← Book details Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 86

Sashe 81

Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Saboda a daidai wannan gaɓar muka fi buƙatarta, kana tunanin taurarin abar bauta za su sauka a kanta ba tare da wani dalili ba? Idan ba ka sani ba ka sani waɗannan taurarin sun sauka a kanta tun tana cikin mahaifiyarta, ka ga kuwa ai kai ma ka san banza ba ta kai zomo kasuwa."

"Lallai kuwa akwai sauran rina a kaba." Dattijo Maharaz ya furta jiki a sanyaye.

Mai gado ta rushe da matsanancin kuka don ba ta taɓa tsammanin wannan rana za ta zo a gare su ba, ganin Dattijo Maharaz da aljanar da ke ɗauke da surar Fargi sun fayyace komai dangane da Jawahir ya sa ta share hawayenta ta fara gaya musu alaƙar da ke tsakaninta da ita, tun daga lokacin da suka tsinci mahaifiyarta a daji tana naƙuda har zuwa mutuwarta da rainon Jawahir har zuwa girmanta.

Shugaba da ke durƙushe a ƙasa ya fara lalube da hannunsa sannan ya furta. "Hakika kin yaudare ni Zumjuttu, ashe ke kura ce lulliɓe da fatar akuya ban sani ba? Kin ci amanata na ba ki yarda ashe ke za ki zama silar durƙushewata, a tunanina da guntun binciken da na gudanar a halwar tsafina kullin Fargi nake gani. Don haka kacokam na mayar da hankalina wurin ganin ƙarfi da yaji sai na dakushe ta, ba zan fasa faɗa miki ba ko a haka kika bar ni kin yi nasara a kaina." Haushin Shugaba ya mamaye Sarki Sulaimanu, sai da ya haɗiyi yawu mai ɗaci sannan ya miƙa hannu zai riƙo Jawahiru da sauri Zumjuttu ta janye Jawahir. Dattijo Maharaz ya naɗe hannuwa a ƙirji yana kallon abin da Zumjuttu take yunƙurin aiwatarwa.

"A baya ku kuke da iko akan Jawahir amma wannan lokacin sai yadda abar bauta ta yi da ita, matsayinta na yanzu ya sha bambam da na baya. Idan kuna tantama za ku iya sarrafa ta ku gani." Ba Mai gado da Sarki Sulaimanu ba hatta Dattijo Maharaz sai da ya tsora ta da jin kalamanta, don ya san ba ƙananan hatsabibai ba ne. "

"Amma me ya sa kuka son cutar da yarinya ƙarama, wacce ba ta san duk abin fa yake faruwa ba." Mahaifin Fargi ya yi maganar yana hawaye, mutanen wurin suka yi tsit kowa yana mamakin abin da yake faruwa.

"Saboda Mahaifiyarta ta sadaukar mana da ruhinta da surarta domin kula da abin cikinta, bari na fayyace muku abin da ba ku sani ba hatta gawar mahaifiyarta sai da ta zama mallakinmu ce don haka abar bauta ta nemar wa 'yarta shahara da gawurtar da za ta ci gaba da amfana da ita. A daidai lokacin da ta cika shekara goma sha bakwai kuma za ta zama sadaukarwa ce ba sai na fayyace hukuncin da abar bauta za ta aiwatar a kanta ba. Ko ma dai mene ne Fargi ta tafka babban kuskure a baya, a tsammaninta abar bauta za ta ƙyale ta ne bayan ta auri ɗan wata zuri'ar da ba tata ba? Kwantan ɓauna kawai ta yi mata don haka wannan shi ne hukuncinta a fakaice. Tun da aka kafa ƙasar nan babu wanda ya taɓa aikata mummunan zunubi kamar wanda ta aikata, ka ga kuwa dole ne a tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro. Saboda ko mutuwar Fargi ma da tafukan hannuwana na hallakata, na so hallaka 'yarta sai abar bauta ta hana ni domin muna buƙatar rayuwarta."

*SHU'UMAR MASARAUTA*

*44*

*Littafin kuɗi ne 500 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*

Basiru na fita daga Masarautar Huddan kai tsaye wata maƙabarta ya nufa da take bayan garin, ya jima a labe yana dube-dube don kada wani ya gan shi a lokacin da zai shiga cikinta, don sharaɗin aikin ba a yin tsafin ɓata idan za a shiga cikin maƙabarta a gudanar da abin da za a yi, sai dai mutum ya shiga da suffarsa ta ainihi.

Ta bayan katanga ya haura sai da ya duba sababbun ƙaburbura sannan ya isa bakin wani sabon kabari, ya saka hannunsa na hagu ya fara ƙwaƙwalarsa da sauri har sai da ya ji ya fara taɓo mamacin da yake ciki, gashin Fulani Umaima ya ɗan damƙa da hannunsa ya zura cikin kabarin sannan ya haɗa da likkafanin gawar, ya zuba ƙasar a cikin sauran gashin Fulani Umaima sannan ya yanki likkafanin ya haɗa, ya ƙarasa mayar da sauran ƙasar wurin cikin kabarin sannan ya miƙe ya fice daga cikin maƙabarta. Kafin ya ƙarasa kogon tsafin mahaifinsa sai da ɗebi ƙasar wani murgujejen shuri sannan ya haɗa da ta gidan tururuwa ya haɗe su gabaɗaya.

"Na gama tsorata da lamarin yaron nan Aljani Duggu kuma jikina ya jima yana ba ni Basiru zai iya zama silar ajalina. Shugaba Zurufu ya shammace ni domin ya ci amanar ajiyar da na ba shi, ya sake ƙeƙasar wa yaron nan da zuciya ka taimake ni a bisa taimakon da ka saba yi mini ya kai madogarata." Boka Shaddas ya yi maganar tamkar zai fashe da kuka saboda tashin hankali.
"Amma kuma ka kusa ka makara Boka Shaddas! Bakin alƙalamin ya kusa bushewa don Shugaba ya gama horar da zuciyar Basiru, a hatsabibanci da rashin imani ya dame ka ya shanye, sai dai a yanzu ma ba za mu rasa taimakon da za mu yi maka ba." Aljani Duggu ya furta.

"Babban taimakon da nake son ka yi mini Aljani Duggu ka kashe mini Basiru, ka kashe mini yaron nan kawai ko hankalina zai kwanta..." Kalaman Boka Shaddas suka katse sakamakon ganin Basiru ya dira cikin kogon dutsen, Murya na rawa ya yi wa Aljani Duggu sallama ya juya wurin Basiru ganin yana sakar masa murmushi.

"Basiru har ka dawo?" Boka Shaddas ya yi maganar yana murmushin yaƙe zuciyarsa na bugawa. "Na dawo gawurtaccan Boka mai shinfiɗaɗɗan tarihi." Basiru ya ba shi amsa yana sakin murmushi.

"Dalilin da ya sa ka ganni na fita babu shiri saboda wani aiki da na saka a gaba kuma a daren yau ake buƙatar ganin kammaluwarsa, amma yanzu komai ya zo ƙarshe tun da na haɗo duka kayan aikin."
"Amma da ka yi magana ai da na sa Aljanun da ke yi mana aiki sun É—ebo maka." Boka Shaddas ya furta murya a sake don ya ga alamar tamkar Basirun bai ji tattaunawar da suke yi shi da Aljani Duggu a lokacin da ya shiga cikin kogon dutse ba.

"A yau ba sai gobe ba za ka yi bankwana da duniya, kafin kasa a kashe ni dama tuni ni na ƙuduri aniyar hallaka ka har lahira." Basiru ya yi maganar a zuciyarsa, amma a fili sai ya saki murmushi ya ce. "Rashin dabarar da ban yi ba kenan." Yana gama maganar ya isa bakin wasu ajiyayyun ƙwara gwal da ke tsaye ragowar naman jikinsu yana ci gaba da zagwanyewa, Zama ya yi a gabansa ya fara ciro kayan aikin da ya samo, ya ci gaba da jan mahaifinsa da hira. Tsafatacciyar askar da ke hannunsa a ciro ya soka a tsakiyar maƙogaron ɗaya daga cikin ƙwarangwal ɗin, take jikinsa ya fara wata irin karkarwa, sai da ya ɗauki lokaci a haka sannan ya zaro ta daga jikinsa, ta yi wani irin jawur tana ɗaukan ido.

"Irin azababban tsafin da yaron nan yake shirin yi sai fa ta kai maƙura nake yin irinsa, shin har da irinsa dama Shugaba ya koya masa?" Boka Shaddas ya tambayi zuciyarsa ƙirjinsa na bugawa, ya sauke ajiyar zuciya a hankali sannan ya ce. "Basiru wa za ka gudanarwa da aikin nan? Tabbas kowaye zai ɗanɗana azaba mafi girma kuma zai fuskanci bala'i mara yankewa." Murmushi Basiru ya yi sai da ya tsoma askar a cikin wani ruwan tsafi mai kama da manƙuli sannan ya furta. "Mai shirin cim ma buri! Domin ya samu biyan buƙatar da a kullin mafarkinsa kenan." Boka Shaddas ya maimaita kalaman Basiru ba tare da ya fahimci wurin da magaanrsa ta dosa ba. Miƙewa ya yi yana ɗan jujjuya askar ya kwashi ƙasar kabari da sauran kayan da ya haɗo ya zuba a cikin wannan ruwan, ya ɗauka ya fara tafiya a ahankali ruwan na ta zaɓalɓala.

Tun da ya fara tafiya gaban Boka Shaddas yake faÉ—uwa har sai da ya ga Basiru ya wuce wurinsa sannan ya runtse idonsa yana sauke ajiyar zuciya.

Cikin Shammata Basiru ya juyo ya kwara masa wannan farin ruwan tsafin a kan Boka Shaddas, matsawa ya yi can gefe ya ga yadda mahaifin nasa ya kwarara ihu cikin azaba. Jikinsa ne ya fara ƙamewa, fatarsa ta fara zagwanyewa ganin haka ya sa Basiru ya ƙarasa wurinsa da wuƙar, ya kai ta goshin Boka Shaddas sannan ya furta. "Ka yi haƙuri da wannan hukuncin da na yanke a kansa domin na jima da mafarkin samun kaina a wannan matsayin da kake kai, mutuwarka ɗaukakata ce don haka ba zan iya ci gaba da hangen ɗaukakata daga nesa ba. Ba iya kai ba, ita ma mahaifiyata akwai aikin da zan sadaukar da ita, ko kuma na aiwatar da wani aikin a kanta, wanda shi ne silar ɗaukakar da zan ci gaba da samu har ƙarshen rayuwata." A galabaice Boka Shaddas ya ɗago ya dubi Basiru hawaye ya fara gangarowa daga ƙandararrun idanunsa da suka fara ƙandarewa. Can jikin ƙwarangwal ɗin da ke tsaye ya nuna ya furta, "Koma can ka dawwama a haka." Tun bai rufe baki ba gangar jikin Boka Shaddas ta ja shi jikin ƙwarangwal ɗin da ke jere waɗanda ba su da adadi. Tsafatacciyar askar hannunsa ya ɗauko ya nufi wurin da mahaifinsa yake tsaye, ya ƙarasa ya soka masa askar a maƙogaronsa. Yana soka masa ita tuni jikinsa ya farar karkarwa naman jikinsa ya fara zagwanyewa yana zuba a ƙasa, sai da ya ga numfashin mahaifinsa ya ɗauke sannan ya zare askar ya mayar da ita wurin da take.
Chapter 81 · 0% Book details