← Book details Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 86

Sashe 42

Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun lokacin da Jawahir ta ga Yarima Muhsin ya faɗi can gefe ta ɗiba a guje don tseratar da kanta, jikinta na karkarwa ta ƙarasa sashen Fulani babba sai a lokacin ta tsaya ta daidaita nutsuwarta. Ta sauke ajiyar zuciya tana mamakin abin da ya jefar da Yarima Muhsin a ƙasa har ta ji yana zuba ihu, Yariman da duk faɗin masarautar nan babu wanda ake tsoro kamarsa. Wani sabon tsoron ya dirar mata, tana tsoron Allah ya sa ba wani abin ne ya same shi ba.

"Ko dai shi ma ɗan iska ne?" Jawahir ta faɗa a zuciyarta, ba ta samu damar ba wa kanta amsa ba kawai ta kutsa kai cikin gidan sakamakon jin sautin kukan 'yan uwan Fulani babba da suka ƙaraso daga masarautarsu.

Kalaman Dattijo Maharaz ba su sa Kamalu ya saki jiki sosai ba don haka a ɗarare ya sake zura kansa, ƙurawa cikin farin dutsen idanu ya yi sannu a hankali ya ga fuskarsa na rikiɗa tana sauyawa. Mamaki ya sake mamaye shi, yana shirin ɗagowa ya ga wani farin maciji sol ya kanannaɗe saman kansa a firgice ya ta ƙarƙare ya zunduma ihu cikin tashin hankali. Tsoronsa ya sake ninkuwa sakamakon jin yadda ƙafarsa ta liƙe ƙam da ƙasa, sai da Dajjito Maharaz ya ci dariya ya more sosai sannan ya furta.

"Da alama Masarautar Huddam na gabda samun shugaban da zai dinga nishaɗantar da su, wannan macijin da kake gani ba zai bar kanka ba matuƙar ba ka sake sunkuyar da kanka saman dutsen ba." Ganin ba shi da wata mafita ya sa Kamalu ya sunkuya ga namakinsa sai gani ya yi macijin ya warwaro daga kansa ya faɗa ciki. Kamalu na shirin ɗagowa ya ga fuskarsa ta fito dal kansa ɗauke da wani rantsattsan rawani mai matuƙar kyau da ɗaukan idanu. Da mamaki ya kai hannunsa saman kansa yana shafawa, ya sake mayar da kansa saman dutsen yana kallo.

"Ka dangwali wancan taɓon da tafin hannuwanka ka shafa a jikin katangar can."

Ba musu Kamalu ya sa hannu cikin tabon mai matuƙar danƙo ya manna a jikin katangar kamar yadda ya ga sawayen wasu a wurin. Yana gamawa Dattijo Maharaz ya ja shi suka nufi wata hanya mai ɗauke da waɗansu manyan tukwanen ƙasa, girman kowacce ɗaya za a iya saka mutum a cikinta. A kan tukunya ta ƙarshe suka tsaya Dattijo Maharaz ya furta, "Ɗora hannuwanka akai." Gabaɗaya Kamalu ya ƙosa da wannan abubuwan da yake saka shi, sai dai kuma haka kawai ya ji zuciyarsa ta gagara bijire masa. Yana ɗora hannuwansa ya ji wata irin busar sarewa a saman kansa, da sauri ya waigo Dattijo Maharaz ya sakar masa murmushi, shi kansa bai san dalili ba amma ya ji wani kaso na ɓacin ran da ke zuciyarsa ya kau. Daga haka suka juya har za su tafi daga can bayansu suka ji an furta.

"Wane ne kai? Mene ne dalilin zuwanka wurin nan mai tsohon tarihi?" Galadina ya yi maganar yana shan gaban Kamalu.

Tun daga ranar da Shugaba ya karɓi ragamar Fargi ya ci gaba da ƙoƙarin sarrafa al'amuran tsafinsa yana ba ta horon da ya dace, sai ya kasance ta taso cikin ƙwarewa da iya sarrafa alƙaluman tsafi da sihiri mutane har mamaki suke yi. A lokacin da ta ka shekara bakwai a duniya a lokacin Shugaba ya sake tsufa don haka koda aikin tsafi aka kawo masa, kusan tare suke aiwatarwa, da yake ta kasance mai kaifin basira har ta fishi gudanar da aiki nan take. Sai ya zamana girmamawar da ake yi wa mahaifinta da Shugaba ta fara karkata zuwa kanta, mahaifinta ko kaɗan bai damu ba sai ma tarin farinciki da yake mamaye shi yake sake tabbatar da a wannan lokacin ne ya san ya samu magajiya.

Shi kuwa shugaba Zurrufu a kullin ya buɗi ido ya ga yadda ɗaukakarsa take yin ƙasa sai baƙinciki ya mamaye shi, tsanar Fargi ta sake mamaye zuciyarsa watarana har sai da ya ji tamkar ya hallaka ta. Amma kuma sai ya danne don har yanzu akwai gaɓar da yake son kaiwa domin cikar muradinsa. A lokacin da Fargi ta cika shekara takwas cif a duniya a sannan babu wani irin tsafi, sihiri da siddabarun da ba ta iya ba. Kai tsaye bokaye da 'yan tsubbun da ke wajen gari suke kawo mata aiki don neman taimakonta, kuma duk aikin da ta saka a gaba sai ta yi galaba a kansa. Cikin wannan shekarun na matashiya Fargi sai aka samu sauye-sauye da dama ta ɓangaren tsubbu da ci gaban samuwar kayan tsafe-tsafe, hatta masu zuwa neman taimako wurinsu sun samu ci gaba domin a wannan lokacin ba Bokaye ne kaɗai suke zuwa wurinsu ba daga cikin masu zuwa wurinsu sun haɗa da; Sarakun, masu neman Mulki ko wata ɗaukaka, 'Yan kasuwa da masu bulaguro, Maharba, Mafarauta, Masunta, Mahauta, 'yan bori da Matan aure musamman waɗanda suke da kishiya ko kuma waɗanda za a yi wa kishiya.

Sai ya kasnce kawunan mutanen Rumzu ya fara wayewa har sukan gina bukkoki da rumfunan da suke zama suna hutawa, har ma suka fara samar da ƙananan rumfunan kasuwa wasu daga cikinsu sukan fita wajen gari su yo sarin wani abu su kawo cikin dajin nasu su sayarwa. A kuma wannan lokacin sai Fargi ta sake samun horo daga jinsin baƙaƙen aljanun ƙarƙashin ƙasa, bisa yadda za ta dinga sarrafa tsafi da shanu musamman baƙaƙe da jajaye don aiwatar da duk wani ƙulli da take buƙatar ƙullawa. Matsala ɗaya ce ta fara yunƙurin ci wa Fargi tuwo a ƙwarya na rashin samun wadatattun shanun aiki, a lokacin da ta kai ƙorafinta wurin Shugaban baƙaƙen Aljanun Sarki Kadmar. Sun jima suna tattanawa sannan suka tsaida matsayar idan ta amince sai su dinga ban gishiri na baka manda, wato ita ta dinga yi musu yankan duk abin da suke so su kuma za su dinga ba ta duk kalar saniyar da take buƙata a lokacin da za ta yi wani aiki.

Zuciyar Fulani Umaima fari tass ta nufi sashen Sarki Abdul'aziz sai dai tana zuwa ta yi tursss sakamakon ganin Takawa da ta yi zaune shi da Mahaifin Fulani Babba sun saka gawarta a gaba suna yi mata addu'a. Ɓacin ranta bai ɓoyu ba har sai da ta bayyana a fili don ko kaɗa ba ta ji labarin Mahaifin Fulani babba zai zo jana'iza ba, tun da tuntuni mahaifiyarta da 'yan uwanta suka iso cikin Masarautar kuma ba tare da shi ba. Tana daga tsaye ƙerere a bakin ƙofa ta furta, "Ranka shi daɗe kuma waye har cikin turakarka? Ina tsammanin mu biyu za mu zauna da ita. "Fulani Umaima ta yi maganar tamkar ba ta gane mahaifin Fulani babba ba.

"A yi hattara Fulani. Mai martaba ya ƙaraso yanzu ba da jimawa ba, za ku iya tafiya ku ba mu wuri." Fulani Umaima tamkar za ta fashe da kuka haka ta ji, tashin hankalinta bai wuce ba ta da dabara ɗaya da za ta ce za ta yi don ta samu sararin shiga har ta aiwatar da ƙudurinta. Kamar ba za ta matsa daga wurin ba ta fita tana jan sagaggiyar ƙafarta, zuciyarta a cunkushe ta koma sashenta.

Tun daga tsakar gidanta ta fara jin yadda ake wurgi da kaya hakan ba ƙaramin mamaki ya ba ta ba, carko-carko ta ga su Inna wuro sun yi cikin ɓacin rai ta buga musu tsawa.

"Uban waye a cikin É—akin nan da kuka yi carko-carko ba za ku iya wanzar da komai ba?"

Inna wuro ce ta yi ƙarfin halin faɗin. "Ranki shi daɗe a gafarce mu, Basiru ne ya shiga ciki kuma ya ba mu umarnin ko da wasa kada mu kuskura mu shiga cikin ɗakin." Rass gabanta ya faɗi, tun ba ta gama jin kalamansu ba ta faɗa cikin ɗakin. Yanayin yadda ta ganshi ba ƙaramin razanata ya yi ba, sak ta ga ya koma mata tamkar boka Shaddas. Cikin zare idanu da rashin tsoro ya dube ta da wata irin kakkaurar murya ya furta. "Ina kika kai littafin nan? Maza ki miƙo mini yanzun nan kar ki ɓata mini lokaci." Haka kawai ta ji toron Basiru ya kamata, don ta ga babu alamar wasa a fuskarsa.

Fulani Umaima sai da ta fita can tsakar gida ta kori Bayinta don gudun kada su ji wata ɓaraka tsakaninta da Basiru, a fara yawo da ita a cikin gidan da ƙananan maganganu sannan ta koma ɗakin.

"Waye ya aiko ka É—aukan littafin nan?"

"Wannan bai shafe ki ba, abu ɗaya kawai nake so ki damƙa mini shi. Idan kuma ba za ki iya ba ki fita ki bar ni na yi aikin gabana." Cike da faɗuwar gaba take bin sa da kallo, don idan kunnuwanta ba gizo suke mata ji ta yi hatta muryasa ta sauya daga tashi ta ainihi zuwa wata murya marar daɗin sauraro.

"Yanzu haka kin dawo daga sashen Takawa ne silar zuwan mahaifin Fulani, kuma jikinki ɗauke yake da gubar da za ki sakawa gawar idan kina son na taimaka miki zan baki layar ɓata da garin kasa uwar bacci a yanzun nan. Za ki shiga cikin ɗakin ki watsa shi nan take za su kwanta nannauyan bacci, sai ki aiwatar da abin da yake gabanki. Amma fa idan kin so, idan ba kya buƙata za ki yi biyu babu domin ko ba yanzu ba na yi rantsuwa da girman Shugaba da horon tsafin da yake ba ni, da kuma sirrin tsafi da sihirinsa ko ba daɗe ko ba jima sai na mallake shi. Gara tun wuri wannan damar kada ta wuce ki." Fulani Umaima kusan mutuwar tsaye ta yi, ruwan mamaki ya mamaye ta; ta yi tsamo a gefe kamar kazar da aka jiƙa da ruwa.
Chapter 42 · 0% Book details