← Book details Akidata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 82

Sashe 54

Akidata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Anwar ya maida su Alhaji Nasir gida, ya shiga part ɗin Fahad, sedai ya tarar da shi da mace suna shan shisha, Anwar ya girgiza kai dan ya saba ganin Anwar a wannan halin, mussman da suna ƙasar waje, Anwar yace "Fahad baka san meya faru da Widad bane da direbanta, ina ta kiranka baka ɗaga ba?"

Fahad ya fesar da hayaƙi yace "Nasani mana"

"Amma ko Daddyn namu ai yakamata kaje ka duba"

Fahad ya kalle shi yace "Daddynku ku suwa? Baza'a dubo shi É—in ba, ni burina duk inda ta shiga a nemo min mata ta, dan nasan wannan tsinannen direban ne ya gudu da ita, kuma sena nuna masa iyakarsa"

Karuwar dake tare da Fahad tace "Baby wai maganar wa kuke yi ne?"

Fahad yace "ba ruwan ki uwar shishshigi, jeki shirya inzo in maida ke gida"

Anwar yace "Fahad se yanzu na sake tabattar da Widad a kan gaskiya take na ƙin yadda da mutane, yanzu Fahad kasan nida kai iyayenmu basu da ƙarfin kaimu ƙasashen waje, amma ya ɗauke mu kamar yaransa, ya kaimu ƙasar waje mukayi karatu, dukkaninmu ba wanda be mallakawa motar hawa ba da gidan kansa, muba komai ba silarsa muka zama wani abu, kalli yadda muke fantamawa a cikin rigar arzikinsa, albarkacin sunansa duk inda muka shiga a faɗin ƙasar nan muna da Alfarma, yau shine Iftila'i ze faɗa masa amma ka nuna halin ko in kula, Anya Fahad kana gayawa kanka gaskiya kuwa "

Fahad yace " A'a sedai idan yanzu zaka fara gayamin gaskiyar "

Yai maganar tareda miƙewa ya shige bedroom ɗinsa, jiki a saɓule Anwar ya baro gidan Bulama ya koma Asibiti, ya bawa Alhaji Nasir Abinci ya canza masa kaya, sedai yaita mamakin rashin ganin mahaifiyarsa taje Asibitin gurin mijinta.

Gida ya koma yana tunanin butulci irin na Fahad, a falo ya tarar da Hajiya Halima tana cin Abinci suna kallon zee world, sedai kamar Amal ce a cikin damuwa.

Anwar yayi sallama suka amsa gaba É—aya, Anwar yace "Mummy meyasa ba kije Asibiti ba?"

"bana jin daÉ—ine, bana son inje inga abunda ze sake É—agamin hankali"

"Amma Mummy ai jikin nasa da sauƙi, kuma yakamata ace ko su Ramla sunje duba shi"

A fusace tace "Ubansu ne da lallai se sunje duba shi, fita ka bani guri dalla"

Buɗe baki yayi yana kallon mahaifiyarsa yana ƙoƙarin tabattar da anya daga bakinta wannan maganar ke fitowa?

Duhu ya fara yi, sauro ya shiga ambaliya a gurin nan, Yusuf ya zauna se akin yi mata fifita yake da wani gutsararren kwali, A hankali Yusuf yace "Kidena musu taurin kai kinji, sannan idan an baki Abincin ki karɓa kici, baze yuwu ki zauna da yunwa ba"

"ba zanci ba" ta bashi amsa

"kin fi son su cigaba da azabtar dake?"

Shiru tayi masa ba tace komai ba, can ya kuma cewa

"dan Allah ki basu abunda suke nema, dan su ƙyale ki ko a yanzu kin galabaita"

"wallahi ko zasu kasheni bazan basu ba, shiyasa nace tun farko su sake ka ni su barni anan"

"tayaya zasu sakeni in tafi, alhalin kina gurinsu sedai kome ze faru ya faru muna tare"

Ajiyar zuciya ta shiga saukewa, tana jin yadda sauro ke shagali akanta, abunda bata saba ba, bata son yin kuka dan yanzu Yusuf ze É—aga hankalinsa

Cikinsu babu wanda ya rintsa, har gari ya waye, taimama sukayi sukayi sallar Asuba.

Fuskar Widad duk ta kumbura saboda sanyi da cizon sauro, kuma har a lokacin jikinta babu ƙwari.

Yusuf yana zaune, yayin da Widad ke kwance akan tabarmar, buɗe ƙofar ɗakin akayi suka sake shigowa su huɗu.

Suka kalli inda Widad ke kwance, É—ayan ya buga mata tsawa yace

"tashi ko in taka ƙafarki in karya banza"

Gyara kwanciya tayi ta juya musu baya, alamar bata da niyyar tashin, yau Yusuf ya ƙara tabbatar da azababben taurin kai da Widad ke dashi.

Da sauri Yusuf yazo inda take ya É—aga ta zaune yace "ya haka ne, so kike yauma su dake ki"

Wani banzan kallo tayiwa shugabn nasu ta É—aunke kai tana hura hanci.

ÆŠayan yace "shegiya se kyau kamar ita tayi kanta, amma zuciyar ta kamar dutse shegiya me kama da sadakar yalla"

Babban su yace "zamuyi maganinta kafin tabar gurin nan, da ganin idonta yunwa take ji, amma saboda taurin kai taƙi cin Abinci, ku ɗakko Abinci ku bata idan taga dama taci"

Shinkafa da wake ce irin garau garau ɗin nan takan 'yan talla, tayi sanyi ƙalau ga ba mai sosai, suka dire mata a gabanta, yunƙurawa tayi zata sake fatali da Abincin Yusuf ya riƙe ta yace "dan Allah ki daure kici, kinga tun shekaranjiya rabonki da Abinci"

Ta kalli idon Yusuf tace "bazan ci ba"

Ɗayan yace "kai dalla ka ƙyaleta mana, kar taci ubanwa tayiwa, Oga ka fara aiki kawai"

Rarrashin duniya Widad tayi mursisi taƙi cin Abinci.

Babban cikinsu ya É—akko wayarsa zeyi kira.

"Nurat ki kaiwa Daddynki tea ɗin nan da baƙinsa, kafin yazo ya ishemu da faɗa"

Nurat ta miƙe ta ɗauki kayan tea ta nufi part ɗin mahaifinta.

Alhaji Munir ya shafa ƙaton cikinsa yace "nifa bakina yaƙi rufuwa ma, nasan dole abun nan yazo hannunmu a yau base gobe ba, nace a tura masa saƙo, kodai ya bayar ko mu cigaba da tsare ta"

Alhaji Musa yace "ba kai kaɗai ba ni kaina ina cikin murna, sun kwana a hannu, Daula yana gadon Asibiti yana ta sharɓar hawaye, mutum se taurin kan tsiya kamar arnen dutse"

Suka kwashe da dariya, Alhaji Haruna yace "dalla ƙyaleshi, gefe guda baze samu Halartar taron shekara na kasuwanci ba, da haka zamu sanar da cewa an samu gagarumar Asara kasuwancin da muke yi, zamu bada fake Account statement, zamu kwashi rabonmu kafin wancan yazo hannunmu, ai daula ya gama yawo wai shi me gaskiya"

Suka sake kwashewa da dariya, wayar Alhaji Haruna ce ta fara ringing, ya É—aga ya sa musu a hands free, Alhaji Haruna yace "Ya me ake ciki ne?"

"Yallaɓai tunda nake aikin nan, ko a maza ban taɓa ganin mutum me baƙin taurin kai kamar yarinyar nan ba, kwana biyu kenan taƙi cin Abinci, ruwa kawai take sha, gashi kamar bata da lafiya kullum tana kwance ko magana seta ga dama take yi"

Alhaji Munir yayi tsaki yace "dalla ku rabu da ita, ku karɓo mana abunda muke buƙata, sannan ku turawa ubanta saƙo shima koya bamu ko kuma ku kashe ta"

Daga wayar akace "An gama Oga, yadda kukace"

Nurat da taje kai musu shayi jikinta ya shiga ɓari, dan tsaf taji hirar da mahaifinta suke yi, cikin sanɗa taje ta ajiye farantin kayan shayin, ta ruga da gudu ɗakinta ta saka hijjabi ta ɗau wayarta ta fice daga gidan.

Babban cikin mutanen wanda suke cewa me Adda ne ya É—akko wata kujera ya zauna a gaban Widad ya kalle ta cikin tsawa yace

"ke kalleni nan, ina takaddun nan suke? Ki gayamin cikin ruwan sanyi ko kuma in kasheki in koma in kashe wancan daƙiƙin uban naki"

Sunkuyar da ka tayi tai shiru, Yusuf yace "Yana miki magana ki gaya masa, su ƙyaleki ki huta"

Kallon Yusuf tayi da jajayen idonta sannan tace "takaddun da suke nema, akwai masu shi nayiwa Daddy Alƙawarin miƙasu ga masu shi, kuma na bawa masu shi suna can suna yawon su a gari, me suke so kuma ince musu"

"ƙarya kike, duk binciken da'akayi sun tabattar da suna wajen ki dan haka ki gayamana inda suke"

A harzuƙe tace "bazan faɗa ba, nace bazan faɗa ba kayi abunda zaka yi!"

Kan bindiga É—aya yasa ya buga mata a baki, take jini ya shiga zuba daga bakinta Yusuf ya gigice ze tashi, suka É—ora masa bindiga aka "kana motsawa zamu fasa kanka da harsashi"

Widad ta tattaro dukkan yawun bakinta, me ɗauke da jini ta tofawa shugabannin nasu tace "wallahi ko me zaki sedai kayi, bazan bayar ba ka koma ka gayawa Azsaluman da suka saku aiki cewar bazan bayar ba, kuma matsorata ne tunda suka gaza fitowa gaba da gaba su karɓi abunda suke so, kuma ko sun kasheni na kafa musu tarkon da ko bayan raina se Asirinsu ya tonu, saboda na sansu kuma na tattara duk wata hujja da yakamata a kansu san......

Bata ƙarasa ba ta kuma jin wani marin a fuskarta, a duk lokacin da suka daki Widad Yusuf ji yake kamar ƙirjinsa ya tsage dan baƙin ciki, sedai ba yadda ya iya muddin yayi wani yunƙuri dabe gamshesu ba zasu mata illa, dan ba imani ne dasu ba, ga Widad bakinta yaƙi mutuwa.

Nurat bata tsaya ko ina ba se gidan su Widad, a waje ta tarar da Anwar ya fito da mota ze fita, Anwar ne ya ganta dan sam bata lura dashi ba yace "Nurat"

ÆŠaga kai tai ta kalle shi sannan tace "Yaya Anwar ashe ka dawo, babu Labari"

Anwar yace "Na dawo, ina zaki haka naga kamar bakya hayyacinki"

Nurat tace "gurin Widad nazo"

Anwar yace "baki san na sace ta ba ita da direbanta?"

Hannu ta ɗora a ka, ta durƙusa a gurin ta fashe da kuka, Anwar ya fito daga motar yace "Nurat lafiya kuwa?"

Nurat tace "lafiya ƙalau, dan Allah kasan wani ɗan uwanta wanda suke yawo tare?"

Anwar yace "Ai Widad bata da É—an uwa"

Nurat tacs "Nasani, wannan zaka ga tare suke yawo, ban san sunashi ba ya cemin É—an uwanta me shi, wani dogo kamar bafulatani, me yawan murmushi"

Anwar yace "ko Yusuf kike nufi?"

Nurat tace "ban san sunansa ba"

Anwar yace "indai Yusuf ne tare suke yawo kam, kuma tare aka sace su"

Zare ido waje tayi tace "tare aka sace su, na shiga uku ni Nurat, meyasa aka sace su?"

Anwar yace "shine abunda bamu sani ba, amma 'yan sanda na nan na bincike yanzu haka zanje Asibiti gurin daddynta ne, daga nan mu koma station"

Nurat tace "zan iya binka in duba shi?"

Anwar yace "meze hana? Muje"

Suka shiga motar suka tafi.

Me Adda ya jinjinawa wannan baƙi taurin kai na Widad, yasa bakin bindiga ya daki kanta dashi ta kurma wani uban ihu tace "wallahi ba zan faɗa ba, sedai kayi min duk abunda zakamin"
Chapter 54 · 0% Book details