← Book details Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 86

Sashe 78

Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Allah ya sani na aminta da kai Dattijo Maharaz ban taɓa rayawa a raina za ka faɗa mini ba daidai, kuma wannan ɓoyayyan sirri ne da babu wanda ya taɓa jin sa daga gare." Sai da Kamalu ya tattaro jarumta murya a dashe ya ci gaba da cewa. "Tun da na buɗi ido na fara jin wani irin yanayi a game da ita, zuciyata ta jima tana azabtuwa a ƙaunarta sai dai a kullin rashin jituwarmu ta sa ban taɓa gangancin bayyana mata sirrin da ke kwance a cikin raina ba. Dattijo Maharaz na jima da dulmiya kogin ƙauna da soyayyar Jawahir, kogin da ya shallake rijiya gaba dubu a tsananin zurfi da nisa, kuma na yi tsalle babu adadi domin na fito daga ciki har yau ban samu nasara ba. Ko Kalaman Muhsin a kan soyayyarta ba su gigita ni tamkar yadda wannan furucin naka ya ɗimauta duniyata ba, yanzu shi kenan aure ya haramta tsakanin da Jawahir Dattijo Maharaz?" Tausayin Kamalu ya kama shi, ya dafa kafaɗarsa sannan ya ce. "Ita bil'adam ce kamar kai Kamalu, kalamaina sun yi tsauri da ka fahimci abin da nake nufi kai tsaye. Ka bari za mu tattauna idan Allah ya kaimu." A sanyaye Kamalu ya amsa masa sannan suka yi sallama ya fice.

Bayan fitar Boka Shaddas Shugaba ya sake kallon wurin da Jawahir ke tsaye tana hawaye ya ce, "Buɗe mini cikinki!" Dire kalamansa ya yi daidai da jin cikinta ya ɗauki raɗaɗi kamar yadda yake yi mata idan tambarin cikinta zai bayyana. Tsoro ya sake mamaye ta, jikinta ya ci gaba da karkarwa ganin ta kai ƙarshen bango ta durƙushe a saman gwiwoyinta ta furta."Don Allah kada ka cutar da ni, ka yi haƙuri idan wani laifin na yi maka." Jin sautin muryar Jawahir ya sake karya zuciyar Mahaifin Fargi.

"Zan yi wata doguwar tafiya mai nisan gaske, tafiyar ba a waiwaye ballanta a dawo baya. Don girman tsafi da sihirin da na buɗe ido kuna auwatarwa, iyayena ku yafe mini idan akwai laifin da na yi muku a baya." Kalama Fargi na bawa suka dawo masa cikin kunnuwansa ana gobe za ta yi tafiyar da har kawo wannan ranar ba ta waiwayo su ba tamkar yadda ta faɗa. Goge ƙwallar idonsa ya yi ya fara tunkarar Shugaba yana jin wata irin ƙwarin gwiwa na ratsa shi, don ba ya jin zai yarda ya sake rasa jinin Fargi a karo na biyu.

"Biyayya ga Shugaba girmamawa amma ce, amma biyayyar da yankin nan suke yi wa Shugaba ita take ba shi lasisin da yake cin karensa babu babbaka a kanmu. Don natsayin abar bauta mu zama jajjirtattu a kan 'yancinmu, hakan ne zai É—arsa wa Shugaba shukku a ka cin kashin da yake aiwatar mana." Ya sake tuna kalaman da Fargi ta faÉ—a masa a ranar da za ta yi bankwana da su.

Kafin Mahaifin Fargi ya ƙarasa tuni Shugaba ya isa gaban Fargi, ganin ya tunkaro ta da wani dogon ƙaho ya sa tsoronta ya tsananta har ta faɗi a can gefen. Da ƙarfin tsiya Shugaba ya ɗaga rigarta ya sa ƙahon hannunsa da niyyar zuƙe duk wata kariya da tasirin da tambarin cikinta ke ɗauke da shi. Wani irin jan haske mai kama da harshen wuta ya mamaye fuskarsa, wata irin azaba ta mamaye saman fuskarsa mai ɗauke da raɗaɗi. Tun da ya ga wannan jan hasken ya gifta masa bai sake ganin komai ba sai ma wani irin zafi da yake ji tamkar an watsa masa ruwan barkono, mamaki ne ya kama Jawahir ƙarara haɗe da tsoro. Hannunta ta kai saman cikinta tana mamakin wai yau wuta ce ta fito daga cikin cikinta.

Ƙaraji da ihun azabar da Shugaba yake yi ya ratsa cikin kogon dutsen gabaɗaya, har ya fara gayyato tsirarun mutanen da ke maƙotaka da shi. Mahaifin Fargi na ganin haka ya ƙarasa wurin Jawahir yana kukan farinciki.

"Tsafi ya albarkaci rayuwarki, saihiri ya ci gaba da baki kariya har abada."

"Ni ba matsafiya ba ce, kuma Inna ta ce mini sihiri da tsafi haramun ne ga duk wanda yake yi, idan ya mutu zai dawwama a wutar jahannama." Jawahir ta faɗa tana ɗan ja da baya, duk da shi ta lura ba ya burin cutar da ita amma shi ɗinma ba ta amince da shi. Daga bakin ƙofar shigowa cikin kogon dutsen suka hangi tsirarun mutane na shigowa fuskokinsu ɗauke da yanayin mamaki. Shugaba can gefe ya faɗi har lokaci murza idanu yake kuma fuskarsa babu alamar ƙonuwa ko jin ciwo, hatta idanunsa tangaram suke a buɗe sai dai gabaɗaya baya ganin komai sai duhu. Sai da mutanen suka gama shigowa sannan suka ga Fargi ta ratso ta jikin bangon kogon dutsen, da mamaki suke bin ta da kallo waɗansu da suka san Fargi a baya baki sake suka fara kallon Jawahir suna kallon Fargi da ke tunkaro su. Kai tsaye wurin Shugaba ta isa sai da ta tsugunna ta dafa kafaɗarsa tun ba ta fara magana ba gaban Shugaba ya faɗi.

"Ya aka yi tasirin tsafinki ya haure nawa? Tabbas kin yi nasara a kaina Fargi."
"Na sha faɗa maka dama mai laya ya kiyayi mai zamani! Ita rana dubu ta ɓarawo ce guda ɗaya ce tak ta me kaya." Tana gama maganar ta watsa masa wani farin garin magani, sannan ta ƙarasa wurin Jawahir da har lokaci tana ƙasa a kwance ta ɗago ta. "Ba tun yau ba, na faɗa miki tsoro ba ya daga cikin ɗabi'a ko halayen zuri'ata. Ki zama mai kare kanki ba sai wani ya kare ki ba." Jawahir ba ta iya furta komai ba, ta ruƙo hannunta suka ƙarasa wurin Mahaifinta. Da hannu ya shafa fuskarta lokaci ɗaya hawaye ya fara bin kumatunta. "Wannan jininka ce, jikarka ce wato 'yar cikin Farginka."

Haka kawai Sarki Sulaiman ya ji zuciyarsa duk babu daɗi abin duniya goma da ashirin ya mamaye shi, tunanin Fargi da rayuwarsu ta baya ta shiga dawo masa don haka ko da daddare da ƙyar bacci ya yi awon gaba da shi, hatta iyalansa sai da suka lura da yanayin da yake ciki. Wani irin bacci ya dinga yi mara daɗi cike da mafarkan Fargi masu tsayawa a rai. Tun asuba ba ta yi ba bacci ya ƙaurace masa, don haka ya ci alwashin a wannan ranar sai ya ziyarci Yankin Rumzu sai dai duk abin da zai faru da shi ya faru. Duk da a baya ma yakan badda kama ya je da kayan abinci niƙi-niƙi ya sa a kai wa iyayen Fargi kuma har kawo wannan lokacin bai daina zuwa ba. Ya tashi da niyyar tafiya sai kuma aka wayi gari Mai babban ɗaki babu lafiya, don haka ya haƙurewa zuwa har zuwa washegari idan jikinta ya yi kyau saboda yanayin girma ga shekarun da suka fara cim mata.

Mai gado kusan yadda ta ga rana haka ta ƙarasa ganin dare saboda tashin hankalin rashin sanin halin da Jawahir take ciki da matsanancin halin da Malam Umaru yake ciki na jinya, sai dai har gari ya waye babu wani ci gaba a ciwon Malam Umaru, hatta tsarki da alwala ita ta ɗaura masa tana rayawa a ranta wataƙila ko niyya ce ya yi ya gabatar da sallar asuba. Gari na wayewa aka dinga shiga yi mata jaje da dubiyar halin da mijinta yake ciki, hatta Ruƙayya sai da jikinta ya yi sanyi ganin halin da yake ciki da kuma ɓatan Jawahir Don haka Inna wuro ita ta ci gaba da ba su kulawar duk abin da Mai gado ta saba yi musu, Abubakar da ƙyar ya ya yarda ta ba shi abinci don sai da Mai gado ta je ta saka baki sannan ya yarda.

Basiru na isa Masarautar Huddam kai tsaye ɗakin duhu wurin da aka rufe su Fulani Umaima ya nufa, wari da ƙarnin da ke tashi a wurin bai hana shi tunkarar ƙofar ba. Da ƙarfi ya doka ƙofar da ƙafarsa ƙofar ta karye cikin takun isa ya shiga ɗakin hannunsa ɗauke da tsafatacciyar askar. Jakadiya da ke zaune a zube kamar kayan wanki cikin tashin hankali ta fara sakin fitsari, duk da jikinta babu ƙwari haka ta fara jan jikinta da ƙyar domin ceton ranta saboda a tsammaninta Basiru kashe su zai yi.

Fulani Umaima ta takure a ƙarshen bango ta yi saranda don azabar da take ciki gara mutuwarta da rayuwarta. Har Basiru ya ƙarasa motsin kirki ba ta iya yi ba sai bin sa da take yi da jemammun idanunta, ta rame sosai ta yi wani irin baƙi ga waɗansu ƙananan farare da jajayen tsutsotsi da ke manne a fatar jikinta. Sai da ya tsugunna a gabanta ya girgiza kai yana yamutsa fuska sannan ya furta.

"Ki kwantar da hankalinki ba kashe ki zan yi ba, É—an wani abu zan samu a wurinki wanda zai amfani duniyata. Don ma mahaÉ—in ya zame mini dole na haÉ—a da ke saboda tasirinki na kasancewarki a matsayin uwa da babu abin da zai kawo ni wannan É—akin."
Chapter 78 · 0% Book details