Sashe 80
Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ungo mayar da littafin nan ciki, jiya na kuɓutar da shi daga hannun Shugaba don na san zai iya ɓatar da shi ko ya ƙone shi domin kowa ya rasa." Kamar mutum mutumi haka Jawahir ta tsaya duk abin da ake saka ta haka take aiwatar da shi, saboda kallo ɗaya za ka yi mata ka fahimci a tsorace take. A hankali ta ƙarasa daidai wurin da ta ciro takobin ta zura littafin, da kansa ta ga yana gangarawa ya shige yana gama shiga ta ji wani abu ya ɗaure mata kai tamkar wacce aka kafa wa hula a kanta har sai da ta kai hannu ta shafa saman goshinta. Luuu ta ji a kanta wata irin juwa na yunƙurin ɗaukanta, tana shirin zubewa ƙasa da sauri Fargi ta riƙo ta tana sakin murmushin. Ruƙo hannunta ta sake yi suka fito daga wannan ruwan sannan ta ja hannunta zuwa bakin wata murgujejejiyar bishiyar kukar da ke maƙota da kogin, jingina ta ta yi a jikinta ta fara motsa bakinta, ta jima a haka sannan ta dafa kafaɗarta nan take suka ɓace daga wurin.
A inda suka bar mutane da Mahaifin Fargi a nan suka koma suka same su tsautsaye carko-carko, Shugaba har kawo lokacin yana tsaye baƙinciki ya mamaye zuciyarsa. Jagora ta yi musu zuwa wajen dutsen sakamakon cunkoson mutanen da suka ƙaru a cikin kogon dutse, da hannunta ɗaya ta fara jan Shugaba a ƙasa duk irin ihun da yake yi ba ta kalle shi ba.
Kamalu yana cikin Masarautar Huddam yana kula da Malam Umaru amma zuciyars da ruhinsa na wurin Jawahir da halin da take ciki, duk wani abu da Malam Umaru yake buƙata shi yake yi masa daga ƙarshe ma gabaɗaya Bayin da ya kira masu taimaka masa ya sallame su. Har cikin dare Kamalu yana jin shige da ficen da Muhsin yake yi da alamar akwai abin da yake son tambaya amma ganin Kamalu ya sa ya haɗiye abin da yake ransa.
Sarki Sulaimanu sai da ya sa aka haɗa musu guzuri da kayan abin da ba a rasa ba sannan Bayi da Sojojin cikin Masarautar suka rufa musu baya, tafiya suka yi mai nisa sannan suka shiga cikin garin Bururu. Kafin su shiga ta cikin ƙofar sai da Sarki Sulaimanu ya isa bakin wata bishiyar kuka da ke gefen ƙofar ya dafa ta da hannunsa na hagu sannan ya furta.
"Sulaimanu ba shi kaɗai ba ne tare yake da mabambamtan fuskoki." Sai da ya tsinki ganyen bishiyar kukar ya damƙa musu kowannensu ya riƙe a hannun hagunsu sannan suka shiga cikin garin, tun daga shigarsu cikin garin su Sarki Abdul'aziz suka sha jinin jikinsu kallo ɗaya za ka yi musu ka fahimci a ɗan tsorace suke.
"Amma me ye fa'idar yin hakan da ka yi Sarki Sulaimanu?" Sarki Abdul'aziz ya tambaya.
"Saboda sun gama tsaface garinsu, tun tasowa ta har zuwa yanzu ban taɓa jin labarin garin da ya yi shuhura a kan aikin tsafi da sihiri tamkar wannan ba. Yin hakan ne zai ba ku damar shi ga cikin garin nan hankali kwance, idan ban yi haka ba akwai matsaltsalun da za su iya biyo baya." Jinjina kai Sarki Abdul'aziz yana mamakin ƙarfin tsafi da sihirin al'ummar Rumzu.
Sarki Sulaiman ya sha mamaki da ya ga garin a yaye tamkar babu mutane don sai tsirari daga cikinsu, kuma duk wanda ya gansu haka zai bi su da kallo har sai sun ɓace wa ganinsu sakamkon bambamcin shigar da suke da ita.
Tun daga nesa Jawahir ta hango Keken dokin Sarki Abdul'aziz, wani irin farinciki ya lulliɓe ta ta zabure za ta tafi da gudu, Fargi ta damƙe hannunta da ƙarfi. Nan take idanun Jawahur ya ciko da ƙwalla, yadda suka hango cincirindon mutane a hanyar kogon dutsen Shugaba ne ya ja hankalin Sarki Sulaimanu, don da har ya yi niyyar fara zuwa gidansu Fargi domin su ɗan huta idan ya so sai Sarki Abdul'aziz ya gudanar da abin da yake tafe da shi, tun da har kawo lokacin bai san dalilin yin wannan tafiyar ba.
Sannu a hankali komai ya shiga dawo masa dangane da alaƙar da ke tsakaninsa da Fargi a lokacin baya.
"Sadaukina yanzu fa watarana sai mu zo garin nan mu da 'ya'yanmu idan ka mayar da ni Masarautarku ko?" Kalama Fargi na baya suka shiga dawo masa a lokacin da ba su jima da yin aure ba.
Ganin yanayin shigarsu ya sa tun da suka tunkari kogon dutsen mutanen da ke wurin suka shiga darewa suna ba su hanya, Tun da Mai gado ta hango Jawahir ta tafi da gudu cikin kuka ta rungume ta ita ma Jawahir ta saka kukan farinciki, da farko ya yi tsammanin idanunsa gizo suke yi masa amma da ya ƙarasa gabanta a nan ya tabbatar da ƙwayar idonsa ba yaudararsa take yi ba. Jikinsa ne ya ɗauki karkarwa kamar mazari ƙirjinsa ya shiga bugu da ƙarfi zuciyarsa tamkar za ta hudo ƙirjinsa, da hannu ya shiga nuna ta bakinsa na rawa ya furta. "Far... Fargi ke ce ƙwayar idona ke gane mini?" Idanunta suka ciko ƙwalla tsantsar tausayinsa ya mamaye ta, ganin haka ya raunata zuciyar Dattijo Maharaz. Jikinsa shi ma ba ƙaramin sanyi ya yi ba yana fargabar kalaman da za su fito daga bakin Fargi don ya san ba zai taɓa yi wa Sarki Sulaimanu daɗi ba, dangane da tsammanin da yake yi a kan Fargi ce a gabansa. Da ido sauran mutane suka ci gaba da bin su da kallo, Sarki Sulaimanu ya waigo wurin Sarki Abdul'aziz cikin farinciki ya ce.
"Ikon Allah ikon gaske, ashe rabon mu gana da Fargi ne ya sa kuka kawo mini wannan gayyatar Sarki Abdul'aziz." Dattijo Maharaz ya yi murmushi sannan ya nuna Jawahir ya furta. "Wannan ita ce silar zuwanmu wurinta, shin har yanzu ba ka gane wace ce ita ba Sarki Sulaimanu?" Ƙurr ya yi Jawahir yana kallonta yana son furta abin da yake cikin zuciyarsa amma tsoron kada ya canka ba daidai ba ya dakatar da shi. "Tun ranr da na fara haɗuwa da ita Fargi nake gani a ƙwayar idon, kuma jikina yana ba ni akwai wata muhimmiyar alaƙar da ke tsakaninsu." Sarki Sulaimanu ya furta cike da shauƙi.
"Wannan yarinyar 'yarka ce, jininka ce ta cikinka." Saukar kalaman Dattijo Maharaz suka yi daidai da jin dum! Da Mai gado ta yi tsakar kanta, Sarki Abdul'aziz ya zaro ido cikin tsananin mamaki.
"Duk rintsi kada ku furta wannan yarinya ba jininku ba ce, don na san dangina da bibiya ko bayan wasu shekaru na tabbata za su iya bankaÉ—o labulen sirrin da na binne." Furucin Mahaifiyar Jawahir na baya ya sake dawo wa Mai gado, ta ji wani sabon tashin hankali ya tsarga mata.
"Kana nufin wannan 'yar Fargi ce?" Sarki Sulaiman ya tambaya kai tsaye. Dattijo Maharaz ya ba shi amsa.
'Tabbas Biri ya yi kama da mutum, wallahi tun ranar da na fara ganinta a Masarautar Huddam na sha jinin jikina." Sarki Sulaimanu ya ƙarasa maganar yana rungume Jawahir a jikinsa.
"Ranka shi daÉ—e idan Jawahir 'yarsa ce mene ne makomata a wurin Jawahir? A gafarce ni idan da kuskure a kalaman da zan faÉ—a, amma sam wannan ba shi ne ainihin mahaifinta ba. Mahaifin Jawahir yana gida ba shi da lafiya, ni nan ni ce mahaifiyarta ni na É—auki cikinta har zuwa haihuwa." A wannan lokacin Sarki Abdul'aziz ya É—an shiga ruÉ—ani, tabbas a tarihin da ya ji Jawahir na daga cikin zuri'ar Rumzu, kuma a iya saninsa Malam Umaru da Mai gado ne iyayenta.
"Me yake shirin faruwa?" Ya furta a fili cikin tsananin mamaki.
"Wallahi-wallahi Fargi matata ce ta sunnah, kuma a shekarun baya akwai cikina a jikinta wanda ba na ko tantama wannan 'yata ce. Don Allah Fargi ki sanar da su gaskiya..."
"Ka gafarce ni Sarki Sulaimanu bisa abin da zai fito daga bakina." Ta furta tana ɗan sunkuyar da kai ƙasa, jikinsa ne ya ɗauki karkawa ƙirjinsa ya buga tsoron abin da za ta faɗa ya mamaye shi. Wannan shi ne ga ƙoshi ga kwanan yunwa, fargabarsa ba ta wuce kada ya ga samu ya ga rashi ba don ko tantama ba ya yi wannan 'yar cikinsa.
"A zahiri na tabbata kowa kallona yake a matsayin Fargi amma ni ba Fargi ba ce." A zabure Sarki Sulaimanu da Mahaifin Fargi suke dube ta jin kalaman da ta furta.
"Fargi ta mutu bayan haihuwar 'yarta Jawahir yau kimanin shekara goma sha Shida kenan, na kasance ina amfani da surarta bisa yarjejeniyar da suka ƙulla tsakaninta da abar bauta tun a wani dare da ta taɓa kai wa abar bauta kokenta. Sunana na ainihi Zumjuttu na kasance ɗaya daga cikin jinsin aljanun da ke ɗaukar surar Mammaci suna gudanar da wasu al'amuran na shi na yau da kullum, kafin Fargi ta mutu ta yi wa abar bauta tukwicin da ita kuma ta damƙa mini wannan ragamar a hannuna, domin na kular mata da duk shige da ficen halin da Jawahir take ciki, har zuwa lokacin da za ta yi tozali da mahaifinta. Kuma koda wani mugun abin ake son na aiwatar da zarar an yi mini yanka an zubar da jini domin na dinga razanarwa ina firgitarwa, an riga da an gama biya kuma ba ya juya wa wannan aikin baya, wanda dalilin haka ne za ku ji ana ce wa fatalwar mutum tana tsoratar da mutane. Daga ƙarshe dai na sauke wannan nauyin da kula da Jawahir, sai kuma Abar bauta ta ɗora mini wani nauyin na mallakawa Jawahir hatsabibin littafin da Hidaya ta ba da labarinta a ciki, silar haka na dinga zuwar mata a fili wani lokacin kuma a cikin mafarkinta. Na ci gaba da kai kawo a cikin rayuwarta har zuwa lokacin Jawahir ta mallaki wannan takobin kamar yadda kuke gani." Aljanar da ke magana da surar Fargi ta ƙarasa maganar tana ɗago hannun Jawahir . A razane Dattijo Maharaz ya ɗago yana duban Zumjuttu rai a matuƙar ɓace.
"Amma me ya sa sai a wannan lokacin za ku ci amanar abin da ta damƙa muku, me ya sa ba ki fayyace ainihin abin da ya sa kike bibiyarta ba?" Dattijo Maharaz ya yi maganar rai a ɓace.