← Book details Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 86

Sashe 24

Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"A don haka su ma waɗannan mushen Saniyar na daga mazauna cikin masarautar nan, kuma a tabbatar an gargaɗi talakawa a kan koda wasa kada wani ya yi gangancin aiwatar da wani ƙudiri game da shanun, abu ɗaya aka lamunce a duk ranar da aka yi tozali da su a tabbatar an kawar da su zuwa babban juji kamar yadda ake yi a baya." Surutu ne ya fara tashi sama-sama kowa ya fara tofa albarkacin bakinsa bayan doguwar tattauna Mai martaba ya shiga gida sannan kowa ya kama gabansa.

A kullin lamarim larurar Fulani Babba ƙara ta'azzara take, abin da yake sake ɗaga mata hankali bai wuce yadda fitsarin da take yi ya ci gaba da bibiyarta har ta kai tana yinsa ido biyu, daga baya sai abin ya zame mata tamkar mai yoyon fitsari ba ta ɗaukan wani lokaci mai tsawo sai zanin jikinta ya jiƙe sharkaf. Da ta ayyana za ta nemi magani game da ciwon ko ta sanar da Sarki Abdul'aziz sai ta ji kanta ya yi nauyi lokaci ɗaya ta manta halin da take ciki, hatta ibada sau tari idan ta yunƙura da niyyar gabatar da sallah sai ta fara wasu-wasin sallar Azahar ce za ta yi ko La'asar. Wani lokacin har sai tambayi Bayinta ko su Khadija idan suna kusa da ita, a ɓangare ɗaya kuma duk ranar da muradin mijinta ya bijiro mata na son ƙeɓewa da shi to ranar haka za ta kwana tana mafarkin Takawa ya zo zai kusance ta ta ƙarfin tsiya kuma duk yunƙurinta na ƙin amince masa haka zai yi amfani da ita ta ƙarfin tsiya sannan ya ɗago yana sheƙa mata wata iriyar dariya. Duk ranar da ta yi wanna mafarkin idan ta wayi gari wuni za ta yi wani irin ruwa mai ɗoyi yana ta fita daga jikinta. Abin ɓoye kusan ya fito fili domin kusan duk Bayin masarautar sun fahimci Fulani Babba ba ta da kwana a wurin Mai martaba, sai dai jifa-jifa ya kan neme ta da rana ta je turakarsa su ɗan taɓa hira shi ma ba wata hirar kirki suke yi ba. Kusan abin sai ya haɗe mata goma da ashirin ga ciwon Abubakar da kullin gaba yake yi ga ita ma nata, domin a wannan lokacin Abubakar bai ciki bambamce tsabar abinci ba da ƙasar da yake rayuwa a cikinta, kowanne ya samu danƙarawa cikinsa yake yi. Ya zama tamkar mujiya hatta bayin da ke yi masa hidima a tsorace suna yi masa su kammala, don sau babu adadi yana kama Bayi idan sun shiga bashi abinci ko gyra shi ya riƙa cizgar gashin kansu yana cinyewa. Dalilin haka ya sa Dogarawa ke ɗaure shi kafin a shiga ɗakin, hatta su kansu sai sun yi da mugun gaske.

A 'yan kwanakin waɗansu irin mafarkai take yi na Abubakar wai yana zaune sai kuma ta ga wani mai tsananin kama da shi ya zo yana jan hannunsa a kan ya miƙe su tafi. A mafarkin da ta yi na ƙarshe kafin ya kama hannun Abubakar sai ya isa gare ta ya furta mata. "Me ya sa bakya sona kika bari na yi nisa da ke, ni ma ɗanki ne don Allah ki dawo da ni gare ki." Hawayen idanunta ta share ta furta. "Ta yaya uwa za ta ƙi abin cikinta ina matuƙar ƙaunarka..." Kalamanta suka katse a lokacin da ta ga ya riƙo hannu Abubakar ya miƙe tsaye tun yana tangal-tangal har ya take ƙafafuwansa, cike da murna ta fara bin su tana ƙwala musu kira amma kafin ta isa sun ɓace wa ganinta." Firgigit ta farka tana sauke ajiyar zuciya, ta yi mamakin nannauyan baccin da ya yi awon gaba da ita da tsakar rana. Sau tari ta kan yi mafarkin ta haifi tagwayen jariri duka maza, amma da ta tashi ɗaukansu sai ta nemi ɗaya ta rasa.

"Barka da tashi uwar gijiyata." Mai gado ta furta da ke gefe zaune a gabanta. "Mai gado na jima ina bacci ko?"

"Ranki shi daÉ—e ai hutu ne kika samu uwar gijiyata."

Fulani babba ta matuƙar aminta da Mai gado saboda yanayin riƙon amana da rashin kwaramniyarta. Sai da Fulani Babba ta tashi zaune sannan ta tattara hankalinta wuri ɗaya ta furta. "Mai gado wata tambaya gare ni."

"Ina sauraronki ranki shi daÉ—e?"

"Don Allah mace na iya haihuwa ba tare da tana cikin hayyacinta ba har ta manta da abin da ta haifa?"

Tafiya suke cikin baƙin dajin da ke cike da ban tsoro, firgici da tashin hankali. Kukan tsuntsayen da ke dajin ya isa ya hautsina kwanyar mai tafiya a cikinsa. Bakin wani kogo suka shiga suna tafe suna faɗin.

"Mu masu bin umarninka ne sau da ƙafa." Jakadiya ce a gaba sai Fulani Umaima da ke biye da ita har suka ƙarasa bakin wata ƙatuwar rijiya da wani Boka ke zaune a saman ruwanta, a madadin ruwa a cikin rijiyar wuta ce ke ci ganga-ganga. Tsirara yake babu sutura a jikinsa, duk da dare ne amma kogon dutsen a haske yake tarwai kamar rana da wani sihirtaccen haskensa.

"Barka da aiki Boka Shaddas, ka yi naka ka yi na kowa duk wanda ya ja da kai ya halaka." Faffaɗar fuska gare shi kamar faranti mai ɗauke da ƙaton hancin, jajayen idanu da jan leɓe. Wata irin dariya ya saki mai kama da kukan jaki." Ku dakata a nan me neman biyan buƙatar ita za ta ƙaraso." Ƙatuwar muryarsa ta ƙaraɗe cikin kogon dutsen, jiki na rawa Fulani Umaima ta fara takawa da sauri har ta isa gare shi. "Daga yau za ki daina sallah da wanka tsarki har tsawon shekara guda, ki tabbata duk abin da muka umarce ki za ki aiwatar mana kuma ki sa a ranki bauƙatarki tamkar ta biya ne."

Fulani Umaima ta furta. "Duka na amince, matuƙar buƙatata za ta biya ko me kake so zan aiwatar da shi." A karo na biyu ya sake sakin dariya mara daɗin saurare. "Ba ma buƙatar tukwicin komai sai na jinin mahaifiyarki, mahaifinki da ɗan cikinki. Sannan kuma dole ne mu lashi zumar jikinki ta hanyar kusanctarki. Matuƙar kika aiwatar da wannan ina mai yi miki rantsuwa da sirrin tsafi da sihirina a duniyar nan babu abin da za ki nema a wurin mu ya gagare ki."

SHU'UMAR MASARAUTA

14

*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

*SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?*
*TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI*
*SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA*

*Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.*

👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.*

*1. Supplements na gyaran jiki ciki da waje*

*2. Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba*

*3. Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya*

*4. Supplements na karawa fata kyau da sheki glowing skin*

*5. Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci*

*6. Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki*

*7. Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu*

*8. Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.*

*9. Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje*

*10. Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*

*11. Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement*

*12. Supplements na gyaran HQ ciki da waje*

*13. Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14. Supplement na whitening/glowing skin*

*15. Supplement for Acne, dark spots remover*

*Da duk wasu nau'in supplement da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*

*Littafin kuɗi ne 500 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*

Jin takun tafiyar su ya sa gaban Kamalu ya ci gaba da faɗuwa jikinsa ya ɗauki karkarwa, can jikin bango ya sake maƙalewa yana fatan kada Allah ya sa su cim masa don shi kansa ya san idan suka gan shi tsaf za su iya kashe shi, ba su yi tsammani ba suka ga Jakadiya ta faɗo cikin soron hannunta ɗauke da aci bal-bal. Tana hango su Galadima ta kalle su da mamaki, "Yautai mugun tsuntsu ma sha miyarka sai ya yi dare.Daga ina kuke da tsohon daren nan?" Ta yi maganar tana kallon Ciroma. "Tararuwa mai wutsiya ganinki ba alheri, ina zuwa haka?" A yatsine ta kalle shi.

"Jikina yana ba ni akwai ƙullin da kuke ɗaurawa don banza ba ta kai zomo kasuwa!" Ciroma ya wayance."Daga cikin gida muke ke fa ina za ki?"
Chapter 24 · 0% Book details