← Book details Akidata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 82

Sashe 21

Akidata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amal ta zumɓura baki tace "kaga ni karɓi kayan nan, kalli yadda take wani riƙe ka aikin banza kawai"

Widad ta shammace ta, tasa hannu ta kifar da farantin ruwan zafin, aikuwa ya zube a ƙafar Amal, Ihu Amal ta saki, wanda ya janyo hankalin Mahaifiyar ta da Ramlah suka taho da sauri.

Idan ba gizo idon Yusuf yake masa ba, tabbas kamar ragowar ƙwayar magani ya gani a ƙasan kofin da'aka zuba tea ɗin, sedai kafin yayi wani yuƙuri

Hajiya Halima taƙarsaso tana cewa  "lafiya, meye haka?"

Cikin kuka da azaba  Amal tace "Mummy, Widad ta ƙonani da ruwan zafi, Mummy ƙafata"

Mummy ta kalli inda Yusuf ke tsaye, Widad na riƙe da shi tace 

"To maye Jarababbe, ka lallaɓa ka Asirce ta ita da uban ta, shine ka koma da baya zaka illatamin 'ya ko? Wallahi ka kiyayeni, kuma kafin kasa kwaɓata tayi ruwa ni zanyi maganin ka, ke kuma" ta nuna Widad dake bayan Yusuf tace
"dan Ubanki ba dai hauka ba, a haka zaki ƙare, Hauka yanzu kika fara shi, daga nan har ƙarshen rayuwar ki, keda hankali sedai ki ganshi a gurin wasu, wannan haukan haka zaki mutu kina yinsa"

Widad ta Jijjiga Yusuf tace  "kai ka gaya musu niba mahaukaciya bace, kuma wallahi idan ta kasheni itama sena kashe ta, gaba ɗayansu sune zasu kasheni, suna tace min mahaukaciya zasu kasheni, wallahi in baka hana su ba ni zan kashe su"

Ramla tace "kaga Malam dalla cikata kazo ka bar gidan nan, tunda babu gadon ka a ciki, ba'a haÉ—a kuÉ—i da matsiyacin uban ka an gina ba"

Wani irin kallo Widad takewa Ramla daga bayan Yusuf.
Kallon da Widad kewa Ramla ne yasa taga kamar Widad ta dawo hankalin ta.

Widad tace  "idan ka tafi ka barni kasheni za suyi, kashe mutane suke yi fa"

Mummy tace  "uwarwa muka kashe miki? Mu bama kisa kumako bamu kashe ki ba mutanen da kike Wulaƙantawa suna nan suna bibiyar ki zasu kashe ki, Mahaukaciyar banza da ta wofi, Allah kaɗai yasan me sukeyi da harta yarda da shi haka, dalla kuzo mu tafi suje su ƙarata, Allah ya ƙara birkita ƙwaƙwalwar ki zauna a haka koma samu mu huta, in ƙwaƙwalwar ki ta birki ce ta Ubanki ma ta birkice kowa ya huta da iskancin ki"

Ramla tace " Mummy watch your words fa, kina ta sakin layi mu tafi kema Amal Allah ya ƙara, maganinki kina ma wannan ɗan isakan direban shisshigi, gashi ai sun ƙonaki a banza nan gaba ma illataki zasuyi"

Shiru Yusuf yayi yabi bayan su da kallo, gaba É—aya tausayin Widad da Mahaifinta ya kama shi.

Ya lallaɓa Widad ya bata youghurt da ƙyar ta sha, tana sha tana masa surutai na shirme, irin na masu taɓin hankali.

"Menene dalilin samun taɓun hankalin Widad?" Yusuf ya tambayi kansa

Kwanciya tayi a jikin sa tana lumshe ido alamar bacci take ji, ƙirjin Yusuf se bugun uku uku yake, Kasancewar ya keɓance da Widad, abunda be taɓa yi ba, a duk lokacin da yayi yunƙurin rabata da jikin sa seta saka ihu kamar ƙaramar yarinya.

Yusuf yayi mamakin iri maganganun da Hajiya Halima da 'ya' yanta suka dinga faɗa akan Widad, koda yake ba abun mamaki bane, duba da Yadda Widad ɗin ke Wulaƙanta su, Amma me sukayi mata take musu haka? " Yusuf yayi Alwashin tone duk wani abubuwa da ake ɓoyewa, kuma ya ƙudurce a ransa zeyi duk me yuwuwa ya jure wulaƙancin Widad yaga ta ina ze temaki rayuwar ta.

Yusuf yai shiru yayi zurfi a cikin tunani, yaji Widad tana ajiyar zuciya alamun tayi bacci, a hankali ya zame ta daga jikin sa, ya kwantar da ita ya lulluɓeta ya fita ya kulle ta a ɗakin yaje yai salla.

Ana idar da Salla Isa yace " Yusuf ashe uwar ɗakinka ce babu lafiya? Ance taƙi buɗewa kowa ƙofa amma tana jin muryar ka ta buɗe, gaskiya kai ɗan baiwa ne, Amma naji ance haukan nata ne ya tashi ko?"

Yusuf ji yayi kamar ya kwaɗawa Isa mari, Amma ya ƙyaleshi ba tare da yace masa komai ba.

Ya koma É—akin nata ya tarar bata farka daga baccin ba.

Falon ta ya koma yana tunani, Ba zato ba tsammani yaji sallamar Mahaifin Widad a falon, Amsawa Yusuf yayi cikin girmamawa tare da risinawa.

Alhaji Nasir a É—an ruÉ—e yace "Sannu babban Mutum, ya me jikin kuma?"

"Alhamdilillah, ta samu bacci"

"Masha Allah"

Yasa kai ya shiga bedroom É—in, ya taka a hankali zuwa gaban gadon Widad ya zauna a gefen ta ya É—agota, idon ta a rufe tana bacci, ya shafa kanta yace
"Allah ya baki lafiya my daughter" ya kalli Yusuf yace  "Nayi mamaki data iya yadda da kai, idan ciwon nan ya tayar mata bata yadda da kowa seni, ko Bulama wani lokacin muɗinma bata yadda damu gaba ɗaya se an mata allurai"

Yusuf yace  "Wane irin ciwo ne haka?"

Alhaji Nasir ya ɗan na Numfashi cike da damuwa yace 
"Yusuf, nasan mutane da yawa suna mata kallon bata da kirki, wasu suna zargina da barin 'yata ta lalace, kawai ina kallon sune, ba tare da nace wa kowa komai ba, Yusuf Widad ita kaÉ—aice' yata dana mallaka, larurar nan ta same ta ne sakamakon kashe mahaifiyar ta akan idon ta"

Zaro ido Yusuf yayi yace  "Innalillahi wa inna ialaihi raji'un"
Alhaji Nasir ya jinjina kai yace  "ƙwarai kuwa, Akwai abunda ya faru da Widad, wanda tun daga lokacin take gudun mutane, ta haɗu da larurar ƙwaƙwalwa, dukda partially ne larurar tata da farko, Amma daga depression ya zarce mata ta samu Arthropophobia,
larurar ƙwaƙwalwa me sa mutum ya dinga jin tsoron mutane, ba mutane ba wani lokacin idan tana cikin larurar ko haske bata so, muna ta magani Sedai har yanzu na gaza samun abunda zesa ta farinciki, kana gani ko fara'ar kirki ba tayi, na yanke shawarar in mata Aure amma tace bata so, dan Allah Yusuf na san kana haƙuri haka nan naji ka kwantamin, dan Allah ka tayani Addu'a, Allah ya bawa 'yata lafiya, ita kaɗai nake da ita, ba uwa ba uba"

Gaba ɗaya tausayin Alhaji Nasir da' yar sa suka cika shi, Yusuf ya numfasa yace  "Insha Allah Alhaji, Amma ba kayi......

"Yallaɓai ya akayi harka shigo ban sani ba? muna can part ɗina muna fafutukar a kira likita yazo ya duba ta, gaba ɗaya yau kwana mukayi ba muyi bacci ba saboda yadda jikin Widad ya rikice, ko Abinci ba wanda ya iya ci yanzu ma mun shiga muyi salla ne ka dawo ban sani ba" Hajiya Halima ke wannan maganar cike da salon bariki da Kissa.

Alhaji Nasir yace "Allah sarki, nasan kina ƙoƙari akan Yarinyar nan, Allah ya saka miki da Alkhairi, ina su Baby Amal ɗinne ko basu san na dawo ba?"

"Amal ma bata jin daɗi, Ramla kuma salla take, ina jiran Widad ta farka ne a bata Abinci, mun samu da ƙyar tayi bacci"

Yusuf kam bin Hajiya Halima yayi da kallo, yana mamakin wannan iya salon barikanci nata, gaba É—aya ta juye kamar tana cikin damuwar gaske.

Yusuf yace "Bari inje gida Alhaji tunda ka dawo"

"Shikenan Yusuf ka gaida gida, nagode sosai Allah yasaka da alkhairi"

"A'a bakomai Yallaɓai" Yusuf yasa kai ya fice, Hajiya Halima tabi bayan sa da harara.

Kan Yusuf ya ƙara ɗaurewa da maganganun da Alhaji Nasir ya gaya masa, yana daf da fita kawai yaga Ramla ta sha gaban sa.
Tsayawa yayi yana kallon ta, ta kalle shi cikin Isa tace
"Bani mukullayen Motar Widad dana É—akin ta dake gurin ka"
Yusuf ya tsuke Fuska yace
"É—an bani hanya zan wuce mana"
"Ni kake kallo kakewa wannan gadarar haka? Zaka bani ko sena maka rashin mutunci?"
"bake kika bani ba, ba kuma ke nakewa aiki ba, dan haka babu ruwan ki dani"
"Kai kalli tsabar Idona, karka kuskura kace zakayi Jayayya dani, naga se wani shisshigi kake kana cusa kai a gurin waccan Mahaukaciyar da ita da Ubanta, to bari kaji in gaya maka, idan ma wani abu kake kwaɗayin samu wallahi ba zaka samu ba, Kuma hauka yanzu Widad ta fara shi daga nan har ƙarshen Rayuwar ta, ba zata sake moruwa ba, gara ka cire wa kanka ƙwalamar wannan daular da dukiyar, yadda kazo a talaka haka zaka koma a matsiyaci, idan kaga dama kaje ka faɗawa duk wanda zaka faɗawa, shawara ta ƙarshe da zan iya baka itace, ka gaggauta Ajiye aikin nan ka ƙara gaba ya fiye maka Alkhairi akan wasa da rayuwar ka"

Murmushi Yusuf yayi ya dubi Ramla yace  "in kinga na bar aiki a gidan nan wanda nakewa aikin ne suka sallameni, kina wani iƙrarin dukiya, dukiya nawace taki a dukiyar nan? Ki kiyayi Yusuf, matsi da takura babu wanda Yusuf be gani ba a rayuwar sa, dan haka ƙaramar barazana irin taki ba zata hanani Aiki na ba, ni babu ruwana da rayuwar da kuke a cikin gidan nan ni aikina kawai nasani, ban guri in wuce ko in hankaɗeki"
Galala tabi Yusuf da kallo, da ma akwai Yadda yake mata magana cikin Izza shima, Me yasa ba yayiwa Widad da take Wulaƙanta shi, lallai maganar Mummy gaskiya ce, ya kamata ayi maganin Yusuf.

Yusuf fa kai ya sake ɗaukar wuta, abun da ya faru yau, ya ƙara tabbatarwa Yusuf akwai wani mugun nufi a zuciyar Hajiya Halima da 'ya' yanta.
Umman Yusuf ta lura da yanayin Yusuf ko iya sakewa yaci Abinci ba yayi, Umma ta kalle shi tace
"Yusuf wai meke damunka ne haka? Naga gaba É—aya kwanan nan na kasa gane kanka, Allah yasa ba wani abun aka kuma yi maka ba?"

"Umma ni a rayuwa ta wani irin ƙalubale ne ban gani ba? Aini lamarin rayuwa ta na miƙawa Allah, aikin da aka bani ne me matuƙar rikitarwa"

Nan ya kwashe komai ya gayawa Umman sa, Umms tayi shiru na wasu 'yan mintuna sannan tace
"lallai wannan lamarine me sarƙaƙiya, nidai fatana ka kula da kanka Yusuf, kayi taka tsan tsan ka cigaba da Addu'a, Amma waye yazo ya nemi da a dinga bawa ita Yarinyar kariya?"

Shiruu Yusuf yayi sannan ya girgiza kai yace  "Wallahi Umma ban sani ba"
Chapter 21 · 0% Book details