← Book details Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 86

Sashe 46

Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ba ni labari yadda aka haihu a ragaya don ganin fuskarki kaɗai ya tabbatar mini akwai wata a ƙasa." Mahaifiyarta ta furta bayan sun shige uwar ɗaki da Fulani Umaima.
"Aikin Bamaguje ne, kin san ko shugaban sheɗanu haka ya gan shi ya ƙyale." Umaima ta furta.

"Ni shaida ce don yanzu haka jiya mahaifinku ya tsayar da ranar da zai yi murabus ya danƙa wa ɗan'uwanki Muhammad." Murmushi Fulani Umaima ta saki sannan ta furta.

"Amma fa ina da gagarumar matsalar yanzu dai tun da a cikin kacaniyar mutuwar nan ake zan ziyarci Bamaguje."

"Wannan karon ba ke kaɗai za ki ziyarce shi ba domin ni kaina akwai abin da ya fara ci mini tuwo a ƙwarya."

Hawaye ne bibbiyu yake zuba a idanun Mai gado da ke gaban gadon da Jawahir take kwance, jikinta ta ɗauki zafi zauuu sai sauke numfashi take sama-sama. Da alama bacci take amma kallo ɗaya idan ka yi mata za ka fahimci a galabaice take, gaban Mai gado na faɗuwa ta kai hannu a hankali ta yaye rigar Jawahir. Dam! Ƙirjinta ya buga da ƙarfi har sai da ta sa hannu biyu ta dafe ƙirjinta, tambarin cikin Jawahir ne ya fito jawur tamkar garwashin wuta.

"Kin saɓa umarnina Jawahir! Ina hango abubuwan da ke ba za ki taɓa hango su ba, amma duk da haka hannunka ba zai taɓa rubewa ka yanke ka yar ba. Ba ni hannunki Jawahir." Mahaifiyarta ta furta tana miƙa wa Jawahir hannu. A ɗan tsorace Jawahir ta fara takawa har zuwa gabanta, gabanta na faɗuwa ta miƙa mata hannunta na hagu. Da ƙarfi mahaifiyarta ta fisgi hannunta sannan ta fara tafiya da ita har ta isa bakin bishiyar da Fulani Umaima ta binne butar da Bamaguje ya bata. "Ki haƙo butar nan ji ki je ki ɗebi ruwan rafin tsamiya, ki je sashen Umaima ki zuba asirin jikin Takawa zai wargaje gabaɗaya. Sannan ki ɗauki butar ki damƙawa Kamalu ita ragowar aikin zuri'ar da ke tare da shi za su nusar da shi abin da zai yi a gaba. Kuna da matuƙar tasiri dangane da junanku sai da arashin ruhi ne ke tsaurara tsattsamar alaƙa a tsakaninku." Mahaifiyarta ta ƙarasa ta damƙi wuyan Jawahir da ƙarfin gaske har sai da ta fara wani irin kakari idanunta suka firfito waje numfashinta na yunƙurin ɗaukewa sannan ta sake ta; ta ci gaba da cewa. "Na yi rantsuwa da girman shahara da fifikon tsafin da na fi gabaɗaya zuri'ata matuƙar kika kuskurewa umarnina sai na hallaka ki da tafukan hannuwa, domin ba zan iya jurar a salwantar da rayuwarki ba tare da cikar muradina da na mahaifinki ba." Wani irin kakari Mai gado ta ji Jawahir tana yi numfashin na ƙoƙarin ɗaukewa, tana shirin tashinta Jawahir ta tashi firgigit a galabaice tana sauke ajiyar zuciya idanunta sun firfito. Hannu biyu Jawahir ta sa a wuyanta ta riƙe har lokacin ba ta daina sauke numfashi ba.

"Sannu Jawahir jikin ne?" A hankali Jawahir ta girgiza mata kai, "Inna shi kenan Fulani ta mutu?" Jawahir ta yi wa Mai gado tambayar don ta kawar da hankalinta, sai da Mai gado ta share hawaye sannan ta furta. "Jawahir har abada ba zan daina kukan rashin Fulani ba." Jawahir ta miƙe a hankali ta ɗauki mayafinta ta ɗora a kafaɗa.

"Ina kuma za ki jawahir ke da zazzaɓi bai gama sauka daga jikinki ba."

"Inna yanzu nan zan dawo." Jawahir ta yi maganar tana ficewa daga É—akin.

Tana tafe gabanta na faɗuwa sai raba ido take cikin matsanancin tashin hankali, kallo ɗaya za ka yi mata ka fahimci ba ta cikin nutsuwarta a haka har ta ƙarasa sashen Sarki Abdul'aziz da ke cike da 'yan gaisuwa. Ta bayan sashen shaƙatawarsa ta zagaya a lokacin babu kowa take tsoro ya sake mamaye ta, daga can bakin wata bishiya ta hangi ƙasanta na fitar da hayaƙi.

"Ga wurin can, ki yi gaggawar tonewa kada ki ɓata lokaci." Ta ji muryar matar da ta yi mafarki da ita raɗau a cikin kunnuwanta, da sauri ta ƙarasa ta fara tonowa ba ta ɗauki lokaci mai tsayi ba ta tone butar nan take ta ji wani irin yammmm tsigar jikinta na tashi. Kai tsaye rafin tsamiya ta nufa ta ɗebi ruwan ciki tana miƙewa ta ga wurin yana juya mata, runtse idonta ta yi ta ji kamar ana tafiya da ita a saman iska. Tana buɗe idonta ga mamaki ta hange ta a soron sashen Fulani Umaima, a cikin mayafinta ta ɗan ɓoye butar ƙirjinta na bugawa matsanancin tsoro ya mamaye ta. Tana nan tsaye lokaci ɗaya ta ji butar ƙarfen ta fara ɗaukan zafi, tamkar ana neman a kwaci butar haka ta fara ji. Tana son ɗaga ƙafarta don ta shiga tsakar gidan Fulani Umaima amma yadda ake fusgarta na neman gargararta. Sai da ta yi da gaske sannan ta iya shiga cikin sashen, ta fara zubawa. Duk wurin da ta zuba ruwan butar sai dai wani baƙin hayaƙi ya tashi, tana gama zubawa da sauri ta fice daga sashen gabanta na tsananin bugawa.

Murmushi ɗauke a saman fuskokinsu suka ƙarasa cikin kogon dutsen Bamaguje, daga can saman dutsen suka hango shi a tsaye riƙe da sandar tsafinsa saboda tsufa ya ranƙwafa sosai jikinsa sai karkarwa yake. Fulani Umaima ta dubi mahaifiyarta tana sakin murmushin don rabon da su kawo wa Bamaguje ziyara a tare a ƙalla an doshi kusan shekara Talatin, Mahaifiyarta ta fara yin gaba ita kuma tana biye da ita.

"Tsafi ya ja linzamin dokin shugaba har zuwa ƙarshen rayuwa, ina gwanin wani ga nawa? Ina mai ƙaryata tsafi ya zo ya ga tushen wurin da ake gudanar da gundarin tsafi. Ka daɗe ka yi ƙarko da shekaru irin na dabina Bamagujena, ina ƙananan Bokaye da 'yan tsubbu ga shugabanku. Wa ya isa ya ja da kai yanzu a ga ƙarshen rayuwarsa! Na gaishe ka madogarata mai yaye mini damuwa da share mini hawaye." Mahafiyar Fulani Umaima ta ƙarasa kirarin tana zubewa a gabansa. Fuskarsa a murtuke babu ko ɗigon fara'a ya ɗago ya kafe Fulani Umaima da kallo. Tana shirin yi mata magana ya saka hannu ya ɗauke ta da matsanancin mari, a yadda yake idan ka ga Bamaguje sai ka rantse idan ya mari mutum ba zai yi wani tasiri ko zafi a jiki ba. Azabar marin ta sa Fulani Umaima ta kusa zubewa, kafin ta kai ƙasa ya sake ɗauke ta da wani marin.

Hankali a matuƙar tashe Umaima da mahaifiyarta suka kafe Bamaguje da kallo, musamman Umaima da ta san laifin da ta aikata dangane da salwantar da littafin hannunta. Da sandar hannunsa ya nuna Umaima nan take ta tafi shuuuuu har ta dangana da bangon dutsen kogon, ya sake nuna ta da sandar hannunsa rai a ɓace nan take ta ƙame ƙam kamar dutse. A razane Mahaifiyarta ta ƙarasa gabansa cikin kuka ta dafa ƙafafuwansa, bai tanka mata ba sai da ya koma mazauninsa na ainihi sannan ya ɗago ya dube ta rai a ɓace.

"Idan na so salwantar da rayuwar Umaima abu ne mai matuƙar sauƙi a wurina, amma tun a wancan karon sai na ɗaga mata ƙafa da ta sa na karya alƙawarin da na ɗauka a kan yarinyar da ta ce za ta kawo mini. Na kawar da kaina ne domin hannunka ba zai taɓa ruɓe ka yanke ba, amma a wannan gaɓar tura ta kai ni bango domin a kan na rasa littafin nan gara na rasa kowa da komai domin shi ne tsanin da zai kai ni ga cin nasarar da na sa a gaba. Don Allah wannan shi ne hukuncin da ya da ce da Umaima, a kan ɗanyan aikin da ta aikata mini. Kuma idan duk bokayan duniya za su haɗu domin su tashe ta ba za su taɓa iyawa ba, har sai na ga damar dawo da ita ainihin surarta. Umaima za ta zauna tamkar dutse a gabana, don haka ki tashi ki ba ni wuri."
*SHU'UMAR MASARAUTA*

*26*

*Littafin kuɗi ne 500 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*

Cikin matsanancin mamaki Sulaiman ya dubi Fargi da ke tsaye a gabansa, mamakin kalamanta ya sa ya dube ta ya furta. "Ta wacce hanya kike ganin zan iya mulkar Masarautarmu bayan Shugaba ya nuna mini alamun rashin nasara?"

"Sai an gwada a kan san na ƙwarai ɗan samari! Ya kamata ka dinga jarraba sa'arka a wurare mabambamta tun da an ce idan hagu ta ƙi sai a koma dama." Tsoro ya mamaye shi aƙ zuciyarsa yana tsoron kada dai yana gaban matsahiyar da yake jin ana faɗin tsafi da duk wani sihiri ba ya taɓa gagararta. Tamkar Fargi ta hangi abin da yake cikin zuciyarsa ta saki murmushi tana faɗin, "Kada ka tsorata domin zubin surar hallita da tauraronka ba na ragwayen mazaje ba ne. Kamar yadda zuciyarka take kokonta ka shaida mata, kana gaban Fargi 'yar matsafa jikar matsafa mai taƙama da alfarmar tsafi da sihiri." Da sauri Sulaiman ya ɗago ya dube ta, ta sakar masa murmushi sannan ta fara takawa a hankali. Da sauri ya sha gabanta a tsorace murya na rawa ya ce. "Tuba nake Shugaba da fatan dai ban aikata wani zunubin ba?" A karo na biyu ta sakar masa murmshi sai da ta ƙarasa ta kama tafin hannunsa ta ƙura masa, sannan ta dunƙule hannunta ta ɗora a saman hannunsa ta ɗan runtse idonta tana furta ɗalasiman tsafi. Duk yadda Sulaiman ya so ƙwacewa sai ya gagara don haka matsanancin tsoro ya sake mamaye shi, har sai da ya saki fitsari a tsaye saboda tashin hankalin abin da ka je ya zo.

"Buɗe hannunka!" Fargi ta furta masa a taƙaice.

Da sauri Sulaiman ya buÉ—e hannu sai ga wani farin rawani ya bayyana a tafin hannunsa, wata zabgegegiyar takobi ta bayyana a ciki da sauri ta taso tamkar za ta tsire idonsa har sai da Sulaiman ya ja da baya.
Chapter 46 · 0% Book details