai jikinsa yake rawa, da sauri ta miƙe ta ɗakko bargo ta rufa masa.

Haƙoransa se karkarwa sukeyi, ta ɗebo ruwa ta duba kayan ta, ta ɗakko wata vest ɗinta, ta shiga shafa masa ruwa a jikinsa, amma kamar tana ƙara rura masa wuta, jifa tayi da abunda take jiƙa masa jikin ta rungume shi ta fashe da kuka.

Share, share and share please 🙏 🙏

(insha Allah ranar 20th ga wata zan fara posting ɗin book 2&3, befi saura page biyu ba in kammala book 1, nagode ga wanda suka fahimceni, wanda suka zageni ma nagode, wanda suka shirya siya zasu iya tuntuɓata ta wannan lambar 07063065680 nagode ƙwarai dagaske, a nunamin ƙauna ta hanyar siyan littafin akan farashi me rahusa, Akwai garaɓasa ga mutum biyar ɗin farko da suka fara siya, cakwakiya da warwara suna book 2&3 don't missed it guys sena jiku"

Domin gyara sharhi, ko shawara
Ayshercool
07063065680

                      _*AƘIDATA*_
       

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA _
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *

I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum

Haƙƙin Mallaka ⚠ : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends

NOT EDITED  (BANYI EDITING BA)

ELEGANT ONLINE WRITER'S

                         PART1
                                Page 42_43

Sosai Widad ke rusa kuka, Yusuf kasa magana yayi sedai ya ƙanƙameta a jikimsa, yana dukan bayanta da sigar rarrashi.

Can ta miƙe cikin hanzari ta fito waje, tana ta goge Hawaye ta samu Gwaggo tace "Mama Yoseef bashi da lafiya"

A gigice Gwaggo tace "Subhanallah, meya sameshi?"

Maimakon Widad tayi magana seta fashe da kuka, Hanne da take wanke wanke take ta dire kwanukan ta miƙe tsaye.

Gwaggo tace "Yi shiru, muje muga jikin nasa"

Hansai ma da Hari gaba É—aya jikinsu yayi sanyi, É—aki gwaggo tabi Widad ta tarar da Yusuf yana ta karkarwa a cikin bargo.

Gwaggo tace "Subhanallah, sannu Yusufa Allah ya baka lafiya"

Be iya magana ba se jinjina mata kai da yayi, Hari tace "Yaya meya abunyi yanzu, ga  Malam baya nan yaje taronsu na masu sarauta"

Hansai tace "ina sauran saiwoyin nan, a jiƙa a bashi mana, kan malam yazo asan abunda yakamata ayi"

Widad ta koma kusa da Yusuf, tana ci gaba da share Hawaye, Hansai tace "Kidena kuka in Allah ya yadda ze samu lafiya"

Hanne ce ta shigo ɗakin itama, ta leƙa taga yadda Yusuf ke rawar jiki, gaba ɗaya se taji jikin ta yayi sanyi, a ranta tace 'dama wannan kinibabbiyar zazzaɓim ya kama'

Suka dinga rarrashin Widad, yayin da Yusuf ko iya ɗaga kansa ba yayi, Hansai ce ta kawo wasu jiƙe jiƙe wai a bawa Yusuf, Widad ta kalli kwanon ta girgiza kai, cikin kuka tace  "A'a wannan abubuwan suna da hatsari ga lafiya, nidai a kai shi Asibiti kawai"

Hari tace "Asibiti, ai kuwa ya mutu ba'a jeba, dan daga nan kafin aje Asibiti har mutum ya mutu akai gawarsa ba'a isa ba"

Sake rushewa Widad tayi da kuka tace "In Allah ya yadda baze mutu ba, semun koma gida tare, dan Allah Yoseef kaji sauƙi"

Gwaggo tace  "Hari kina da matsala wallahi, wace irin magana ce haka ba tsari, kalli yadda kika sake tayar mata da hankali fa"

Hari tace "Wallahi Yaya ni bada wani abu na faɗa ba, misali dai na bata, amma Wudas kiyi haƙuri, Insha Allah ze warke amma Asibiti kam kafin aje shi sedai idan amalanke za'a samo a ɗorashi, a fita can wajen gari sannan...

Hansai tace" haba Hari, ana rarrashin ta kina ƙara Sakata kuka, Amarya karki damu insha Allah za'a kai shi Asibiti bari Malam yazo "

Widad ta riƙe hannun Yusuf tana ci gaba da kuka, Hanne tace " Sannu Allah ya baka lafiya "

Har magariba sannan megari ya dawo, ya tarar da zancen rashin lafiyar Yusuf, megari yace  " me aka bashi na magani? "

Hansai tace " Na jiƙo tazargade nace a bashi, matarsa tace baza'a bashi ba sedai akai shi Asibiti"

Megari yace "Kin san mutan birni, basu fiye amfani da irin wannan magunguna namu ba, Amma yadda za'a kai Yusuf Asibiti nake ji, kafin Aje ya ƙara galabaita, dan miƙaƙiyar tafiya ce ta gaske"

Widad tace "Yanzu duk garin nan babu Asibiti, ko chemist babu?"

Hindu tace "kamis É—ayane a garin nan, shima a cikin kasuwar yamma da gari yaje, ba'a buÉ—eshi se ranar kasuwa"

Dafe kai Widad tayi tana faÉ—in "Innalillahi wa inna ialaihi raji'un, wane irin abune haka, gari kamar wannan me É—auke da al'umma suna rayuwa a ciki, ace babu gurin shan magani, Yasalam sannu Yoseef Allah ya baka lafiya"

Bece komai ba, se riƙe hannayenta da yayi, da hannu yayi mata nuni da zeyi alwala, Gwaggo ta bada ruwan ɗumi, Widad ta sirka masa, se a ɗaki yayi alwalar dan ko tsakar gida baya iya fita, saboda azabar sanyin da yake ji.

A zaune Yusuf yayi salla, Widad idanunta har sunyi jawur saboda kukan da tayi, ta kalle shi tace "me zaka ci? Kaga tun safe baka ci Abinci ba"

Girgiza mata kai yayi, alamar baya son komai "

Ya nemi guri ze sake kwanciya, Widad tace " kwanciyar nan zata ƙara kashe maka jikine, ka bari gobe in Allah ya kaimu duk yadda za'ayi za'a san yadda za'a kaika Asibiti kaji, sannu Allah ya baka lafiya "

Ta ƙarasa maganar idonta fal hawaye.

Murmushi Yusuf yayi, ya kai hannunsa dake rawa fuskarta ya goge mata hawaye tare da girgiza mata kai, alamar ta dena kuka.
Chapter 77 · 0% Book details