← Book details Akidata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 82

Sashe 11

Akidata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yusuf na barin gurin Murtala me bawa shukoki ruwa yace
"wai kunga abunda na gani ko kuwa?"

Nura yace "mun gani, kai kaga wata irin kwarkwasa da take masa? , anya yarinyar nan Amal ba san shi take ba? Kaga wani iyayi da take yi tana fari da idi"

Murtala yace "Amma kuwa da ta faɗo, duk zuƙa zuƙan Samarin dake zuwa gurin ta? duk iya yin da wulaƙancin nata ta ƙare a direba, wallahi da tayi faɗuwar baƙar tasa"

Isa yace "to ai gara Amal ɗin akan yayar ta Ramla, kun san agola musamman in aka samu guri akwai iskanci, yadda suke hura hanci suna Wulaƙanta mutane kai kace gidan ubansu ne, Amma fa duk da haka gara nasu lafiya ne akan 'yar masu gida wai wa yaga Azaba, idan bata ga dama ba fuskarta idan ka kalla seka yi fitsari a wando, saboda sam bata da rangwame, Azababbiyar Yarinya idonta fiƙi fiƙi kamar me maye"

Nura yace "wallahi ko san haɗa hanya da yarinyar nan bana yi, nagode Allah da yasa ba ita nake tuƙawa ba baban ta nake tuƙawa, ni nayi mamaki ma yadda Yusuf ɗin nan har yanzu basu samu saɓani taci mutuncin sa ba, dan naga wani jin kan sa yake shima, musamman idan yana jan manyan motocin nan se kace na gadon ubansa, kamar har mantawa yake direba ne shi"

Isa ya gyara zama ya waiga sannan ya ƙara ƙasa da muryar sa yace

"ku nifa ban gama yadda da Yusuf ɗin nan ba, kuna ganin sa wani haɗaɗɗe da shi, kullum tsaf tsaf da shi, babu alamar wahala a tare da shi, ga jan aji duk yafi mu kyan gani sannan ace ya ƙare a direba anya babu lauje cikin naɗi a wannan harkar kuwa?"

Murtalah yace "Nima nayi wannan tunanin, amma ya zamu san gaskiyar lamarin? Dan ya fara bani haushi wallahi, yadda megidan nan ya fara wani girmama shi wai yana da sunan yayan sa, har wani Yaya na yake ce masa shi kuma yana washe baki yana sunkuyar da kai, damabidan mutum yavfiye sunkuyar da kai munafuki ne"

Isa yace "ku ƙyale shi zan bugi cikin sani inji ko zamu samu wani bayanin muji, ai duniya seda labari, Amma ina tunanin ta yadda za'ayi kamar wannan da beyi kama da wanda yake cikin wahala ba yazo yana aikin direba"

Yusuf ya ƙudurcewa ransa ze ɗan dinga sakarwa Amal, domin samun sanin wasu abubuwa da suka shige masa duhu game da yanayin tsarin Rayuwar mutanen gidan. Suna tafiya a hanya Amal tace

"Yusuf dan Allah ka dinga haƙuri da abunda Widad take maka, sam abunda tayi maka ɗazu banji daɗi ba wallahi haka take bata san darajar ɗan Adam ba mussman talaka, bata da mutunci, mu kanmu haƙuri kawai muke da ita sam bama jin daɗin zama da ita, shiyasa babu wanda yayi farinciki da dawowarta"

Yusuf da sauri yace "A'a uwa É—akina ce fa ranki ya daÉ—e, ya zaki ce bata da mutunci a gabana? ai bazan ji daÉ—i ba gaskiya banji daÉ—in yadda kika aibata ta ba"

Kallon Yusuf tayi galala cike da mamaki tace "kana nufin baka ji haushin abunda tayi maka bane? Ai ba ƙarya nayi mata ba, da tana da mutunci da bata muzanta maka ba, harta jefe ka da key a fuska ba"

Yusuf yayi murmushi yace "yana da kyau mu dinga girmama doka kafin muyi ƙorafin anci zarafin mu, ko ba'ayi mana adalci ba, da hannu na na saka hannu akan dokokin ta kafin in fara mata aiki, na saka hannu na amince da zanbi sharuɗan data gindaya min, dan haka tunda ni na saɓa abunda na sakawa hannu, komai tayi min be kamata inji haushi ba, ko kuma ince bata da kirki ba, idan nayi haka banyi wa kaina adalci ba"

Amal tayi ajiyar zuciya tace "indai wannan ce kai da kanka zaka dawo daga rakiyar ta saboda wulaƙancin ta, dan wataran seta maka abunda zesa ka tsaneta tamkar mutuwar ka, tun bamu kai haka ba mahaifiyar mu ta auri mahaifin ta muke zaune tare, Amma bamu da daraja ko ƙima a idon ta, kai bamu ba har mahaifiyar mu bata ɗagawa ƙafa, Alhaji Bulama ne ya bada shawarar a bar ƙasar nan da ita, shine ma muka samu muka huta na wasu shekaru kafin ta dawo, se a dinga fakewa da bata da lafiya, tana taka mutane tana nuna isa da Izza"

Yusuf yace "bata da lafiya kuma? Kamar ya bata da lafiya, Meke damun ta?"

Ɗan taɓe baki Amal tayi tace "wai bata da lafiyar ƙwaƙwalwa, ko da yake me lafiyar ƙwaƙwalwa baze abunda take ba, wannan dukiyar ta mahaifin ta, da ita take taƙama da ita take wulaƙanta mutane, ta yaga duk wanda yayi mata abunda yake saɓanin raa'yin ta, aikin banza, dukiyar da'ake farautar ranta akanta, Amma take da damar Wulaƙanta mutane saboda ita"

Da sauri Yusuf yace "kamar ya farautar rai? Ranwa ake farauta, saboda dukiya?"

"Ran Widad ɗin mana, yana ɗaya daga cikin dalilin da yasa ta bar ƙasar nan fa, bayan larurar Ƙwaƙwalwa da take dashi ana farautar ranta ne, tunda maman ta ta rasu take fama da larurar ƙwaƙwalwa, kuma a kazo ana nema a kashe ta, abundai gashi nan, Amma kodan wulaƙanta mutane da take dole wani yai ƙudurin kashe ta ya huce takaicinsa, bayan wulaƙancin da take wa mutane, har ɗaure mutane take sa ayi"

Jinjina kai Yusuf yayi yana kuma nazarin maganganun Amal, baya so ya cika ta da tambayoyi, karta fuskanci wani abu dan haka yayi shiru yana É—an satar kallon Amal yana tunani a ransa.

Yusuf ya kai Amal wani katafaren mall kaman yadda ta buƙata ta dinga ɗibar kaya, sannan tace Yusuf ya ɗauki abunda ya keso.
"A'a nagode amma ni bana buƙatar komai"
Amal tace "haba Yusuf dan Allah ka É—auka, karka ji komai"
Fafur Yusuf yaƙi yadda ya ɗau komai se haƙura tayi.

Bayan sun dawo gida tace dan Allah ya taya ta ɗaukar kayan da ta siyo, babu musu ya ɗau kayan yabi bayan ta kamar yadda suke da Widad, Sedai tun a babban falon ƙasa suka ci karo da hakimar ƙafar ta ɗaya kan ɗaya tana shan tea, gefen ta kuma tana bawa magenta madara, bata kula su ba su kayi gaba za su wuce, muryar ta suka jiyo tace

"Stop there" ta faÉ—a kai tsaye cikin bada umarni, gaba É—aya suka tsaya suna jiran me za tace.

Se da ta ja wasu seconds sannan tace

"Amal yaushe muka fara sharing ɗin abu nida ke ne ban sani ba? Ya akayi matsayinki har ya kai kiyi amfani da abina ba tare da kin nemi izini na ba?" tai maganar tare da miƙewa tsaye, tavtako ta zo har inda suke tsaye ta kalli Amal, ta tsaida dubanta kan Amal, Amma tace wa Yusu

"waye ya É—auke ka aiki a cikin gidan nan?"

"kece ranki ya daÉ—e" ya faÉ—a cikin girmamawa

"Wa kayi wa aiki yanzu?" tai maganar me cike da bayyanar da tsantsar Izzar ta

" 'yar uwarki ranki ya daÉ—e" ya bata amsa

Ta ɗan lumshe ido sannan ta buɗe tace "Na taɓa gaya maka ina da ɗan uwan ko' yar uwa ne?"

"A'a"

"lokacin dana É—auke ka aiki na gaya maka nida wani zakayiwa aiki?"

"A'a" ya sake bata amsa

Ta maida idon ta kan Yusuf cikin É—aga sauti tace

"Ka karyamin doka karo na biyu da wani suna ya kamata in kira kane? Bagidajen ina ne kai? Ko kuma ince daga wani jejin kake? a haka you look civilized amma kwata2 shashasha ne kai, hala ka manta akan death contract kayi signing? Inaga ka manta ne, ko kuma ka É—auka wasa ne shiyasa kake wasa da rayuwar ka"

Ya girgiza mata kai alamar A'a

Hayaniyar da Hajiya Halima take ji sama sama ne ya sa ta fito ita da ramlah suka tsaya suka yi cirko cirko a falon Widad tana ta zuba tsiyata kunta san ranta.

Widad tace "Yanzu ina maka hukunci se ka kirani azzaluma ko? Saboda haka ɗabi'ar ku ta matsiyatan mutane take, ku kullum akan daidai kuke masu kuɗi kuma Azzalumi ko?, dukda bana maimaita magana yau zaka sani na maimaita, Ni Widad ban yadda da kowa ba, duk yadda muke da mutum karyamin dokoki na daidai suke da yunƙurin cin amana ta, kuma penalty ɗin wanda yaci amana ta, bana jin tantirin talaka wanda bashi da komai kamar ka ze iya ɗauka "

Amal tace " haba Widad be kama......

Ɗaga mata hannu Widad tayi ba tare da ta kalli Amal ba tace "har yanzu 'yar alfarma ce ke a cikin gidan nan, matsayinki be kai na 'yar masu gida ba, karki ƙara gangancin ina magana ki katseni ko kisamin baki, idan ba haka ba kin san sauran, kai kuma daga yau nikaɗai kake wa aiki a cikin gidan nan, ban yadda wani ya saka aiki kayi ba, duk wanda yace kai wani abu kace Widad kake wa aiki ba wani ba, sannan kayi a rabin salary ɗinka shine hukuncin karya min doka da kayi har sau biyu dismiss from here"

Yusuf ya risina ya ɗanyi murmushi yace "godiya nake uwaɗakina, Allah ya ƙara girma Insha Allah zanyi ƙoƙari in kiyaye dokokin ki, bazan ƙara karya miki doka ba, Allah ya huci zuciyar ki"

Gaba É—aya suka bi Yusuf da kallo wato shi duk wannan cin zarafin da aka yi masa godiya yayi, lallai wani talakan Jaki ne, besan ciwon kansa ba, Ramlah ta faÉ—a a ranta.

Widad ta kallesu ɗaya bayan ɗaya tace "bana buƙatar kowa a falon nan, madam zaki iya jan zugarki ku ɓace min daga nan"

Saboda tsabar baƙinciki da takaici Amal watsi tayi da kayan shopping ɗin da tayi a falon, tai cikin part ɗinsu da gudu tana kuka, abun yayi yawa taji zafin cin mutuncin da akayiwa Yusuf ga tsabar wulaƙanci da suke fuskanta a gidan nan se kace Almajirai, kokuma wasu bayi.

Ramlah ta kalli mahaifiyar su tace
"Mummy am tired wallahi enough is enough are we slaves? see how this little baby is shouting at both of us including you, Mummy you have to do something"
Kafin Mummy tayi magana Amal ta shigo tana kuka.

Mummy tace "Amal meya saki kuka?"
Chapter 11 · 0% Book details