← Book details Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 86

Sashe 33

Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"A gafarce ni uwar gijiyata babu abin da na gani. Sannu Gimbiyar mata In shaa Allahu, Allah zai buɗi ido lafiya." Fulani Umaima ba ta iya amsawa ba sakamakon jin nishi ya taho mata, sai kuma ta ji tamkar an saka farata masu tsini ana fisgar ƙasanta hakan ya sa ta sake riƙe Inna wuro nan take jariri ya faɗo babu jimawa mabiya ta biyo baya. Inna wuro na kai idonta kan jaririn ƙirrr ta ga ya zuba mata ido yana kallonta babu ko ƙiftawa, sai kuma idanunsa na juya mata kamar ana gara ƙwallo, a haka ta ga ya mayar da idonsa kan Fulani Umaima yana hararta ita ma fuskarsa tamkar ba ta jariri ba, lokaci ɗaya Inna wuro ta ji wani irin tsoro ya kamata da sauri ta kawar da kanta gefe. Babu yadda ta iya haka ta sa hannu ta yanke mabiyar ta naɗe ta gyara wurin, sai dai idan ba gizau idonta ya yi mata ba har gani ta yi yanayin surar fuskar jaririn tana rikiɗa daga wannan kammanin zuwa wani, a zabure ta sake kai idonta kansa don yadda ta ji faratan hannuwansa sun karce da ƙarfi har sai da wurin ya yi shati, don haka ta yi saurin kawar da kanta gefe gabanta na matsanancin bugawa.

Duk wani aiki da Ungozoma take aiwatarwa Inna wuro ce ta gudanar a cikin daren, kafin wani lokaci Fulani Umaima ta fito shar ita da jaririnta. Tun da Inna wuro ta fita wankin kayan da aka ɓata Fulani Umaima ta ɗauki jaririn ta ƙura masa idanu, fuskarsa faffaɗa ce mai ɗauke da ɗan buɗaɗɗan hanci da manyan idanuwansa ma su ban tsoro. Kuma jarirantakarsa ba ta ɓoye jajayen idanunsa ba, lokaci ɗaya ta ji gabanta ya yi mummunar faɗuwa don babu ta inda jaririn nan ya ɗauko kamannin Sarki Abdul'aziz ko kuma kammaninta.

"Kar dai a ce wannan ɗan Boka Shaddas ne?" Fulani Umaima ta faɗa a hankali ƙirjinta na bugawa. Ba ta da amsar tambayarta don haka ta ja bakinta ta tsuke, suna haɗa ido da jaririn sai ta ga tamkar harara yake wurga mata, a ɓangare guda kuma yadda kansa yake suɗal babu ko ɗigon gashi a jiki. Sai da Inna wuro ta gama komai sannan Fulani Umaima ta ba ta umarnin zuwa ta sanar a lungu da saƙon cikin masarautar, har zuwa wurin Jakadiya don ta sanar da Sarki Abdul'aziz.

Idan lokacin bikin ya zo mutanen Rumzu kan É—auki kwanaki biyar suna shagali, kuma kowacce rana da kalar dabbar da za su yanka su yi watanda da ita. Sai dai daga amarya har ango ana gasa musu naman tantabaru kullin, don su ba sa cin naman da 'yan biki za su ci. Ana gobe za su tare sai a kai su bakin bishiyar kukar da suke bautawa su yi tsirara su kwana a haka domin ta saka albarka, a kan sabuwar rayuwar da za su fara gudanarwa. Washegari da sassafe sai duka 'yan garin sun taru a bakin bishiyar don yi wa abar bauta godiya sannan a kai amarya da ango É—akinsu.

Tun daren ranar Jawahir ban da tsala kuka babu abin da take yi, duk yadda aka kai ga rarrashinta abin ya ci tura. Haka Mai gado ta saka ta a gaba ita ma ta fara zubar da ƙwalla don a tsammaninta wani abu ne yake damun Jawahir. Sai kusan doshin asuba sannan ta samu bacci ya yi awon gaba da ita.

Ayarin waɗansu baƙaƙen mutane ya gani tafe sun dunfaru sashen Mai martaba hannuwansu ɗauke da miyagun makamai, cikin sanɗa yake biye da su da zarar ya ga za su waigo sai ya yi saurin laɓewa a wani lungun. Yana biye da su har suka shiga ɗakin Mai martaba, ta gefen da yake hangarsu wani jariri ya gani fuskarsa sam ba ta yi kama da ta ainihin jarirai ba. Yana nan tsaye ya ga jaririn ya dira a gaban Takawa.

"Ni ne ajalinka wallahi sai na kashe ka na kashe duka mutanen masarautar nan! Sai mun kafa sabuwar da'ira ni da mahaifina domin wannan masarautar ba ta dace da shi ko kai ba. Mahaifiyata Fulani Umaima ce, ita ma ba zan bar ta ba har sai na hallaka domin na tabbata nan gaba tana iya hallaka mahaifina." Yana gama faɗar haka ya bushe da wata irin dariya, daga cikin bakina wani baƙin jini ne ya fara ɗiga. Jin motsin Kamalu ya sa gabaɗaya suka kallo wurin da yake ɓoye, suka dunfaro shi gadan-gadan da niyyar hallaka shi.

"Kamalu! Kamalu me yake damunka?" Kalaman Baffajo suka tashe shi daga mummunan mafarkin da yake yi. Ya haɗa gumi sharkaf jikinsa sai karkawa yake, tsoro ƙarara ya bayyana a idonsa. Da sauri Baffajo ya rungume shi a jikinsa ya fara tofa masa addu'a sai da ya ga Kamalu ya dawo cikin nutsuwarsa sannan ya ɗago shi ya ce.

"Mafarki ka yi ne Kamalu? Kullin fa ina gaya maka idan za ka kwanta ka ɗauko wannan layar da na baka ka saka ta a ƙasan kanka. Dubi hannunka kamar ka Kamalu a ce ko guru babu a jikinka, an ya kamalu rayuwa za ta tafi haka?"

"Baffajo za su kashe Mai martaba, wallahi har mutanen masarautar nan gabaɗaya ni ma gab nake da su kashe ni. Kuma jaririn ya ce mini wai ɗan Fulani Umaima ne, shi ne yake fesar da jini wallahi har kaina ya nufo zai hallaka ni." Ya ƙarasa maganar yana cusa kansa a cikin ƙafafuwansa. A wannan karon jikin Baffajo ba ƙaramin sanyi ya yi ba, fargaba ta dirar masa da jin kamalan Kamalu na ƙarshe. Ya dafa kafaɗarsa.

"Ka yi shiru Kamalu kada ka saka mu a matsala, ka daina ambatar sunan iyayen gidanmu idan aka ji kashinmu ya bushe. Babu wata halitta da za ta iya cutar da mu In shaa Allah. Idan Allah ya kai mu gobe zan shiga dawa na haɗo maka turaren miyagu da ƙwanƙwamai ka ji." Kai kawai Kamalu ya iya gyaɗawa amma har lokacin ƙirjinsa bugawa yake.

Tun a cikin daren Inna wuro ta fita ta sakin guɗa tana shelar haihuwar Fulani Umaima, kafin wani lokaci gabaɗaya maganar ta karaɗe cikin masarautar. Mai martaba da ya ji maganar ya nuna farincikinsa sai dai babu wani ɗoki da nuna zumuɗin irin wanda ya yi a lokacin da ta haifi Muhsin. A yanzu babba burinsa bai wuce ya ga Allah ya sauki Sailubansa lafiya ba. Bayan Inna wuro ta gama shelar tana komawa wurin Fulani Umaima ta sallame ta tare da yi mata alƙawarin babbar kyauta zuwa wayewar gari. Tun da farar safiya Inna wuro da sauran Bayin Fulani Umaima suka shiga yi mata hidimar ɗora ruwan wanka da abin da ba a rasa ba, Fulani babba ma tun da wuri ta shiga yi mata barka sai dai ita kanta Fulani Umaima a ƙasan zuciyarta kunyar nuna wa mutane jaririn take don gani take kamar wani zai yi mata wata fassarar, ko a gano jaririn ba jinin Takawa ba ne.

Tun a ranar da ta haife shi wani abu ya nemi ɗaure mata kai, idan ta fita zuwa banɗaki ko yin wani uzurin, tana dawowa za ta ci karo da ɓoyayyun kayan tsafinta a gefen jaririn. Wani lokacin ma har akwatin da ta ajiye littafin da Bamaguje ya ba ta take ganin a kawo ta tsakiyar ɗakin, idan zuma ta ajiye ko nono da kunu suma haka za ta zo tarar an shanye kusan rabi ko fi ma. Wani lokacin kuma a yi mata faca-faca da shi a ɓata mata ɗaki, tsoro-tsoro ta fara ji don idan take bin jaririn da kallo kuma ƙir haka za ta ga ya kafe ta da ido yana kallo.

*Fulani Umaima ta samo daidai da ita.*🤣🤣🤣🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️

SHU'UMAR MASARAUTA

19

*Littafin kuɗi ne 500 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*

Ganin tsaiwa da saƙa da warwara ba zai kai ta ba ya sa Fulani Umaima ɗan ƙwanƙwasa ƙofar da ɗan ƙarfi haɗe da ɓoye sihirtacciyar butar a cikin zaninta.

"Waye nan?" Ta ji an furta, ana ƙarasowa wurin ƙofar.

"Muna buƙatar ganawa da Mai martaba."Cewar Fulani Umaima.

Da mamaki Dogarin yake duban Fulani don a lokacin dare ya yi kusan sha biyu ta É—an gota. "Allah ya taimake ki ranka shi daÉ—e ya jima da kwanciya..."

"Kana nufin ba zan iya ganinsa ba?" Fulani Umaima ta furta a harzuƙe. Babu musu ya turo ƙofar sai da ta shiga ta wurga masa harara sannan ta wuce cikin sashen Mai martaba. Tana shiga soron ƙarshe ta ja ƙofarsa ta datse cikin sanɗa ta wuce ta ƙofar sashen shaƙawatar Sarki Abdul'aziz, duhun daren bai sa Fulani Umaima ta tsorata ba don haka sai da ta yi tafiya mai nisa sannan ta tsugunna a bakin wata bishiya ta fara haƙawa da sauri. Sai da ta tabbatar da ta yi haƙa mai ɗan zurfi sannan ta tura butar ta mayar da ƙasar ta rufe, a fili ta saki murmushin samun nasara tana jin wani farinciki na ratsa ta tamkar wacca aka yi wa kyautar aljanna. Da sauri ta kewaya ta buɗe ɗakin Sarki Abdul'aziz bakinta ɗauke da sallama a lokacin tuni ya jima da yin bacci, sai da ta jima a tsaye tana kallonsa sannan ta bubbuga ƙafarsa. Da mamaki yake kallonta ya yunƙura ya tashi zaune yana shirin yin magana ta riga shi.

"Wallahi tsora ta ni ake yi yanzu haka bacci ya gagari idanuna." Mamaki ya bayyana ƙarara a fuskarsa. "Tsoro fa? Me yake tsora ta ki?"

"Tafiya nake ji sai kuma na ji an koma!" Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya furta. "Shi kenan sai ki kwanta a nan." Yana gama maganar ya matsa mata, a yadda ta lura sam bai ji daÉ—in kwananta ba. A fakaice Fulani Umaima ta sakar masa harara.

"Da ni kake zancan ba dai kana wani rawar ƙafa a kan Fulani Babba ba kai wai mai mata, za mu gauraya ne." Fulani Umaima ta yi maganar a zuciyarta. Rage kayan jikinta ta fara yi sannan ta koma gefen Takawa ta kwanta zuciyarta ƙal saboda tsabar farinciki kasa runtse idanunta ta yi ba ta san lokacin da bacci ya ɗauke ta.
Chapter 33 · 0% Book details