← Book details Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 86

Sashe 83

Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ki ji tsoron Allah kina hallitar Ubangiji amma kin dulmiyar da Bayin Allahn nan, me ya sa kin san gaskiya amma kika lulluɓe su kike damƙa musu ƙarya?"
"Saboda ita ta fi karɓuwa a doron ƙasa, wai ma me ya sa kake son bayyana ainihin wace ce ni a gaban al'ummata?" Suka ji an sake furtawa daga cikin murgujejiyar bishiyar kukar gabansu. Tambayarta har ta so ba wa Dattijo Maharaz dariya, ya ƙarasa gaban bishiyar kukar ya dafa ta sannan ya ce.

" Idan babu damuwa zan sa a kira mini waɗansu muhimman bayin Allah domin a kawo ƙarshen komai suma waɗannan mutanen su fara rayuwa irin ta mutane ba ta dabbobi ba."

"Kar ka kuskura ka tara mini jama'a idan ba haka ba wallahi sai ranka ya ɓaci, fushina mai tsananj zai sauka a kanka." Dattijo Maharaz bai bi ta kanta ba, ya ambato sunan ɗaya daga cikin 'ya'yansa sannan ya ba shi umarnin gayyato masa Babban Malami, jin haka ya sa Sarki Abdul'aziz ya ce idan babu damuwa a taho da Alaramma wato shugaban limaman garin Huddam. Sai da Dattijo Maharaz ya gargaɗi ɗansa Shu'aibu da ya bi ta sigar da Alaramma zai fahimce shi don kar ya tsora da shi sannan ya sallame shi, yana gargaɗinsa da kada ya ɓata lokaci.

Waigawa ya yi wurin mutanen da suka yi tsaye carko-carko ya ce, "Shin kun taɓa jin labarin wani addinin bayan wannan da kuke bautawa." Hayaniya ce ta ɗan kaure wasu sun amsa masa wasu kuma suka nuna ƙalubalantarsa don sun lura yana son wulanƙanta abar bautarsu ne a gabansu.

"Da daɗewa na taɓa jin labarin addinin bautar wuta, bautar gumaka, bautar ruwa sai kuma wani addini wai musulunci. Amma shi a wurin masu kawo mana aikin asiri muke jin sa." Wani tsoho ya yi wa Dattijo Maharaz bayani, murmushi ya yi sannan ya furta. "Tabbas Addinin musulunci shi ne addinin gaskiya wanda kowanne bawa idan ya bi shi zai kai shi har cikin aljannah. Wannan abar bautar taku ita kanta hallitar Allah ce, jinsina ce wato jinsin Aljanu. Ko a yanzu idan na so aiwatar da abin da take yi muku nan take zan gudanar muku da shi, tana wasa da hankalanku ne amma ga wanda bai aminta da abin da nake faɗa muku ba ya zuba idanu zai ku ga ikon Allah." Rufe bakin Dattijo Maharaz sai ga Shu'aibu, Alaramma da Babban Malami. Shu'aibu da Babban Malami dukkansu cikin siffar bil'adam suke tamkar mutane ba jinsin aljanu ba.

"Barka da zuwa babban Malami, mun taso ka babu shiri a yi mini afuwa dole ce ta sa haka." Dattijo Maharaz ya furta cikin girmamawa.
"Assalamu alaikum. Barkanka dai Dattijo Maharaz ai tun da na ji haka na san babban uzuri ne ya haifar da haka, amma ina fatan ba Dela ce ta É—auko mini wata maganar ba." Babban Malami ya furta yana kallon Abar bauta da har lokacin ba ta bayyana kanta sauran mutanen su ganta ba. Da mamaki Dattijo Maharaz ya ce. "Malam da ma ka santa ne?" Murmushin takaici Malam Liman ya yi ya ce.

"Ban yi mamakin jin haka daga bakinka ba Marahaz, domin tun shekaru masu yawa a baya na sallama Dela daga matsayin 'yata. Ka san É—a ne ka haife shi ba ka haifi halinsa ba." Mamaki ya sake mamaye Dattijo Maharaz da su Sarki Sulaimanu, nan take ya zayyane wa Babban malami duk abin da yake faruwa yana gama sauraronsa ya furta.

"Innalillahi Wa'inna'lahir Raji'un! Yanzu Dela hatsabibancinki har ya kai ki dinga haɗa kanki da Ubangiji Dela? Na yi da-na-sanin haihuwarki tir da irinki a doron ƙasa."
"Tun da ka sallama ni me ya yi saura Don Allah Baba ka tsame kanka daga cikin maganar nan." Abar bauta ta furta cikin tsiwa.

Mamaki ne ya mamaye mutanen wurin wai Abar bautarsu da ta ce musu ita take hallitarsu take ciyar da su ta shayar da su ita ce har take da mahaifi kuma yake tsaye a gabansu.

"Tun da har kika shiga hurumin Ubangiji ai sai in da ƙarfina ya ƙare a kanki, ko kaɗan rayuwarki ba ta da amfani, ashe kin san da Ubangiji kika ɗora su a wata hanyar daban. Allah wadaran halinki Dela na san har abada ba za ki sauya halinki ba." Malam Liman ya yi maganar ƙwallah na zuba daga idonsa.

Sai da suka ɗaura alwala shi da Alaramma sannan suka fara karanta ayoyin da suke magana akan azaba, nan take ita da muƙarrabanta suka fara ihu da ƙaraji cikin tashin hankali. Tsiraru daga cikin mutanen wurin suka fara yanke jiki suna faɗuwa na su aljanun suna tashi, sun jima suna karatun Alƙur'ani tun suna jin muryoyi daban-daban har sautin ya fara raguwa wanda hakane ne ya tabbatar musu da sun ƙone wasu sai abin da ba a rasa ba. Zumjuttu tun da aka fara karatun ta gudu cikin jin tsananin azaba.

Suna nan tsaye carko-carko suka ga wata hallita ta bayyana, tamkar tsuntsu haka take. Kanta akwai manyan ƙaho guda biyu, ta bayanta akwai jela sai ƙafafuwanta kamar na doki idanun uku a fuskarta. Da gudu suka ja da baya har su Sarki Abdul'azia, cikin ɓacin rai Mahaifinta ya ce. "Ki dubi dubban al'ummar nan ina za ki je da hakkinsu, tun wuri ki fito ki sanar da su ke ba Ubangiji ba ce. Ke hallitar Allah ce kuma ko a yanzu zai iya ɗaukar rayuwarki. Ki sanarda su Allah S.W.A. Shi ne Ubangiji sammai da ƙassai, Ubangijin mutum da alja kuma Ubangiji duk wata halitta da ke faɗin duniyar nan."

*SHU'UMAR MASARAUTA*

*45*

*Littafin kuɗi ne 500 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*

🔚🔚🔚🔚🔚🔚

Lokacin da Fargi ta isa wurin abar bauta zubewa ta yi bisa gwiwoyinta ta rushe da matsanancin kuka, sai da ta yi mai isarta sannan ta yi sujjada a gaban bishiyar ta furta. "A kowanne lokaci Shugaba zai iya É—aukan mummunan mataki a kaina, Abar bauta da ke na dogara ke ce madogarata."
"Zan taimaka miki da dukkan taimakon da muka saba yi miki, ki tashi ki koma gida a daren yau ki dawo gare mu domin akwai buƙatun mutane da dama a gabanmu idan muka gama da su za mu ji da na ki." Abar bauta ta furta mata cikin kulawa, sai a lokacin Fargi ta ji ƙwarin gwiwa ta yunƙura za ta tafi, sai dai miƙewar da za ta yi ta ji mararta ta karta mata. A hankali ta fara takawa kafin ta ƙarasa gidansu ta lura da inkiyar da Sarku Sulaimanu yake yi mata idan ya kawo mata ziyara, sai da ta ɗan jingina da bishiyar Tsamiyar da ke gefenta sannan ta furta ɗalasiman tsafinta ta ɓace daga wurin, a inda suka saba haɗuwa ta same shi yana ganinta ya ƙarasa sa sauri ya riƙo hannunta.

"Uwar Biyu barka da fitowa." Daidaita nutsuwarta ta yi don kada ya fahimci damuwarta.

"Yau ka yi mini kyau Sarkina?" Fargi ta furta tana zuba masa idanu.
"Ni kuma kin rame mini yau Fargi me yake damunki?"
"Ciwon mara nake sama-sama." Ta furta tana ɗan yamutsa fuska. Da sauri ya ce, 'To ko dai abin ya zo ne?" Rufe idanunta ta yi da sauri cikin jin kunya, ya riƙe hanunta suka ƙarasa wurin dokinsa. Tabarmar kabar da ke saman dokinsa ya ɗauko ya shinfiɗa musu suka zauna suna ci gaba da hira, tun da Sarki Sulaimanu yake zuwa wurin Fargi bai taɓa daɗewa a wurinta kamar na wannan lokacin ba, don har sai da duhun magriba ya yi suna zaune a wurin. Sun yi hira sosai wata hirar ma ba sa dire ta Fargi take ɗauko masa wata. Wata su yi a kan abin da za ta haifa wata kuma a kan yanayin rayuwa, har a game da iyayenta sai da ta sanar da shi don haka duka damuwar da take ciki ta yaye mata. A wannan ranar Sarki Sulaimanu har zai hau dokinsa ya tafi Fargi ta coge wuri ɗaya a kan sai ya yi mata rakiya, wannan ita ce rana ta farko da Sarki Sulaimanu ya taɓa bayyana a zahiri ya yi wa Fargi rakiya har zuwa ƙofar gidansu, duk nutanen da suka wuce sai sun bi su da kallo amma shakkun Fargi ya sa ba wanda ya tanka mata. A ƙofar gida ma sun jima suna hira har sai da Fargi ta gaji don kanta ta sallame shi sannan ya tafi da cewar zai dawo washegari ya sake ganin sauƙin jikin nata. Da kansa ya shigar mata da duk kayayyakin da taho mata da shi gefen bukkarta sannan ya tafi har sai da Fargi ta daina hangensa sannan ta koma cikin gida.

Washegari asubar fari suka ji hayaniya da kace-nace a ƙofar gidansu kafin sun yi wani yunƙuri su ka ji an fara kai duka kan kararen da suka zagaye ɗakunan bukkokinsu da shi.

"A kashe ta sai an kashe ta tun da ta aikata babban kuskure wannan umarni ne daga wurin Shugaba."
"Ba za mu saurarawa maci amanar zuri'armu ba."
"A fito mana da Fargi domin ba za ta watsa wa Shugaba ƙasa a ido ba." Ire-iren kalaman da suka dinga ji suna tashi kenan daga bakunan mutane, cikin firgici Mahaifiyar Fargi ta riƙo hannunta ta bayan bukkarsu ta furta. "Maza ku gudu Fargi, ba na son Shugaba ya kashe mini ki, ɓace daga wurin nan Fargi tsafi da sihiri zai dafa miki." Ganin tashin hankalin da mahaifanta ke ciki ya sa ta fara zubar da ƙwallah, ba ta son barinsu cikin tashin hankali don haka ta girgiza kanta tana faɗin.
Chapter 83 · 0% Book details