Sashe 50
Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ita ce farincikin zuciyata da nake kwana nake ta shi da begenta, ita ce ta ja linzamin dokin zuciyata har nake jin babu sauran wata 'ya mace da za ta samu fada a wurina. Ita ɗin ta musamman ce zinariya ce, tauraruwa kuma hasken zuciya. Ammi wannan ita ce yarinyar da na faɗa tarkon ƙaunarta ba tare da na sani ba..." A zabure Fulani Umaima ta miƙe tsaye jikinta na karkarwa ta katse shi. "Wannan yarinyar?"
Da wani irin sauri ya ji ƙafarsa na fisgarsa zuwa sashen Sarki Abdul'aziz, amma zuciyarsa na gargaɗin kada ya je ya aikata aikin da kan iya kai shi ga fuskantar mummunan hukunci. Amma kuma ya gagara sanin yadda zai dakatar da yanayin da yake ji don har jin sa yake tamkar yana tafiya a saman iska. A lokacin da ya ƙarasa sashen Sarki Abdul'aziz shiru wurin, da yake da alama babu Dogarawan ƙofa, daga can gefen sashen lambu ya hangi masu hidimar wurin suna gyara ƙananun shukokin da ke wurin dangin su: Karas, ɗata, salak da sauransu. Bai tsaya buga ƙofa ko neman izini ba kai tsaye ya faɗa turakar Sarki Abdul'aziz, a lokacin yana kwance da alama hutawa yake. Ganin Kamalu ya shiga ɗakin ya sa Sarki Abdul'aziz tashi zaune da sauri cike da mamaki.
"Waye yake yunƙurin nuna mana rashin ɗa'a zai tako har makwancinmu muna hutawa. Bukar! Bukar!" Sarki Abdul'aziz ya kira shigaban Dogaran da ke kula da sashensa amma shiru babu amsa. Ganin Kamalu ya doshin uwar ɗakinsa ya sa Sarki Abdul'aziz ya rufa masa baya, Kamalu na shiga ɗakin ya ji kansa na juya masa. Taƙama da izzar mulki suka mamaye shi, cikin takun isa da ƙasaita ya tunkari daɗaɗɗan gidan tururuwar da ke kallon shurin cikin ɗaki ya ɗora butar a saman gidan tururwar. Daga gefensa ya ji an furta.
"Yau Kamalu ne har cikin zuri'ata? Lallai da alama gaggarumin al'amari zai faru, sai dai ina jimamin da wannan ziyarar ba wurina ka kawo ta ba."
Da mamaki Kamalu ya kalli Dattijo Maharaz ya furta. "Dattijo Maharaz kai nake gani." Kafin Dattijo Maharaz ya ba shi amsa Sarki Abdul'aziz ya ƙarasa bakin ƙofar ya furta. "Wane ne kai? Me ya kawo ka har cikin turakarmu kuma me kake yi a wurin nan?"
*SHU'UMAR MASARAUTA*
*28*
*Littafin kuɗi ne 500 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*
Boka Shaddas na daga gefe ya zuba wa Basiru ido ganin yadda yake gudanar da alƙaluman tsafi, zuciyarsa ce ta yi fes farin ciki ya mamaye shi don ko a yanzu ya mutu ya san ya bar wa duniya magajinsa. A bakin wata ƙatuwar tukunyar ƙasa yake zaune ya ɗebo wasu turarrika ya zuba sannan ya ci gaba da surutai yana ambatar sunan A'ishatu, Nura, Bala da Nasiru, ta gefensa Boka Shaddas ya zaune ya yi masa jinjina da hannu.
"Aikin matar jiya kake yi ne?" Sai da Basiru ya gama jero sunanyen baƙaƙen aljanun da ya tura waɗanda za su yi masa aiki sannan ya furta. "Aikin jiya na riga da na zartar da shi, a yanzu haka ina gudanar da aikin Hansatu wacce ta kawo aikin 'yayan mijinta da ta ce a haukatar da biyu, ɗaya kuma a zaunar da shi ta ƙarshen a saka mata baƙin jini. Shi kuma Uban na mallake mata shi, na tura musu aljani Zurgungu shi zai gama aiwatar da komai. Na yi masa tuwkwicin jinin jariri sabuwar haihuwa da baƙaƙen jakuna, bayan wannan ina tunanin na gama da aikina na yau."
Murmushi Boka Shaddas ya yi ya dafa kafaɗar Basiru, "Fiye da haka na san za ka aikata domin ina ji a jikina sai ka fi ni gawurta da shahara a harkar tsafi da sihiri. Amma ba ka tunanin Mahaifiyarka za ta shiga damuwar rashin ganinka har tsawon waɗannan kwanakin ba ka leƙa wurinta ba?" Shiru Basiru ya yi kamar mai nazari sannan ya furta. "Zamana a wurin nan shi ya fi mini alfanu domin tun wankan tsafin da ka yi mini a duk lokacin da na kalle ta sha'awarta mamaye ni take yi, kuma na san ba za ta ba ni dama ba kuma idan na neme ta ta yi yunƙurin hana ni zan iya illatata ko ma na hallakata gabaɗaya. Babban burina ɗaya ne ya rage mini a duniya wanda ba tun yau ba nake mafarkin samu kuma nake haramar yunƙurin cim masa."
"Wanne irin buri ne?" Boka Shaddas ya yi saurin tambayarsa.
"Masarautar Huddam! Babban burina bai wuce na mallake ta ba ta dawo ƙarƙashin ikona, masarautar da ta gawurta da ƙasaitattun aljanu ita nake so ta rikiɗe zuwa Masarautar Matsafan da babu kamarta a faɗim duniya. Burin Mahaifiyata Muhsin ya gaji Takawa, ni kuma burina ka samu nasarar kammala karanta labarin Hidaya don ka samu nasarar da za ta kai ka gaba har ni ma na mulki nahiya da yankin da nake so."
Ƙurrr Boka Shaddas ya yi wa Basiru yana auna kalamansa, bai tanka masa ba ya tashi ya je bakin wani rami ya fara motsa baki. Take littafin ya fara tutsowa daga ƙarƙashin ƙasa ya fito.
Da mamaki Yarima Muhsin yake bin Fulani Umaima da kallo ganin yanayin da ta yi maganar. "Ammi wai me yake faruwa..." Tun bai rufe baki ba Fulani Umaima ta É—auke fuskarsa da mari, tuni Jawahir ta matsa can jikin bango jiki na rawa.
"Wai me yake damunki ne Ammi a kan me za ki mare ni don na gaya miki abin da yake cikin raina." Yarima Muhsin ya yi maganar a ƙufule tamkar zai rama marin da mahaifiyarsa ta yi masa.
Fulani Umaima ta wurgawa Jawahir mugun kallo tana sake tuno tone butar da ta yi mata, wata irin zuciya ce ta ciyo ta don haka ta yi kukan kura za ta janyo Jawahir ganin haka ya sa Jawahir ta fita da gudu tana kwalla ihu cikin tashin hankali.
"Me kike yi ne haka Ammi?" Muhsin ya furta cikin ƙaraji.
"Wannan yarinyar annamimiya ce, maƙiyyarmu ce Muhsin ka fita daga harkar yarinyar nan..."
"Ki furta mini komai amma ban da kalmar rabuwa don wallahi ko Takawa bai isa ya hana ni aurenta ba, ke kin auri wanda kike so don haka babu ruwanki da rayuwata ni ma ki bar ni na yi sabgar gabana kawai, duk wata damuwa matsalarki ce." Yarima Muhsin ya ƙarasa maganar yana ficewa daga ɗakin ya rufa wa Jawahir baya.
"Da ace ka san matsayinsa da ba ka tsaya kana tambayarsa dalilin zuwansa wurin nan ba Sarki Abdul'aziz." Dattijo Maharaz ya yi maganar yana jingina da bango. A razane Sarki Abdul'aziz ya dubi wurin da yake jin muryar da ko a mafarki ya ji ta sai ya tantance ta.
"Wane ne kai? Me ya sa kake son yaudarata da muryar Dattijon da nake matuƙar ganin girmansa da mutumtawa?"
Murmushi Dattijo Maharaz ya sakar masa sannan ya furta. "Ba yaudara ba ce Sarki Abdul'aziz! Kuma ba gizo ƙwayar idanunka take yi maka ba, kana tare da Dattijo Maharaz, Dattijon da yake matuƙar farinciki da ganin irin girmamawar da zuri'ar aminsa suke masa." A take Sarki Abdul'aziz ya saki baki da hanci cikin tsananin mamaki domin wannan shi ne karo na farko da ya taɓa sanya ƙwayar idonsa a surar Dattijo Maharaz a zahiri duk da ya fito masa a cikin surar mutane, sakamakon tun yana ƙarami sai dai ya ji muryarsa a bakin shurin da ya buɗe ido da ganinsa a turakar mahaifinsa.
"Ya aka yi aka haihu a ragaya Dattijo Maharaz? Me ya sa ba ka taɓa bayyana mini kanka ba sai yanzu?"
Kafin Dattijo Maharaz ya ba wa Sarki Abdul'aziz amsa suka ji wani irin ƙas ƙas ƙas a daidai wurin da Kamalu ya ajiye butar, wata irin katantanwa ta fara yi sannan wani farin hayaƙi ya fara fita daga cikin gidan tururuwar. Nan take Kamalu ya fara fita daga hayyacinsa, a hankali ya fara takawa don ya ƙarasa kan gidan tururwar, da sauri Dattijo Maharaz ya sha gaban Kamalu hankali a tashe yana faɗin.
"Kada ka yi mini haka Furhussam! Kada ka aiwatar da abin da zai zo daga baya ana da-na-sani." Dattijo Maharaz ya furta a É—an razane.
"Ka matsa daga gabana Maharaz, kada ka yi gangancin dawo da borno dawaki. Abin da ya faru ya riga da ya wuce don haka kowa ya yi harkar gabansa." Furhussam da yake magana ta jikin Kamalu ya furta yayin da Dattijo Maharaz ya sha gabansa.
"A yarjejeniya da muka taɓa yi babu ɗaukar ɗaya hallita ɗaya daga cikin zuri'ar Masarautar nan." Faɗuwa ƙasa Kamalau ya yi, nan take wani gajeren mutum baƙi wuluk mai fafaɗar fuska, kansa ɗauke da wata hular ƙarfe ruwan zaiba ya ce. "Maharaz ba na tunanin akwai wani mahaluki da ya isa ya sa na gagara zartar da hukuncin da na yi niyya, ba tun yanzu ba ya rayu cikin kulawa da ikonmu. Don me zai sa bayan ya gama aiwatar da abin da muka jima muna buri ba zan ɗauke shi ba?" Gaban Sarki Abdul'aziz ya shiga bugawa. Ya dubi ɓangaren Dattijo Maharaz a ɗan rikice, "Me yake faruwa Dattijo Maharaz? Ina jin tsoron kada wani sabon al'amari ya faru da al'ummar cikin masarautata."
"Wannan tsohuwar daɗaɗɗiyar gaba ce Sarki Abdul'aziz, wannan yaron kuma da kake gani makusancinka ne kuma makusancin wannan karagar da kake kai ne. Ban yi niyyar furta wannan maganar ba amma tun da na lura Furhussam bai riƙe alƙwarin da muka ɗauka ba zan fayyace maka komai amma sai yaron nan ya dawo hayyacinsa don na yi masa alƙawarin hakan." Dattjio Maharaz ya ƙarasa maganar yana matsawa gaban Kamalu da ke kwance jikinsa na wata irin karkarwa.