Sashe 59
Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
"Ba haka nake nufi ba Dattijo Maharaz, ina fatan za ka yi mini kyakkayawar fahimta farin jakada. Duk magidancin da ya tsinci irin waɗannan kalaman a kan iyalansa dole zai samu shakku da shiga ruɗani Dattijo Maharaz." Murmushi Dattijo Maharaz ya saki sannan ya furta. "Na fahimci kalamanka Sarki Abdul'aziz amma ka san bahaushe yakan ce dole gyaɗa ta yi mai idan ta ƙi ta sha matsa, ka matsa matarka iya bakin ƙoƙarinka na tabbata za ta fito da duk bayanan da kake buƙata. Idan kuma hagu ta ƙi sai a koma dama amma kuma kafin wannan waƙa a bakin mai ita ai tafi daɗin sauraro." Sarki Abdul'azizi juyar da kansa ya yi yana kallon Fulani Umaima da ita kaɗai take ta zabga uban gumi.
"Ya aka yi yaron nan ya zama ɗana alhalin ban san da haihuwarsa ba? Wace ce mahaifiyarsa? Kuma ya aka yi ban san da ciki da haihuwarsa ba? Ba yau nake tare da Dattijo Maharaz ba na tabbata ko wanina ba zai yi wa ƙarya ba ballantana ni da zuri'ata." Sarki Abdul'aziz ya yi maganar yana tsare Umaima da idanu.
"Ba ni da ɗaya daga cikin amsoshin tambayoyin da kake tuhuma ta a kai. Me ya sa haka Ranka shi daɗe? Me ya sa sai ni za a tuhuma da irin wannan maganganun alhalin ba ni kaɗai ce iyalinka ba?" Fulani Umaima ta yi maganar cikin nuna dakiya da ƙwarin gwiwa. "Umaima!" Sarki Abdul'aziz ta ambata da wata irin muryar da ba su taɓa jin ya yi magana da ita ba saboda tsananin ɓacin rai.
"Wane ne yaron nan?"
"Ban san shi ba"
"Idan ba ki san shi ba ai kin san Boka Bamaguje ko?" Dattijo Maharaz ya wurga mata tambaya.
A razane Fulani Umaima ta dubi Dattijo Maharaz a fili cikinta ya ba da sautin ƙuuuu! Har sai da Yarima Muhsin da Sailuba suka bi ta da kallo.
Boka Shaddas sai da ya jima da fita sannan Basiru ya miƙe zuciyarsa ƙal ya fara takawa har ya isa bakin ramin da mahaifinsa yake ɓoye littafin, sai da ya gudanar da duk wani abin da mahaifinsa yake yi na tsaface-tsaface kafin ya ɗauko littafin sannan littafin ya fara tutsowa daga ƙasa. Sai da ya gama fitowa ya saka hannu ya ɗauka ya ƙyaƙyace da wata mahaukaciyar dariya, ya jima yana yin mai isarsa sannan ya ɗauki wata farar takarda ya ajiye ta a ƙasa ya sa sandar tsafinsa ya bugi farar takardar nan take takardar ta rikiɗe zuwa surar littafin da ya ɗauke daga cikin wurin. Rungume littafin ya yi a ƙirjinsa babu jimawa ya ji wani abu ɗaaau tamkar ya harbi zuciyarsa, da sauri ya ɗago littafin yana ƙare wa bangon littafin kallo sai ya sake mayar da shi ƙirjinsa ya rungume da hannunsa ɗaya. Har ya je ƙofar fita daga kogon dutsen sai ya hangi wani kurtun giya, ya ɗauko shi ya ɗaga kansa ya ɗaɗɗaka sannan ya fice kai tsaye ya nufi cikin Masarautar Huddam.
Jakadiya tun da ta koma ɗakinta ta shiga saƙa da warwarar makomar rayuwarta, a ganinta wannan karon tonen kaza da ke iya kaita ta tono wuƙar yanka kanta ce ya faɗo kanta. Da farko ta karaya sosai, amma da wani tsagin zuciyar tata ya hararo mata irin cin zarafin da za ta yi wa Fulani Umaima kuma Sailubanta ta warke sai wata irin ƙwarin gwiwa ya ratsa ta. Miƙewa ta yi ta ɗauki garin maganin da Shugaba Zurufu ya bata, ta juye shi a cikin ƙwarya ta tuɓe kayanta sai da ta kullo ƙofar ɗakinta sannan ta fara faɗin waɗansu sunaye tana yi tana watsa ruwan ajikinta sannan ta yi turaren sihirin da ya bata. Tana gamawa kuma fargabarta ta koma kan hanyar da ta samu damar ganin Basiru, don ita sai a lokacin ma ta ga wawtarta saboda a ɗebe ta haure sama da kwana biyar ba ta saka shi a cikin idanunta ba.
"Ki je sashensa mana!" Tsagin zuciyarta ya ba ta amsa. "Wataƙila ma idan kika samu damar kai masa Basiru yau ya fasa haɗa ki da ɗan autan aljanin da zai turmushe ki." Zuciyarta ta sake raya mata. A gurguje ta saka kayanta ko garin maganin jikinta bai gama bushewa ba ta fice daga ɗakinta, kai tsaye ta wuce sashen Fulani Umaima sakamakon soronsu ɗaya sai dai ɓangaren su Yarima Muhsin daban na Fulani Umaima daban. Tun daga bakin ƙofa Jakadiya ta fara jin waɗansu irin surutan Basiru har sai da tsora ta, leƙawa ta yi ta windo ta hango shi yana birgima duk ya ɓata jikinsa da aman giyar da ya sha, a gefe ɗaya kuma littafin da ya ɗauko yana riƙe a hannunsa na hagu. Da sauri Jakadiya ta faɗa ɗakin jikinta har rawa yake ta tsugunna a gabansa, "Barka da hutawa Saraki!" Jakadiya ta furta don ta ga irin yanayin amsar da zai ba ta.
"Ki... tafi ni na... gama da sh... na... ɗauke masa... littafin... tsafi ya... ba ni... dama..." A fili Jakadiya ta saki murmushi ta riƙo hannunsa da ƙarfin gaske sannan furta. "Zuruful-Bukusu Barduku kass." Sai da ta furta haka sau uku sannan suka ɓace daga wurin, suka buɗi ido a cikin kogon dutsen Shugaba zurufu.
Da matsanancin mamaki Shugaba Zurufu yake bin Jakadiya da kallo, miƙewa ya yi jiki na makyarkyata ya ƙarasa gaban Basiru sannan ya ɗauke littafin da ke hannunsa. A lokacin da zai ɗauke littafin har sai da Basiru ya ɗago da sauri, Shugaba Zurufu ya hura masa sihirtacciyar iska, take Basiru ya faɗi gefe guda jikinsa ya yi wani irin laushi yana numfashi kaɗan-kaɗan.
"Kin cika jajirtacciya Jakadiya, don haka ya zame mini dole na biya miki buƙatarki."
Al'amuran da ke faruwa ba ƙaramin dagula wa Kamalu kwanya suka yi ba, tun tasowar shi sam ba shi da son hatsaniya ko tashin hankali don haka ya miƙe tsaye ya furta, "Dattijo Maharaz ni dai zan je wurin Baffajo, ka gafarce Ranka shi daɗe idan har na yi kuskure a kalamaina." Kamalu ya ƙarasa maganar yana russuna wa Sarki Abdul'aziz. Tausayin Kamalu ya kama Dattijo Maharaz, idanunsa suka ciko da ƙwalla sannan ya furta. "Tun da kake ba ka taɓa jin ɗuminsa ba, ba ka taɓa jin gatan da kowanne mai uba yake ji ba musamman da ka kasance asalin mai gata gaba da baya. Don Allah Abdul'aziz ka rungume yaron nan ko ya ji abin da sauran 'ya'ya suke ji." Tun ba rufe baki ba Sarki Abdul'aziz ya riƙo hannunsa, Kamalu sororo ya yi yana jinjina taushin hannun Takawa saɓanin na shi da ya saba da wahala da yake tamkar katako saboda tauri. Mamakinsa ya ninku da ya sake jin Takawa ya rungume shi tsam a jikinsa.
"Wai yau nine a tare da Mai martaba ko idanuwana da gangar jikina ne suke yaudarata? Ya Allah idan mafarki nake yi kada ka farkar da ni yanzu domin na ji irin ni'imar da masu mulki suke ji a rayuwarsu." Kamalu ya yi maganar a hankali, a tsammaninsa a cikin zuciyarsa ya yi ta. "Ba mafarki kake yi ba Kamalu, idan kuma kana tantama yanzu ne za ka tabbbatar da haka." Dattaji Maharaz ya furta yana nuna bangon É—akin Sarki Abdul'aziz.
"Ya kai Dattijo Maharaz shin me ye dalilinka na yi mini kutse a lokacin da nake gudanar da aikina a cikin halwar tsafina?" Bamaguje ya yi maganar cike da damuwa. "Ina neman afuwarka Boka Bamaguje bisa shiga haƙƙinka a daidai gaɓar da ba ka tsammace ni ba. Shin ko ka san wannan baiwar Alahr da bawan Allahn nan?" Dattijo Maharaz ya nuna Fulani Umaima da Kamalu.
"Wacce irin magana kake yi mini Maharaz? Tambayar wannan a wurina tamkar cin fuska ne da cin zarafina domin Umaima jinina ce 'yata ce ta cikina halak-malak ni ne mahaifinta. Shi kuma wannan yaron ban san shi ba, sai dai zan iya shiga halwar tsafina na bincika tauraronsa..."
"Ƙarya kake Bamaguje! Wallahi ƙarya kake ni ba 'yarka ba ce. Wallahi sharri zai yi mini ranka shi daɗe ni ban san shi ba ban ma taɓa ganinsa ba." Murmushin Dattako Dattijo Maharaz ya saki. Lokaci ɗaya fuskar Bamaguje ta murtuke rai a ɓace ya nuna Fulani Umaima ya furta. "A yau ba sai gobe ba na rantse da girman tsafina da sihirin da nake taƙama da shi sai na nuna miki ke ɗin 'yata ce babu wani mahaluki da zai sake yi mini iko da ke."
*SHU'UMAR MASARAUTA*
*33*
*Littafin kuɗi ne 500 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*