Sashe 76
Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Shekararki biyu da fara ciwon da ya same ki Ibrahim bai taɓa gazawa a kanki ba, babu inda bai zaga ba domin ya ga kin samu lafiya amma ba a dace ba. Ni kaina na aika ƙasashe da dama a kullin jiya i'yau, don haka na sa aka kira mini shi na yi masa nasiha a kan zaman da yake yi babu aure, sannan muka sa ya rubuta miki takardar saki. Da ƙyar da suɗin goshi ya rubuta miki saki ɗaya, sai dai a yadda labari ya zo mana har kwanciya jinya ya yi. Bayan ya sawwaƙe miki da wasu wattani ya yi aure ashe ajalinsa a kusa yake don matar da ya aura ma da tsohon ciki ya mutu ya bar ta. Shi ma addu'a za ki masa, domin Ibrahim ya matuƙar nuna miki kulawa."
Sai da Yaya Halima ta sha kuka mai isarta sannan Mai martaba ya yi mata bayanin duk abin da ya faruwa a Masarautar Huddam, da kuma hukuncin da ya yanke game da ba wa Sarki Abdul'aziz auren wata 'yar tashi, daga ƙarshe ya tabbatar mata da ita ce wacce ya zaɓar wa Sarki Abdul'aziz tun da ta samu lafiya. Jin kalaman Mahaifinta ba ƙaramin ɗimautata ya yi ba, ganin halin da ta shiga ya sa ya sallame ta a kan ta je ta yi nazari idan an kwana biyu zai sake ji daga gare ta.
Daga can gefe Boka Shaddas ya tsaya yana kallon Shugaba Zurufu, yana son tambayarsa matsayin Basiru wani irin tsoro ya mamaye shi. Yana nan tsaye ya ga ya yayyfa wa Jawahir ruwa nan take ta fara motsi a hankali ta fara buɗe idonta, zumbur ta miƙe tsaye tana ƙarewa wurin kallo sannu a hankali komai ya shiga dawo mata. Tsoro ya sake mamaye ta a lokacin da ta yi tozali da Shugaba Zurufu da yake a duke saboda tsufa. "Kamar kumbo kamar kayanta, wannan kama ta yi kama tamkar an tsaga kara ke da mahaifiyarki." Ja da baya Jawahir ta fara yi Shugaba Zurufa yana sake tunkararta.
"Na riga da na cika aikinka ina ɗana Basiru yake?" Boka Shaddas ya furta murya babu alamun wasa. Waigowa Shugaba Zurufu ya yi a hankali jikinsa na karkarwa, fuska ɗauke da murmushi ya zuba wa Boka Shaddas idanu har sai da gabansa ya faɗi. Don ya tabbata banza ba ta kai zomo kasuwa wannan murmushin da Shugaba yake yi ba zai tashi a banza ba. "Me kake ci na baka na zuwa Shaddas ai duk gaggawar Ungozoma ta bari a haife." Boka Shaddas ya yi ƙwafa bai tanka masa, Shugaba Zurufu ya fara matsawa gaban Jawahir sannan ya furta.
"Ɗaga mini rigarki." Rass gaban Jawahir ya faɗi. "Don Allah waye kai, ku duba girman Allah kada ku cutar da ni." Cak Shugaba Zurufu ya tsaya yana jinjina kai sannan ya furta. "Tabbas ko iya haka Fargi ta bar mu ta kusa yin galaba a kanmu, ta ci alwashin yaɗa zuri'armu abin da ba ta sani ba har addininmu ta so dakushewa." Kafin ya rufe bakinsa ya ga wata tsuntsuwa ta ratso ta jikin bango cikin shammata ta warci littafin labarin Hidaya da tun kwantar da Jawahir a kan farin dutsen ya faɗi a ƙasa. Daga Boka Shaddas har Shugaba Zurufu bin tsuntsuwar suka yi da kallo, da sauri Shugaba ya yunƙura da zummar ya ƙwato shi amma sai ya gagara.
Daga can bakin ƙofa wani Dattojo ne tafe da ɗanyan naman bunsuru ɗauke a saman kafaɗarsa, sai da ya ƙarasa gaban Shugaba ya zube yana haki sannan ya furta. "An aiwatar da komai Shugaba shin akwai abin da kake buƙata?" Ganyen da ke ɗaure a jikin dattijon Shugaba ya sunkuya ya goge gumin goshinsa cike da wulaƙanci sannan ya furta. "Babu buƙatar wani abu amma kalli can?" Ya yi maganar yana nuna wurin da Jawahir take tsaye.
A gajiye Dattijon ya miƙe yana bin wurin da kallo haɗe da ƙura wa Jawahir ido, lokaci ɗaya jikinsa ya ɗauki karkarwa bakinsa na rawa ya nuna Jawahir yana faɗin. "Faff... Fargi! Ke idanuwana suke gani ko gizo suke yi mini." Cikin yanayin mamaki Jawahir ta bi shi da kallo sam ba ta fahimci abin da suke nufi ba.
"Shugaba Fargi ta dawo gare mu." Mahaifin Fargi ya yi maganar cikin tsananin farinciki, hawaye bibbiyu ya fara zuba daga idanunsa. "Na daÉ—e da fidda rai da sake yin tozali da ke ashe akwai sauran ganawarmu a gaba..."
"Wannan ba Fargi ba ce." Kalaman Shugaba Zurufu suka katse Mahaifin Fargi. Shiru ya yi yana ci gaba da kallon Jawahir don da a ce ba laifi ba ne da ya musa kalaman da ya ji Shugaba ya yi.
"Wannan jinin Fargi da Sarki Sulaimanu ce, kuma ni na aika aka ɗauko mini ita domin na san mahaifiyarta ba za ta bar ni haka ba. Don haka za ta ci gaba da zama a ƙarƙashin ikona, na sha baƙar wahala kafin na bankaɗo ainihin wurin da ta ɓoye ta. Tabbas Fargi hatsabibiya ce ta ƙarshe, ni kuma na nuna mata duk girman kuka bagaruwa ce babba." Kuka Mahaifin Fargi ya fashe da shi yana jin tausayin rayuwar yarinyar da ba ta san rikiscin da ya wakana a shekaru goma sha shida da suka wuce ba. Ya san ba shi da ta cewa don haka ya ja bakinsa ya yi shiru, saboda tun ranar da Fargi ta bar cikin garin suka koma masa tamkar Bayi shi da mahaifiyarta da 'yan uwanta maza.
"Na gaji da gafara sa ban ga ƙaho ba Shugaba ka ba ni ɗana na wuce da shi." Boka Shaddas ya furta a ƙagauce. Shugaba bai tanka masa ba wuce can bangon ɗakin da ya taɓa ɓoye Basiru sannan ya zura hannu ya janyo shi, cikin wata irin tafiyar taƙama da ƙasaita Basiru yake taku ɗaiɗai yana bin mutanen kogon dutsen da kallo har suka ƙarasa wurin mahaifinsa. Hannu Boka Shaddas ya kai zai ruƙo hannun Basiru da sauri ya Basiru ya ɗaga masa hannu.
"Dakata! Ni ba ƙaramin yaro ba ne." Ya furta da wata irin ƙatuwar murya. A ɗan tsorace Boka Shaddas ya dube shi sannan ya mayar da kallonsa kan Shugaba. "Na ga sauye-sauye game da Basiru, me ya faru Shugaba Zurufu?"
"Guda ka ba ni kuma ni ma guda na damƙa maka ka ga babu kare bin damo!" Shubaba ya furta a taƙaice.
"Idan za ka wuce ka zo mu tafi ka da ka ɓata mini lokaci idan ba haka ba zan koma wurin da na fito." Basiru ya furta yana wurga jajayen idanunsa masu kama da sabon borkono. Boka Shaddas ba shi da mafita a dole ya rufa wa Basiru baya har suka fice daga cikin kogon dutsen, zuciyarsa na wasu-wasin sauyin da Basiru ya samu.
Tun da Malam Umaru yanke jiki suka faɗi ko kaɗan Bawa Lawandi bai motsa ba, shi kansa Umaru cikin fitar hayyaci yake juya kansa daga kwance ba tare da ya san inda kansa yake ba. Kamar daga sama Mai gado na zagayowa ta hange su a ƙasa, cikin tashin hankali ta ƙwalla ihu ta faɗa kan Umaru tana jijjiga shi haɗe da kiran sunansa. Ganin kukan ba zai kai ta ba ya sa ta fita a guje tana kururuwa neman ɗauki, nan take Bayi suka cika sashenta aka shiga yayyafa musu ruwa sai dai ko kaɗan Lawandi bai motsa ba a nan suka tabbatar da rai ya yi halinsa. Malam Umaru aka ɗauka a ka kai ɗakin Mai gado a lokacin ya daina jujjuya kansa sai dai zuru ya yi yana bin mutane da kallo, duk yadda Mai gado ta so ya yi magana sai dai ya bi ta da kallo.
Wannan mummunan yanayin da ya afkar musu ba ƙaramin ƙaɗa mutane ya yi ba, musamman mutuwar Bawa Lawandi da ya kasance mutum mai barkwanci ga kyakkyawar mu'amala da mutane. Duk wannan abin da yake faruwa babu wanda hankalinsa ya kai kan Jawahir, sai bayan da aka sallaci gawar Bawa Lawandi sannan Mai gado ta farga da rashin ganin Jawahir. Wani sabon tashin hankalin ne ya mamaye ta da aka bincika ciki da wajen Masarauta ba tare da anganta ba, hasali ma Ruƙayya ta bada tabbacin ta ga shigarta ɗaki, sai dai ta ce ba ta ga giftawarta ba. Nan take labarin ɓatan Jawahir ya zagaye cikin masarautar sai dai wannan al'amarin ba ƙaramin ɗaga hankulan mutane ya yi ba sakamakon babu baƙon fuska ɗaya da suka yi tozali da shi ballantana a zargi wani abu daga gare shi.
Shi kansa Sarki Abdul'aziz ya kaɗu da jin labarin abin da ya faru, a ɓangare ɗaya ya fara tunanin ko saboda Muhsin ya nuna ita yake so shi ya sa ta yi haka, don a lokacin da Muhsin ya yi maganar ya lura da ɓacin rai a saman fuskarta. Tun a daren ranar Sarki Abdul'aziz ya sake baza sojojin masarautar da dogarawa don su ci gaba da binciken ciki da wajen masarauta ko za su gano wani labari.
Lokacin da Kamalu ya ji labarin ɓatan Jawahir zuciyarsa tamkar za ta buga shi kaɗai ya dinga zagaye a ɗaki yana sake jin haushin Muhsin ya mamaye shi, don shi ma gani yake duk ta silarsa ce Jawahir ta ɓace. Da zuciya ta ɗebe shi kasa haƙuri ya yi ya wuce ɗakin Muhsin, ko neman izini bai yi ba ya faɗa ɗakin a lokacin ya samu Muhsin zaune ya zuba tagumi da hannuwansa biyu.
"Tun wuri tun ba a je ko ina ba ka yi gaggawar janye soyayyarka a kan yarinyar nan domin ba ta ƙaunarka, domin kana ganin yadda kalamansa suka sa aka neme ta sama da ƙasa aka rasa." Kamalu ya furta da tsananin baƙinciki.