Sashe 43
Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Wai yau Basiru ne a gabana yake furta mini baƙaƙen maganganu? Tabɗijam! Ya zame mini wajibi na tashi tsaye a kan yaron nan. Bamaguje! Ya zame mini dole na je wurin Bamaguje, to amma ta ina za ni wurin Bamaguje bayan kuma ƙahon da nake busawa yana cikin akwatin can, sannan kuma a nan littafin wurin Bamaguje yake." Fulani Umaima ta yi wannan zancan a zuciyarta. Tamkar wanda ya ga abin da yake cikin ranta haka Basiru ya furta mata, "Ungo wannan, ki aiwatar da shi nan take. Idan kin gama da wannan kya tsaya yin shawarar yadda za ki ɓullo wa lamarina, wai tun daga yanzu ne na fara baki tsoro da mamaki? Kada ki yaudari kanki don ni da kike gani garnaƙaƙin dutse ce kowa ja da ni shi zai faɗi." Da mamaki take bin shi da kallo, jikinta na ɗan rawa ta matsa baya.
"Waye ya baka wannan abin Basiru? Ya kake yin abu kamar boko ko matsafi? Wane ne Shugaban da kake magana? Basiru duka nawa shekarunka suke?"
"Karɓa za ki yi ko tambaya za ki ci gaba da wurgo min?." Ya furta mata a taƙaice.
Wannan shi ne ga ƙoshi ga kwanan yunwa, Fulani Umaima ta faɗa kogin tunani, gani take idan ta yi biyu ta tashi a tutar babu don ta matuƙar tsorata da Basiru da sigar da ya ɓullo mata. Babu yadda ta iya don haka ta yi ƙundunbala ta miƙa hannunta, "Zan karɓa amma sai ka fice mini daga ɗaki!" Miƙa mata ƙullin maganin da layar ya yi sannan ya ɗaga kafaɗa cikin halin ko-in-kula ya fice daga ɗakin. Wannan ita ce rana ta farko da Fulani Umaima ta yi dana-sanin haihuwar Basiru a rayuwarta, tun daga yanzu yaron na matuƙar ba ta tsoro musamman yadda yake faɗa mata magana kai tsaye ba tare da shakka ko shayi ba. Sai da ta tabbatar da Basiru ya fita daga sashensa ya koma sashensu sannan ta nannaɗe layar da cusa a jikinta tana jin zuciyarta shar cikin murnar cikar muradinta. Basiru da ke laɓe yana wurga idanu sai da ya ga wucewar mahaifiyarsa sannan ya fito yana sakin shu'umar dariya, yana zuwa ƙofar ɗakinta ya huro iska daga bakinsa take ƙofar ta buɗe ya faɗa cikin ɗakin ya sake turo ta kamar yadda mahaifiyarsa ta yi a baya.
Kamar mayunwacin zakin da ke neman abinci ido rufe haka Basiru ya ci gaba da hargitsa ɗakin yana neman littafin wurin Bamaguje, ya ɗan shafe lokaci mai tsaho sannan ya hango tsohuwar akwatin da ke ƙarƙashin gado. Haka kawai ya ji gabansa ya yanke ya faɗi, take ya ɗora zarginsa a kan wannan akwatin. Da sauri ya shiga kiciniyar buɗe ta cikin nasara ya buɗe, idanunsa suka sauka a kan sihirtaccan littafin da Boka Shaddas ya umarce shi da ya kai masa. Hannunsa na rawa ya sa ya ɗauko littafin nan take ya ji wani irin zuuuuu har tsakiyar kansa, tamkar wanda ake fusga haka ya dinga ji da ƙyar ya iya miƙe wa tsaye ya runtse idanunsa ya fara karanta waɗansu kalmomin tsafin da Boka Shaddas ya koyar da shi, nan take ya ɓace daga cikin ɗakin ya sauka cikin tsibirin Boka Shaddas. Suna haɗa idanu suka sakar wa juna murmushin samun nasara, Boka Shaddas ya nuna wa Basiru gefensa sannan ya furta. "Maza zo ka zauna Jarumina,. Tabbas barewa ba za ta yi gudu ɗanta ya rarrafa ba, ba na haufi a kanka gwarzona ko ba na raye ba zan yi kukan rashin magaji na ƙwarai ba."
*SHU'UMAR MASARAUTA*
*24*
*Littafin kuɗi ne 500 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*
"Na ɗauko na ɗora ki a wannan matsayin ne domin a kawar da Abdul'aziz amma sai na lura da tafiyar kunkurin da aikin yake yi a wurinki, me ya sa haka Umama? Me ya sa aka shafe waɗannan watannin babu wani bayani. Ya zame mana wajibi mu kawar da shi cikin 'yan kwanakin nan idan ba haka ba wankin hula zai iya kaimu dare, daga nan kuma komai zai iya faruwa don haka wacce dabara gare ki da kike ganin za mu kawar da shi ba tare da asirinmu ya tonu ba?" Fulani Asabe ta ƙarasa maganar tana zuba wa Umaima ido. A yatsine ta dube ta sannan ta tura baki gaba, "Ni fa gaskiya Inna ba zan ita kashe Takawa ba don gaskiya na fara son shi, kuma su Galadima su haƙura mana dama can Allah ya rubuta ba su da rabo..." Tun ba ta ƙarasa maganar ba Fulani Asabe ta ɗauke ta mari, a fusace ta nuna ta da yatsa.
"Har ni za ki faɗawa wannan maganar? To ko Uwarki ba ta isa ta faɗa mini wannan maganar ba ballantana ke! Na san ta hanyar ta zan ɓullo miki idan kin san wata ai ba ki san wata ba." A ƙufule Umaima ta murguɗa baki, "Wallahi tsaf sai na tona, atoh sai na tona asirin kowa ma ya tonu, shi kenan sai a yi biyu babu." Fulani Asabe har ta kai bakin ƙofa ta waigo da sauri, take ta karanci Umaima don haka ta koma ta zauna a kusa da ita.
"Ba ki da wayo Umaima, ina son a kashe Abdul'aziz ne domin mu samu wani kaso me tsoka, kina ga fa har yanzu ko ɓatan wata ba ki yi ba. Haka za mu zuba ido waccan yarinyar ta ƙwace gidan? Kin ga idan aka kawar da shi ba sai a ɗaura muku aure da Galadima ba?" Shiru Umaima ta yi kamar mai nazari sannan ta ɗago ta furta, "Na fahimta Inna ni kaina haushin ta nake ji don ma Allah ya sa mata take haifa." Daga haka Fulani Asabe ta fice zuciyarta cunkushe da tunani. "Tabbas na yarda harɓi ga ɗan jaki gado ne, wato ni Umaima za ta nuna wa ita jinin Kilishi ce? Da ni take zancen cikin biyu dole za a yi ɗaya tun da har ta fara zancan tona mini asiri dole na san abin yi a kanta."
Tun daga wannan ranar daga Umaima har Fulani Asabe kowa da abin da yake saƙawa a zuciyarsa, a cikin 'yan kwanakin nan ne kuma Allah ya yi wa mahaifiyar Sarki Abdul'aziz rasuwa sakamakon 'yar gajeriyar jinyar da ta yi. Dalilin da ya sa Iyayen Umaima da na Fulani babba suka zo yi wa Sarki Usman da Sarki Abdul'aziz gaisuwa, kuma a wannan zuwan da suka yi ne Umaima ta shaida wa mahaifiyarta yadda suka yi da Fulani Asabe.
"Duk da Asabe 'yar uwata ce hakan ba zai hana na kawar da ita idan tana son kawo mini matsala ba. Ki bar mini komai a hannuna, daga yau daga rana mai kamar ta yau ita da 'ya'yanta ba za su sake É—aga baki a kan sarauta da mulki a cikin gidan nan ba." Mahaifiyar Umaima ta yi maganar cikin cin alwashi.
"Fiye da haka na san za ki aikata ranki shi daÉ—e. Ba don kada na koÉ—a ki har ki ga kamar zuga ce nake yi miki ba, da sai na ce a kaf faÉ—in duniyar nan babu wanda ya kai ni sa'ar samun mahaifiya." Murmushi mahaifiyar tata ta saki.
"A kan farincikinku zan iya aiwatar da komai domin komai ba komai ba ne a wurina."
Basiru ya saki murmushin farincikin jin daɗin yabon da Boka Shaddas ya yi masa, fuskarsa ta sake faɗaɗan ƙaton hancinsa ya sake bajewa yayin da fakekiyar fuskarsa ta ƙara bajewa. "Ni mai biyayya ne a gare ka hatta rayuwar mahaifiyata idan ka na buƙata sai na ɗauko maka ita." Basiru ya faɗa cikin nuna bajinta.
Ƙuri Boka Shaddas ya yi yana kallonsa haɗe da nazartar halaye da ɗabi'un yaron. Lokaci ɗaya ya ji ƙirjinsa ya buga don gani yake tamkar yaron ya fi shi bushewar zuciya da rashin imani, amma gudun kada Basiru ya fahimci wani abu ya sa ya sakar masa murmushi sannan ya ɗebi wani ruwa mai yauƙi ya zuba a kan littafin. Lokaci ɗaya littafin ya fara fitar da wani farin hayaƙi sannan ya kai hannu ya buɗe shi, daidai wurin da Fulani Umaima ta tsaya da karatu ya buɗo don haka ya saki shu'umin murmushi ya ɗago ya dubi Basiru.
"Tabbas mun taki babbar sa'a domin Mahaifiyarka, ta ci ƙarfin karatun littafin. Da ace mun yi bori da sanyin jiki da tuni wani zancan ake ba wannan ba, sakamakon gab take da kammalawa kuma tana kammalawa za ta kai matuƙar ƙololuwar nasara. Daga haka ta mayarwa da Bamaguje littafinsa, ka ga kenan da mun tashi a tubar babu kuma babu wata amfana da za mu yi." Basiru ya yi wa Boka Shaddas jinjina da hannu.
"Ba za ta taɓa yin nasara a kanmu ba." Boka Shaddas ya jinjina kai sannan ya ɗan fara duba shafin da ya ci karo da shi.
"Duk da kasancewar zuri'ar mahaifinki sun fito ne daga zuri'ar Bargi su ne suke mulkar yankin nan bakiɗaya, wato kakanninki sune da sarautar masarautar nan. Kuma hakan ba ya hana su yin rayuwarsu ta bakin teku da koguna ba ne, dalilin da ya har suka samu kyakkaywar alaƙa tsakaninsu da jinsin Aljanun cikin ƙarƙashin ruwa waɗanda ake kira da Jinnul-Gawwas. Har ta kai sun buɗe musu su kan gansu suna iyo a cikin ruwa kamar yadda mutane ke shiga su yo su ɗin kifi, a irin wannan lokacin ne idan tsautsayi ya gifta da ajali sai ka ga sun janye mutum can cikin ƙarƙashin ruwa sai sun gama zuƙe jininsa sun ƙwaƙwale wasu hallitu na jikinsa sai su turo shi sama, wannan lamari sai ya fara damun mahaifin Kakanki har ya samu Sarkin Aljanunsu na ruwa suka yi doguwar tattaunawa suka tsayar da matsaya, a kan sun daina cin kowannen bil'adam na wannan yankin sai shekara-shekara, za su ci mutum uku saɓanin a baya da suke cin babu adadi.
Ganin hakan ne ya kawo masala shi ya sa mahaifin kakanki ya amince, kuma da yake Sarkin jinnul-gawwas Dattijon ƙwarai ne sai ya tsawatar wa da sauran waɗanda suke ƙasansa ba tare da wani ya karya alƙawarin da aka zartar ba."