← Book details Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 86

Sashe 41

Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Mutuwa fa Inna? Kina nufin Fulani Babba dai tamu ce ta mutu." Salatin da suka ji daga waje da kururuwa ne ya sa Mai gado ta yi saurin fita, wasu daga cikin Bayin tuni suka fara koke-koke da kururuwa wannan ta sa jikinta ya sake yin sanyi don ta fahimci labarin mutuwar ya zo gare su.

Waɗannan sawayen hannuwana tsofaffin Sarakunan masarautar da suka yi zamani a masarautar nan ne, wannan ramin taɓon da kake gani tun zamanin mahaifina ya haƙa shi. Dubi can ka gani." Dattijo Maharaz ya nuna wa Kamalu wani farin dutse cikinsa wani mudubi ne mai ɗaukar ido. "Leƙa fuskarka ka gani!"

Babu musu Kamalu ya leƙa fuskarsa, a ɗan razane ya ɗago kansa cikin tsoro. Dattijo Maharaz ya saki murmushi, "Kada ka tsorata Sadauki sake leƙa fuskarka hakan ya kasance tamkar sunna ne a cikin masarautar nan ga duk wani mai matuƙar muhimmanci gare ta."

Kafin wani lokaci tuni maganar mutuwar Fulani babba ta zaga lungu da saƙon da ke masarautar Huddam, mutane da dama sun jimanta mutuwarta kama daga cikin Bayi Kuyangu, Dogarai Hadimai da duk waɗanda suke rayuwa a cikin masarautar. Duk wanda zai buɗe baki sai dai ya faɗi alkairi da kyawun halinta, a ɓangare guda kuma mutane suka fara jimanta yanayin sabuwar rayuwar da Abubakar zai fuskanta ta maraici a nan gaba.

Tun ba a ɗauki lokaci ba Sarki Abdul'aziz ya sa aka rubuta wasiƙa zuwa masaarautar Mahaifan Fulani babba domin a shaida musu da mutuwarta cikin gaggawa, tun daga cikin gari har zuwa sauran ƙasashen da ke maƙota da ƙasar Huddam suka shiga aiko masa da tarin takardun ta'aziya.

"Haƙiƙa mun yi babban rashin da har abada ba za mu samun gurbin da zai maye mana shi ba, Allah ya huci zuciyar Mai martaba ya sanya maka dangana. A madadina da na iyalan ƙasa da masarautar Huddam muna mai yi maka ta'aziyar rashin Fulani Babba." Fulani Umaima ta ƙarasa maganar cikin zubar da ƙwalla. Sai da ya share ƙwalla ya dube ta.

"Shi kenan fa Fulani ta yi nisa da mu? Umaima kina ganin zan ci gaba da jin daɗin gudanar da al'amuran mulkin ƙasar nan a yanzu."

"Idan ba za ka iya ba ai sai ka yi murabus ka damƙawa Yarima Muhsin tun dama a yanzu ya kawo ƙarfi." Ta furta a zuciya tana watsa masa harara a fakaice.

"Da taimakon Allah ka haye wannan karagar Sarkina kuma na tabbata da taimakonSa za ka ci gaba da gudanar da al'amuran masarautar nan. Ka yi tawakkali domin Ubangiji da ya ba mu Fulani Shi ne ya buƙace ta a daidai wannan lokacin. A wannan lokacin addu'armu kaɗai Fulani take buƙata Ranka shi daɗe." Ajiyar zuciya ya sauke idanunsa ya runtse da suka yi jawur. "Ina sake alfahari da ke Umaima Allah ya yi miki albarka, ita kuma halinta na gari ya bita." Fulani Umaima ta sunne kai ƙasa sannan ta amsa.

"Amma wani hanzari ba gudu ba ranka shi daɗe, na ce mai zai hana idan aka shirya Fulani a dawo da ita sashenka tun da dai kwanan keso za ta yi ina ga sai ya fi don ka samu damar yi mata addu'a cikin nutsuwa, addu'arka na da matuƙar tasiri a gare ta. Ni kaina zan zauna tare da kai don abin da ya yi Fulani shi ya yi ni, kaico rayuwar duniya kaico mutuwa ta yi mana yankan ƙauna." Fulani Umaima ta ƙarasa maganar tana fashewa da matsanancin kuka. Jikin Sarki Abdul'aziz ya yi sanyi, don haka kai tsaye ya amsa a ganinsa zancen da Fulani Umaima ta yi har a zuciyarta ma haka ne.

A tsaye yake ya yi tsirara a bakin wata ƙorama wacce take cike da jini, mamaki ne ya matuƙar kama shi sakamakon wayar gari da ya yi ya tsinci kansa a wurin kamar yadda yake yawan ganinsa a mafarki. Waigawa ya yi yana ƙarewa baƙon wurin kallo yana tunanin inda ya taɓa ganinsa a makamancin wurin nan. Yana shirin yin magana yaji an sheƙo masa wani ruwa kamar an ɗaurye namansa sannan aka fara waɗansu irin surutai da ba ya iya gane su, an jima ana abu ɗaya sannan ya ji an sake kwara masa ruwan a jikinsa. Ta cikin ƙoramar jinin ya ga wani mutum ya fito daga ciki hannunsa ɗauke da wata gajeriyar wuƙa, baƙa wuluk sai sheƙi take yi. Mamakinsa ya sake ninkuwa sakamakon ganin matsananciyar kamar da suke yi da mutumin.

"Ba kai ba ne shugaba da nake yawan mafarki da shi?" Boka Shadda ya bushe da dariya, "Ba kama ba ce taurarona ni É—in dai ne." Yawu Basiru ya haÉ—iya cike da mamaki.
"To ya aka yi na gan ni a nan? Wai ma wane ne kai?" Basiru ya yi maganar a zuciyarsa. Bai gama saƙa da warwara ba ya ji mutumin ya fesa masa wani ruwa a fuskarsa, take ya ji wani yanayi ya ratsa shi zuciyarsa ta shiga azalzalarsa, babu zato mutumin ya burma masa wuƙar hannunsa a ƙahon zuciyarsa sai dai ko kaɗan bai ji zafi ba sai ma wani irin sanyi da ya fara ratsa ilahirin jikinsa. Ya waiga cikin sanyin jiki yana kallon boka Shaddas.

"Ungo saka rigarka!" Boka Shaddas ya furta yana miƙa masa kayansa, babu musu Basiru ya karɓi kayansa ya fara sawa Shaddas ya furta.

"Daga nan maza ka je ɗakin mahaifiyarka ka buɗe akwatin da take ɓoye duk wani sirrinta, za ka ga wani tsafataccan littafi ka kawo mini. Kada ka manta duk abin da za ka yi mini domin nasararmu ce, kai jajirtacce ne kada ka ba ni kunya magajin babban bokan da babu kamarsa a faɗin nahiyar nan." Jin kanbabawar da Boka Shaddas yake yi masa ya sa Basiri sake samun ƙwarin gwiwa bayan wankan tsafin da aka yi masa, cike da ƙarfin zuciya ya fice daga cikin kogon tsafin.

Lokacin da ta ji labarin an kai gawar Fulani babba turakar Takawa farinciki ne ya lulluɓe ta, ɗaurarriyar fatar da ke hannunta ta shiga juyawa tana sakin murmushi a hankali. Babban mayafi ta ɗauko ta naɗe jikinta da shi sannan ta lalubo carbin da sai da ta sha wuya kafin ta samo shi, ta soke ƙulalliyar fatar wurinta ta janyo ƙauren ɗakinta ta fito, sannan ta gargaɗi Bayinta da ko da wasa kada wanda ya tura mata ɗaki kai tsaye ta nufi sashen Sarki Abdul'aziz da ƙudurin duk rintsi sai ta aiwatar da mugun ƙudurinta kafin gawar Fulani babba ta bar wannan gidan. Tana fita Basiru ya fito daga bayan katangar da yake ɓoya, ya saki dariyar farinciki mummunar fuskarsa ta sake turɓunewa sannan ya faɗa cikin ɗakin mahaifiyarsa, da niyyar cim ma ƙurinsa da na shugabansa don ya ci alwashin duk rintsi sai ya ɗauko littafin da ke cikin ɗakin kamar yadda Boka Shaddas ya ba shi umarni.
SHU'UMAR MASARAUTA

23

*Littafin kuɗi ne 500 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*

Kamar kazar da ta tono wuƙa haka Jawahir take tafe a sanyaye jiki babu ƙwari sakamakon yankan ƙaunar da mutuwa ta yi musu kwatsam babi zato babu tsammani, hawaye ne bibbbuyu suke zuba daga idanunta gabanta na ci gaba da faɗuwa ta bi ta hanyar baya zuwa sashen Fulani babba tana jin wani irin ɗaci a zuciyarta. Tun bayan da Mai gado ta sanar da ita mutuwar Fulani babba duk wani tsoro da firgici suka ƙaurace mata, babba tashin hankalinta bai wuce ta isa ta ga gawar Fulani babba ba, duk da ba ta da tabbacin za ta iya kwalli da gawar saboda yadda take jin ta.

A zaune yake a kan kujerar gefensa kayan marmari da kayan lambu ne ya zura musu idanu tamkar yana son gano wani abu daga jikinsu, a baya ya É—auki huÉ—ubar mahaifiyarsa game da kishiyar mahaifiyar tashi amma sannu a hankali da ya fara girma ya sauka daga dokin zugar da huÉ—ubar tsiyar da take yi masa. Ajiyar zuciya ya sauke sannan a hankali ya furta.

"Allah ya jiƙanta."

Kamar daga sama haka ya fara jin shassheƙar kukanta, karaf idanunsa suka sauka a kanta. Zumbur! Ya miƙe tsaye gabansa na faɗuwa bakinsa na rawa ya furta, "Ke... ke ... ce?" Cak Jawahir ta tsaya cikin kaɗuwa sakamakon ganin Yarima Muhsin a gabanta, a hankali ta fara ja da baya har ta ji bango ya tokare ta. Takowa ya fara yi don ya sake gasgata idanunsa ba gizo suke yi masa ba, ya ɗauki kwana da kwanaki yana zama a wurin ko Allah zai sa ya ganta amma ko mai kama da ita bai taɓa gani ba. Duk taku ɗaya idan ya yi sai ya ji bugun ƙirjinsa ya tsananta, ganin haka ya sa Jawahir ta sake mannewa da bango ta haɗa hannuwanta biyu alamar roƙo ƙirjinta na bugawa ta furta.

"Don Allah ka yi haƙuri ranka shi daɗe, wallahi rannan ma tsautsayi ne."

Jawahir ta ƙarasa maganar tana runtse idanunta ganin ya ƙarasa kanta gadan-gadan, sautin ajiyar zuciyarsa ta ji a fuskarta tana buɗe idanu ta ga ya yi mata rumfa.

"Kin ga ire-iren zargin da ake yi wa su Salame, ko da wasa kada na kuskura na ga kin shige wa wani namiji. 'Yar iska ita ce take mu'amala da maza ko kina son ke ma a dinga kiranki da wannan sunan?" Jawahir ta tuna irin huÉ—ubar da Mai gado ta yi mata watarana.

Take jikinta ya ɗauki karkarwa, ta fara yunƙurin ja da baya amma babu zato ta ji ya fisgo hannunta ta faɗo jikinsa. Wani irin zuuuu Yarima Muhsin ya ji saboda azaba bai san lokacin da ya faɗi can gefe ba, wata irin azaba ya ji tana ratsa hannuwansa cike da raɗaɗi kamar ya sa hannuwansa a wuta. Cije baki ya yi yana yarfe hannu bai yi tsammani ba ya ji kukan wata baƙar saniya a bayansa, a hargitse ya ɗago da mamaki yana kallonta don ko a mafarki bai taɓa ganin saniya mai girma da baƙi kamarta ba. Ƙuri ta yi tana kallonsa tamkar wacce take shirin gwabza faɗa, a hankali ya fara ja da baya Saniyar ta fara tunkaro shi har sai da ya dangana da wata bishiya da ke bayansa.
Chapter 41 · 0% Book details