← Book details Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 86

Sashe 54

Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ka shanye ƙwayayen abin da za ka haifa Muhsin, ka gafarce ni ba da kai nake yi ba da mahaifiyarka nake yi don haka dalili ne ya sa aikina ya biyo ta kanka. Alƙawarin na ɗauka ko zan tafi tsirara sai na cusa wa Umaima ɓacin rai a zuciyarta, ka yafe ni Muhsin kai da ganin ɗan cikinka sai dai a lahira idan ana haihuwa a can." Jakadiya ta wassafa waɗannan kalaman a zuciyarsa har sai da murmushinta ya bayyana a fili, ta karɓi ƙwaryar wurinsa ta yi masa sallama ta fice zuciyarta fes.
*SHU'UMAR MASARAUTA*

*30*

*Littafin kuɗi ne 500 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*

A lokacin da soyayyar Fargi da Sulaiman ta yi ƙarfi sai ya zama hatta waɗansu sirrikan na alƙaluman tsafi da sihiri Fargi ta fara koya masa, don ma Yarima Sulaiman ya kasance matsoracin gaske shi ya sa ba ya iya gudanar da wani aikin kai tsaye. Fargi ita ta yi tsayuwar tsayin daka ta yi wa Sulaiman aikin da zai gaji karagar mahaifinsa, sai dai tashin farko Mahaifinsa sai da ya ɗaura masa aure da 'ya'yan abokansa biyu sannan aka yi bikin naɗin sarautarsa. A wannan ranar Fargi shiga daji ta yi cikin firgici da tashin hankalin da ba ta taɓa tsammani ba, shi kansa Sulaiman bai taɓa tsammanin haka daga wurin mahaifinsa don sai da ya ji a duniya dama bai taɓa samun karagar mulkin ba a rayuwarsa.

"Ban san me ya sa Takawa zai raunata zuciyata ba." Sabon Sarki Sulaiman ya furta a lokacin da ya ratsa cikin ƙungurmin dajin da Fargi ta keɓe kanta a ciki. "Ya aka yi ka san ina wurin nan? Me ka zo za ka yi mini kai da kake da sabbin mata har biy..." Da sauri ya sa hannu a bakinta ya katse ta.

"Ke kaɗai ce matata! Da ke zuciyata ta saba kuma har abada da ke za ta rayu. Ban san so ba sai a kanki, ban taɓa ɗanɗanarsa ba sai da kika lasa mini zumarsa. Ke zuciyata ce, zuciyar da a duk bugun numfashi take jerenta hawa da saukar farashin ƙaunarki a zuciyata. Fargiii!" Sulaiman ya furta da wani irin yanayi. A sanyaye ta ɗago ta dube shi nan take idanunta suka sake cikowa da ƙwallah.

"Ban taɓa sanin haka soyayyarka ta yi tasiri a zuciyata ba Sulaiman, ina yi maka son da har abada ba na jin akwai hallitar da za ta yi maka kwatankwacinsa. Ina kishinka sai dai a yanzu ka yi mini nisa." Kuka ya ɗan ci ƙarfinta sai da ta yi mai isarta ta ci gaba.

"Ka yi mini nisa Sulaiman, nisan da ba na hangen akwai ranar kusantowarsa. Kwatankwacin nisan da sararin samaniya ta yi ƙasa. Yanzu shi kenan ka zama mallakacin wasu soyayyarka ta tashi a banza..." Kukan da ya kwace mata ne ya gayyato haƙoranta suka datse harshenta, ta durƙushe a ƙasa tana fashewa da wani irin matsanancin kuka mai cin zuciya. Da sauri Sulaiman ya ruƙo hannun Fargi ya fara janta har sun fara nisa ta ɗan dakata tana tambayarsa.

"Ina za ka kai ni?"

"Zan kai ki a ɗaura mana aure a yau ɗin, domin ba zan iya rasa ki ba. Ba zan iya mallaka wa waɗansu kaina ba ke ba, ba zan iya sadaukar da komai nawa ba sai a kanki." Fargi ba ta amsa ba ta ci gaba da bin sa tamkar raƙumi da akala.

Sarki Abdul'aziz ya fito fes cikin ƙasaitacciyar alkyabba sai baza ƙamshi yake yi, sai dai ga duk wanda zai yi masa kallon ƙurulla zai fahimci akwai wani abu da yake damunsa a ƙasan ransa. An cika gaban Sarki Sulaiman da kayan ciye-ciye da kayan maƙulashe, da fara'a Sarki Abdul'aziz ya shiga ɗakin saukar baƙin suka shiga gaisawa cikin karamci da mutumta juna.

Sarki Abdul'aziz ya girmi Sarki Sulaiman nesa ba kusa ba sai dai kasancewarsa mai sanin ya kamata da girmama na gaba, uwa-uba dattako da sanin mutumci ɗan adam ya sa ta su ta zo ɗaya shi da Sarki Abdul'aziz. Don haka a wannan karon Sarki Abdul'aziz yana zaune takarda ta iso daga ƙasar Bahdi a kan Mai martaba Sarki Sulaiman zai kawo masa ziyara a kan muhimmiyar maganar da za ta kawo shi.

"Allah ya taimaki Uba kuma shugaba a gare mu Sarkin Sarakuna Sarki Abdu'aziz." Wata irin izza ce ta sake kanainaye Sarki Abdul'aziz, ya saki murmushin gefen baki.

"Da alama Sarki Sulaimanu da tsokana a kalamansa." Sarki Sulaiman ya saki murmushi sannan ya ci gaba da ce wa. "Kuma a haƙiƙanin gaskiya tsokana ba ta cancanci giftawa ta gaban mutanen da suke shirin zama surukai." Sarki Abdul'aziz ya girgiza kai yana dariya don Sarki Sulaimanu mutum ne mai barkwanci.

"Ranka shi daɗe magana ta gaskiya neman iri ne ya kawo mu wurinku, idan babu damuwa ina son haɗa aure da ɗan wurinka Yarima Muhsin da 'yar wurina Raihan! Saboda ina kwaɗayin wannan zumuncin namu ya sake ƙarfi har cikin zuri'armu. Amma fa idan babu takura ranka shi daɗe, idan kuma akwai sai mu yi wa fatan kowa Allah ya haɗa shi da rabonsa na alheri." Tun Sarki Sulaiman bai gama maganar ba Sarki Abdul'aziz ya saki murmushin farinciki. "Mun yi murna da waɗannan kalaman naka Mai martaba, kuma mun amince da wannan maganar ko bayan ranmu wannan maganar ba za ta taɓa sauyawa ba. Ba don kada na yi azarɓaɓi ba, da sai na ce wannan auren a ɗaura shi a ranar juma'a mai zuwa." Cikin farinciki Sarki Sulaiman ya amsa wa Sarki Abdul'aziz sannan suka ci gaba da tattaunawa a kan muhimman batutuwa dangane da yadda auren zai kasance. Daga ƙarshe Sarki Sulaiman da Sarki Abdul'aziz suka tsayar da ranar aure makwanni huɗu masu zuwa. Sarki Sulaimanu ya yi wa Sarki Abdul'aziz sallama da shi da Bafadawa da 'yan rakiyarsa suka koma Masarautarsu ta Bahdi cikin matsanancin farinciki.

Inna wuro tun da yamma ta ƙarato take saka ran ganin Kamalu amma babu shi babu alamarsa, tun tana tsammanin ko wani aikin ne ya riƙe su har ta fara shiga damuwa. Ganin su Salisu abokan Kamalu sun dawo hakan ya sake firgita ta, musamman da ta tambaye shi Kamalu gabaɗaya suka shaida mata rabonsu da shi tun da safe. A ɗimauce Inna wuro, Baffajo da sauran tsirarun Bayin suka shiga cikin Masarautar suna nemansa amma babu Kamalu babu alamarsa, tun suna ganin abin kamar wasa har aka shafe kwana guda ba tare da an ga Kamalu ko gawarsa ba. Tun a daren ranar zazzaɓi mai zafi ya rufe Inna wuro da Baffajo saboda matsananciyar damuwa da suka shiga, kallo ɗaya za ka yi musu ka fahimci suna cikin matsananciyar damuwa don ko abinci ranar ba su iya ci ba.

"Wallahi ni dai na gaji da yin bauta a wurin nan haka kawai wari ya addabe ka, saboda Allah don dai shi Bawa ba shi da gata sai a ce kowanne cin kashi shi zai ɗauka. Hanne dubi wancan zanin na Sailuba ban da ruwan mugunya da tsutsotsi babu komai a ciki." Hanne ta sauke ajiyar zuciya bayan ta gana sauraron Furaira sannan ta furta. "Wallahi gara ke Furaira nesa ba kusa ba, idan kin wanke ai shi kenan sai wani ya sake ɓaci. Ni kina ga kullin ina tare da ita ina aikin kashe mata kwarkwata, ga uban ɗoyin da nake shaƙewa. Wallahi ni kaina na ƙagu na sauya..." Kalaman Hanne suka katse sakamakon hango Jakadiya da ta yi a tsaye.

"To tsofaffin munafukai, uban me kuke tattaunawa?" Take suka yi tsilli-tsilli cikin tashin hankali, fargabarsu ɗaya Allah ya sa Jakadiya ba ta ji abin da suke faɗa. "Babu komai Jakadiya hutawa muke." Furaira ta wayance. Jakadiya ƙwafa ta yi sannan ta wuce wurin Sailuba da ke kance a ɗaki ta yashe ƙafafuwa tana shan iska.

Ɗoyin da ya daki hancin Jakadiya ne ya sa ta ɗan ja baya da sauri, gabanta ya buga dum! Da matsanancin ƙarfi. Ta zura wa Sailuba idanu cikin tashin hankalin, Sailuba da ke kwance ta bi Jakadiya da jemammun idanunta cikin sare rai da yanke ƙauna. "Sailuba idanuwana ne suke yi mini gizo ko da gaske haka kika sake lalacewa. Yanzu warin da ke fita daga jikinki har ya ta'azzara haka?" Sailuba ba ta tanka wa Jakadiya ba saboda tsananin takaicin da ya cunkushe ta, a duk faɗin duniya gani take babu wanda ya jefa ta a wannan halin sama da mahaifiyarta.

"Dama kowa ya sayi rariya ai ya san za ta zubar da ruwa Inna! Kin fi ni sanin wace ce Umaima a kan me za ki tsaya kina tambayata? Na nemar wa kaina mafita amma kin ce ba haka ba kin ga idan na mutu shi kenan kin kowa ya huta. Ita Umaima hankalinta zai kwanta ta mallaki mijinta ita kaɗai, ni kuma na samu salama a rayuwata ke kuma ki huta da yawon neman magani." Sailuba ta ƙarashe maganar ƙwalla na zuba daga idanunta.

Tun da sabuwar lalurar nan ta samu Sailuba wannan ce rana ta farko ta kalamanta suka daki zuciyar Jakadiya, wata irin nadama game da auren Sailuba da Takawa ta mamaye ta. A sanyaye ta tsugunna idanunta suka ciko da ƙwallah.

"Jakadiya wannan maganin Takawa da kansa ne ya ce ki kawo mini? Amma dai na ji daÉ—i ko ba komai a wannan karon Takawa ya nuna mini kulawa. Allah ya sa idan na haife cikin nan albarkacinsa ya sa na ci gaba da samun kulawa daga gare shi." Kalaman Fulani babba na baya suka dawo wa Jakadiya raÉ—au a cikin kunnuwanta, a lokacin da ta kai mata wani garin turare da suka haÉ—a baki da Fulani Umaima a zuwan Sarki Abdul'aziz ne ya bayar da shi.

"Allah ka gafarta wa Fulani babba, Ubangiji ka sa ta yafe mini abin da na aikata mata. Ya Allah kada ka jarabce ni da haƙƙinta a kaina." Jakadiya ta furta zuciya a raunane.

"Inna me kalamanki suke nufi? Shin kin taɓa yi wa Fulani babba wani abu ne?" Ajiyar zuciya Jakadiya ta sauke sannan ta furta. "Ba huruminki ba ne Sailuba."
Chapter 54 · 0% Book details