← Book details Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 86

Sashe 31

Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ka bi mariƙiyarka don ka yi dace da mariƙa na gari. Amma ina son yau da daddare ka ce musu su baka labarin abin da ya faru a Dajin Wushushe a daidai gefen ƙoramar Ɗinya, a ranar bikin shaɗi." Kai kwai Kamalu ya iya gyaɗa masa sakamaon fisgar hannunsa da Inna wuro take yi har suka ƙarasa cikin sashensu na Bayi. Ganin yanayin yadda su Inna wuro suka shiga ya sa Baffajo ya ƙura mata ido. Duk abin da ya faru Inna wuro ta kwashe ta ba wa Baffajo labari, Baffajo ya kalli Kamalu sannan ya dafa kafaɗarsa.

"Kamaludeen!" Baffajo ya kira shi da wani irin yanayi. "Ba tun yau ba jikina ya jima yana ba ni kai na musamman ne sai dai ina tsoron kada miyagun su saka mini kai a gaba. Don Allah ka riƙa takatsantsan, ka ga yanzu kai da 'yar uwarka A'iru ne kaɗai kuka rage mini." Murmushi Kamalu ya yi don a tsammaninsa Baffajo rufe shi zai yi da faɗa, Inna wuro za ta yi magana Kamalu ya dakatar da ita.

"Baffajo wai mene ne ya faru a Dajin Wushushe a daidai gefen ƙoramar Ɗinya, ranar bikin shaɗi..." Kallon da ya ga sun wurga masa a tare kusan lokaci ɗaya ne ya katse ƙarshen maganarsa, take tsoro ya mamaye zuciyarsa ya ɗan ja da baya.

"Waye ya ce ka yi mana wannan tambayar?"

"Ba komai za ka riƙa sanar da su Baffajo ba, idan ka na son na dinga amsa maka tambayarka. Idan sun tambaye ka kawai ka ce musu mafarki ka yi, ka yi mini alƙawari?"

Tsawar da Baffajo ya buga wa Kamalu ce ta dawo da shi hayyacinsa a lokacin da ya lula duniyar tunanin wata hira da suka taɓa yi da Dattijo Maharazu.
"Baffajo kawai a mafarki ne aka ce na tambaye ku!"

"Daga yau idan na sake jin makamanciyar wannan maganar sai ranka ya yi mummunan ɓaci ka ji me na ce?" Kamalu ya amsa wa Baffajo cikin matsanancin tsoro.

Hawayen takaici, damuwa da tashin hankali ne ke rige-rigen tsiyayowa daga kwarmin idonta, ta tura kanta cikin ƙafafuwanta kamar ƙaramar yarinya sai da ta yi kuka mai isarta sannan Fulani babba ta furta. "Ya Ubangiji ina godiya bisa wannan jarabta da kake yi mini, Ya Allah ka yaye mini wannan miyagun al'amura da suke bijirowa rayuwata ko na yi mu'amala da mijina kamar kowacce mace." Kuka ne ya ci ƙarfinta ta jima a haka sannan ta faɗa banɗaki ta watsa ruwa ta koma kan gado ta yi lamo kamar mara lafiya.

Sai da dare ya tsala sosai kamar sabuwar munafuka Jakadiya ta bi bayan ɗakunan Bayi ta nufi bakin wata bishiyar ɗorawa hannunta ɗaya ɗauke da beran da Boka Shaddas ya ba ta, da sauri-sauri ta hau haƙa rami ta tura beran da ransa cikin ramin ta mayar da ƙasar ta rufe sannan ta taso zuciyar ƙal kamar wacce aka yi wa bushara da Aljanna. A ranar Jakadiya bacci ta yi sosai don har sai da ta kusa makara sallar Asuba, saboda tsananin farinciki.

Tun da Fulani Umaima ta zo duniya maganar auren Mai martaba ce abu na biyu da ya yi mummunan ɗaga mata hankali, daga lokacin da Bamaguje ya sanar da ita Fulani Babba na da cikin Abubakar sai wannan maganar. Haka ta yi ta faɗi tashi daga wannan boka zuwa wannan boka sai dai ita kanta tana zuwa ne amma babu wani sauyi ko ci gaba da ake samu daga wurin Mai martaba, sai ana iya kiran ci gaban na mai haƙar rijiya sakamakon wani zaman doya da majar da suka cigaba da yi, cikin tsangwama, kyara da hantara dga wurin Mai martaba.

Ganin haka ya sa ta ƙuduri niyyar zuwa wurin Takawa don ta kwantar da kai cikin kissa da kisisina. Wanka ta tsala ta yi kyau sosai sai dai kuma ta ɗan faɗa fuskarta ta yi fayau, bayan Sallar Magriba ta isa Turakar Mai martaba a lokacin ko iso ba ta jira ba. Ƙamshin turarenta ne ya buge shi, a hankali ya ɗago yana kallonta sai kuma ya kawar da kai gefe ya amsa mata sallamar a ciki.

"Yanzu a kan ƙasƙantacciyar Baiwa Sailuba Mai marta ya mayar da ni bora, lallai duniya juyi-juyi kwaɗo ya buga tsalle ya faɗa ruwan zafi." Fulani Umaima ta yi maganar a zuciya. Murmushin yaƙe ta aro ta yafa wa fuskarta sannan ta ƙarasa har gaban gadon da yake kwance.

"Ni mai laifi a gare ka ce kuma ban farka daga halin da na tsinci kaina a ciki ba sai da na fahimci muhimmancin abin da kake ƙoƙarin aiwatarwa. Don Allah ka yafe mini Sarkina, na gane kuskurena kuma a shirye nake na karɓi duk wani hukunci daga gare ka komai tsaurinsa." Fulani Umaima ta ƙarasa maganar cike da rauni, ƙwallah ta fara gangaro mata ta fara shasshekar kuka mai jan hankali.

"Tun da ma can ba mu riƙe ki ba kawai mun ɗaga miki ƙafa ne domin mun lura kina buƙatar haka." Wani ƙululun baƙinciki ya sake mamaye ta ganin yadda yake sha mata ƙamshi. Ta ruƙo hannuwansa har lokacin tana zubar da hawaye ta furta, "Sai nake ganin kamar Mai martaba bai gamsu da tubana ba, ranka shi daɗe za ka iya hukunta ni da duk abin da ka yi niyya matuƙar zai sanyaya zuciyarka. Ban fahimci alkairi ne yake ƙwanƙwaso mana ƙofa game da auren Sailuba ba sai a mafarki da na yi jiya, tabbas Sailuba za ta zame mana tamkar yabanyar da kowanne manomi yake burin samu a gonarsa. Na ga tarun alkairai a game da ita har zuwa Yarima, dalilin da ya sa na fahimci kuskurena tun farko. Amma idan kana buƙatar na baka wuri zan wuce ranka shi daɗe matuƙar hakan zai sanyaya zuciyarka." Tun lokacin da ya ji Fulanin Umaima ta ambaci sunan Sailuba wani farinciki ya mamaye birnin zuciyarsa, tana shirin miƙewa ya kamo hannuwanta ya zaunar da ita kusa da shi. "Mun fahimci kuskurenki, don haka a kiyaye duk wani abu da zai taɓa martabar da mutumcin Sailuba." A ɗan razane ta dube shi jin waɗannan kalaman na Takawa masu kama da ruwan dalma a cikin kunnuwanta, babu yadda ta iya haka ta danne ta ƙaƙalo murmushin ƙarfin hali. Ta yi ƙoƙarin bin Yarima a sha kiɗa duk don ta kai ga cim ma muradinta. Dare ranar daga Fulani har Sarki Abdul'aziz sun gudanar da shi cikin matuƙar farinciki musamman Fulani Umaima ta ga ta mantar da Takawa 'yar togaciyar da ta shiga tsakaninsu. Dalilin da ya sa ta sake sakin jiki aka shiga shagalin bukukun kamar babu komai a ranta.

Rana ba ta ƙarya sai dai uwar ɗiya ta ji kunya. Kamar yadda Mai martaba ya faɗa ranar juma'a aka ɗaura auren Khadija da Yarima Safwan, sai kuma Sailuba da Sarki Abdul'aziz. Gidan ya kacame sosai baƙi ta ko'ina ɓarkowa suke suna taya Mai martaba murna. Kafin wani lokaci tuni masu wasan gargajiya da 'yan bori suka fara cin kasuwarsu cikin ƙwarewa da tabbatar da al'adun hausa. Jakadiya wani irin farinciki ta riƙa ji kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha, haka daga ɓangaren Bayi zuciyoyinsu tas sakamakon wannan ranar ta kasance musu tamkar ranar cin gashin kai. Bayan sallar juma'a aka shirya Khadija cikin shiga ta alfarma da ƙasaita, aka miƙa ta wurin Takawa ta kansa ya riƙe mata hannu bayan ya yi mata doguwar nasiha ya wuce da ita motar da za a wuce da ita Masarautar Gumel. Fulani babba ta yi kuka sosai don ji take kamar an yage mata wata gaɓa daga jikinta, sai 'yan uwanta da suka zo suka dinga tausarta har aka tafi da Khadija.

Daga ɓangaren Fulani Umaima 'yan uwanta suma sun zo da yawansu, sai dai ba ta ji da daɗi ba da ta ga Mahaifiyarta ba ta zo ba, sai mahaifinta da yayyanta maza ne kaɗai suka zo ɗaurin aure. Ta so a ce mahaifiyarta ta zo ko ta kawo mata mafitar halin da take ciki amma ta ci alwashin idan aka gama biki komai ya lafa za ta kai ziyara ta musamman wurin mahaifiyarta.

A cikin jerin sashen matan Sarki Abdul'aziz aka gyara wa Sailuba nata sashen, ya tsaru sosai ya fita gwanin birgewa. A daren ranar aka shirya Sailuba cikin tsadaddiyar alkyabba baƙa wacce aka yi wa adon fararan duwatsu, sai baza wani irin sihirtaccan ƙamshi take yi kai tsaye aka wuce da ita sashen Mai martaba. Bayan zaman Sailuba babu jimawa ya sa aka kira masa su Fulani Umaima, sai da suka zauna sannan ya haɗa su gabaɗaya ya yi musu nasiha tare da fatan kowanne zai riƙe matsayinsa. Kamar babu abin da ke ran Fulani Umaima haka ta riƙa amsawa tana sakin murmushi har sai da abin ya ba wa Fulani Babba mamaki. Bayan ya gama yi musu faɗa ya sallami su Fulani Babba suka fice, sai dai zuciyoyinsu duk babu daɗi domin shi kishi kumallon mata ne duk yadda ka so danne shi sai ya motsa.

Sarki Abdul'aziz ban da murmushi babu abin da yake yi har ya isa wurin da Sailuba ke zaune, a hankali ya ye mata hular alkyabbarta yana sakar mata murmushi. Ɗan sunne kai ƙasa ta yi cike da kissa.

"Barka da shigowa Sadaukin Sarakai kuma adalin shugaba!" Ta furta a hankali.

"Barkanki dai sarauniyar matan duniya." Ya yi maganar cikin kulawa da nuna tsantsar soyayya ya fara rage kayan jikinsa sannan ya rage mata nata kayan. Sailuba ta saki murmushi a zuciyarta tana mamakin wai yau ita ce a gefen Sarki Abdul'aziz, sarkin da ke mulkar masarautar da kowacce mace za ta so a ce ta haɗa iri da ita. Gasassun kaji da kayan marmari ya riƙa ɗauka da kansa yana ciyar da Sailuba, ita kuwa ganin irin kulawar da yake ba ta ya sa ta sake narkewa cikin kissar da ta sake fizgarsa da jan hankalinsa.

Tun da Fulani Umaima ta koma ɗakinta wani abu mai ɗaci ya tokare mata maƙoshi, cikin ƙunan zuciya ta yanke shawarar zubar da makamanta don ta kai wa Bamaguje ziyarar ko zai yi mata magani. A birkice ta ɗauko akwatinta har ta kai hannu za ta ɗauki ƙahon ta busa.
Chapter 31 · 0% Book details