Sashe 28
Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Watarana Sarki Abdul'aziz ya aika a kira Khadija a lokacin Jawahir na hannunta, duk yadda ta yi ta ajiye ta Jawahir ta ƙi yadda, don haka ta riƙe mata hannu suka fara takawa cikin birgewa duk wurin da suka bi sai an bi su da kallo. Suna shiga cikin turakar Mai martaba sai Jawahir ta cake a taƙi shiga idanunta sauke a kan shurin da ke cikin uwar ɗakin, da saka hannu tana nunawa haɗe da yin gwarancin da ba kowa zai gane ba. Ganin haka ya sa Khadija ta riƙo ta sai da ƙyar Jawahir ta shiga duk a tsorace take kamar wani ne yake yi mata gargaɗi. Sai da Khadija ta tsugunna cikin girmamawa ta gaishe da mahaifinta a zuciyarta tana mamakin kiran da ya yi mata. A hankali Jawahir ta tashi ta fara ɗan tsalle-tsallenta a ɗakin dalilin da ya sa ba su bi ta kanta ba.
"Khadija mun aika a kira ki ne sakamakon Sarki Gumel Sarki Almustafa ya nema wa ɗansa Yarima Safwan aurenki kuma na ba shi ke duniya da lafiya." Ko kaɗan ta so a ce an ba ta zaɓi wurin zaɓar mijin aure amma babu yadda ta iya musamman da ta tuna matsayin mahaifiyarsu a cikin masarautar.
"Godiya nake da zaɓinka ranka shi daɗe, Allah ja da kwana ya jiƙan mai Mai babban ɗaki." Murmushi ya sakar mata yana cikin magana suka ji motsin Jawahir ta wuce can uwar ɗakin Sarki Abdul'aziz, a bakin tsohuwar rijiyar ta tsaya ta fara bubbuga murfin rijiyar cikin gwarancin da take yi take faɗin. "Afuɗe... afuɗe ni ce... danzo ciki, afuɗe ..." Da sauri Khadija ta ɗauko ta tun kafin su fito Jawahir ta tsanyare da matsanancin kuka tana waiwayen rijiyar da Baiwa Maimuna take ciki. Sarki Abdul'aziz ya sallami Khadija sannan suka fice har bayan wani lokaci ba ta daina kuka ba.
"Kin tabbata a kan idanuwanki ya ci wannan tufar da na damƙa miki?"
"Me za a fasa Inna? Wallahi ita ya fara ci ma." Sailuba ta faɗa cike da farinciki. "Haba na gaji da gafara sa ban ga ƙaho ba, har yau so muke ya furta maganar aure amma shiru kake ji kamar an shuka dusa, don haka na koma jiya na sake karɓo miki na sha yanzu magani yanzu. Boka Shaddas ya ce mu bada zuwa nan da kwana biyu." Jakadiya ta ƙarasa maganar tana washe baki. Sailuba ta rungume ta, "Inna ina mai shaida miki matuƙar na auri Takawa, zan murzan kambun da har abada Umaima ba za ta murza shi ba, sai na shayar da ita ruwan mamaki daga ƙarshe na nuna mata bakin rijiya ba wurin wasan makaho ba ne."
Bayan Kwana Biyar
A ƙallah kusan watanni uku kenan da ta lura kullin alaƙarta da Sarki Abdul'aziz ƙara baya take, ta sha mamaki matuƙa duk da ya san cikin da take ɗauke da shi wanda a ƙalla ya tafi watanni biyar, nesa ba kusa ba ya fi ba ta kulawa a lokacin da take ɗauke da cikin Ruƙayya amma sai ta yi masa uzuri sakamakon 'yan tafiye-tafiye da yake yawan yi a lokacin. Babban tashin hankalinta bai wuce ganin yadda Boka Shaddas a mafarkinta da har kullin yake ƙyaƙyata mata dariyar ƙeta ba.
A yau ma da ta ji Sarki Abdul'aziz ya neme ta a turakarsa cike da zumuɗi ta shirya sai dai tana shiga ta yi turus sakamakon ganin Fulani Babba a gefe ta yi kyau abin ta babu laifi, sai dai zuciyarta cike da fargabar kada fitsarin da ke yoyo daga jikinta ya zubo Mai martaba ya kore ta ko ya yi mata wulaƙanci a gaban Fulani Umaima ba . A wulaƙance ta dube ta sannan ta zauna can kusa da Takawa tana ɗaga hanci tana basarwa.
"To da farko dai, Assalamu alaikum. Mun tara ku ne domin mu sanar da ku wasu muhimman abubuwan akhairi guda biyu. Na farko mun gama yanke magana mu da Sarkin Gumel mun tsayar da ranar ɗaurin auren Khadija da Yarima Safwan ranar juma'a mai zuwa, mun taƙaita abin ne sakamakon ana yin auren zai tafi ƙasar Mai duguri harkokin kasuwancinsa, don haka ba ma buƙatar ɓata lokaci. Fulani Babba ta yi shiru a tunaninta Fulani Umaima za ta amsa ta yi mata kara tun da zancan auren Khadija ake yi, shi ya sa ta yi shiru ta yi wa Fulani Umaima kara ba ta amsa ba.
"Abu na gaba kuma da zan sanar da ku har ila yau a dai wannan juma'ar ne ni ma zan É—aura aure da Baiwa Sailuba wacce tuni na 'yantata ta zama 'yar cikin gida, ina fatan za ku ba ni haÉ—in kai domin zama cikin kwanciyar hankali da lumana."
Na ce ko akwai mai zuwa mu je dannar ƙirjin Umaima😕
SHU'UMAR MASARAUTA
16
*Littafin kuɗi ne 500 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*
A razane Fulani Umaima ta miƙe tsaye jikinta na karkarwa har ta manta da cikin da ke jikinta, baki na rawa ta nuna Takawa don tuni idanunta suka rufe har manta matsayinsa a gare ta.
"Me kake faɗa? Ka na nufin Sailuba baiwar gidan nan? Sailuba ƙasƙantacciyar baiwar da ba ta isa a 'yantata ba? Wallahi ba ka isa ba, ba zai taɓa faruwa ba, kai da ƙarin aure har abada." Cikin zuciyarta Fulani babba ta saki murmushin mugunta don ko kaɗan auren Takawa bai ɗaɗa ta da ƙasa ba, tun da ta san da ita da babu a gidan duk ɗaya ne ba ta saura fada a wurin Takawa.
"Fulani ya kamata a san a gaban wanda ake magana, idan ba haka ba ranki zai yi mummunan ɓaci, zan zartar miki da mummunan hukuncin da ba ki taɓa tsammani ba. Na 'yanta Sailuba domin ita ce zaɓina wacce zuciyata take da muraɗin shimfiɗa rayuwar aure a tare da ita." Sarki Abdul'aziz ya furta cike da tsare gida. Kamar butum-butumi haka Fulani Umaima ta zuba masa idanu don gani ta yi ya koma mata kalarsa ta ainihi, a ɗan tsorace ta dube shi tana maimaita kalamansa a fili cike da mamaki.
"Ina taya Mai martaba murna da fatan alheri a kan tagwayen labaran da ya sanar da mu masu ɗauke da farinciki, ba tun yau ba na san kai jajirtaccan gwarzon mazaje ne. Allah ya baka ikon kwatanta adalci domin kai ɗin mai adalci ne, kuma na tabbata za ta ci gaba da adalci kamar yadda kake yi a kodayaushe. Shigowar Sailuba cikin zuri'arka babban alkairi ne da ke tattare da faranta rai Zakina, na san ko mata ɗari a tara maka ba za ka taɓa za ni kunya ba." Fulani Babba ta yi maganar cikin sanyin murya da karyewar zuciya tana tunanin yaushe za ta koma kamar da a wurin Mai martaba, sai dai ta yi ƙoƙarin danne ɗacin da ke ranta ne domin ta fahimci zuciyar Takawa ta yi nisan kiwo a kan Sailuba, kuma duk wanda ya nemi ya nuna adawarsa game da auren ta lura zai iya shata masa layin da ke iya kai shi ga ƙunci haɗe da ɓacin rai. Ta san tana da zafin kishi a kan mijinta kuma uban 'ya'yanta, sai dai kuma dole ta adana kishinta har zuwa lokacin da zai yi mata amfani.
Ya ji daɗin kalamanta sosai don haka ya sakar mata murmushi yana shirin ba ta amsa Fulani Umaima ta furta. "Munafukar banza munafukar wofi algunguma marar kishin kai, idan ke mai hankali ce ya kamata mu haɗa kai da ke don yaƙar annobar da ke shirin dumfaro rayuwarmu. Amma ku yi ku gama wallahi da ni kuke zancan, domin ni warki ce daidai da ƙungun kowacce shegiya." Daga haka ta fice daga ɗakin fuuu kamar za ta tashi sama. Ƙwallah ya gani a saman fuskar Fulani babba tana jin wani irin yanayi don rabonta da keɓewa da Takawa har ta manta, ba ta ji motsinsa ba sai ji ta yi ya tsugunna a gabanta.
"Me yake damunki tauraruwata?"
"Me ye ma bai dame ni ba a faɗin duniyar nan?" Ta furta a zuci, ta saki baki jin kalmar da ya furta mata, amma a fili sai ta girgiza kai, hannu ya sa ya goge mata fuska ya furta. "Ya kamata Fulani ta je don ta samu hutu." Galala ta yi tana mamakin wai yau Takawa ne yake furta mata kalamai masu taushi. Har bakin ƙofa ya mata rakiya ta wuce sashenta zuciyarta fes hatta Bayin da ke hidima a sashenta sai da suka fahimci sauyi daga gare ta.
Yanayin yadda ya ga mahaifiyarsa ba ƙaramin mamaki ya ba shi ba, ya so ya basar amma ganin irin tashin hankalin da take ciki ya sa ya furta. "Ummina shin wani abu ya faru ne?" Idanunta jawur kamar sabon barkono ta dube shi.
"Mene ne ma bai faru ba Yarima? Wai Takawa ne zai yi aure, auren ma ya rasa wa zai aura sai ƙasƙantacciyar Baiwa Sailuba 'yar wurin Jakadiya." Taɓe baki taga ya yi cikin halin ko'in kula. "To me ye abin damuwa Ummi..." Wata irin razananniyar tsawa ta yi masa har sai da ya razana don tun da ya zo duniya mahaifiyarsa ba ta taɓa yi masa haka ba. "Fice ka ba ni wuri sakaran banza mara tunani da kishin mahaifiyarsa." Da sauri ya fita don ya gama tsorata da yanayinta, ta shiga kaiwa da kawowa tana tunanin mafita. Kai tsaye ta sa aka kira mata Jakadiya, har ƙosawa ta yi kafin Jakadiya ta ƙaraso ɗakinta. Jakadiya babu damuwa ko ɗar a ranta don wani irin faɗi da girman kai ne yake ratsa ta.