← Book details Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 86

Sashe 55

Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ba hurumina ba ne amma ai ta silata kike neman yafiyar Ubangiji. Inna me kika aikata ne da abubuwa suka caɓe mana lokaci guda. Ni fa na fara ɗora zargi a kanki don na tabbata ruwa ba ya tsami banza."

"Zan shawarci Takawa domin na fantsama nema miki magana, ba zan zura ido na ga kin lalace a banza ba, idan ta kama ma na ɗauke ki na mayar da ke can sashena tun da na lura idan na tsaya kallon ruwa kwaɗo zai iya yi mini ƙafa." Daga haka Jakadiya ta fice daga ɗakin zuciyarta na suya.

Ta kowacce fuska abin duniya goma da ashirin ne ya mamaye zuciyar Fulani Umaima, hannuwa bibbiyu ta zauna ta rafka uban tagumi tana tuna irin rayuwar jin daÉ—i da rashin tarin matsalolin da ta yi a baya.

"Ta wacce hanya zan samu damar yankar gashin kan Basiru? An ya Muhsin zai ba ni haɗin kai a kan abin da nake buƙata na kai yarinyar nan wurin Shugaba kuwa?" Fulani Umaima ta watsa wa kanta tambayoyi, murmushin da ya jima bai sauka a saman fuskarta ba ne ya suɓuce mata da ta tuna dabarar da ta faɗo mata game da Muhsin.

Ta yunƙura za ta miƙe ta sake jin ƙasanta ya zazzago mata, tsoro ne ya sake kamata don a kullin ƙasanta sake zazzagowa yake yi. "Me ya sa haka? Me ya sa al'amurana suka caɓe lokaci ɗaya?" Daga can bayanta ta ji an furta.

"Saboda ni ma ba ki bar ni na zauna lafiya a lokacin da nake raye ba." Raɗau ta ji muryar Fulanu babba a kunnuwanta. Da sauri ta waiga a ɗan tsorace karaf idanunta suka sauka a kan ƙanjamammiyar mage ta zuba mata idanunta masu abin tsoro. Matsanancin tsoro ne ya sake mamaye Fulani Umaima tana shirin guduwa azabar da ke addabarta ta sa ta faɗi ƙasa, tana daga zaune ta fara jan jiki a hankali magen ta ci gaba da tunkaro ta har sai da ta ƙarasa gabanta.

"Duk inda za ki je ina biye da ke Umaima!" Magen ta furta sannan ta nutse ƙarƙashin ƙasa ta ɓace daga wurin. Rashin samarwa kai mafita da damuwar da ta cunkushe Fulani Umaima ta sa ta fashe da wani irin kuka mai cin zuciya. Inna wuro ce ta faɗa ɗakin a firgice jin sautin kukan Fulani Umaima. "Allah ya taimaki uwar ɗakina ya ƙara wa Fulani lafiya. Ranki shi daɗe shi daɗe..." Da sauri Fulani Umaima ta katse Inna wuro. "Inna wuro muna buƙatar keɓewa." Inna wuro ta fice da sauri don ita kanta har lokacin tana cikin matsananciyar damuwar rashin ganin Kamalu.

Furhussam na ɗaukan Kamalu ya fara zabga matsanancin gudu bai sauke shi a ko ina ba sai a can ƙungurmin dajin Buhdu, a can cikin ƙaton wani farin dutse mai matuƙar ɗaukar idanu. Dajin cike yake da dogayen bishiyoyi a jajjere tamkar wani ne ya dasa su. Sai dai kallo ɗaya idan ka yi take hantar cikinka za ta kaɗa sakamakon yadda suffarsu take da yanayin tsoratarwa. Dutsen a mulmule yake babu ƙofa ko a huda ko kaɗan a jikinsa, sai da ya tsaya a wurin sannan ya ɗora tafin hannunsa a jikin dutsen, nan take ya tsage gida biyu wani ruwa mai garai-garai ya fara ɓulɓulowa daga ciki. Ta cikin ruwan Furhussam ya shiga, yana shiga dutsen ya sake haɗewa ya mulmule. Hallitu ne kala-kala a ciki waɗansu ɗauke suke da siffar tsuntsaye kawunansu ɗauke da ƙaho, waɗansu kuma siffar jikin birrai gare su bayansu ɗauke da jeluna. Duk ta hanyar da Furhussam ya wuce ɗaya bayan ɗaya hallitun suke zubewa ƙasa suna gaida shi cikin wani irin sarƙaƙƙen yare.

Tafiya ya ɗanyi ma nisa sannan ya isa tsakiyar babban filin da wata ƙatuwar rijiya a ciki, yana buɗe murfin rijiyar take wani ƙasaitaccen gado ya bayyana.

Da kansa ya ɗora Kamalu a kan gadon, daga ɓangaren hagu Hullat ce tafe cikin surar tsuntsu mai ɗan ban tsoro ita da yarta Furtuhmu, sai da suka ƙarasa gaban gadon sannan suka rikiɗe cikin surar bil'adam. Furtuhmu ce ta matsa gefensa cikin shauƙi ta sa hannu ta shafi gefen fuskarsa, a hankali Kamalu ya sauke ajiyar zuciya sannan ya buɗe idanunsa. A hankali yake bin wurin da kallon mamaki, ya ƙura wa Furtuhmu kallo yana jin tamkar ya taɓa sanin fuskarta. "Barka da hutawa." Ta furta masa a taƙaice. Furhussam da ya rikiɗe zuwa siffar da Dattijo Maharaz yake zuwar wa Kamalu ya matsa kusa da shi ya furta. "Kamalu ka farka kenan? Barka da tashi Sadauki." Sai a lokacin Kalamu ya sauke ajiyar zuciya hankalinsa ya kwanta. "Dattijo Maharaz ina ne nan ka kawo ni?" Murmushi ya sakar masa.

"Kada ka ɗaga hankalinka Kamalu nan ne wurin da za ku samu 'yancin kanku kai da iyayenka." Rufe bakinsa ke da wuya sai ga waɗansu dattijai sun ƙaraso wurinsa masu ɗauke da siffar Inna wuro, Baffajo da A'iru. Murmushi Kamalu ya sakar musu yana sake jin karamci da ƙaunar Dattijo Maharaz a zuciyarsa.

Sarki Abdul'aziz tun da ya kwanta ban da juyi babu abin da yake yi, tunaninnika da dama suka mamaye kwanyarsa yana sake juya kalaman Dattijo Maharaz. Abubuwan da suka faru a ɗakinsa suka ci gaba da dawo masa, a ɓangare ɗaya ga tagwayen larurorin matansa da suka fara ci masa tuwo a ƙwarya.
"Idan Dattijo Maharaz ya warware maka zare da abawa ka ƙara aure." Wani tsagin na zuciyarsa ya shawarce shi.

"Kada ka yi aure ka dai nema musu magani, ina ganin shi zai fi maka sauƙi tun da kana gani a sakacinka ka rasa matarka kuma uwar 'ya'yanka."Zuciyarsa ta sake shawartarsa.

"Don Allah ranka shi daɗe ka nemo mini magani, ni kaɗai na san irin azabar da nake ciki a kullin ji nake ana fisgar ƙasana tamkar zai fito waje." Kalaman Fulani babba suka dawo masa cikin kunnuwansa. "Astagafirullah! Allah ka gafarta wa Fatima Ubangiji ka yafe mini akan sakacin da na yi a kanta." Sarki Abdul'aziz ya furta a fili idanunsa na cikowa da ƙwalla.

Duk da ya kasance abokin 'yar tsamarta ne ba ƙaramin jimamin ɓatansa ta yi ba, a ɓangare ɗaya fargabarta ta ninku da ta tuna kusan ta silarta hakan ya faru sai dai ta gagara furta kowa har Mai gado. A duk lokacin da ta keɓe ba ta da aiki sai tunanin halin da yake ciki, wani lokacin har zubar da ƙwalla take yi. Wannan ne karo na farko da Jawahir ta ji ba za ta sake biyewa umarnin matar da ke zuwar mata a mafarki ba koda za ta hallaka. Hatta Mai gado sai da ta fahimci halin damuwar da Jawahir take ciki don haka ta tsare ta da tambaya.

"Jawahir wani abu yana damunki ne? Ko mafarki kika sake yi da matar nan?"
"Inna ina tunanin halin da Kamalu yake ciki ne! Ko ya mutu ko yana raye Allah ne masani." Jawahir ta ƙarasa maganar kamar za ta yi kuka.

"Addu'a ita za mu ci gaba da yi, idan muna nuna karayarmu a fili za mu sake raunata zuciyar Inna wuro don haka kika ga a kullin nake sake ƙarfafar gwiwarta."

Lokacin da Muhsin ya gama shan furar wurin Jakadiya tana fita bacci ya yi awon gaba da shi, ya jima yana bacci har bayan sallar Isha'i. Bayan ya tashi ya ɗan ji damuwarsa ta ragu don haka ya wuce ya ɗauro alwala ya gabatar da sallolin da suke kansa, zamansa babu jimawa fuskar Jawahir ta ci gaba da dawo masa a hankali murmushi ya suɓuce masa.

Fulani Umaima sai da ta yi wanka ta sake gyara jikinta ta tura ƙaton tsumma ƙasanta domin ya dinga tare ruwan da ke fita daga jikinta, ta rame sosai fuskarta ta yi fayau tamkar wacce ta jima tana jinya. Kai tsaye sashe Muhsin ta nufa a wannan karon ko Baiwa ɗaya ba ta bari ta yi mata rakiya ba, a lokacin da ta je yana zaune zugum cikin damuwa. Da sallama ta shiga sai dai ciki-ciki ya amsa mata ya ɗauke kansa gefe, a kusa da shi ta zauna ta aro murmushin yaƙe ta furta.

"Na zo bikon Sarkin gobe."
"Hmmm!' Kawai Muhsin ya ce.

"A baya na yi maka mummunar Fahimta ne Yarima, a tsammanina Yarima mai jiran gado tamkarka bai dace da auren Baiwa ba. Amma a yanzu da na fahimci irin soyayyar da kake yi mata na amince ɗari bisa ɗari Sarkin gobe, da kaina zan wuce har gaban Takawa domin na yi maka iso a kan neman aurenta." Sai a lokacin Yarima Muhsin ya saki fuskarsa, ya ruƙo hannun mahaifiyarsa cikin farinciki.

"Na ji daɗi ƙwarai da kika fahimce ni Ammi! A daren nan kuwa zan yi gaggawar dakatar da Jakadiya tun da kin sauko..." A razane Fulani Umaima ta katse shi.

"Wacce Jakadiya? Me za ka dakatar da ita?"
*SHU'UMAR MASARAUTA*

*31*

*Littafin kuɗi ne 500 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*

Sarki Sulaiman tare da maƙarrabansa cikin farinciki suka koma masarautarsu, tun bai shiga cikin sashensa ba kai tsaye wata ƙofa ya shiga wacce aka sassaƙa da zallar farin ƙarfe, sai walwali take tana ɗaukan idanu. Kusan ya zame masa al'ada duk fita idan zai yi ko bayan ya dawo daga wani wuri sai ya shiga cikin wannan ƙofar. Babban ɗaki ne da aka ƙawata shi da kayan alatun more rayuwa, a tsakiyar ɗakin an sassaƙa wata ƙatuwar tantamara wacce aka yi mata adon fentin fari da baƙi sai waɗansu duwatsu da aka manna mata a jiki. Sai da ya ƙarasa ya sumbace ta sannan ya fito ya fice kai tsaye ya wuce sashensa, da saukarsa babu jimawa aka haɗa masa ruwan wanka ya shiga ya gaggasa jikinsa sannan ya zura 'yar shararsa ta shan iska ya bayar da umarni Jakadiya ta kira masa matansa gabaɗaya kowacce tare da iyalanta.

Sun yi matuƙar mamakin jin kiran da yake yi musu don haka kowacce zuciyarta cike da wasu-wasin dalilin tarasu ta ƙarasa.
Chapter 55 · 0% Book details