← Book details Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 86

Sashe 45

Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lokacin da Kamalu ya ji tambayar Galadima ya ɗan so ya duburburce, Dattijo Maharaz ya dafa kafaɗarsa ya furta. "Ka ce masa ita karaga tana ga mamallakinta ne ba wanda yake son mallakarta ƙarfi da yaji ba, jinin Marigayi Sarki Muhammad Safwan har abada ba ya buƙatar tilastawa. Mai karaga yana ga abarsa duk rintsi duk wuya, kuma ko ba-daɗe ko ba-jima mai ita zai maye gurbinsa." Kamar yadda Kamalu ya ji haka ya sanarwa da Galadima. Take ya lura da yanayin firgici da tashin hankalin da ya shiga, lokaci ɗaya Galadima ya ji ƙafafuwansa na namenan gagarar ɗaukar nauyin gangar jikinsa. Ganin haka ya sa Dattijo Maharaz ya ja hannun Kamalau suka fice daga cikin soron. "Wane ne shi? Ya aka yi ya san wannan furucin tsohon furucin, ɗan waye shi da zai faɗi wannan maganar mai tasiri ga wanda zai iya baƙuntar karagar Masarauta?" Da sauri Galadima ya bi bayansu amma sama da ƙasa ya nemi Kamalu ya rasa.

Dattijo Maharaz da Kamalu suna fita suka ci karo da Baffajo da yake ta bulayin neman Kamalu, da sauri ya damƙi hannunsa suka ɗauki siiririyar hanyar da a ta sada su da sashen bayi. A wannan lokacin Dattijo Maharaz ya so sanar da Kamalu tushen labarinsa da asalinsa, amma sanin firgicin da ke tare da Baffajo dangane da maganar da Kamalu ya ji daga gare su ya sa ya ƙale shi sai bayan wani lokaci, amma ya ci alwashin a haɗuwarsa ta gaba zai feɗe masa biri har wutsiya. Idan ya so duk wacce za a yi sai a yi tsakaninsa da zuri'a da suka yi kane-kane a cikin rayuwar Kamalu.
*SHU'UMAR MASARAUTA*

*25*

*Littafin kuɗi ne 500 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*

Kiran sallar asubar farko ne ya farkar da Sarki Abdu'aziz daga nannauyan baccin da ya yi awon gaba da su, haka kawai ya ji jikinsa ya yi masa nauyi da tsami kamar wanda aka yi wa duka. A ɓangare ɗaya yana mamakin yadda bacci ya yi awon gaba da su duk da irin mummunan halin da suke ciki, a hankalin ya miƙe ya fita ya ɗauro alwala yana shigowa ya ga Mai martaba mahaifin Fulani babba ya tashi. Da kanshi ya zuba masa ruwa a buta ya ajiye masa, sannan ya koma gefe ya zauna ya zuba wa gawar Fulani babba idanu da ke kwance babu motsi.

"Sarkina watarana fa daga mu biyun nan za mu koma mu uku, daga haka fa sai a gan mu har da jikoki ko?"
"Ina matuƙar ƙaunarka Sadaukina, shi ya sa nake addu'ar Allah ya sa na riga ka mutuwa don ba zan iya jure rashinka ba."
"Don Allah a duk lokacin da kake gaban gawata ina son ka shaida Wa Ubangiji ni mai biyayyar aure ce kamar yadda kake faɗa, ko roƙa mini yafiyar laifukana ka kuma nema mini salama a cikin makwancina." Lokaci ɗaya kalaman Fulani Babba na tsahon shekarun baya suka dawo masa, a lokacin ba su fi shekara biyu da aure ba don ko Fulani Umaima bai aura ba.

"Ke 'yar aljanna ce Fatima! Ke mai biyayyar aure ce Fatima. Allah ya gafarta miki Ubangiji ya ni'imta makwancin da za mu kai ki, amma me ya sa za ki tafi ki bar ni? Me ya sa mutuwarki ta shammace ni..." Kuka ya ci ƙarfin Sarki Abdul'aziz dalilin haka ya gagara ƙarasa kalaman bakinsa, har yanzu gani yake mutuwarta tamkar mafarki ce da yake fatan farkawarsa a kowanne lokaci. Sai a yanzu ne yake tuna irin zaman 'yan marinar da suka dinga yi tsakaninsa da ita yana mamakin musababbin faruwar haka. Wani irin ɗaci ya mamaye zuciyarsa tare da nadama, da-na-sani da kaicon cusgunawar da ya yi mata, babban takaicinsa bai wuce yadda nadamar ta zo masa a lokacin da ba za ta yi masa amfani ba.

"Taso mu je masallaci sun shiga Sallah, sai haƙuri Abdul'aziz kuka ba zai dawo mana da Fatima ba." Mahaifin Fulani babba ya yi maganar yana janyo hannun Sarki Abdul'aziz, masallaci suka wuce kowannensu zuciya babu daɗi.

"Lafiya kika aika kirana da wannan farar asubar Sailuba? Wallahi ba ƙaramin faɗar mini da gaba kika yi ba, mene ne yake faruwa?" Jakadiya ta yi maganar ƙasa-ƙasa. Kalaman Jakadiya a madadin su sanyaya zuciyarta sai kawai ta fashe da matsanancin kuka, da sauri Jakadiya ta matsa wurin Sailuba tana zama a gefenta wani irin wari ya mamaye hancinta. Da sauri ta ja baya tana ɗan toshe hanci gabanta na tsananin bugawa. "Wani me ye wannan yake wari Sailuba?" Da mamaki Sailuba ke kallon jikinta don ita babu wani da take ji, sai da ta share hawayenta sannan ta furta. "Inna tun daren jiya nake tsula fitsarin kwance ga wani ruwa mai ɗoyi na fita daga ƙasana, ina zuwa banɗaki na yi wanka na ga kwarkwata na faɗowa daga kaina na shiga uku Inna ina tsoron kada irin ciwon Fulani ya same ni."

"Jakadiya ni warkice daidai da ƙugun kowacce shegiya, ki rubuta ki ajiye Umaima ba kanwar lasa ba ce kuma ko an ci birnin kura ba a taɓa ba wa ingarman kare dillanci. Wallahi ni Umaima sai na muzanta rayuwarku na maisheku ƙanƙantattun marasa amfani." Take kalaman Fulani Umaima na baya suka dawo cikin kunnuwan Jakadiya, wani irin matsanancin tsoro ya dirar mata.

"Fitsari fa Sailuba? Kina nufin fitsarin kwance?" Sailuba ta gyaÉ—a kai tana share hawaye.

"To ai ni yanzu ma wani irin warin jaɓa na ji kina yi, na san wannan ba zai wuce sharrin Umaima ba. Wato dai abin da nake zargi ya tabbata, ta gama da Fulani babba yanzu za ta dawo kanki." Sailuba ta zaro idanu a firgice.

"Na rantse da girman Allah, kwarankwatsa dubu da ɗoriya ko zan yi yawo tsirara sai na nuna wa Fulani Umaima ta tsokano tsuliyar autan dodo. Sai na nusar da ita duk girman bishiyar kuka bagaruwa ce babba, ni Jakadiya na yi artabu da waɗanda suka ninke Umaima a fanin hatsabibanci da tsafi na yi galaba. Wallahi-wallahi sai na shammace ta; ta ɓangaren da ba ta taɓa tsammani ba. Sai na cusa mata baƙincikin da har abada ba za manta da shafina ba, kuma sai na ɗanɗana mata azabar da ruwa ko teku bai isa ya sanyaya mata uƙubar da take ciki ba. Ki kwantar da hankalinki Sailuba matuƙar ina numfashi, sai Umaima ta durƙusa da gwiwoyi biyu a gabanki tana neman afuwarki."

Yarjejeniyar da Fargi ta ƙulla tsakaninta da baƙaƙen aljanun ita ta sake ba ta damar samun ɗaukaka mafi rinjaye a cikin dajinsu, har ya zama ayyukan tsafi da dama sun koma hannunwanta sai dai idan ta ga aikin ya yi mata sai ta miƙa wa Shugaba Zurufu ya tayata. Wannan ɗaukakar da Fargi ta sake samu sai ta sake ninka ƙiyayyarta da ke cikin zuciyar Shugaba, har ya fara keɓantacciyar shawara da shugabannin aljanu domin su ba shi mafitar da zai hallakar da ita a ruwan sanyi amma hakan bai samu ba.

A lokacin da Fargi ta kai shekara goma sha uku ta fara zama budurwa, kyawun sura da na halitta suka bayyanar mata. Baƙa ce ba can sosai ba, sai dai doguwa ce tana da tsayi ba ta da kauri sosai. A wannan lokacin cika da ƙasaitar tsafinta ta tunbatsa don haka samarin cikin zuri'arsu suke shakkar tunkararta da niyyar ƙulla soyayya, sakamakon tsoron kada ta fusata har ta ɗauki mummunan hukunci a kansu. A na cikin wannan yanayin kwatsam Boka Ɗan tani ya kawo Ɗan sarkin ƙasar Bahdi wurin Shugaba a kan ayi masa aikin da za a hallaka yayansa idan ya so ya gaji karagar mahaifinsa. Shugaba Zurufu duk yadda ya so ya buga aikin Sulaiman sai lamarin ya gagare shi sakamakon shi ma Yariman da aka kawo mahaifiyarsa a tsaye take tsayin daka wurin tsubacce-tsubacce, a wani binciken da ya yi ma ya gano shi da kansa ya yi wa mahaifiyar Yariman aikin da Mahaifinsa zai yi murabus ya damƙa masa. Ganin babu nasara ya sa Shugaba ya sallami Sulaiman ba tare da yin nasara ba, a sanyaye ya fito daga kogon dutsen ya hange ta a tsaye a jikin dokinsa tana aiwatar da ɗan tsafe-tsafenta da fuskar dokinsa. Idan ta shafa fuskarsa sai ta koma zuwa da saniya, agwagwa, zaki, kura da duk sauran kayan namun dajin da take buƙata.

"Idan aka bar shi da fuskar damisa yau ina na kama?" Sulaiman ya yi maganar cikin zolaya. Waigowa ta yi ta sakar masa murmushi. "Sadaukin namiji ba a san shi da jin tsoro ba. Kai da kake burin zama Sarkin Bahdi dole ka janyo bargon jarumta ka lulluɓawa kanka." Kallon mamaki ya bi ta da shi, ta ɗan matsa daf da shi.

"Za ka samu sarautar Masarautar Bahdi indai da yawan numfashi amma kuma sai dai ba ta sigar da kake buƙata ba." A karo na biyu ya sake zuba mata idanu da matsanancin mamaki.

Kasancewar duk wasu masukantan Fulani babba sun hallara, gari na ɗan washewa aka fito da gawar Fulani Babba, dubannan mutanen manya da yara ne suka sallaci gawarta sannan aka wuce da ita gidanta na gaskiya. Sarakuna daga ƙasashe da dama ne suka ziyarci Sarki Abdul'aziz domin yi masa ta'aziyyar rashin uwar gidansa, kuma uwar 'ya'yansa. Ilahirin mutane gidan kowanne ka dube shi cikin alhini da jimamin mutuwar Fulani babba yake, Abubakar da ke ɗakinsa sai bin mutane yake da kallo ba tare da ya san abin da yake faruwa ba. Abu ɗaya yake yi kuka idan ya ji yunwa ta dame shi, kuma da ya ga baƙin fuskar ba bai saba gani ba sun shiga ɗakinsa sai ya fara bige-bige yana son cakumo mutum. Mahaifiyar Fulani babba ban da kuka babu abin da take musamman da ta kalli Abubuwar, Su Khadija kowacce ta zo da 'ya'yanta amma kallo ɗaya za ka yi musu ka fahimci suna cikin matsananciyar damuwa.

Mahaifiyar Fulani Umaima da 'yan uwanta ba su iso ba sai bayan da aka kai gawar Fulani Umaima, kallo ɗaya mahaifiyarta ta yi mata ta fahimci akwai wata a ƙasa game da mutuwar Fulani babba.
Chapter 45 · 0% Book details