← Book details Akidata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 82

Sashe 27

Akidata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A ranta tace 'dama suma talakawa suna jin wannan shauƙin da ƙaunar na iyaye, inama Ammi na tana raye nima in kwanta a jikin ta in ji daɗi'
Ba tayi aune ba taji hawayen da bata shirya zubowarsu ba. Cire glass É—in fuskarta tayi tana goge hawayen idon ta, katse wayar Yusuf yayi ya kalleta yace
"lafiya dai?"
"Lafiya cigaba da tuƙinka, ina so muje gurin nan kafin 5"
Ya jinjina kai ya ci gaba da tuƙin, wani katafaren hotel ne, motocine suke shiga suna fita a ciki, kowa harkar gaban sa yake yi, sedai mafi akasari kallo ɗaya zakayi wa mafi yawa daga mutanen dake shiga suna fita, ka gano rashin tarbiyya da ta ido a tattare dasu, musamman matan duba da yanayin irin shigar dake jikin su.

Yusuf yayi parking yana kallon Widad, ta buɗe motar ta tsaya tana ƙarewa harabar hotel ɗin kallo.
Da sauri Yusuf ya fito daga motar yana kallon ta, ta dubeshi tace  "wait for me here"
ta sa kai da nufin shiga cikin hotel ɗin, da yawa mazan dake gurin nan hankalinsu ya dawo kanta, Widad ta haɗu iya haɗuwa, wani takaici ne ya kama Yusuf, ace 'yar musulmi ce da wannan shigar a wannan gurɓataccen gurin.
Bin bayanta ya kuma yi da sauri, ta tsaya ta kalle shi tace 
"I said you should wait me inside the car, don't let anyone to see you here, don't tarnish your image because of me"
Ta sake juyawa, ba zato cikin zafin nama da zafin rai Yusuf ya riƙo Widad gaba ɗaya zuciyar su ta buga a tare, Yusuf ya kalli cikin idon ta yace
"Guri irin wannan be dace da mace me daraja kamar ki ba, Mahaifinki babban mutum ne be kamata aga 'yarsa a irin wannan gurin ba, ke mace ce kuma me daraja bekamata kowane gara ya dinga kallon surar jikin ki haka ba, think about it"
Nutsuwa Widad tayi seda ya gama tsaf sannan tace 
"Cikani tun kan in wanka maka mari a gurin nan, kai waye da zaka gayamin abunda ya dace dani? this is my life style not yours, dalla Cikani Malam kana ɓatamin lokaci ni"

A hankali Yusuf yace  "I am musulm, ina kishin yadda mutane ke ƙare miki kallo a haka, kalli irin mutanen dake gurin nan, da yawan su karuwai ne fa da mutanen banza, shigarki bata da maraba da wanda matan gurin nan marasa daraja suka yi"

Cikin isa tace masa "koba maruwanci ba, Nima shi nazo yi, am prostitute karka ƙara shiga rayuwa ta, na gaya maks"

Ta juya ta shiga Hotel ɗin da sauri, wani baƙin ciki ne ya tokare zuciyar Yusuf, ya koma mota ya zauna yana tunani a ransa
'to wai kai Yusuf banda shisshigi ina ruwanka da ita ne?'
Wata zuciyar ta tambaye shi.

Yana nan zaune a mota kusan mintuna Arba'in, gajiya yayi da zaman motar ya fito ya zauna akan motar yana ƙurawa hanyar da Widad tabi ido.
Ba tsammani ya hangota tana fitowa, sedai fuskarta ɗauke da hawaye tana ta share hawayen da handkerchief, inda motar su take ta nufo idanunta jawur, wani ne ya biyo ta yana ƙoƙarin tsaida ita yayi mata Magana amma bata tsaya ba, tana zuwa ta buɗe motar ta shige.
Yusuf ya zagaya ya shiga ya kunna motar, gaba É—aya se yaji ya tsargu da yanayin daya ganta, gaba É—aya hankalinsa ya tashi "Are you ok?"

"Do you have any conscience with me being ok or not?" ta tambaye shi a hasale

"Yes i have" ya bata amsa, tsaki tayi ta ɗauke kanta tace 
"drive very fast please" gudu sosai Yusuf yake amma azalzalarsa take wai ya ƙara gudu, kuma still bata dena kukan ba, kuka take me fallasa da tsantsar ɓacin rai da damuwa.
Guri Yusuf ya samu yayi parking ya juyo yana kallonta, ba tace komai ba tasa hannu a jakarta ta É—akko wayar ta, ta É—an daddana sannan ta saka a kunnen ta, tayi shiru na wasu 'yan mintuna sannan tace "Hello Daddy"

Yusuf baya jin me mahaifin Widad ke cewa, cikin kuka tace  "please Daddy I want Flight back to U. K, i regret coming back to Nigeria, please Daddy talk to Bulama ask him to set up my visa"

Shiru ta ɗanyi sannan tace  "Daddy don't take it for granted please, i can't define what happens today, dan Allah kace ayimin visa in koma"

"Daddy why? Kayi shekaru ba tare da ni ba se yanzu zaka ce baka so inyi nesa da kai? Karo na biyu ina neman abu kana ƙin Yimin, shikenan Daddy bayan ciwon Ƙwaƙwalwa am at risk of having cardiac attack" ta saki wayar ƙasa ta cigaba da kuka.

Yusuf ya cika da mamakin meyasa Widad kuka haka? Akwai buƙatar yasan me taje yi Hotel.

"malam kayi sauri ka maida ni gida, ka tsaya kana kallo na"

"Bazan iya tuƙin ba muddin zan cigaba da jin kukan ki" yai maganar fuskarsa ɗauke da damuwa

A hankali ta É—ago idanunta da suka yi jawur, ta saka ana Yusuf tana son gano gaskiyar abunda ya faÉ—a

"to meye haÉ—inka dani da kuka na ze dame ka, just drive ba ruwan ka da kukana, kayi abunda ke gabanka"

A hankali ya kunna motar, ya bata wuta ya cigaba da tuƙi, sedai gaba ɗaya hankalin sa baya jikin sa, yana can yana tunani daban daban.

Ihun Widad ne ya dawo dashi hayyacin sa, sannan ya lura da abunda ke shirin faruwa, duk yadda yayi ƙoƙarin kaucewa motar, seda me motar ya daki tasu.

Dafe kai Yusuf yayi yace  "Subhanallah"

A fusace ta kalli Yusuf "Are you out of your sense, see how you ruin my life, kashe ni kake so kayi? Baka gani ne? Dama so kake ka kasheni, an haÉ—a baki da kai zaka kashe ni ko? Dama na sani"

Kafin Yusuf ya bata amsa tuni me waccan motar ya fito yana zazzaga bala'i, an lotsa masa mota se an biya shi.

Yusuf ya buɗe motar ya fita jiki ba ƙwari, ya kalli mutumin ze kai shekaru Arba'in, Yusuf yace 
"Dan Allah kayi haƙuri, birki ne ya ƙwacemin, kuma kaga traffic ta tsaida hannun ka amma baka tsaya ba, kuma ni na riga na taho da gudu, amma dai kayi haƙuri"

"Shut up my friend, ni zaka gayawa traffic ta tsaida hannu na? Titin naka ne kai kaÉ—ai da zaka dinga wannan gudun, banza shashasha kuma wallahi seka biya ni asarar da kayi min kokuma kaga abunda zan maka"

Tuni mutane suka fara taruwa, suka cika gurin ana ta bawa Mutumin nan haƙuri, dukda zagin da yakewa Yusuf amma haƙuri yake bashi, amma mutumin nan ya rintse ido yana zazzaga masifa yana cin zarafin Yusuf, hakimar kuwa ko fitowa ba tayi ba tana mota a zaune.

Yusuf yace "Amma naga idan laifi ne fa kaine kayi bani ba, Amma se baka haƙuri nake kana cigaba da cimin mutunci a gaban mutane, shikenan Yimin duk abunda zaka iya ka huce"

Yusuf dama gashi a cikin damuwa yake, ga shi ze zagin sa mutumin yake, aikuwa nan da nan temper É—insa ta hau zuciyar sa ta shiga tafasa, dan haka se yayi shiru ya dena cewa komai.

Mutumin ya cigaba da zazzaga masifa "Do you know who I am da zaka dingamin magana da gadara,? I will show you what am capable of doing, sena nuna maka ni waye, sena sa an sauke maka wannan rashin É—a'ar taka mara tarbiyya kawai"

"You are nobody More than stupid Malam, waye kai idan har kai wani ne bazaka tsaya kana É—aga murya akan wannan banzan gwangwanin motar taka ba, kayi abunda zaka yi an bige motar taka, ina son inga kai waye, kuma me zaka iya?"

Gaba É—aya suka juyo inda Widad ke magana da jajayen idanunta.

Mutumin ya kalli Widad yace
"Lallai ka É—akko karuwa a mota, dole ka É—agamin murya danka birgeta, zanyi maganin ku daga kai har ita"
Ya ciro wayarsa yana waya.

Yusuf a harzuƙe zeyi magana Widad ta ɗaga masa hannu alamar yayi shiru.
Ta ɗakko wayar ta tayi 'yan taɓe taɓe.

Mutane suka ja gefe suna son ganin ƙarshen dramar, mintuna kaɗan sega motar 'yan sanda, suka zo suna wuri wuri, mutumin ya nuna musu Yusuf yace  "gashi nan shine, ku kama shi shida wannan koɗaɗiyar Yarinya me kama da sadakar Yalla"

Tuni É—aya daga É—an sandan yaje ya cakumo Yusuf, sedai me É—an sandan ya jiyo bindiga a jikin Yusuf!!!

SHARE PLEASE 🙏

__Masha Allah nagode da addu'oinku Daddy yana samun sauƙi Alhamdilillah nagode sosai Allah yasaka da alkhairi __

Ayshercool
07063065680

_*AƘIDA TA*_

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*

_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_

The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *

I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mum

https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=in

ELEGANT ONLINE WRITER'S

PART1
Page 12

ÆŠan sandan ya zare ido zeyi magana, Yusuf yayi saurin girgiza masa kai, ya juya ya kalli Widad yaga hankalinta baya kansu.

A hankali ya zura hannu a aljihun sa ya É—akko ID card ya nunawa É—an sandan, washe baki É—an sandan yayi yana niyyar sarawa Yusuf, amma Yusuf ya girgiza masa kai yace

"Dan Allah Yallaɓai ku duba lamarin nan, ni bani da laifi a abunda ya faru, kuma na bashi haƙuri yaƙi haƙura"

Mutumin ya ƙaraso inda su Yusuf suke yace  "kaga Ku tafi da shi ajiyata ne, ku kulle shi har se nazo station ɗin"

ÆŠan sandan Ya kalli Yusuf zeyi magana, sega wasu 'yan sandan sunzo, motar da' yan sandan suka zo ze tabattar maka da manyan wanda mutumin ya kirane, nan na farkon suka shiga sarawa wanda Widad ta kira.

Widad tace  "ina so a duba Accident ɗin nan, idan direba nane yake da laifi, zan biya shi kuɗin motar sa uku, idan kuma shi yayi laifin ze durƙusa ya bamu haƙuri, saboda cin zarafi da ɓata mana lokaci da yayi, in kuma yaƙi a tafi da shi, ajiyata ne a kulle shi se nazo"
Chapter 27 · 0% Book details