Sashe 52
Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta farko na aure ta ne silar rashin wankan tsarkin da ba ta yi yadda ya kamata sakamakon na taɓa wucewa na ji Malam Liman yana yi wa su Dattijo nasiha a kan kyautata wankan jinin al'ada da na haihuwa kai har ma da wankan najasa. Ta biyun na aure ta ne saboda yadda nake ganin tana wanka a banɗaki babu addu'a sai surarta ta matuƙar jan hankalina, kuma har yau ta gagara samun mijin aure kai duk wani haske da taurarinta na dasashe su ko saurayo ba ta yi. Ta ukun kuma na aure ta ne saboda kwanciya baccin dare da take yi babu addu'a kai babu ɗankwali ita kuma na bar ta ta yi auren amma kuma haihuwa ce na ƙi barinta ta yi sai yawan ɓari da nake saka ta. Kasan dalili Abdul'aziz?" Cike zaƙuwa Sarki Abdul'aziz ya furta. "Sai ka faɗa Sarki Furhussam."
*SHU'UMAR MASARAUTA*
*29*
*Littafin kuɗi ne 500 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*
Murmushi Basiru ya saki sakamakon gano sirrin yadda mahaifinsa ya ɓoye littafin da yadda ake fito da shi. Sai kuma yadda shi kansa a nan gaba ba zai sha wahalar sace shi a ruwan sanyi ba, Boka Shaddas ya ɗauko littafin ya koma kusa da Basiru ya zauna.
"Ina matuƙar ƙaunarka Shaddas babban burina bai wuce na ga ka zama gawurtaccan bokan da har duniya ta tashi ba za a taɓa mantawa da shi ba, zan mallaka maka duka ƙarfin tsafina domin kai kaɗai ne jinina da ke yawo a doron ƙasa."
"Na ji daɗin wannan sadaukarwar taka mahaifina Boka Bawa, tukwicin da zan yi maka bai wuce na hallaka ka ba domin amfaninka ya ƙare a wurina. Tun ban kai shekara goma ba nake saka ido don na gano sirrin da zan kwashe duka sirrin tsafinka, amma sai yau hakan ta kasance. Ina yi maka kyakkayawan fata da kwanciya mai kyau a rayuwarka ta barzahu." Kalaman Boka Shaddas da na mahaifinsa na baya suka dawo cikin kunnuwansa tamkar a lokacin suke tattauna su, a gaɓar da mahaifinsa ya mallaka masa ƙarfin tsafinsa shi kuma ya hallaka shi. Shi kansa yana son mallaka wa Basiru halwar tsafinsa amma yana tsoron kada nan take Basirun ya hallaka shi, murmushi ya sakar wa Basiru suna haɗa ido ya furta. "Ban taɓa sanin haka ɗa yake da daɗi ba sai yanzu da na mallake ka, kafin kai na mallaki 'ya'ya biyu amma ban taɓa jin ƙaunarsu kamar kai ba. Basiru ya sakar masa murmushi sannan ya furta.
"Da sannu zan ɗauke littafin nan na hallakaka domin na mallaki duk wata ɗaukaka da ke taƙama da ita." Basiru ya raya a zuciyarsa amma a fili sai ya furta.
"Ba na ganin amfanin karanta wannan labarin, me zai hana mu je kai tsaye da aiwatar da abin da ya kamata." Basiru ya ƙarasa maganar yana zura wa Mahaifinsa daƙwa-daƙwan idanunsa.
"Tabbas har yanzu da sauranka a halwar tsafi Basiru, babban amfaninsa ga duk wanda ya ƙwallafa rai a kansa dole ne ya karanta labarin nan. Kada ka zama mai gaggawa a harkar tsafi da sihiri domin ba zai taɓa haifar maka da ɗa mai ido ba, kada ka nemi shahara da ɗaukaka idan har ba ka zama gwani a harkar ba." Basiru ya sake zuba wa Boka Shaddas na mujiya yana wani nazari daban, Boka Shaddas bai sake magana ba ya buɗo wurin da ya tsaya duk da shi kansa ba daɗin jin karatunsa yake ba, tun da ba daga farko ya fara karantawa ba amma babu yadda ya iya tun da idan ya ce zai karanta daga farko zai matuƙar ɓata lokaci.
Sarki Hafiz shiru ya yi yana kallona da alama tambayoyina ne suka yi yunƙurin daskarar da shi, ya ɗan ɗauki lokaci a haka sannan ya furta mini. "Gabaɗaya ban san ta yadda aka haihu a ragaya ba amma idan kika bi ni a sannu zan warware miki zare da abawa, abu ɗaya na sani mahaifiyarki ta sha wuya matuƙa kuma ta galabaita. Soyayya ta yi tasiri a rayuwarta kuma ita ce tsanin da ta kai ta ga halin da ta tsinci kanta a ciki." Ajiyar zuciya na sauke a fili cike da jinjina kai cike da damuwa, haka kawai na ji takaicin Aljanin da ya ƙulla soyayya da mahaifiyata.
"Tun ranar da aka ɗaura auren mahaifinki da mahaifiyarki suka fara fuskantar matsaloli ta ɓangarori da dama, domin a labarin da kakana ya bani ya ce shi ɗan autan Darri ne yake saka mahaifiyarki yin abubuwa da dama ba tare da ta sani ba. Kuma tsananin soyayyar da mahaifinki yake yi mata ya sa duk wani cin kashi da mahaifiyarki za ta yi masa ba ya yin fushi ko ya ɗauki mataki. Sun shafe shekaru da dama a cikin zaman doya da manja ba tare da wata kyakkyawar alaƙa a tsakaninsu ba, kuma a wannan lokacin aka naɗa wa mahaifinki saraurar Masarautar nan bayan rasuwar Mahaifinsa. Da yin bikin naɗin Mahaifinki ko wata guda ba a rufa ba ya yi murabus ya damƙa wa mahaifiyarki ragamar mulkin gabaɗaya, a wannan lokacin ne mahaifiyarki ta kafa tarihi domin ita ce mace ta farko da ta fara zama Sarauniya a masarautar nan. A wannan lokacin sai mahaifinki ya samu kan mahaifiyarki har ta ɗan fara ba shi kulawa, dalilin haka ya sa ya sake sakankancewa a soyayyarta. Kwatsan sai aka wayi gari mahaifiyarki ta samu ciki, tun da ta samu ciki yake wahalar da ita ƙarshe sai ɓarinsa ta yi.
Kakana ya ba ni labarin tun daga wannan lokacin sai ciki ya ƙi zama a jikin mahaifiyarki, ashe abin da ba a sani ba a bayan fage Ɗan auran Darri ne yake ɓarar da cikin a duk lokacin da ta same shi. Tafiya ta ci gaba da tafiya har mahaifiyarki ta sake komawa 'yar gidan jiya sakamakon ashe a ɓoye ɗan autan Darri ne yake kanainaye ta da daɗaɗan kalamai har ya yi nasara a kanta, kwatsam babu zato sai aka wayi gari Mahaifiyarki ta yi murabus daga kan karagarta ta damƙa masa. A wannan lokacin an ce ran mahaifinki ba ƙaramin ɓaci ya yi ba har sai da ya ƙaurace mata na tsawon makwanni, ita kuma abin da Mahaifiyarki ba ta sani ba ɗan autan Darri yana mata fadanci ne domin ya ƙarɓo wa masoyayiyarsa karagar masarautar nan ne. Kin san wace ce Masoyiyar ɗan autan darri?" Na riski tambayar Sarki Hafiz a tsakar kaina.
Yadda Basiru ya yunƙura da sauro zai wafce littafin ne ya sa Boka Shaddas ya yi saurin rufe shi, da mamaki yake bin Basiru da kallo cikin wayancewa ya furta. "Ya kai babban boka mai taƙama da tsafi da sihiri. Ni fa na ƙagauta mu kai ƙarshen labarin nan, don haka nake son karɓa na ƙarasa shi ko ma cim ma abin da muka sa a gaba." Ajiyar zuciya Boka Shaddas ya yi a karo na farko da ya ji ya ɗora zarginsa a kan Basiru, don haka bai tanka masa ba sai da tashi ya ƙarasa can wurin da ya ɗauko littafin ya mayar da shi cikin ƙarƙashin ƙasa, sannan ya koma gefen Basiru ya zauna.
Sai da Furhussam ya saki murmushi sannan ya furta, "Saboda ba zan juri ganin tana ba wa 'ya'yan da ba nawa ba kula, don a lokacin kusan haihuwata uku da ita." Jinjina kai Sarki Abdul'aziz ya yi cike da tsananin mamaki. Ya riski Furhussam ya ci gaba da cewa.
"Tun yaron nan yana tsumma muke kula da al'amuran rayuwarsa, kai hatta addinin da yake kai ba don son raina yake yi ba sai don babu yadda zan yi ne. A shekarun baya na so na ɗauke hankalinsa zuwa ga addininmu na bautar ruwa, sai Hullat ta gargaɗe ni da na ƙyale shi ya yi addinin da yake so don ko kaɗan ba ta son abin da zai takura wa Kamalu. Cikin haka yake rayuwa kuma duk shekara ina ɗaukarsa na sake gabatar da shi ga zuri'ata a matsayinsa na mamamallakin karaga kuma mijin mafi soyuwar jikata, sai dai nakan jefa masa wasu-wasu har na ya dinga ganin abin kamar ya faru kamar kuma bai faru a gaske ba. Akwai lokaci da dama da matar ubansa take nufarsa da miyagun abubuwa da kaina nake karya shi ko na dakatar da shi, kuma ina mata wannan kawaicin ne saboda kusancina da mahaifinta amma da tuni na hallaka ta. Girmansa da nake gani ne ya sa ko zancan hakan ban taɓa yi masa ba, har dai ta haƙura ta watsar da komai. A yanzu haka zancan da nake yi maka saura watanni uku cif-cif mu yi shagalin bikin tariyarsu, don haka na ci alwashin matuƙar ina raye babu yaron nan babu auren wata hallita bayan jikata. Sannan wannan butar da ya zo ya ajiye ka san ta mece ce?"
Tun Furhussam bai ambaci sunan Sarki Abdul'aziz ba ya girgiza masa kai, sannan Furhussam ya ci gaba da cewa.
"Wannan sihirtacciyar butar a ƙallah ta shafe sama da shekara dubu biyar, kuma an tono ta ne daga ƙarƙashin ƙasar Rumi da ke fadar Sarki ɓaƙaƙen aljanun ƙarƙashin duwatsu. Haƙiƙa Kamalu ya ɗora ƙwarya a gurbinta, domin alwashi ne ga magabatanmu a kan wannan butar ga duk wanda ya dawo da ita duk abin da ya yi niyya dangane da buƙatar ransa nan take za a zartar masa da ita. Amma na yi mamakin dalilin da ya sa Fargi ba ta aiko ɗiyarta ta zartar da wannan aikin ba." Da mamaki Sarki Abdul'aziz ya furta.
"Shin dama wata ce ta turo shi? Wace ce ce ita?"
"Ba faɗar labarinta ne ya kawo ni ba Sarki Abdul'aziz, ka bari idan na zartar da abin da yake gabana zan iya feɗe maka biri har wutsiyarsa." Fursussam ya furta cike sa ƙagauta.