← Book details Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 86

Sashe 63

Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shugaba zurufu ya jima a tsaye yana ƙarewa wutar kallo sannan ya juya da zimmar ya ƙarasa wurin Basiru da ke kwance, a jikin bango ya hangi inuwarta ta yi tsaye riƙe da ƙugu. Ƙuri ya yi yana kallonta sannan ya sauke ajiyar zuwa ya fara tunkarar bangon, kamar yadda yake tunkarar inuwar haka ya lura ita ma inuwar tana tunkaro shi.

"Babu wanda ya isa ya aikata mini haka sai ke Fargi! Me kike nema da ni da ba za ki fita daga rayuwata ba?"
"Saboda kai ne sila kuma tsanin da ka ɗora ni a doron da neke kai har na dulmiya kogin bakincikin da har duniya ta tashi ba zan taɓa fita daga cikinsa ba. Ka cutar da zuciya da ganagar jikina Shugaba, ka assassa rarrabar zuƙatan da ke cike da shauƙi da begen junansu. Ka azabtar da muradinmu a daidai gaɓar da muke buƙatar kulawar junanmu, ban san sai yaushe za ka goge tabon da ke damɓare a zuciyata ba. Amma ka sani ina mai yi maka kyakkayawan albishir, yadda ka dagula lissafin rayuwarmu daga farinciki zuwa baƙi haka zan dulmiya taka kuma na ƙuntata maka..."

"Dakata Fargi! Idan maye ya manta uwar jariri ba za taɓa mantawa ba. Zan sake tunasar da ke bakin rijiya ba wurin wasan makaho ba ne, don haka tun wuri ki kama gabanki idan ba haka ba ranki zai yi mummunan ɓaci." Shugaba Zurufu ya katse ta cikin tsawa jikinsa na karkarwa.

"Tun da ka ji makaho ya ce a yi wasan jifa ai kasan ya taki dutse ne Shugaba, har duniya ta tashi matsayinka na shugabana yana nan a idona amma ka sani ni yaɗin mage ce da ba a cinsa a zauna lafiya." Daga haka Shugaba ya ga inuwar Fargi ta ɗauke, gwaruwar ajiyar zuciya ya sauke gabansa na faɗuwa ya juya da niyyar ƙarasawa bakin halwar tsafinsa. Idanunsa suka sauka a kan Basiru da ke kwance tamkar baya numfashi, wani tunani ne ya faɗo masa ya nan take ya kece da wata mahaukaciyar dariya har sa da duka kogon dutsen ya ɗauka gabaɗaya.

Can ƙarshen dutsen na shi ya koma ya fuskanci wurin da Basiri yake kwance ya furta, "Zo zo zo." Take tsafinsa ya zuƙo Basiru da ke kwance, zuwa bangon dutsen. Motsa bakinsa Shugaba ya ci gaba da yi Basiru ya ci gaba da zuƙewa cikin jikin dutsen, Basiru na gama shigewa ciki Shugaba Zurufu ya sake kecewa dariya sannan ya furta. "Na gama da babinka Shaddas, ina nan zaune a mazaunina za ka kawo mini kanka, kuma ta hanyarka ne zan cim ma muradina a kanki. Zan taho gare ki Fargi, duk da tsafi ya tabbatar mini da kin mutu amma na yi mamakin sake dawowarki. Zan zo gare ki a wannan karon ba za ki ji ta daɗi ba."

Ganin kowa yana neman arcewa Dattijo Maharaz ya miƙe tsaye ya sha gaban Baiwa Maimuna da hallitarta ta rikiɗe zuwa wata siffar, "Tsaya a nan!"
"Saboda me za ka dakatar da ni?"
"Saboda hallitarki na yunƙurin razana bayin Allah." Dattajo Maharaz ya ba ta amsa.
"Ka san irin uƙubar da nake ciki tsawon wanɗannan shekarun? Ka san ƙalubalen da na fuskanta kuwa? Ka san me ake kira duhu da tsanani ko ka san me ake kira da zafin rijiya?" Baiwa Maimuna ta furta ta wata irin murya tamkar za ta fashe da kuka sannan ta ci gaba.

"Tun da har ba ka sani ba ka ƙyale ni na zartar da muradin da ke raina, an cutar da ni an zalince ni iya zalinta. An dakusar mini da rayuwa da burinkan da nake shirin cim ma tun a wancan lokacin..."
"Ba ke kaɗai aka zalinta ba, an zakinci mutane da dama a wurin nan don haka ki dakata abi komai a sannu." Dattojo Maharaz ya furta mata. Can gefe ta koma ta zauna tana hararar Fulani Umaima, lokaci-lokaci tana yin ƙwafa. Da ƙyar da suɗin goshi Dattojo Maharaz ya shawo kan mutanen cikin ɗakin suka zauna saboda tsoron Baiwa Maimuna, sannan ya dubi Sarki Abdul'aziz ya furta.

"A yanzu komai ya kamalla Sarki Abdul'aziz, sai dai na ce maka dabara ta rage wa mai shiga rijiya ya dira ta ka ko ya faɗa da ƙafafuwa. Ina ganin ni zan gusa domin na gama abin da ya dace, nauyi na ɗauka a kaina sai na kare martaba da ƙimar zuri'ar aminina marigayi Muhammad Safwan..."
"Amma ta inda aka hau ta nan ake sauka farin jakada, fari mai farar aniya dattijon da sai an bincika dubban al'umma kafin a samu kamarsa. Idan ka gusa a yanzu ni da iyalina ba za mu yafe maka ba Dattijo Maharaz ya kamata ka zauna ka ƙarasa warware mana zare da abawa. " Sarki Abdul'aziz ya katse Dattijo Maharaz. Sai da ya saki murmushi sannan ya furta.

"Allah ya gafarta wa Muhammad Safwan! Tabbas jini a duk inda yake jini ne. Ka yi gadon iya furta daɗaɗan kalamai Sarki Abdul'aziz sai dai ko ƙafar aminina ba ka kama ba, zan zauna tamkar yadda ka ce kuma zan yi abin da ya dace amma ba na fatan ka ce na yi maka katsalandan a duk hukuncin da na yanke." Sarki Abdul'aziz ya yi masa jinjina na hannu sannna ya ce. "Gabaɗaya kai da kaya duka mallakar wuya ne tsoho mai ran ƙarfe.

Tun daga farkon kogon dutsen Boka Shaddas yake bin ko ina da kallo har ya ƙarasa tsakiyarsa, a tsakiyar kogon dutsen ya tsugunna ya buga ƙasar da tafin hannunsa. Nan take ƙasar wurin ta fara sauya launi sai wurin ya fara rikiɗa tamkar mudubi haka wurin ya fara nuna masa tun daga farkon ɗauke littafin da Basiru ya yi har zuwa ficewarsa da tafiyarsa da Jakadiya wurin Shugaba Zurufu. Wani irin ihu da ƙaraji ya yi ya miƙe a zabure, daƙwa-daƙwan idanunsa suka sake fitowa waje, fuskarsa ta murtuke jikinsa har karkawa yake saboda ɓacin rai. A bakin rijiyar da yake gudanar da tsafinsa ya tsugunna ya rintse idanunsa sannan ya ci gaba da karatan ɗalasiman tsafinsa. Ya jima yana abu ɗaya sannan ya fara surutai cikin matsanancin ɓacin rai.

"Na yi rantsuwa da girman tsafi da sihirin da ya zame mini madogara, madogarar da zai ɗora ni a tirbar da babu taɓewa ko da-na-sani. Sai na nuna wa Jakadiya ko an ci birnin kura ba a bawa gawurtaccan kare dillanci, sai na nuna mata ba za ta ci amanata a banza ba sai ta ci ta. Kuma shi ma Basiru sai na hukunta shi da hukunci mai tsanani bayan na fanso gangar jiki da ruhinsa kamar yadda burin Shugaba Zurufu yake." Boka Shaddas yana gama maganar ya haɗe tafukan hannuwansa biyu ya buga da ƙasa, lokaci ɗaya ya ɓace daga wurin.

Dattojo Maharaz ya dubi Inna wuro sai da ya sakar mata murmushi ya furta. "An gano iyayen Kamalu." Firgigit Inna wuro da Baffajo suka ɗago suna maimata kalamansa. "Kana nufin Kamaluna an gano iyayensa?" Inna wuro ta sake tambaya murya a sanyaye, gyaɗa mata kai Dattijo Maharaz ya yi a madadin Inna wuro ta nuna farincikinta sai suka ga ta rushe da kuka. Shiru suka yi sai da ta yi mai isarta sannan ta furta. "Ko shi ya sa suka ɗauke mini shi kwana biyu ban sanya shi a idanuna ba? Yanzu raba ni da kai za su Kamalu?" Inna wuro ta ƙarasa maganar tana rushewa da kuka, ta sake ƙanƙame Kamalu kamar wani zai ƙwace shi.

"Hai aradun Allah babu mai raba mu da Kamalu, wai ma waye ya gano iyayensa? Ni ban yarda ba kawai so ake a ƙwace mana shi kuma babu wanda ya isa, yaron nan yana tsumma na ɗauke shi da hannuna yanzu katsam rana ɗaya ace an ga iyayensa." Baffajo ya yi maganar yana haɗe fuska.

"Duk da sun kasance suna da 'ya'yan da suka haifa sun nuna masa ƙauna tamkar ɗan cikinsu kuma ba su taɓa nuna bambamci a tsakaninsu ba, ni shaida ne a kan kulawa da ƙaunar da suka nuna masa tabbas sun cika jajirtattun iyaye na ƙwarai. "Kalaman Dattijo Maharaz suka ratsa Sarki Abdul'aziz. Farinciki ya mamaye shi bisa yadda ya ga suna nuna masa tsantaar kulawa. "Babu wanda zai raba ku da shi." Sarki Abdul'aziz ya furta fuskarsa ɗauke da murmushi. Da sauri Baffajo ya zube a gabansa, "Allah ya taimake ka ya ƙara maka lafiya, baya goya marayu uban marayu uban marasa gata masu iyaye da gatan ma ka gama musu komai. Mun san kai adali ne don Allah kada ka bari a zalici yaron nan a raba mu da shi." Tun da ya fara maganar Takawa yake murmushi tamkar babu wani tabon ɓacin rai a ransa.

"Kai tsaye kana magana da mahaifin Kamalu Baffajo, ina nufin Sarki Abdul'aziz shi ne mahaifin Kamalunku." Ba iya su Inna wuro ba hatta Jakadiya da Jawahir sai da suka razana da jin furucin Dattijo Maharaz, baki na rawa Baffajo ya furta. "Shi ranka shi daÉ—e shi... shi... ne mahaifin... Kamaluna?"

Dattijo Maharaz ya gyaɗa masa kai. "Ina ganin wannan shi zai sake ba wa kowa tabbacin haka." Ya ƙarasa maganar yana nuna jikin bangon ɗakin, gefen wurin da Jakadiya take zaune nan take hoton lokacin da Fulani Babba ta haihu ya fito da shawarar da Jakadiya ta bayar zuwa bayar da Kamalu da Fulani Umaima ta yi a fitar da shi. Sun shagala da kallon abin da ya faru cikin kiɗima, razani da tashin hankali Dattijo Mahazar ya katse, sannan ya dubi Jakadiya. Tun bai yi mata magana ba ta fashe da kuka cike da nadama.
"Allah ya isa tsakanina da Umaima, kin cuce ni kin saka ni a halaka." Jakadiya ta furta tana sake rushewa da kuka.

Fulani Umaima ta sunkuyar da kai ƙasa ta fara zirarar da ƙwallah murya a sanyaye ta furta. "Tabbas na yarda rana dubu ta ɓarawo ce rana ɗaya ce tak ta me kaya, tun kafin ka aure ni nake cin duniyata da tsinken tsire har kafin lokacin da duniya ta yi mini atishawar kaji, duk abin da ya faru ni ce sila. Da hannuna da gabban jiki tare da taimakon wannan tsinannan mutumin da yake iƙirarin mahaifina ne shi. Na zalinci Fulani na zalince ka ranka shi daɗe."
Chapter 63 · 0% Book details