← Book details Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 86

Sashe 85

Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Halimatu ga iyayenku a zaune muna so mu ji hukuncin da kuka yanke?" Idanunta suka ciko da ƙwallah ta ce. "Allah ya taimake ka ba na ƙi maganarka ba ne, amma duk lokacin da na tuna mijin Fatima zan aura sai hankalina ya tashi, ni fa yaya ce a wurin Fatima Sarki Abdul'aziz kuma sirikina ne..."
"Gabaɗaya a kalamanki babu hujja Halimatu, ya kamata mu zubar da al'ada mu kama abin da Addini ya zo da shi, babu inda aka ce don ƙanwa ta mutu yaya ba za ta auri mijinta ba, amma idan kuna ganin ba ku aminta ba; ba za mu yi muku dole ba." Mai martaba ya katse ta. "Na amince ranka shi daɗe har cikin raina." Murmushi ya bayyana a saman fuskokinsu. "Allah ya yi muku albarka." Yaya Halima ta amsa da Amin.

A wannan ranar Mai martaba ya rubuta wasiƙa ya aika ta Masarautar Huddam wurin Sarki Abdul'aziz, na amincewa da aura masa Yaya Halima a matsayin matar aure.

Tafiya suka yi mai nisan gaske har sai da suka kwana a hanya sannan suka ƙarasa, a lokacin da suka isa Masrautar Huddam cikin zumuɗi Mai gado ta nufi sashenta domin sanar da Malam Umaru sabon labarin ban al'ajabin da ya faru a garinsu Fargi, sai dai turus ta yi sakamakon ganin mutane ana yunƙurin fito da makara ɗauke da gawa a ciki. Kamalu na ganinta ya matsa gefe yana zubar da ƙwallah.

"Baba ka na ina?" Muryar Jawahir ta karaÉ—e wurin a lokacin da ta taho da gudu, ita ma turus ta yi tana bin mutane da makara a hannu da kallo.

"Kamalu mai ya faru?" Mai gado ta tambaye shi a ruÉ—e.

"Ki yi haƙuri Mai gado, dukkan mai rai mammaci ne dukkanmu can ne ƙarshenmu. Malam Umaru jinya ta ƙare wa'adi ya cika..."
"A'a Baffajo ba dai Umaruna ba, Umaru a raye na tafi na bar shi ka bar faɗa mini ya mutu." Mai gado ta katse Baffajo a firgice. Da sauri Jawahir ta tunkari Kamalu, hawaye na zuba ta furta. "Don Allah da gaske ne abin da Baffajo ya faɗa?" Gyaɗa mata kai ya yi jin haka ya sa Jawahir ta rushe da matsanancin kuka. Sai da aka yi wa Mai gado nasihohi da ban baki sannan ta matsa gaban gawar Malam Umaru ta fara yi masa addu'a, ta ɗora hannunta a saman jikinsa kuka ya ci ƙarfinta.

"Ina fargabar ranar da zan mutu na bar ku ke da Jawahir Mai gado, don Allah ko ba na raye kada ki yi wa yarinyar nan riƙon sakainar kashi."
"Kin san ranar É—aurin auren Jawahir In shaa Allahu duk wanda zai aure ta É—inki iri É—aya zan yi mana ni da shi."
"Mai gado me ya kamata mu fara siya na auren yarinyar nan ne?" Ire-iren maganganun Malam Umaru na baya suka dawo mata cikin kunnuwanta. Inna wuro ce ta janye ta sannan aka fitar da gawar. Sarki Abdul'aziz shi kansa ba ƙaramin kaɗuwa ya yi da jin mutuwarsa ba. Shi ya sallaci gawar da su Sarki Sulaiman sannan aka wuce da shi gidansa na gaskiya.

Sai da suka yi wanka suka huta suka ci abinci sannan Sarki Sulaiman ya buƙaci tafiya da Jawahir a cewarsa bayan wani lokaci zai dawo da ita, saboda so yake ta san dangi kowa ya santa, da farko Mai gado ta so nuna rashin jin daɗinta hakan ya sa Jawahir ta ƙi amincewa da bin Mahaifinta har sai da Mai gado ta ɗan tsawatar mata. Gabaɗaya suka ɗunguma har mahaifan Fargi suka nufi masarautar Sarki Sulaimanu. Sarki Abdul'aziz da saurah Fadawansa suka yi musu rakiya har bayan gari. Sai dai kafin su tafi Sarki Abdul'aziz ya tabbatar wa da Sarki Sulaimanu Mahaifan Fargi za su ci gaba da zama a cikin Masarautar Huddam gabaɗaya.

Saƙon Mai martaba da ya ƙarasa wurin Sarki Abdul'aziz ba ƙaramin faranta masa rai ya yi ba, don haka ya samu Waziri da sauran 'Yan uwan mahaifinsa waɗanda suke raye ya tura su domin su yi duk abin da ya dace. Da yake ya san hannunka ba ya ruɓewa ka yanke ka yar sai da ya sa aka yi wa su Ciroma da Galadima magana, Ciroma ne ya amince da zuwa domim shi tuni ya zubar da makamansa amma Galadima ko kyakkayawar amsa bai bayar ba. Wani abin farinciki suna isa Mai martaba ya sa aka ɗaura auren Sarki Abdul'aziz da Yaya Halima, sannan a wannan ranar masu kawo ta suka nufi Masarautar Huddam. Sarki Abdul'aziz bai yi mamaki ba domin ya san Mai martaba mutum ne mai karamci da dattako, waɗansu sababbin ɗakuna da aka gina aka gyara wa Yaya Halima ta tare a ciki. Nan da nan labarin auren Sarki Abdul'aziz da Yaya Halima ya karaɗe cikin masarautar Huddam, baƙin da suka rako ta Takawa ya sa aka haɗa musu Sha tara ta arziƙi. Da Sailuba ta ji labari tamkar ta haɗi yi zuciya ta mutu saboda baƙinciki, da gayya 'yan matan da manyan matan Bayi suka din ga shiga suna yi mata habaici saboda baƙinciki, sai ta rushe da kukan nadama da da-na-sanin abin da Mahaifiyarta ta ja mata, don ta san har abada taɓon da ta yi musu ba zai taɓa gogewa ba. Kuma a washegarin da aka kawo Yaya Halima ne Sarki Abdul'aziz ya naɗa Inna wuro a matsayin Jakadiyarsa, wannan matsayin sai ya zo musu a bazata daga ita har Baffajo. Takanas suka zube a cikin fadarsa suka shiga zabga masa godiya, shi kansa Kamalu ba ƙaramin daɗin hakan ya ji ba don ya san fiye da haka ma su Inna wuro sun cancanta.

Bayan da Sarki Sulaimanu ya gama gabatar da Fargi babu mutum ɗaya da ya amince da kalamansa ciki kuwa har da Mahaifiyarsa, kuma nan take ƙananan maganganu suka fara tashi wasu ma suka fara gulmar Sarki Abdul'aziz ya haifi Shegiya babu aure, takanas ya sa aka kira masa Jakadiya da Waziru waɗanda suka zame masa Shaida, da farko Waziri har zuciyarsa ta fara wassfa masa ya ƙaryata Sarki Sulaimanu amma da ya tuna ƙauyen da suka je da amininsa da ya zama waliyin Fargi, za su iya furta gaskiya nan take ya zayyane gaskiyar abin da ya sani. A hakan ma Mai babban ɗaki ba ta yadda ba sai da ta sa aka tashi waɗansu manyan Fada zuwa garin da Waziru ya ce a nan aka ɗaura aurensu suka yi bincike sannan suka aminta da ita, ya zayyana musu irin kisan zalincin da aka yi wa Fargi da halin da Jawahir ta yi yunƙurin shiga duka a sanadinsa. Nan take Mai babban ɗaki ta gane kuskurensu na ƙin barinsa ya auri zaɓinsa, suka rungumi Jawahir cikin soyayya da kulawa sai dai daga ɓangaren matansa ƙiri-ƙiri suka nuna kishinsu a fili, sai Sarki Sulaimanu da Mai babban ɗaki suka tsawatar musu sannan suka sauko kuke kulawa da ita.

Bayan da suka kwana biyu suka huta ne kuma aka fara shiga da Jawahir cikin dangi 'yan uwa da abokan arziƙi, Jawahir har mamaki take yi ganin irin gatan da take samu, a ɓangare ɗaya kuma idan mutuwar Malam Umaru ta faɗo mata sai ta shiga ɗaki ta ci kuka ta more.

"Wai ni ma 'Yar Sarki?" Ta wurga wa kanta tambaya tana sakin murmushi, kallon alƙaryar da take ciki take tana jinjina irin wahalhalun da bayi suke sha don jin ta take tamkar a cikin aljanna.

"Ranka shi daÉ—e! Don Allah wata alfarma gar ni." Sarki Sulaimanu ya zuba wa Jawahir ido cikin tsananin soyayya, don jin Jawahir yake ta fi dukkan 'ya'yansa samun fada a zuciyarsa. "Muna sauraronku tafi a kai tsaye Jawahiruna."

"Don Allah a dinga kula da rayuwar Bayi da halin da suke ciki, ranka shi daɗe a dinga duba cima da wurin makwancinsu. Na taso cikin ƙangin bauta da Bayi, na san wahala da rashin 'yanci da ke cikin rayuwar Bayi da 'ya'yansu idan da hali a dinga kyautata musu ko da ba za su kai matsayin iyalin Sarki ba. " Jawahir ta sauke numfashi ta ci gaba. "Ba iya Masarautar Huddam ba, a wannan gidan ma na ga irin rayuwar da na fuskanta a baya. Don Allah a tausaya musu domin suma 'ya'ya ne kamar mu." Murmushi Sarki Sulaimanu ya yi jin yadda take zayyana zance tamkar mahaifiyarta. "Tabbas barewa ba za ta yi gudu ɗanta ya yi rarrafe ba. Fargi ba za ta taɓa gogewa daga zuciyarmu ba har sai mun daina numfashi, In shaa Allahu za mu kyautata wa Bayi kamar yadda kuka buƙata, za kuma mu wae musu rana guda a mako domin shaƙata."
"Godiya nake ranka shi daÉ—e." Jawahir ta furta cikin girmamawa.

Bayan Wani Lokaci

Kamar yadda Sarki Sulaimanu ya alƙawarta bayan da su Jawahir suka samu kwanaki masu yawa, suka shirya da kayan alfarma tare da tsarabar sha tara ta arziƙi suka nufo Masarautar Huddam haɗe da maganar auren su Kamalu. Jawahir na zuwa Sashen Mai gado ta nufa da gudu ta rungume ta sai da ta suka ɗan sha kukansu na rashin Malam Umaru, suka sake jajantawa kansu sannan ta shiga ba ta labarin duk abin da ya faru. Bayin cikin masarautar manya da yara suka shiga tururuwar zuwa ganin Jawahir, nan ta fara ganin kulawa da soyayyar da suke nuna mata. Wasu daga cikinsu har mamakin yadda suke haba-haba da ita take.
Ɗakin Abubakar ta shiga ta same shi a zaune, yana ganinta ya sakar mata murnushi alamun ya gane ta, a hankali ya yunƙura ya fara tafiya yana ɗan layi kamar zai faɗi har ya ƙarasa wurin Jawahir. Daɗi ne ya kamata ganin jikin Abubakar ya ƙara kyau don Sarki Abdul'aziz ya dage da nema masa magani sosai, gwaranci ya shiga yi mata tana biye masa suna ciki haka Ruƙayya ta shiga suka ci gaba da hira.
Chapter 85 · 0% Book details