← Book details Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 86

Sashe 53

Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Sarki Abdul'aziz ina son ka ƙare wa yaron nan kallo tun daga yatsun ƙafarsa har zuwa tsakiyar kansa." Dattijo Maharaz ya furta yana harɗe hannuwansa biyu a ƙirji. Lokaci na farko kenan da ƙirjin Sarkin Abdul'aziz ya buga a daidai lokacin da ya sauke ƙwayar idonsa a saman yatsun Kamalu da ke ɗauke da cindo irin nasa, ya ci gaba da kallonsa har zuwa saman yatsun hannuwansa da ba su da maraba da na jikinsa. Tarin tunaninnika suka rikito wa kwanyarsa, don haka ya ɗago da mamaki yana shirin wurga wa Dattijo Maharaz tambaya ya katse shi.

"Wannan yaron makusancinka ne, magajinka ne kuma shi É—in jininka ne."

Mamakin Sarki Abdul'aziz ya ninku a sanyaye ya ce. "Ban gane ba Dattijo Maharaz."

"Ina nufin wannan yaron Kamalu da muke dambarwa a kansa É—anka ne na cikinka halak-malak, kuma babu ko tantama ko a yanzu zai iya hayewa saman karagarka."

Cikin shammata Furhussam ya ɗauki Kamalu ya bigi bangon ɗakin nan take ya ɓace da shi, hankalin Dattijo Maharaz ba ƙaramin tashi ya yi ba. A gaggauce ya dubi Sarki Abdul'aziz ya furta, "Kada ka furta wannan maganar ga kowa har sai na dawo gare ka." Daga haka shi ma Dattijo Maharz ya ɓace daga wurin.

Bamaguje shi da Fulani Umaima ba su sauka a ko'ina ba sai a kogon dutsen tsafin Shugaba Zurufu, yana rakaɓe a jikin bango ya tsufa tukuf don har ya fi Bamaguje tsufa nesa ba kusa ba. Kallo ɗaya idan ka yi masa ba za ka taɓa tsammanin zai iya motsi ba ballantaba ya iya aiwatar da wani mugun abu. Ƙurrr ya yi wa Fulani Umaima da ke rakaɓe a gefe tana zare idanu cikin tashin hankali.

"A wacce rana kika haifi Basiru?" Shugaba Zurufu ya wurga mata tambaya yana kafe ta da shanyayyun idanunsa. "Wallahi na manta ba zan iya tunawa ba."

"Kin haifi asara! Domin kin ɗebo ruwan dafa kanki Umaima. Yanzu dai ina son ki ɗebo mini gashin kansa, ki kuma ki ɗebo mini sawun ƙafarsa. Kuma zan ba ki asirin da zai taimaka miki wanda da za ki kawo mini wannan Yarinyar da ƙafafuwanta har cikin kogon tsafina, domin na yi binciken abin da Bamaguje zai bincika a kanta." Tun bai gama maganar ba gaban Fulani Umaima yake faɗuwa, don yadda take shakkar Basiru ko Takawa ba ta tsoronsa haka. Za ta yi magana ta ji wannan abin ya sake tunkuɗo mata cikin azaba ta zuba ihu tana rirriƙe Bamaguje, a hankali ta ji ya fara lafa mata sai ga wani ruwa tamkar na mugunya yana gangarowa daga ƙasanta. A dudduƙe haka Shugaba Zurufu ya tako a hankali har ya ƙarasa gabanta ya tsugunna, kuka Fulani Umaima ta fashe da shi ta dubi Bamaguje.

"Bamaguje ka shiga lamurana ka duba halin da nake ciki." Wannan karon a fili ya nuna tausayinta don haka ya sunkuyar da kansa ƙasa.

"Har a kullin ina faɗa miki hannunka ba ya taɓa ruɓewa ka yanke ka wurgar, tun a ranar da kika ziyarce ni na fuskanci matsalarki Umaima. Sai dai kash! Har kawo yau na gagara samun mafitar ciwon da yake tattare da ke, bayan wancan dalilin na littafin labarin Hidaya dama na ci alwashin kawo ki wurin Shugaba domin ya taimaka miki." Shugaba zurufu ya ɗauki wata tsumburarriyar mujiya ya ɗora a ƙasan Fulani Umaima nan take ta fara tsotsa tamkar wacce take cin abinci.

"Ka yi alfahari da tsafi da sihiri Bamaguje tabbas za ta warke, da a ce wannan mujiyar ba ta sha gurɓataccan ruwan nan ba da ba za ta taɓa warkewa ba." Daga Bamaguje har Fulani Umaima rige-rigen sauke ajiyar zuciya suka yi, Bamaguje na shirin sake yin magana Shugaba ya katse shi.

"Sai dai ba zan aiwatar da aikinta ba har sai na kammala sauran waɗanda muka saka a gaba, yanzu dai ta tabbata ta cika alƙawarin da ta ɗaukar mana na kawo gashin jikin Basiru da yarinyar nan." Da sauri Fulani Umaima ta hau gyaɗa kai sannan Shugaba ya ɗebo tarin magunguna da kayan tsubbace-tsubbace ya damƙa mata haɗe da sallamarsu.

Suna isa tsibirin Bamaguje Fulani Umaima ta dube shi cikin damuwa, sannan ta zayyane masa abin da yake tsakanin Yarima Muhsin da Jawahir. Sai da ya yi shiru kamar ba zai amsa ba sannan ya ƙyaƙyace da dariya ya furta. "Kada ki damu da wannan Umaima, ki zuba idanu domin Shugaba Zurufu hatsabibin mutum ne. Tun da kika ji na jinjina wa zalinci da tsantsar mugun aikinsa kin san ba zan yi mana zaɓen tumun dare ba." Jiki a sanyaye Fulani Umaima ta gyaɗa masa kai, ta miƙe cikin hawaye don duk lokacin da wannan naman hallitar ya tunkuɗo mata ji take tamkar ranta zai fita. Fulani Umaima har ta fara tafiya Bamaguje ya ce.

"Umaima!"

Yanayin yadda ya yi maganar ya sa ta tsaya cak, sannan ta waigo tana share hawaye. "Ina son sanar da ke wata muhimmiyar magana amma ina tunanin ma'aunin da za ki jinginata, amma zan taushi zuciya har zuwa bayan warwarar matsalolin da kike ciki domin ranar wanka ba a ɓoyon cibi." A wannan karon ma sake jinjina kanta ta yi don haka ta ci gaba da tafiya har ta koma cikin masarautar Huddam.

Har Yarima Muhsin ya jima da fita Jawahir ba ta iya tashi zaune ba, sai can bayan wani lokaci tana kwance a ƙuryar gado ta ji an ɗaga labulen ɗakin. Uwar soro ce ta saki murmushi sannanta ce.

"Jawahiru wato yau kin tsokano wutsiyar ɗan autan dodo ko? Wallahi sai kin yaba wa aya zaƙinta." Daga haka ta fice daga ɗakin tana sakin murmushin mugunta.

"Ina tsananin ƙaunarki! Saboda ke farincikina ce." Raɗau kalaman Muhsin suka dawo cikin kwanyarta, take ƙirjinta ya hau dakan lugude. "Ke fa baiwa ce me Yarima ya gani a jikinki da zai ce yana so? An ya ba kunnuwanki ne suke neman yaudararki ba?" Ɗaya daga cikin tsagin zuciyarta ya gargaɗe ta. Tana nan zaune ta ga Mai gado ta faɗo ɗakin kallo ɗaya za ka yi mata ka fahimci tana cikin matsananciyar damuwa.

"Wanne laifin kika yi wa Yarima da na ji an ce ya biyo ki har cikin ɗaki? Jawahir wai me ya sa ba kya tunawa da matsayinmu a cikin gidan ne? Mu fa bayi ne ƙasƙantattu a kan me za ki dinga shiga hurumin ɗan masu gida?" Lokaci ɗaya Jawahir ta duburburce don ko karen hauka ne ya cije ta ba za ta taɓa ce wa Innarta Yarima ce wa ya yi yaja sonta.

"Inna tsautsayi ne ya sa na bige shi." Jawahir ta furta a sanyaye.

"Ki shiga hankalinki Jawahir, kin san dai yadda Yarima yake a cikin gidan nan idan ba haka ba muna zaune za ki kunto mana masifar da za ta nemi ta gagare mu." Da kai Jawahir ta amsa sannan Mai gado ta sake ficewa daga É—akin.

Sarki Abdul'aziz ya shafe sama da minti biyar a tsaye yana juya kalaman Dattijo Maharaz a cikin ransa, a ɓangare ɗaya kuma zuciyarsa na yunƙurin amincewa da abin da kunnuwansa suka ji.

"Ta yaya zai zama jininka bayan ba ka taɓa saninsa a cikin 'ya'yanka ba?"
"An ya Dattijo Maharaz ba yaudararka yake son yi ba?"
"Ɗan mutum a ce ɗanka ne kamar a mafarki, idan ɗanka ne wace ce uwarsa? Kuma a yaushe aka haife shi?" Tarin tambayoyin da Sarki Abdul'azi ya dinga yi wa kansa kenan amma ya gagara samar wa kansa amsoshinsu. Da ƙyar ya iya jan shanyayyun ƙafafuwansa ya koma rumfa (Falo) ya zauna ya rafka uban tagumi.

"Yaron nan makusancin Masarautar nan ne, É—anka ne, jininka ne kuma Magajinka ne." Kalaman Dattijo na baya suka dawo masa raÉ—au a cikin kunnuwansa. Sallamar da Jakadiya da wasu 'yan matan bayi suka ne ya katse masa tunanin da yake yi, a sanyaye ya É—ago ya dube su hannuwansu É—auke da manyan tire sai a lokacin ya tuna da shirin tarbar Sarkin Bahdi wato Sarki Sulaiman bn Abdulwahab.

"Barka da hutawa ranka shi daɗe ɗawisu mai yawan Ado. Allah ya ja zamanin Mai martaba, sukari ba ka yi farin banza ba bangon zuma kowa ya raɓe ka sai ya lasa." Jakadiya ta yi maganar tana yi masa jinjina da hannu, sannan ta ci gaba da cewa. "Allah ya taimaki Mai martaba ya ƙara wa Sarki lafiya. Sarki Sulaimanu na ƙasar Bahdi ya samu ikon ƙarasowa." Ajiyar zuciya Sarki Abdul'aziz ya sauke a sanyaye ya furta.

"Jakadiya a sanar da Shamaki a ba wa Sarki Sulaimanu kulawa kafin mu ƙaraso, me aka zube a gabanmu haka Jakadiya?" Jakadiya da hankalinta ya tafi wani wurin sai a lokacin ta lura da kuskuren da ta tafka, abin motsa bakin da za ta saka Bayi su kai masaukin baƙi sune ta sa suka ɗebo suka kawo sashen Takawa.

"Allah ya taimake ka abin saukar ɓaƙi za mu kai sashen Baƙi, shi ne muka biyo don mu sanar da kai isowar Sarki Sulaimanu." Jakadiya ta yi maganar cikin wayancewa.

"A ba nu wuri Jakadiya." Sarki Abdul'aziz ya furta a taƙaice. Da sauri suka miƙe gabaɗaya suka fice. Jakadiya na kammala abin da yake gabanta cikin zumuɗi ta wuce sashen Yarima Muhsin don ta cim ma kuɗirinta a kansa.

"A iya tsammanina Yarima ya fi ƙarfin kowacce yarinya a ciki da wajen masarautar nan, kaicon wannan rana da na buɗe ido na ga hawaye a idanun Yarima domin wata 'ya mace." A sanyaye Yarima Muhsin ya ɗago yana kallon Jakadiya ya sake sunkuyar da kai ƙasa. "Ka share hawayenka Yariman masarauta, Sarkin gobe da yardar Allah. Ba Jawahir ba ko wacce 'ya kake muradi In shaa Allahu sai ka mallake ta Uban ɗakina."

"Jakadiya dama sunanta Jawahir?" Jakadiya ta yi murmunshin yin nasara.

"Karɓi wannan fura ce na dama maka ita mai sanyi ka sha ko zuciyarka ta yi sanyi Uban gidana. Sunanta Jawahir kuma sunan Mahaifiyarta Mai gado, yarinyar tamkar 'ya ce a wurina don haka kuwa da kai da kaya ai duka mallakar wuya ne. Ni nan zan wuce maka gaba har gaban Takawa a game da aurenta matuƙar hakan zai faranta maka." A fili Muhsin ya saki murmushin farinciki. Ya miƙa hannu ya karɓi ƙwaryar hannun Jakadiya, ta zauna a gefe suna hira yana sha har ya shanye furar tass.
Chapter 53 · 0% Book details