Sashe 37
Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ƙirjin Kamalu ya ci gaba da bugawa jin labarin da Baffajo yake ba shi, wani irin nauyi kansa ya yi har yaji ƙafafuwansa na yunƙurin bijirewa nauyinsa. Da sauri ya fice daga ɗakin, ya ci gaba da wurga ƙafarsa cikin sauri ba tare da ya san inda yake sa ƙafarsa ba. Can wani ɗan siririn lungu ya bi mai tsananin duhun itace, ya sa mu bakin bishiyar ɗorawar da ke wurin ya zauna. Hannuwa biyu ya sa ya dafe kansa cikin matsananciyar damuwa, tamkar ƙaramin yaro haka ƙwalla ta fara bin idanuwansa zuciyarsa na yi masa ƙuna.
"A wannan lokacin da kake ciki sam kuka ba zai fisshe ka ba, kuka da raunin zuciya bai yi daidai da tsarin zubin hallita da ruhinka ba. Ina sake yi maka tuni da kai ba kamar su ba ne, ina ɗora ka a hanya ne saboda aminantakar da ke tsakanina da marigayi Sarki Muhammad Safwan. Ba ni da ikon da zan shiga huruminka domin zuri'ar da ke tare da kai akwai jiƙaƙƙiyar 'yar tsamar da ke tsakaninmu don haka na ke yunƙurin ɗora ka a hanya, idan na nemi na fayyace maka komai zan iya jefa zuri'ata da ta mutanen cikin gidan nan cikin rijiya gaba dubu, da babu rai ɗaya da zai iya tsalle ballantana ya fito. Burinsu su ci gaba da zama tare da kai domin su riƙa cin gajiyarka, amma na tabbata ko ba daɗe ko ba jima akwai lokacin da gaskiya za ta yi halinta. Ina mai haƙurƙurtar da kai mummunan lamarin da zai afka wa rayuwarka babu tsammani, sai dai ina mai shawartarka da ka sanyaya zuciyarka a lokacin da komai zai bayyanar maka." Gama jin kalamansa ya sa Kamalu ya ɗago a sanyaye, ko kaɗan bai fahimci kalamansa ba don haka ya sake sunkuyar da kai haɗe da faɗa wa duniyar tunani.
Jakadiya ta matuƙar tsorata da ganin yadda Fulani babba ta koma a cikin kwana ɗaya jal tamkar wacce ta shekara guda tana jinya.
"Jakadiya ki dubi Allah ki ce wa Takawa ina buƙatar ganinsa, akwai kalaman sirrin da suke cikin zuciyata da nake son sanar da shi, kalaman da shi kaɗai ya cancanci saninsu don a ganina watarana za su yi masa amfani." Fulani babba ta yi maganar murya can ƙasa idaununta har sun fara shanyewa.
"Idan gemun ɗan'uwanka ya kama da wuta maza yi saurin yayyafawa naka ruwa." Jakadiya ta yi maganar a zuciyarta, saboda ganin jikin Fulani babba ba ƙaramin tsoratata ya yi ba. Jiki a sanyaye ta fice kai tsaye ta nufi sashen Takawa a wannan karon tausayin Fulani babba ne ƙarara a zuciyarta.
"Allah ya taimaki ubangidana wani muhimmin saƙo ne tafe da ni ranka shi daɗe." Jakadiya ta furta cikin girmamawa.
"Muna sauraronki Jakadiya."
"Allah ya taimake ka Fulani ta wayi gari cikin matsananciyar jinya har ta kai tana son ganinka domin ta ba ka wasiyya." Take annurin fuskarsa ya É—auke har sai da Jakadiya ta sha jinin jiminta.
"Jakadiya a fice a ba mu wuri muna tattaunawar sirri da manyan baƙi, a je a ce wa Fulani Umaima ta yi duk abin da ta ga ya dace game da magungunan da za a aika mata, idan da hali a gaggauta aikawa sashen ma'ajiyar magunguna idan mun kammala za mu san abin yi."
"Ai na san dama biri ya yi kama da mutum, kallo É—aya na yi wa Fulani na fahimci tsafin Umaima ne ya ci ta, ya zame mini dole na tashi tsaye a kan Sailuba." Jakafiya ta yi maganar a cikin zuciyarta.
"Jakadiya muna buƙatar a ba mu wuri, ba ma buƙatar sake ganin kowa a sashenmu." Kalaman Sarki Abdul'aziz suka sauka raɗau a saman kunnuwan Jakadiya, baƙinciki da ya cika ta kai tsaye sai ta koma sashen Fulani babba ta sanarwa da Mai gado saƙon Mai martaba sannan ta wuce sashen Sailuba don hankalinta ba ƙaramin tashi ya yi ba.
Wani irin zafi Fulani babba take ji a cikin jikinta tamkar ana ɗana mata rodin da ke cikin wuta, daga ƙafarta zuwa ƙirjinta wani abu ne take jin yana yi mata yawo duk inda ta ji abin ya sauka a jikinta sai dai ta ji tamkar yana yagar fatar jikinta. A galabaice murya can ƙasa ta furta.
"Mai gado ki taimaka miki, jikina zafi yake don Allah ki taimaka mini mutuwa zan yi." Mai gado ta goge hawayen idonta, "Ranki shi daÉ—e ba za ki mutu ba In shaa Allah za ki samu lafiya." Da Baiwa Zainaba ta É—ebo garwashi ta É—auko wani turaren miyagu, aka fara turarawa a cikin É—akin.
"Mai gado ƙasana zazzagowa yake ki taimaka za su yage mini ƙasana." Fulani ta yi maganar tana sa hannuwa biyu a ƙasanta tana dannewa, wani irin zuuu ta ji saman mamanta. Ta ƙwalla ƙara cikin azaba tana kai hannu ƙirjinta. "Ƙirjina Mai gado, don Allah ki kira mini Takawa ki kawo mini Abubakar zan yi masa kallon ƙarshe."
*Littafin kuɗi ne 500 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*
Dafa kafaÉ—arsa Dattijo Maharaz ya yi sannan ya furta.
"Kada ka sare!"
Kamalu da kwanyarsa ke barazanar tarwatsewa ya furta. "Don Allah ka rabu da ni na ji da abin da yake damuna." Shiru Dattijon ya yi har zuwa É—an wani lokaci.
"Da alama fushin zuciya na iya yin galaba a kanka wanda hakan zai iya kai ka ga turbar danasani. Da sannu, za ka fahimci abin da nake son nusar da kai." Daga haka Dajjito Mahraz sai ya yi gaba abin sa, har ya ɗan yi wa Kamalu nisa sai kuma Kamalu ya ga rashin dacewar abin da ya yi masa, da sauri ya miƙe ya rufa masa baya. Bai san dalili ba amma haka kawai yake jin gabaɗaya wunin ranar jikinsa babu daɗi ga wata irin faɗuwar gaba da ta saka shi a gaba, ilahirin jikinsa a mace yake don haka koda ya ƙarasa wurin Dattijo Maharaz ya ɗan jingina da wata bishiyar darbejiya kansa na wani irin sara masa.
Bayan fitar Jakadiya da kansa Sarki Abdul'aziz ya tashi ya ƙara gyara rufin labulen ɗakin, haka kawai ya ji wata irin tsanar Fulani babba ta mamaye zuciyarsa. A ɓangare guda kuma rashin kuzarin da ke tare da shi ya haddasa masa ciwon jiki, bayan sun gama tattaunawa da baƙin wurinsa ya ji ilahirin jikinsa ya mutu ciwon kai ya lulluɓe shi, bayan sun tafi kwanciya ya yi saboda yadda tsagin kansa yake ciwo tamkar zai tarwatse masa. Lokaci-lokaci ƙirjinsa na bugawa bai san dalili ba, yana nan kwance bacci ya yi awon gaba da shi.
A ranar da Fulani babba ta samu labarin auren Sarki Abdul'aziz da Umaima ba ƙaramin damuwa ta shiga, take kishin mijinta ya mamaye ta amma gudun kada magautanta su fahimci lagonta ya sa ta nuna tamkar abin bai dame ta ba. Lokacin da aka ɗaura auren Fulani Umaima da Sarki Abdul'aziz a sannan Fulani Babba tana da 'ya ɗaya wato Khadija sai kuma tsohon cikin Sakina, don haka Fulani Umaima tun farko ta shiga da niyyar salwantar da abin da yake cikin Fulani babba. Amma da yake mahaifiyarta ta ɗora ta a turbar zuwa wurin Bamaguje take ya yi mata binciken abin da za ta haifa wato 'ya mace ce, dalilin haka ya sa Fulani Umaima ba ta damu ba take ganin tamkar dama ita ake jira ta zo cikin masarautar ta haifo Yarima mai jiran gado.
Hankalin mahaifiyarta da ita kanta bai gama tashi ba sai lokacin da ta shafe sama da watanni ba tare ɓatan wata ba, kamar haɗin baki suna cikin fafutukar neman magani sai Fulani Asabe ta zo mata da maganar da ta nemi girgiza hanjin cikinsu.
Ƙuri shugaba Zurufu ya yi wa Fargi da ke hannun mahaifinta sannan ya nuna wani farin kaskon ƙarfe da ke tafarfasa da ruwan zafi, da hannu ya nuna masa kason sannan ya furta.
"Ka ajiye ta a nan domin na tsaurara bincike a kanta."
Babu musu mahaifinta ya ɗora ta a saman ruwan zafin ta ci gaba da mutsu-mutsu, sannan Shugaba Zurufu ya ɗebo wani jan gari mai haɗe waɗansu gajerun ƙasusuwa ya watsa mata. Wani haske ya gani ya gifta masa, sannu a hankali hasken ya dusashe sai wani zanen farin doki ya bayyana a saman goshinta. Da sauri Shugaba Shaddas ya saka hannu a saman goshin nata domin ya kwashen fararen taurarinta, bai yi tsammani ba ya ji wata irin haniniyar doki a saman kansa. Da sauri ya waiga bai ga komai ba don haka ya sauke ajiyar zuciya a kasalce.
"Al'amarinta daban yake, na lura da baƙon lamarin da ke tattare da ita. Akwai ɗaukaka marara gushewa domin sanin kanku ne tsafi ko sihirin da ya shafi dawaki alheri ne. Don haka ina mai yi maka albishiri da karɓar wannan yarinya a matsayin waccan zan horar da horarwata ta musamman, na yi maka alƙwari matuƙar ta samu horon daga gare ni za ta maye gurbina da duk wata gawurtar tsafina. Yanzu ina buƙatar ka ɗauke ta zuwa gaban abin bauta don samun albarka mafi girma daga gare shi."
Zuciyar Mahaifin Fargi fes ya karɓe ta ya fice da ita zuwa wurin abin bauta.
Kafin wani lokaci tuni labarin karamcin da Shugaba Zurufu ta yi wa Fargi ya watsu, sai girma da mutumcin mahaifinta ya sake lulluɓe idanun al'ummar Rumzu. Suka ci gaba da yi masa fadanci kowa na son nuna kulawa a gare shi, a ɓangare ɗaya kuma Shugaba Zurufu ba ƙaramin mamakin lamarin yarinyar ya yi ba, don haka ya ɓullo da wannan dabarar da rainon ta a hannunsa ko ba komai zai samu damar shiga halwar tsafinsa don ya kwashe tarin arziƙin da ke ɗauke a cikin rayuwarta.
Zuciyar Mai gado ta gama karyewa cikin ɗimauta da tashin hankali ta ƙarasa wurin Fulani babba ta rungume ta tana sakin kuka cike da tausayi. A wannan lokacin Fulani babba ta gama galabaita numfashinta ya fara sarƙewa cikin haki sama-sama ta furta. "Don Allah... ki kira mini... Takawa." Da sauri Mai gado ta miƙe jiki na rawa ta fice da niyyar zuwa sashen Takawa, a babban tsakar gida ta haɗu da Fulani Umaima saboda tashin hankali ko lura da ita ba ta yi ba.