← Book details Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 86

Sashe 86

Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Kafin su Sarki Abdul'aziz su zauna tsayar da maganar aurensu Kamalu sai da ya aika aka kira Kamalu, Muhsin da Jawahir.
"Ba tun yau ba Jawahiruna na ce ba zan yi miki auren dole ba, don haka na sa a kira ki don na ji ta bakinki shin kina son Muhsin." Dire kalaman Sarki Abdul'aziz suka yi daidai da bugun ƙirjin Kamalu. A razane ya ɗago yana kallonta ta sunkuyar da kai ƙasa idanunta suka ciko da ƙwalla ba tare da ta amsa ba. "Duk yadda kuka yanke daidai ne ranki shi daɗe." Ta ƙarasa maganar hawaye na zuba.

"Jawahir a yi magana muna sauraronki ke za ki zauna da shi ba mu ba." Cewar Sarki Abdul'aziz don ya ji daÉ—in yadda Sarki Sulaimanu ya yi masa kara.
"A gafarce ni ranka shi daÉ—e amma Jawahir ba ta son Muhsin." Kamalu ya furta kai tsaye.

Daga Sarki Sulaimanu har Sarki Abdul'aziz idanu suka zuba masa, ya sunkuyar da kai ƙasa ya furta. "Na san Jawahir farin sani ba tun yanzu ba wallahi ba ta son Muhsin..."
"Ƙarya kake munafuki." Muhsin ya katse shi a harzuƙe. Murmushi irin na manya Sarki Abdul'aziz ya yi ya ce. "Tsakanin Kamalu da Muhsin wa kike so?" Da sauri Jawahir ta ɗago ta dubi Kamalu, ta yi saurin goge hawayenta ta saki murmushi ta sunkuyar da kai ƙasa.

"Kamalu kike so?" Ya sake wurga mata tambaya, da sauri ta gyaÉ—a kai sannan ta fice daga É—akin tana dariya.
"Za mu aura miki wanda kika so Jawahiruna saboda haka ku tashi ku ba mu wuri."
"Dama ni na jima ina ganin bambamci ai, ni na san ba ƙaunata ake yi ba idan ba haka ba ai har mahaifiyata da tuni an fito da ita. Kuma wallahi babu wanda ya iya ya hana ni aurenta." Muhsin ya yi magnanar yana fita daga ɗakin.

"Matuƙar muna numfashi za mu aura wa Jawahir zaɓin ranta, duka 'ya'yana ne amma kowa na san nutsuwa da ɗabu'unsa. Amma muna neman alfarmar a ɗaga mana bikin nan zuwa makwanni biyar masu zuwa, sakamkon muna jiran Mai gado saura kwana huɗu ta fita daga Takaba. In shaa Allahu akwai aikin alkairin da za mu zartar a kanta." Sarki Abdul'aziz ya furta yana murmushi.
"Ranka shi daÉ—e da alama kai ma sharce amarcin kake shirin yi, shi ke nan babu damuwa Allah Ya nuna mana." GabaÉ—aya suka saka dariya.

Takaicin da ya kama Muhsin kai tsaye sashen ɓangaren ɗakin duhu ya nufa, yana tafe yana hawaye ko gabansa ba ya gani duk wurin da ya wuce kallonsa Bayi suke yi. Tsayuwarsa a wurin ƙofar ya ga yadda Mahaifiyarsa ta sake lalacewa, ƙoƙon kanta ya yi waɗansu mula-mulan ƙuraje, da alama duk sun ɗuri ruwa. Basiru ya hanga tsaye a gabanta da wata kaifaffiyar askar, duk yadda Fulani Umaima take yi masa roƙo da magiya bai saurare ta ba. Askar ya miƙa da niyyar ya yanki kunenta Bamaguje ya dira a gabansa, daga fuskarsa har jikinsa a daddauje yake, sai taintsiyar hannun Bamaguje da take a guntule. Kafin Basiru ya yi wani yunƙuri Bamaguje ya ɗauke ta suka ɓace, Fulani Umaima ta shiga ƙwalla ƙarara tana faɗin ya sauke amma ko ta kanta Bamaguje bai bi ba, ganin haka ya harzuƙa Basiru ya kwarara ƙara shi ma ya rufa masa baya, ya ɓace nan take.

A ɗimauce Muhsin ya yi cikin gida ya sanar da mahaifinsa halin da ake ciki, Sarki Abdul'aziz shi da Sarki Sulaimanu ne suka je wurin tun a nesa suka dakata saboda wari, ya saka Dogarai suka duba ɗakin sai dai babu Fulani Umaima babu dalilinta, sai Jakadiya da take galabaice cikin dagwalon ƙazanta. Takawa ya bayar da umarnin a fito da Jakadiya a sallame ta daga Masarautar Huddam.

Komawarta sashen Mai gado ta ji jikinta ya É—an É—auki É—umi, daga tsakiyar cikinta ta ji ya fara É—aukan zafi. Tana É—aga rigarta ta ga tambarin bishiyar abar bauta ya sake bayyana, ta buÉ—e baki za ta yi magana kenan ta neme shi ta rasa.

"Ko dai idanuwana ne suka niyyar yadarata?" Jawahir ta wurga wa kanta tambaya.
"Da zarar kin sake ganin wannan tambarin na cikinki, ki tashi ki ɗaura alwala ki fara karatun alƙur'ani, kuma ki sanar da Maharaz ya sanar da ni." Jawahir ta tuno kalam Babban Malami na baya a cikin kunnuwanta.

Ajiyar zuciya Nimrah ta sauke bayan ta rufe ƙaton littafin da take karanta wa ƙawayenta su Intisar, wanda a bayansa aka rubuta SHU'UMAR MASARAUTA da babban baƙi. Ta kalli su Nihal da ke gabanta ta furta.

"Kun san dalilin da ya sa na fara rubutu har na zama marubuciya da maƙasudin rubuta lattafin nan?"
"Amma dai ba kina nufin labarin ya ƙare ba?" Nawwarah ta tambaya tana kwaɓe fuska.
"Sai kun ba ni amsar tambayata." Nimrah furta tana rungume ƙaton littafin a ƙirjinta. Cikin haɗin baki suka furta mata.

"A'a Sister Nimrah sai kin faÉ—a." don sun damu su ji daga gare ta.

"Ranar da Umma ta ba ni labarin Mahaifiyarta! Saboda labarin cike yake da almara, zalinci ban tausayi da taɓa zuciya." Nihal ta yi sauri faɗin, "Wai kina nufin Jadda dai kakarku ita ce Jawahir ɗin da kika karanta mana labarinta?" Dariya Nimra ta yi ta ce, "Kina mamaki ne?" Lokaci ɗaya suka gyaɗa mata kai.

"Ƙwarai kuwa ita ce, don kafin na fara rubutun labarin nan sai da na je na sake jin komai tiryan-tiryan daga bakinta sannan na rubuta shi."
"Lallai ashe Jadda ta ga duniya. Amma don Allah da gaske labarin a nan ya ƙare?" Intisar ta tambaya kamar za ta yi kuka. Miƙa mata littafin Nimra ta yi ta ce, "Ga shi nan ki duba idan ƙarya nake miki." Marairaice murya Intisar ta yi ta ce. "Amma bayan tafiyar Fulani Umaima ina Bamaguje ya kai ta? Ya suka ƙarke da Basiru? Kuma wai a ciki wa Jadda take aura Muhsin Ko Kamalu? Ni fa duk tarzomar da aka yi ban ji kin ce Sarki Abdul'aziz ya saki Fulani Umaima ba, kuma wane ne ya gaji Sarki Abdul'aziz? Wai ya aka yi aka kwana a ragaya?" Nimra ta ɗaka mata duka a cinya haɗe da miƙewa tsaye ta ce.

"Sannu 'yar Jarida sai ki bari na yi sallar magariba na dawo, kin san dai kullin huɗubar Mai martaba kenan a dinga sallah a farkon lokacinta." Nimrah ta ƙarasa maganar tana ficewa daga ɗakin, Intisar da Nihal har rige-rigen ɗaukar littafin suke yi. Nihal ta sake duba bangon littafin a fili ta furta. "SHU'UMAR MASARAUTA. Labari mai almara da tsaya wa a rai."

TAMMAT BI HAMULILLAH
Ina matuƙar godiya ga Allah S.W.A da ya ba ni ikon kammala wannan littafi na SHU'UMAR MASARAUTA.

Gadiya mai tarin yawa a gare ku masoya waɗanda suka sa kuɗinsu suka sayi littafina wannam ma soyayya ce, ina mai jinjina muku bisa yadda kuka ɗauki kwanaki kuna bibiyar littafin nan Allah ya bar ƙauna. 🥰❤️

Na ce ba🌚 'Ni maYar adam ce wato tara dai nake ban cika goma ba, na tabbata kun ga kurakuran da ba a rasa ba a yafe ni, kuskuren ciki Allah ya yafe mana darasin da ke cikin labarin Allah ya ba mu ikon ɗauka.

*DON ALLAH DON GIRMAN ALLAH DA ZATINSA, DON SOYAYYAR DA KUKE WA ANNABI MUHAMMAD S.A.W KADA KU HAƊA MINI DOCUMENT ZAN HAƊA DA KAINA, DON ALLAH BA DON NI BA."*👏🏻👏🏻

Ummou Aslam Bint Adam🌚
Chapter 86 · 0% Book details