← Book details Akidata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 82

Sashe 82

Akidata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

" Kaga sauraramin dan Allah, bana son maganar banza data wofi, na sani ka sani Anwar baze iya aikata laifin da ake tuhumarsa ba"

"A'a karki  shedeshi, ba'a shedar ɗa a zamanin nan"

"Bulama, na gama magana da kai, zanje inyi abunda ya dace kawai"

Bulama yace "abunda ya dace kamar yaya?"

"Ka zuba ido zaka gani, bar ganin kai É—an uwanane zan iya yin komai akan É—ana, na gaya maka"

Bulama yace "hmm kibi a sannu dai, kin san ido ya fara dawowa kanki yadda kike wadaƙa da wasu daga cikin kadarorin mijinki? Mutane sun san me kike aikatawa, ki sani tsalle ɗaya ke kai mutum rijiya, amma se yayi dubu be fito ba"

Tsaki tayi, ta É—au mukullin motarta tace "wannan kuma kai ta shafa bani ba, nasan abunda nakeyi"

Tai waje abunta, tana fita Bulama ya ɗau waya, ya danna yasa a kunnensa yayi shiru, can kuma yace "Yawwa kana jina da kyau, ina son ku ƙara tsananta tsaro da sa ido akan yaron nan Anwar, under no circumstances zaku bada belinsa, ku matsa se ya faɗi inda Daula yake, dan uwarsa ba abunda ba zata iya ba"

Daga cam ɓangaren yace "Ok sir an gama Insha Allah"

Bayan barin Hajiya Halima Office É—in Alhaji Musa, su Alhaji Haruna suka dira, dukda haushinsu da Musa yake ji, amma ya maze ya sakar musu fuska yace "kun san yanzun nan wannan mahaukaciyar ta bar gurin nan"

Alhaji Haruna yace "wa kenan?"

"Hajiya Halima mana, tazo nan tana ta banbami, wai munƙi saka baki a sakar mata ɗa"

Alhaji Munir yace "ƙyale wannan mahaukaciyar, ni wata shawara nazo mana da ita"

Suka tattara masa hankalinsu, suna saurarensa  "Abunda nake gani shine, mu samu lauyoyin Daula, mu siye su, su saka hannu su fitar mana da wasu daga kadororinsa, a sasu a kasuwa a karya su, sannan ayi takaddun ƙarya, muce muna binsa zunzurtun bashi"

Alhaji Haruna yace "kayi magana mekyau, sedai abunda ka manta shine, lawayoyinsa basu san kan dukiyarsa kamar yadda wannan koÉ—aÉ—iyar 'yar ta sani ba, ta san komai tasan inda komai yake"

Alhaji Munir yace "to tunda yanzu ba ita babu ubanta aise muyi yadda zamuyi mu kwashi rabonmu, ko so kuke se wannan mahaukaciyar matar tasa ta ƙarar da komai ita da' ya'yanta? A ɓoye fa se saida kadarorinsa sukeyi, haka zamu zauna mu zuba ido."

Alhaji Musa ya nisa yace "duk naji ta bakin ku, kuma kowa yazo da magana me kyau, zamu jarraba lawyoyin suma, danni yanzu kuÉ—in tsayawa takara nake nema"

Kallonsa sukayi gaba É—aya sukace "kamar ya tsayawa takara?"

"kamar yadda na gaya muku, bazan zauna bani ga tsuntsu bani da tarko ba"

Alhaji Haruna yace "hala ka manta da baƙin fentin da kake da shi, a dalilin Daula?"

"ina fa na manta, sedai a ƙasar nan indai kana da kuɗi ba abunda baze yuwu ba"

"Amma baka ganin hakan, ya saɓa da Yarjejeniyar mu, idan kayi haka kamar ka zame daga cikinmu ne, kuma me zaka cewa Bukar?"

"Bukar ubanane, ko haifata yayi? Ba gudu ba ja da baya, ina tare da ku amma tabbas zanyi takara"

Gaba ɗaya Yusuf ya fara jin kunyar mutanen da yake ja salla, musamman idan ya tuna abunda Widad tayi a gaban su, tunda su hakan kamar baƙon al'amarine a gare su, haka nan ya ɗan dinga basarwa, sukayi sallar magariba da isha'i suna ta sake duba shi.

Widad jin shiru Yusuf be shigo ba, yasa ta fito tsakar gida ta samu wani ɗan gidan Hansai tace masa  "kaga ɗan jeka waje ka cewa Yoseef in jini nace, baze dawo ba se sauron ya sake cizonsa yazo ya kwantamin?"

Gwaggo dake alwala tace "A'a kul kaje ka faɗi haka, kace tace  'dan Allah ya shigo gida, kar sauro ya kuma cizonsa'"

Widad tace "to ai kusan abunda na faÉ—a kika maimaita"

Gwaggo tace "A'a ke naki umarni da kashedi kika yi, aishi miji abun lallaɓawane da tattalawa, ki kalli yadda kika damu da bashi da lafiya, ki dinga masa magana da girmamawa kinji Amarya, yana da kirki mijinki, kema ki dinga tausasa harshen ki a kansa"

Widad tace "To Hajiya Mama"

Gwaggo tace "ni  a Hajiya, to me rai baya fidda rai da rahama, amma abun da wuya"

"Insha Allah indai da rai da rabo, zaki je saudi Arabia in dai Allah be ɗau rayuwar wani daga cikin mu ba, idan muka koma gida lafiya zaki je ƙasa me tsarki"

Tsaki Hanne tayi tace "san a sani, ji wata ƙarya kuma da son nuna iyawa, karma kisa rai ana gayamiki gaibu"

"Ke! Ki kiyayeni, dake muke taÉ—in, ina ruwan ki Hanne ki kiyayeni fa"

Widad ta juya kawai ta koma ɗaki, ta ɗakko ƙaramar fitilarsu ta kunna, batirin ma ya fara sanyi.

Ta zauna tayi shiru tana tunani, sallamar Yusuf ce tasa ta É—ago ta amsa masa, yaje kusa da ita ya zauna, daya kalleta se tausayinta ya kama shi yace "gani naji ance kina nemana"

"shine tun la'asar kaƙi dawowa, se sauro ya kuma cizonka ko?"

"Ai na warke, Alhamdilillah"
"dan ka warke shine se kaje, ka kuma kwaso wani zazzaɓin, kazo ka ɗagamin hankali"

"Insha Allah na warware ai, ance jinina ma yayi ƙasa, dole in dinga cin ganyayyaki"

"Sannu kaji jiki ai"

"Gaskiya muje ki dawomin da jinina dana baki"

"wai jininsa, jinin naka ma duk malaria ya ƙara samun zazzaɓi, zan biya ka jinin ka harda riba ma"

Dariya Yusuf yayi yace "ni iya nawa nake so, bana son naki danni bana son jinin me taurin kai"

"kai kai, nice me taurin kai? Zaka ga taurin kai'

Kwanciya yayi a kafaÉ—arta yace " dan Allah a sake rungumeni mana, i need your body warm "

Ture shi tayi tace 'kaje kaji É—umin bargo mana"

Cikin kwantar da kai yace "A' a ni gaskiya naki nake so, ai naga yau ke kika rungumeni, idan muka koma gida sena gayawa Ummana, nima ince kina rungumeni"

Widad tace "ai kai ka fara bani ba, ka koyamin abunda ban iya ba"

Dariya Yusuf yayi yace "nayi mamakin yadda kika damu da rashin lafiya ta My queen"

"A cikin AƘIDATA babu butulci, bana manta alkhairi, bazan taɓa manta wahalar daka sha saboda rayuwa ta ba, idan na nuna halin ko in kula ga kafiyarka to tabbas banwa kaina adalci ba, dukda ana faɗin bani da kirki, banj da mutunci amma bana manta alkhairi"

Yusuf yace "waye yace miki baki da kirki, kina da kirki uwaÉ—akina"

"Hmm yoseef kenan, ka dena kareni danka burgeni, amma nasan bani da kirki kamar yadda da yawa mutane ke faÉ—a"

"ba kareki nake dan na burgeki ba, ina faÉ—a miki gaskiya ne kawai, amma kince bakya manta alkhairi, amma meyasa bakwa jituwa da Saleh, dukda irin taimakonmi da yayi?"

"saboda bana yafiya ga mutane ma'abota fuska biyu, da fari mahaifina ya yarda da shi da ɗam uwansa, amma ya koma ɓangaren maƙiyanmu, yanzu ya kuma dawowa ɓangaren mu, wani tabbaci muke dashi na muma baze sake juya mana baya ba? Duk yardar da nayiwa mutum, duk girman Alkhairin da yayumin, muddin yaci amanata koya min ƙarya to tabbas ze shafe dukkan alkhairansa a idona, bana yafewa mayaudari da maƙaryaci ko me fuska biyu, wannan itace AƘIDATA!!!

TOFA! Alhamdilillah nan na kawo ƙarshen kashi na ɗaya a littafin AƘIDATA,

ÆŠanÉ—ano daga Littafi na biyu

(idanunta sunyi jawur, kamar wadda aka zubawa barkono saboda kuka, ta sunkuyaf da kanta ta shafi ciknta, cikin zubda hawaye tace "wace amsa zan bawa abunda yake cikina, idan har ya girma ya samu labarin mahaifiyarsa taje kotu ta bada sheda akan mahaifinsa an kai shi prison, kaicona haɗuwa ta da Yusuf ta zame masa babbar ƙaddara a rayuwarsa, ya sadaukar da rayuwarsa don in ganta tawa, amma maƙiyana sun na ƙoƙarin cin galaba akanmu, abun da basu sani ba shine...............)

Karku bari a baku labari, saƙar labarin mukayi a na farko, tufaka da warwarar gami da cakwakiyar suna littafi na biyu dana uku, anan gwaramar take

SHINE MEYE LABARIN YUSUF?
MEYE LABARIN WIDAD?
WAYE MAMALLAKIN ABUNDA AKE NEMA A HANNUN WIDAD?
MEYE ABUNDA AKE NEMAN?
WAYE YA SACE DAULA?
SHIN ZASU BARO ƘAUYEN NAN?
ZASU KOMA GIDA DA WANNAN AUREN?
YA ZATA KAYA TSAKANIN WANNAN MANYAN ALHAZAI?
YA WIDAD ZATA YI IDAN TA GANE YUSUF JAMI'IN TSARO NE YA MATA ƘARYA?

Akwai cakwakiya me tarin yawa karku bari a baku labari, ga masu buƙatar siya

Normal group duka littafi biyun ₦300
Idan kuma ɗaya zaki siya ₦200

VIP ₦ 500

Inkuma sena gama zaki sai complete document ₦700

Account Number
Aisha Adam
0009450228
Ja'iz Bank

Ko katin MTN banda VTU please
A turo evidence of payment ta 07063065680

Zan fara posting É—in littafi na biyu dana uku, ranar 20 ga watan October

Masu neman complete zasu sameshi ranar biyar ga watan November insha Allah

Domin gyara, sharhi ko shawara
Ayshercool. 07063065680

Nagode da ƙaunar da kuka nunamin
Chapter 82 · 0% Book details