Sashe 26
Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"A don haka su ma waɗannan mushen Saniyar na daga mazauna cikin masarautar nan, kuma a tabbatar an gargaɗi talakawa a kan koda wasa kada wani ya yi gangancin aiwatar da wani ƙudiri game da shanun, abu ɗaya aka lamunce a duk ranar da aka yi tozali da su a tabbatar an kawar da su zuwa babban juji kamar yadda ake yi a baya." Surutu ne ya fara tashi sama-sama kowa ya fara tofa albarkacin bakinsa bayan doguwar tattauna Mai martaba ya shiga gida sannan kowa ya kama gabansa.
A kullin lamarim larurar Fulani Babba ƙara ta'azzara take, abin da yake sake ɗaga mata hankali bai wuce yadda fitsarin da take yi ya ci gaba da bibiyarta har ta kai tana yinsa ido biyu, daga baya sai abin ya zame mata tamkar mai yoyon fitsari ba ta ɗaukan wani lokaci mai tsawo sai zanin jikinta ya jiƙe sharkaf. Da ta ayyana za ta nemi magani game da ciwon ko ta sanar da Sarki Abdul'aziz sai ta ji kanta ya yi nauyi lokaci ɗaya ta manta halin da take ciki, hatta ibada sau tari idan ta yunƙura da niyyar gabatar da sallah sai ta fara wasu-wasin sallar Azahar ce za ta yi ko La'asar. Wani lokacin har sai tambayi Bayinta ko su Khadija idan suna kusa da ita, a ɓangare ɗaya kuma duk ranar da muradin mijinta ya bijiro mata na son ƙeɓewa da shi to ranar haka za ta kwana tana mafarkin Takawa ya zo zai kusance ta ta ƙarfin tsiya kuma duk yunƙurinta na ƙin amince masa haka zai yi amfani da ita ta ƙarfin tsiya sannan ya ɗago yana sheƙa mata wata iriyar dariya. Duk ranar da ta yi wanna mafarkin idan ta wayi gari wuni za ta yi wani irin ruwa mai ɗoyi yana ta fita daga jikinta. Abin ɓoye kusan ya fito fili domin kusan duk Bayin masarautar sun fahimci Fulani Babba ba ta da kwana a wurin Mai martaba, sai dai jifa-jifa ya kan neme ta da rana ta je turakarsa su ɗan taɓa hira shi ma ba wata hirar kirki suke yi ba. Kusan abin sai ya haɗe mata goma da ashirin ga ciwon Abubakar da kullin gaba yake yi ga ita ma nata, domin a wannan lokacin Abubakar bai ciki bambamce tsabar abinci ba da ƙasar da yake rayuwa a cikinta, kowanne ya samu danƙarawa cikinsa yake yi. Ya zama tamkar mujiya hatta bayin da ke yi masa hidima a tsorace suna yi masa su kammala, don sau babu adadi yana kama Bayi idan sun shiga bashi abinci ko gyra shi ya riƙa cizgar gashin kansu yana cinyewa. Dalilin haka ya sa Dogarawa ke ɗaure shi kafin a shiga ɗakin, hatta su kansu sai sun yi da mugun gaske.
A 'yan kwanakin waɗansu irin mafarkai take yi na Abubakar wai yana zaune sai kuma ta ga wani mai tsananin kama da shi ya zo yana jan hannunsa a kan ya miƙe su tafi. A mafarkin da ta yi na ƙarshe kafin ya kama hannun Abubakar sai ya isa gare ta ya furta mata. "Me ya sa bakya sona kika bari na yi nisa da ke, ni ma ɗanki ne don Allah ki dawo da ni gare ki." Hawayen idanunta ta share ta furta. "Ta yaya uwa za ta ƙi abin cikinta ina matuƙar ƙaunarka..." Kalamanta suka katse a lokacin da ta ga ya riƙo hannu Abubakar ya miƙe tsaye tun yana tangal-tangal har ya take ƙafafuwansa, cike da murna ta fara bin su tana ƙwala musu kira amma kafin ta isa sun ɓace wa ganinta." Firgigit ta farka tana sauke ajiyar zuciya, ta yi mamakin nannauyan baccin da ya yi awon gaba da ita da tsakar rana. Sau tari ta kan yi mafarkin ta haifi tagwayen jariri duka maza, amma da ta tashi ɗaukansu sai ta nemi ɗaya ta rasa.
"Barka da tashi uwar gijiyata." Mai gado ta furta da ke gefe zaune a gabanta. "Mai gado na jima ina bacci ko?"
"Ranki shi daÉ—e ai hutu ne kika samu uwar gijiyata."
Fulani babba ta matuƙar aminta da Mai gado saboda yanayin riƙon amana da rashin kwaramniyarta. Sai da Fulani Babba ta tashi zaune sannan ta tattara hankalinta wuri ɗaya ta furta. "Mai gado wata tambaya gare ni."
"Ina sauraronki ranki shi daÉ—e?"
"Don Allah mace na iya haihuwa ba tare da tana cikin hayyacinta ba har ta manta da abin da ta haifa?"
Tafiya suke cikin baƙin dajin da ke cike da ban tsoro, firgici da tashin hankali. Kukan tsuntsayen da ke dajin ya isa ya hautsina kwanyar mai tafiya a cikinsa. Bakin wani kogo suka shiga suna tafe suna faɗin.
"Mu masu bin umarninka ne sau da ƙafa." Jakadiya ce a gaba sai Fulani Umaima da ke biye da ita har suka ƙarasa bakin wata ƙatuwar rijiya da wani Boka ke zaune a saman ruwanta, a madadin ruwa a cikin rijiyar wuta ce ke ci ganga-ganga. Tsirara yake babu sutura a jikinsa, duk da dare ne amma kogon dutsen a haske yake tarwai kamar rana da wani sihirtaccen haskensa.
"Barka da aiki Boka Shaddas, ka yi naka ka yi na kowa duk wanda ya ja da kai ya halaka." Faffaɗar fuska gare shi kamar faranti mai ɗauke da ƙaton hancin, jajayen idanu da jan leɓe. Wata irin dariya ya saki mai kama da kukan jaki." Ku dakata a nan me neman biyan buƙatar ita za ta ƙaraso." Ƙatuwar muryarsa ta ƙaraɗe cikin kogon dutsen, jiki na rawa Fulani Umaima ta fara takawa da sauri har ta isa gare shi. "Daga yau za ki daina sallah da wanka tsarki har tsawon shekara guda, ki tabbata duk abin da muka umarce ki za ki aiwatar mana kuma ki sa a ranki bauƙatarki tamkar ta biya ne."
Fulani Umaima ta furta. "Duka na amince, matuƙar buƙatata za ta biya ko me kake so zan aiwatar da shi." A karo na biyu ya sake sakin dariya mara daɗin saurare. "Ba ma buƙatar tukwicin komai sai na jinin mahaifiyarki, mahaifinki da ɗan cikinki. Sannan kuma dole ne mu lashi zumar jikinki ta hanyar kusanctarki. Matuƙar kika aiwatar da wannan ina mai yi miki rantsuwa da sirrin tsafi da sihirina a duniyar nan babu abin da za ki nema a wurin mu ya gagare ki."
SHU'UMAR MASARAUTA
15
*Littafin kuɗi ne 500 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*
Yanayin da Fulani take ciki na rashin Ruƙayya ya sake tunzura ta game da Bayinta don haka kowannensu yake kaffa-kaffa da shayin yin abin da zai saɓa mata. Ko motsi kaɗan idan ka yi matuƙar bai yi mata ba nan take za ra zartar maka da mummunan hukunci. Dama yaya lafiyar kura ballantana ta ci nama. Lokacin da mutanen Masarautar mahaifanta suka ƙarasa Masarautar Huddam domin yin gaisuwa sai Bayinta suka samu sauƙi game da tsangwama da ƙyarar da suke fuskanta. Ranar larabar da Boka Shaddas ya umarce ta a ranar ne ta je turakar Sarki Abdul'aziz don ta aiwatar da ƙudurinta, ta ji daɗi matuƙa da ta samu turakar tashi ba ya nan. Da sauri ta ɓarɓada maganin a saman gadon sa ta yadda ƙwayar ido ba za ta yi saurin fahimtar komai ba. Ta kewaya banɗaki ta haɗa masa ruwan wanka tana fitowa ta ji shigowarsa, cikin kissa ta sakar masa murmushi. Martanin murmushi ya mayar mata don bai manta ba rabon da ya ga fara'arta tun kafim rasuwar Ruƙayya, ya rungoma ta jikinsa suka zauna a gefen gado yana kallon fuskarta da ta yi fayau saboda ramar da ta yi.
"Sarkina barka da hutawa, da fatan kana cikin walwala da farinciki?" Tallafota ya yi suna fuskantar juna.
"Sarauniyata kin fi kyau a haka don Allah ki cire komai daga ranki. A lokacin da Allah ya ba mu Ruƙayya bai shawarce mu ba, don haka da zai karɓe ta ba zai yi shawara da mu na. In shaa Allah, zai ƙara azurta mu da wasu masu albarka a nan gaba." Take idanunta suka ciko da ƙwalla, ganin haka ya sa ya goge mata yana kwantar da ita a ƙirjinsa.
"A baya ne nake kewar Ruƙayya Sarkina domin shaƙuwar ɗa da mahaifi daban take, ta fi gaban duk mai tunani. Babu wacce za ta fahimci hali da damuwar da nake ciki mahaifiya kamar. Damuwata ta yaye ƙunci ya kau, a yanzu tun da ina da kai ba za ka sake ganin ƙwalla a saman fuskata ba, ka zame mini taurarom da ke hasken birnin zuciyata don kawar da duhun da ya ratsa ta na 'yan kwanakin d suka shuɗe. Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana Sadaukina, kulawarka a gare ni na ƙara mini ƙwarin gwiwa ɗari bisa ɗari." Ya ji daɗin kalamanta ƙwarai don haka ya ci gaba da bubbuga bayanta, babu jimawa hirar ta su ta fara sauya salo har Fulani Umaima ta ribace shi suka gudanar da mu'amala a saman shimfiɗar kamar yadda boka Shaddas ya gaya mata. A wannan karon Takawa ne ya fara zuwa banɗaki ya tsaftace jikinsa da ruwan da Fulani ta haɗa masa wanda ya ji magani da sihirtattun turaruka masu ƙamshi, bayan ya fito ita ma ta faɗa ta yi wanka ta dawo kusa da shi ta kwanta.
"Ki taso mu je bakin bishiyar kukar can kada ki sa na yi asarar kuɗina Sailuba, ke fa idan kika sa kanki kin fiye gardama da taurin kai." Jakadiya ta yi maganar ƙasa-ƙasa ganin Sailuba na ɓata fuska.
"Inna ya za a yi a ce na tuɓe a bakin bishiya da tsohon daren nan don Allah, ni wallahi kunya nake ji ba zan iya ba."