← Book details Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 86

Sashe 35

Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Duk ma inda kika ɓoye shi sai na lalubo shi, saboda dole ne na cika umarnin mai gida. Don haka idan kere na yawo zabo na yawo dole watarana za a haɗu. Ki rubuta ki ajiye ko da arziƙi ko da tsiya sai na mallaka masa littafin nan." Yana gama maganar ya gegare ta ya wuce har yana bangazarta ya fice daga ɗakin.

"Duk rintsi kada ki sake wani ya ƙwace littafin nan daga wurinki Umaima."
"Ke ba kamar sauran kowa ba ce a wurina don haka na damƙa miki wannan sihirtaccan littafin ki kula da shi."
"Ina fatan dai kin yi wa littafin nan kyakkyawar maɓoya?"
"Ina sake jan hankalinki kada ki saki jiki da kowa a kan wannan littafin duk kusancinki da mutum koda É—an cikinki ne!" Ire-iren kalaman da Bamaguje yake furta mata kenan a lokutan baya idan ta ziyarce shi, ajiyar zuciya ta sauke ta shiga kiciniyar gyaran uwar É—akinta don ba ta barin kowacce Baiwa ta shigar mata É—aki saboda kayan tsubbace-tsubaccan da ta rataye.

Sai da Jawahir ta ɗaga rigarta ta ɗora hannunta saman tambarin cikinta ta yi kasaƙe kamar wacce take sauraron wani abu sannan ta furta, "Tsohuwar guba ce da ta bi ilahirin jiki da ruhinsa, ban san tsahon lokacin da ta ɗauka a jikinsa ba amma ta riga da ta illatar da ruhi da gangar jikinsa." Jawahir ta ɗan ɗago ta kalli Mai gado. "Na san faɗa za ki yi mini Inna amma da na sanar wa Fulani Babba don a nema masa magani." Shiru Mai gado ta yi tana nazari.

"Idan kina dakatar da ita za ta daina sanar da ke halin da take ciki." Tsagin zuciyar Mai gado ta gargaɗe ta. Sai da ta sake janyo Jawahir jiki sannan ta furta. "Jawahir duk cikin gidan nan babu wacce nake so nake ƙauna har a raina kamar Fulani babba, to amma ki dubi matsayinmu a cikin gidan nan. Mu ƙasƙantattu ne da ba su da 'yan kansu ballantana galihu, ban da Allah Ya sa Fulani babba ta ja mu a jiki da bautar da za mu dinga yi irin ta su Laure ce. Furta irin waɗannan maganganun matuƙar suka fito sarari ba zai haifar mana da ɗa mai ido ba, Idan kin yi mafarki ko wani tunanin ya zo miki ki same ni a ɗaki ki riƙa gaya mini idan ya so sai mu tattauna ni da mahaifinki." Ganin Mai gado ta bata ƙwarin gwiwa ya sa ta ji daɗi har ta faɗaɗa fara'arta a fili, fita ta yi don ta ɗauro alwala Mai gado ta bi bayanta da kallo cikin jimami da matsananciyar damuwa.

Sai da ta tabbatar su Jawahir sun tafi sussuƙar gero sannan ta kira Umaru don su tattauna matsalar da Jawahir take son ɓallo musu.

"Malam ba ya ta haihu fa?"

"Kamar yaya?" Ya tambaye ta fuska É—auke da damuwa.

"Da alama zancan mahafiyar yarinyar nan na ci gaba da bayyana, idan ba ka manta ba da kanta ta ce mana 'yarta ce za ta bayyana surar jinsi da ta hallitar zuri'arsu bakiɗaya." Duk abin da Jawahir ta faɗa wa Mai gado tas ta kwashe ta gaya masa, shiru ya yi sannan ya furta. "Ki ci gaba da jan ta a jiki kada ki bari ta furta wata maganar da za ta kai ga jawo mana matsala, zan shirya fitar sirri akwai wani Mai magani da na ji Mai martaba ya sa an karɓo wa Fulani magani a wurinsa." Sai da Mai gado ta ji haka sannan ta ɗan saki ranta ta ci gaba da harkokinta.

Sai da asuba ta yi sannan Fulani babba ta iya buɗe idonta, ta yunƙura da niyyar tashi lokaci ɗaya ta ji jikinta tamkar an ɗaɗɗaure ta. Motsa ƙafarta take son yi amma sai ta ji ilahirin jikinta ya yi mata nauyi dum! Kamar an danne ta da narkeken dutse, wani abu da ya sake ɗaga hankalinta yadda take jin jikinta tamkar ba nata ba. Tana daga kwance ta fara ƙwalla wa Mai gado kira ita da Baiwa Zainaba amma shiru babu wanda ya amsa mata. Tana nan kwance hawaye ya fara gangaro mata don duk yadda ta so iya motsa jikinta abin ya gagara, sai da gari ya waye tangararan ta fara jiyo gwarancin Abubakar don ta tabbata yunwa yake ji. Babu jimawa ta ji sallamar Baiwa Zainaba, da sauri ta fara jera mata kira. Jin kiran ba na lafiya ba ne ya sa Baiwa Zainab ta faɗa ɗakin da sauri.

"Allah ya taimake ki ranki shi daÉ—e."

Take zuciyar Fulani Babba ta karye murya na rawa ta furta, "Shigo Zainab." A hankali Baiwa Zainab ta shiga É—akin.

"Zainab wata ƙaddarar ta sake rikito wa rayuwata, tun asuba idona biyu amma na gagara motsa koda ɗan yatsana ne. Maza je ki kira mini Mai gado ki ce ta zo cikin gaggawa."

SHU'UMAR MASARAUTA

20

*Littafin kuɗi ne 500 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*

Tun da ya yi wa Baffajo tambayar ƙirjinsa yake bugawa fat fat fat zuciyarsa tamkar za ta hudo ƙirjinsa, fargabarsa ɗaya kada ya ji mummunan labari a kan tushen asali da samuwarsa.

"Kamalu da waɗannan hannuwan nawa na tsinto ka a cikin kogon wata ƙatuwar bishiyar kukar da ke cikin ƙasurgumin wani dajin da ke cikin Rigar Arɗo wanda ake kira da Dajin Wushushe da ke gefen ƙoramar Ɗinya, a ranar da ake gudanar da babban bikin shaɗi tun safe na tashi da kasalar jiki ban san dalili ba don har na fasa fita kiwon Shanu sai kawai wata zuciyar ta shawarce ni da na bi bayan su Salele. Cikin ƙudurar Ubangiji bayan na tafi sai wani irin zazzaɓi ya rufe ni, don haka na nemi gefen bishiya na ɗan kishinhiɗa don jikina babu ƙwari. Kamar almara ina zaune sai na fara jin kukan jariri daga gefena, nan take na ciro guruna da layun da ke ƙuguna don a tunanina ko mutanen nan dajin ne suke niyyar buɗe mini idanu da tsakar rana, har na fara haramar yin turare sai idanuwan suka kai kanka kana kwance cikin kogon bishiyar kukar da kallonta kaɗai sai da ya hargitsa mini kwanta. Wata irin juwa na ji tana yunƙurin ɗaukata, idanuwana suka fara yi mini gizo har nake ganin bishiyar tamkar tana tafiya a bisa kanta. Kamar na wuce sai kuma nake jin zuciyata ta yi rauni ba zan iya barinka ba. Idan idanuwana ba gizo suke yi mini ba a lokacin da na fara tunkarar murgujejiyar bishiyar kukar, har gani na yi tamar tana matsawa baya da kanta. A haka na ci gaba da tafiya zuciyata na rawa har na ɗora hannuna a kanka na ɗauko, sai dai abin da ya matuƙar ba ni mamaki bai wuce ganin wani zagayayyan jini a saman kanka ba tamkar wanda aka ɗora hular sarauta.

Wani abu da ya sake tsinka mini rai ganin na kai hannuna kanka don na goge jinin kai amma kuma sai na ga tamkar danƙare yake a fatar jikinka, a haka na rungume ka har zuwa gida na kawo wa Innarka kai sai dai muna zuwa gida wannan jinin babu shi babu alamarsa. Ina tunanin hankalina ya kwanta sai kuma muka lura da wani baƙon al'amari a tattare da kai wanda ba mu taɓa ganin halittar ɗan adam da irinsa ba."

Lokacin da Mahaifiyar Fulani Umaima ta samu Umaima da buƙatar Fulani Asabe ta zo da ita, tamkar dama tana son abin a ranta don ko a fuska ba ta musa ba. A ranar da Fulani Asabe za ta koma a ranar suka wuce tare da Fulani Umaima.

Fulani Umaima tun tasowarta fitsararriyace ga rashin tsoro duk wani abu da za ka yi mata baraza da shi ba zai tsorata ta ba. Uwa-uba kafiya, taurin kai ta taurin zuciya. Tana da matuƙar wayo sosai don lokaci ɗaya ba za ka taɓa gane ainihin halayya da ɗabi'unta ba, tun ba ta kai haka ba ta iya makirci, kissa da kisisina saboda ko a cikin Masarautarsu Mahaifiyarta ba ta jin ko ɗar a game da ita, kuma duk cikin 'ya'yanta ta fi ji da ita. A ranar da ta fara tozali da Sarki Abdul'aziz a ranar kwana ta yi tana ayyana abubuwa da dama a cikin zuciyarta, a yadda zuciyarta ta yi nisan kiwo a kansa ba ta jin za ta iya rabuwa da shi kamar yadda Fulani Asabe ta ce za su yi auren jeka na yi ka.

Sannu a hankali sai ta fara shige wa Fulani babba tana yi mata hidimar ɗan aikace-aikace da taya ta hira, da farko daga Mai babban ɗaki har Fulani babba babu wanda ya saki jiki da ita, sai daga baya da suka ga yanayin kyawawan ɗabi'un d Umaima ta nuna musu sai suka sako jiki da ita. Makwan Umaima takwas Fulani Asabe ta ba ta wani farin kwalli ta ce ta saka shi kuma ta tabbatar da sun haɗa ido ita da Sarki Abdul'aziz, daɗi ya lulluɓe Umaima har murnarta ta bayyana a fili.

"Ba na son sakarci fa, kada ki ɗauka auren jindaɗi da kwanciyar hankali za ki yi." Da kamar Fulani Umaima ta musa amma sai ta ƙaƙalo murmushi ta furta. "Ba ina yin murmushin saboda wata manufa ba Inna, ina sakin murmushin murna da jin daɗin ganin mulki da sarautar gidan nan sun kusa dawowa tafin hannunmu ne." Fulani Asabe ta saki murmushin farinciki.

"Shi ya sa nake ƙaunarki uwar ɗakina." Shiru Fulani Umaima ta yi tana bin Fulani Asabe da kallon ba ki da hankali, don haka ta sake kwantar da kanta har lokacin da Allah ya haɗa fuskarta da Sarki Abdul'aziz. A ranar da ya yi tozali da ita a ranar ne ya yi tattaki har zuwa wurin Mahaifinsa da maganarta. Bai hana shi ba don ganin shi ne shugaba kuma wakilin Masarauta, don haka cikar kamalarsa za ta ƙaru ne idan ya tara iyali sama da ɗaya. A lokacin da Mai babban ɗaki ta samu wannan labarin ranta ba ƙaramin ɓaci ya yi ba, don haka kawai ta ji Umaima ba ta kwanta mata ba, take ta nuna wa Sarki Usman rashin amincewarta amma sai bai ba ta goyon bayan ba.
Chapter 35 · 0% Book details