Sashe 69
Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
"Ni mahaifiyarki ce ki daina tsora ta da ni." Gyaɗa kanta Jawahir ta yi sannan matar ta ci gaba da cewa. "Ungo wannan riƙe." Ta miƙa mata littafin da ke ɗauke da labarin hidaya, a baya ban ɗauke shi da muhimmanci ba, amma a yanzu da Shugaba yake son shiga gona ta dole zan nuna masa ya yi sake ɗan zaki ya girma. A tsammaninsa ya ƙone littafin gabaɗaya kowa ya rasa, bai sai a lokacin da ya jefa shi wuta abin da bai sani ba a kan hannuna ya ɗora shi ba. Wannan littafin ki adana shi ba na son ko Mai gado ta san da shi, shafi kaɗan ya rage ki kammala karatunsa, idan kin kammala kuma zan sanar da ke abin da za ki gudanar a nan gaba." Ta ci gaba da gaya mata ƙa'idojin littafin da kuma yadda za ta karanta shi. Har ta miƙe za ta fita sannan ta juya ta furta, "Ki tabbatar da kin ɓoye shi yadda wani ba zai samu nasarar ƙwace shi daga wurinki ba." Gyaɗa mata kai kawai Jawahir take sannan ta ɗaga labulen ta fice daga ɗakin.
Juya littafin Jawahir ta fata yi tana mamakin dalilin damƙa mata shi, ba don ta gargaɗe ta kada ta sanar da Mai gado ba da ta nuna mata shi. Ta shi ta yi ta bankaɗa ƙarƙashin gadonsu ta tura shi can ƙasan wani ƙullin kayanta sannan ta zauna shiru tana tunanin lokacin da za ta samu ta karanta shi.
Murmushi Dattijo Maharaz ya yi ya ce, "Na gode ƙwarai da wannan karamcin da ka nuna mini ranka shi daɗe, kuma a yanzu ba ni da wata buƙata da nake da ita sai dai ko shi Sarki Abdul'aziz idan yana da ta cewa." Wata kunya ta mamaye Sarki Abdul'aziz ya kasa furta komai sai sunkuyar da kai ƙasa da ya yi yana yi wa Mai martaba godiya.
Dattijo Maharaz ya dubi wurin da Kamalu yake zaune ya ce. "Wane ne kai? Ita ce tambayar da a kusan kullin muka haɗu da kai Kamalu sai ka wurga mini ita, na sha kawar da hankalinka tun kana ƙarami amma idan ba ka manta ba a baya na yi maka alƙawarin sanar da kai asalina da tushena da ma dangantakar da ke tsakanina da Marigiyin Aminina Sarki Muhammad Safwan." Kamalu ya saki Murmushi sanna ya furta. "Ka daɗe kana ja mini rai don haka ma na haƙura Dattijo Maharaz." Dattijo Maharaz ya ce, "Yanzu sai ka fi jin armashi da daɗin labarin saɓanin lokacin baya da ba lallai ka fahimci abin da nake so ka fahimta ba. Kamar yadda waɗanda suka sani da waɗanda ba su sani ba zan sake sanar da ku, ni dai ba bil'adam ba ne. Na fito ne daga jinsin Jinnu, sai dai kuma ni da iyalaina duka musulmai ne."
Damuwar yau da gobe ta sa Fargi ta tunkari Sarki Sulaiman dangane da halin da take ciki na bayyanar cikinta da ƙalubalen da za ta fuskanta. Wannan shi ne ga ƙoshi ga kwanan yunwa, shi a ɓangaren matansa babu wacce take ciki har mahaifiyarsa ta fara ƙorafi, ga ita kuma Fargi da ciki amma babu halin bayyanawa. Lallashinta ya yi sannan ya shiga tunanin mafitar da za su samawar wa kansu. Da farko har shawara ya ba ta akan ko ya ɗauke ta ya samar mata gida ta zauna sai ta ga wannan ba mafita ba ce, don Shugaba na iya binciko halin da take ciki.
Watarana tana zaune a ɗakin mahaifiyarta a lokacin cikin jikinta ya shiga wata na huɗu, ya bi jikinta ta yi ƙiba ta murje ta yi kyau. Shugaba ya aiko da kiranta, haka kawai ta ji gabanta na faɗuwa amma gudun kada ya fahimci halin da take ciki ya sa ta shirya ta je wurinsa.
"Wannan ne mijin da kika aura, kuma mahaifin abin da yake cikin?" Shugaba ya wurga mata tambaya yana hasko mata hoton Sarki Sulaiman.
*SHU'UMAR MASARAUTA*
*38*
*Littafin kuɗi ne 500 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*
Cike da jin daɗin kalaman Dattijo Maharaz mutanen ɗakin suke gyaɗa kawunansu, har ya yunƙura zai ci gaba da magana Bamaguje da ke gefe ya ce. "Zan gusa haka Maharaz tun da na kammala abin da ya kawo ni, kamar yadda na gaya maka a baya lafiya ta fara rauni a gare ni..." Kalaman Bamaguje suka katse sakamakon wata irin cafka da suka ga wannan hallitar mai ɗauke da surar Baiwa Maimuna ta yi masa. A zabure su Mai martaba suka miƙe saboda tashin hankali, Bamaguje ya kwarara wata irin ƙara wace ta sake razana mutanen da ke cikin ɗakin, tamkar ba shi ya yi ta ba. Nan take Bamaguje ya fara yunƙurin amfani da alƙaluman tsafinsa da sihiri amma sai ya gagara aiwatar da koma, a ɓangare ɗaya kuma Guzzu ya ci gaba da kai masa cafka ta ko ina. Da ƙyar Bamaguje ya samu ya bugi ƙasa tare da furta waɗansu kalmomin tsafi nan take suka ɓace gabaɗaya.
Ajiyar zuciya gabaÉ—aya suka sauke Mai martaba na shirin magana Sarki Abdul'aziz ya zayyane masa duk abin da ya faru game da Baiwa Maimuna, a nan suka sake jinjima al'amarin Fulani Umaima da rashin imaninsu ita da Bamaguje. Dattijo Maharaz na daga wurin da yake zaune bayan duk sun koma sun zauna, ya ci gaba da cewa.
"Sunana Maharaz bn Muhammad Ishaƙ. Asalinmu mun kasance 'yan ƙasar Misra, sakamakon a can aka haifi magabatanmu wato iyayen kakanninmu kusan kimanin ɗaruruwan shekarun da suka gabata. Ina da matan aure biyu da 'ya'ya goma sha biyar, yayin da maza suka fi yawa a ciki. A yadda na samu labari daga cikin kundun labaran tarihi, asalin wanda ya fara zama a wannan ƙasar kakan-kakana ne mai suna Huzaifa. An ce dalilin barowarsa daga Misra bai wuce auren dole da ake shirya za a yi masa shi da wata 'yar uwarsa ba, silar haka ta sa ya yi nisa da gida ko ya samu farinciki har ya auri wacce yake so. An ce ya shafe sama da shekara saba'in a ƙasar nan ba tare da kowanne jinsi ba har Allah ya haɗa shi da matar aure mai suna Zuwaira, ita kuma ta kasance daga cikin jinsin aljanun ƙarƙashin ƙasa saɓanin mu da muka kasance Jinnul-turabiy. Wannan auratayyar ita ta haddasa zuri'a mai girma, kuma a yadda na ji labari kakan-kakana Huzaifa ya tara iyali mai matuƙar girma sai suka samu baƙuncin Aljani Rabo wanda ya kasance daga jinsin baƙaƙen aljanun doron ƙasa, kuma shi ne asali da tusheh samuwar Shugaba Furhussam wanda muka fafata da shi a baya.
Sun ci gaba da rayuwa har kowa ya tara iyalinsa cikin karamci da mutumta juna, na samu labarin cewar a daidai wannan gaɓar sai waɗansu Fulani da buzaye suka yada zango a daidai daular da Huzaifa ya kafa. Rabo har ya so su tashi waɗannan Fulanin waɗanda da alama gudun hijira suka yo suka yada zango a nan sai Huzaifa ya hana shi a yadda aka ce ya nuna masa cewar tun da ba shiga huruminsu suka yi ba gara a ƙyale su. Zaman Fulanin nan da buzaye sai ya zama suma sun kafa na su garin suka naɗa shugabanni har zuwa masu masarautu a cikinsu. Sanu a hankali suka ci gaba da bunƙasa har ya zamana Masarautar Huddam ta fara gawurta, kuma babu wani ƙalubale da suke fuskanta daga wurin jinsin Huzaifa da Rabo tare da iyalansu." Dattijo Maharaz ya dakatar da maganar da yake yi sakamakon ɗaga hannunsa da Kamalu ya yi alamun akwai tambayar da yake son yi.
"Shin yaushe ne alaƙa ta shiga tsakanin aljanu da mutanen masarautar nan? Kuma ina neman ƙarin haske game da rafin tsamiya sai kuma..." Kamalu ya yi sauri katse maganarsa. Dattijo Maharaz ya lura da haka don haka ya ce. "Sai kuma me Kamalu? Yi tambayarka kanka tsaye."
"Sai kuma Shurin da kake rayuwa a cikinsa wanda yake cikin turakar Mai martaba, yaushe aka kafa shi a wurin?" Dattijo Maharaz ya saki murmushi sannan ya furta. "Ni kaina ban san ranar da aka kafa wannan shurin ba, wannan shurin ya kasance mai tsohon tarihi domin Kakana ya ce mini shi kansa zuwa ya yi ya tarar da shi. Amma an yi mini cikakken bayani game da dalilin wanzuwarsa a wurin."
"Muna sauraronka Datijo Maharaz." Sarki Abdul'aziz ya faɗa cike da zaƙuwa.
"A wancan lokacin mai tsawo an ba ni labarin cewar Huzaifa shi ya kasance tamkar jagora kuma shugaba har ya kasance sauran al'ummar jinsina sun damƙa masa sarauta, wacce a ita ce take tafe har kawo kaina. Kuma a lokacin da kakana ya karɓi mulki daga hannun mahaifinsa an ce a lokacin ne kuma Marigayi Sarki Sadiƙƙu yake kan mulki cikin masarautar mutanen masarautar Huddam."
"Idan na fahimci labarinka Dattijo Maharaz kana nufin wannan masarautar ta huddam ta kasance masarautar da jinsi biyu suke mulkarta? Jinsin fararen aljanu da kuma jinsin bil'adama?" Mai martaba Maifin Fulani Babba ya tambaya.