← Book details Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 86

Sashe 49

Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shugaba Zurufu ya jima a halwar tsafinsa yana bincike game da Sulaiman da Fargi, yayin da ya ci karo da wani ƙaton haske mamaye da duka tauraronsu. Duk yadda ya so gano ainihin mene ne sai ya gagara fahimtar komai, sai dai jikinsa yana ba shi akwai wani sabon al'amari da zai faru a nan gaba wanda yake ji ba zai zame masa alheri ba.

"Fargi babu ke babu yi wa yaron nan aiki wannan umarni ne nake ba ki ba shawara ba, don haka kada ki ƙulla wata alaƙa da shi." Shugaba Zurufu ya furta wa Fargi a lokacin da ya kirata. "Saboda me Shugaba? Ina ganin aikinsa ba aiki ne mai wahala ba."

Tun da Fargi ta zo duniya wannan ce maganar ja'in'ja ta farko da ta taɓa shiga tsakaninsu, don haka Shugaba Zurufu ya sake kafe ta da idanu yana yana nazartarta. Ganin haka ta sa Fargi ta nemi yafiya a wurinsa sannan ta nuna masa ba za ta sake shiga sabgar Sulaiman ba, amma a ƙasan zuciyarta ba ta jin za ta iya yanke alaƙarta da shi sakamakon baƙon yanayin da ya ratsa zuciyarta.

Tun daga wannan ranar sai ya zamana Fargi ta yi takatsantsan wurin gudanar da mu'amala a tsakaninta da Sulaiman, tun suna mu'amala a matsayin zumunci har alaƙarsu ta fara rikiɗewa zuwa soyayya. Kuma duk wannan soyayyar suna gudanar da ita ne a masarautarsu Sulaiman a sirrance ba tare da wani ya sani ba, a duk lokacin da ta so ziyartarsa kai tsaye take rikiɗa zuwa siffar tantabara sai ta sauka a wurin shaƙatawarsa. Shi kuma Sulaiman yana ganinta yake shaidata don haka suka gina soyayyarsu mai ƙarfi ba tare da mutum ɗaya daga cikin zuri'arta sun fahimci haka ba. A duk lokacin da ta tuna babban zunubi ne wani daga cikin zuri'arsu ya ƙulla soyayya da wani jinsin da ba nasu ba, sai hankalinta ya kai matuƙar ƙolokuwar tashi fargabarta bai wuce kaca su kashe ta ita da Sulaiman ba su soke gawarsu a jikin bishiyar abar bauta.

Duk da a kan idanunta Jakadiya ta aiwatar da abin da Boka Shaddas ya saka ta amma har lokacin babu walwala a tattare da ita. Duk yadda Jakadiya ta kai ga son lallashinta da ban baki tuni Sailuba ta yi nisan kiwon da ba ta jin kira.

"Inna yau ita ce rana ta farko da na yi da-na-sanin aurena da Takawa, don Allah yanzu Inna wacce irin riba muka samu? Tun d aka yi auren nan babu kwanciyar hankali daga wannan sai wannan, tura da kai ni bango gaskiya zan je na nemi takardar saki a wurin Takawa idan ya so na samu Umaima ta karya duk wani kaidi da ta ƙulla mini kin ga na yarda ƙwallon mangwaro dole zan huta da ƙuda..."

"Dakata mini sakarya mara sanin kishin kai." Jakadiya ta katse Sailuba a hassale. "Kina son ki zubar mini da ƙima a wurin Umaima ne? Wallahi idan kika aikata wannan ɗanyen rashin hankalin sai na tsine miki albarka, domin da ki watsa mini ƙasa a gaban Umaima gara ki watsa mini a idon duniya." Jin haka ya sa Sailuba ta sake fashewa da matsanancin kuka.

Tashin hankalin Fulani Umaima ya sake ninkuwa sakamakon jin motsi a uwar ɗakinta, da sauri ta leƙa ciki amma babu kowa don haka ta koma ta zauna ta rafka uban tagumi. Babban abin da yake sake ci mata tuwo a ƙwarya bai wuce yadda a kullin kusancinta da Takawa yake sake nisanta ba, ta lura tun bayan rasuwar Fulani babba ba ya ta tata da kullin maganarsa tana kan Abubakar. A ɓangare ɗaya kuma ga ƙyama, da hantarar da yake yawan yi mata, ta lura hatta Sailuba da take ɗoyi tana zubar da ruwa mai wari ba ta fuskantar tsangwamar da take fuskanta a wurinsa, sai dai ita ma Sailuban ba wani shirin arziƙi suke yi ba don ta ji labarin ko zuwa sashen Takawa ta daina yi. Ita kanta ganin cin kashin ya yi yawa ya sa ta janye jikinta gefe har lokacin da za ta shawo kan matsalar gabaɗaya.

"Me ya sa matsalolina suke rikitowa rayuwata a daidai gaɓar da na ci burin cin duniyata da tsinke tsire, a lokacin baya babban tunanin Fulani babba ce matsalata amma me ya sa bayan na kawar da ita sai matsaloli suke sake kunno mini kai?"

"Saboda kowa ya sayi rariya ya san za ta zubda ruwa. Kuma duk wanda ya ce tukunyar wani ba za ta tafasa ba ta shi ko ɗumi ba za ta yi ba, ai tarin masifa da bala'in yanzu kila fara gani Umaima." Jakadiya ta katse Fulani Umaima rai a ɓace.

"Wa ya kasa da ke ballantana ki ɗauka, don Allah Jakadiya ki je ki ji da matsalar gabanki. Kada ki yi la'akari da halin da nake ciki don kowa ya biya allonsa wankewa yake." Fulani Umaima ta ƙarasa maganar tana shigewa uwar ɗaki, don yadda zuciyarta take a dagule ba ta jin za ta iya biye wa Jakadiya. Jakadiya ta ja guntun tsaki sannan ta fice daga ɗakin.

Tunanin Fulani Umaima kacokan ya tafi a kan yadda za ta kawo wa Bamaguje yarinyar da ya bata umarni, lokaci ɗaya ta saki shu'umin murmushi da wata shawara ta faɗo mata. Da sauri ta fita ta sa aka kira mata Uwar Bayi ta bata umarnin a tattara mata 'Bayi yara da manya domin a faɗarta za ta 'yanta yaran Bayi goma iyayensu biyar. Nan take babu jimawa Uwar Bayi ta tafi sashensu na Bayi ta sanar da saƙon Fulani Umaima, cike da murna Bayin suka fara tururuwa suna taruwa a babban filin harabar masarautar suna jiran fitowar Fulani Umaima kowa a zuciyarsa yana fatan Allah ya sa yana daga cikin masu rabon da za a 'yanta.

Ɗaya bayan ɗaya haka Fulani Umaima ta sa aka diga wucewa da Bayi ko za ta yi tozali da ita amma ko mai kama da ita ba ta gani ba, don haka cikin yanke ƙauna ta zaɓi waɗanda suke da rabo a gurguje ta nufi sashenta don a wannan karon ta yanke shawarar zuwa wurin Bamaguje don ta gaji da jegon jakar da take yi babu dare babu rana ba tare da biyan buƙata ba.

Tun bayan da Jawahir ta kai wa Kamalu butar hannunta ta wuce sashensu na Bayi haka kawai take jin tamkar ta sauke wani babban nauyin da yake kanta, a lokacin da ta koma Mai gado ba ta nan don haka ta ɗan sha ragowar kokon da ta rage sannan ta koma ta kwanta tana tunanin rayuwa. Duk yadda ta ji Bayin sashensu na tururwar zuwa wurin zaɓen da Fulani Umaima za ta yi haka kawai ta ji ba ta son zuwa, don ba ƙaramin tsanar matar ta yi ba, jin hayaniyar za ta takura mata ya sa ta sake ficewa daga ɗakin kai tsaye ta wuce kogin tsamiya ta zauna tana wasa da ruwa. Tun tana cikin damuwa har damuwar tata ta yaye sakamakon yadda ruwan yake rikiɗe mata yana wani irin tsiri kamar zai rufe ta sai kuma ya tafi da gudu ya sake dawowa, ta jima a bakin ruwan har sai da ta gaji don kanta sannan ta bar wurin. Har za ta koma sashensu na Bayi sai ta yanke shawarar zuwa ta gano halin da Abubakar yake ciki duk da ta san Mai gado ba za ta bar ta shiga wurinsa ba.

Tamkar dirar mikiya haka Jawahir ta ci karo da shi a mararrabar ƙofofin da suke tsakanin sashen Fulani Umaima da Fulani babba, yadda ta ga ya yi saranda kamar mutum-mutum ne ya sa ita ma ta daskare cikin faɗuwar gaba. A wannan karon bai matso kusa da ita ba sai ma murmushi ya sakar mata, mamaki ne ƙarara ya bayyana a saman fuskarta.

"Barka... da hutawa... ranka shi daɗe." Jawahir ta yi ƙarfin yin maganar muryarta na rawa.

"Me ya sa kike jin tsorona?" Yarima Muhsin ya wurga mata tambaya a madadin ya amsa mata. "Amm... dama... dama... haƙuri zan baka..." Tun da ta fara magana ya kafe bakinta da kallo haka kawai ya ji ƙirjinsa na bugawa, sha'awa da soyayyarta na fisgarsa.

"Laifin me kika yi mini da za ki ba ni haƙuri?"

"Ƙila fa ya manta abin kika yi masa, indai kuwa ya manta ki rufa wa kanki asiri ki yi shiru." Zuciyarta ta raya mata. Tana shirin yin magana ta ji motsin tafiya a bayanta, wani irin turare mara daɗi ya bugi hancinta. Da sauri ta juya karaf idanuwanta suka sauka a kan Fulani Umaima da ke tafe fuska a haɗe Bayinta biyu na biye da ita a baya.

"Keee! Ke idanuwana suke gani?" Fulani Umaima ta yi maganar cikin suɓutar baki sakamakon rashin tsammanin ganin Jawahir. Tsoron Jawahir ya ninku a ɓangare ɗaya kuma haushin Fulani Umaima ya turniƙe ta. Tamkar ba za ta gaida Fulani ba haka Jawahir ta zuba mata manyan idanunta, idan ba gizo idanun Fulani Umaima suke yi mata ba har gani ƙwayar idon Jawahir tana rikiɗe mata zuwa wata siffar daban.

"Barka da hutawa ranki shi daÉ—e." Kalaman Jawahir suka daki majiyar sautin Fulani Umaima.

Sai da Fulani Umaima ta waiga ta sallami Bayinta sannan ya juya wurin Jawahir tana shirin yin magana Yarima Muhsin ya katse ta.

"Ammi dama kin santa ne?"

"Ku biyo ni ciki yanzu-yanzu." Fulani Umaima ta furta, tana gama maganar ta shiga cikin gida. Rass! Gaban Jawahir ya faɗi don haka ta ji ba ta aminta da kiran da Fulani Umaima ta yi mata ba, tun da ta san babu wani abu da ya taɓa haɗa su ballanata ta ce ko wani kuskure ta yi mata.

"Mu je ciki." Ta riski kalaman Yarima Muhsin cikin tattausan lafazi. Kamar kazar da ƙwai ya fashe wa a ciki haka Jawahir ta shiga sashen Fulani Umaima tana tafe tana ƙarewa sashen kallo, duk taku ɗaya idan ta yi haka take jin bugun ƙirjinta yana tsananta har suka shiga rumfar (Falo) Fulani Umaima.

"Ammi ashe ke ma kin santa? Amma na jima ina wahalar da rayuwata." Yarima Muhsin ya yi maganar cike da shauƙin farinciki.

"Wace ce ita?" Fulani Umaima ta tambaya shi fuska babu walwa, ta wurga wa Jawahir wani ƙasƙantaccan kallo cike da tsana.
Chapter 49 · 0% Book details