← Book details Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 86

Sashe 14

Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abu ɗaya ne ya fara damun Mai gado da yake faruwa da Jawahir cikin dare, duk lokacin da ta farka don ta ba ta nonon akuya da dare sai ta ga wani baƙin jini ya tsattsafo a goshinta, idan kamar bacci ya ɗauke ta har asuba ta yi, sai da ga goshin na ta ya yi ɗan duhu amma babu jinin a jiki, zuwa wayewar gari kuma sai ta nemi komai ta rasa jinin ya washe. Tun tana barin maganar a ranta har ta taɓa tashin Umaru ta sanar da shi, shi kansa ya yi mamaki amma gudun kada ƙilu ta ja bau! Ya ce su zuba wa sarautar Allan ido tun da ba ta kuka wataƙila abin ya mata ciwo. Kwanan Jawahir goma Mai gari ya aika a kira masa Umaru, tun da Umaru ya ji kiran Mai gari gabansa ya faɗi har sai da Mai gado ta ƙarfafa masa gwiwa sannan ya nufi gidan Mai gari cikin wasuwasi.

Yana zuwa aka yi masa iso har cikin shagonsa da yake hutawa a soro, ganin Malam Malmo ya sake tsinka zuciyarsa. Dole ƙanwar na ƙi ya zuba wa fuskarsa murmushin yaƙe cike da girmamawa ya gaishe su. "Umaru ka sani a gaban Mai gari kake don haka muke son duk maganar da muka tambaye ka ta zama gaskiyarka za ka faɗa. Wace ce yarinyar da ka zo da ita kuma a ina ka same ta?" Malam Malmo ya jefa masa tambaya. "Allah ya baka yawan rai wallahi tsintarta muka yi..."

"Idan tsintarta kuka yi ina mahaifiyarta? Ko kuna nufin jaririya É—anyar haihuwa za ta kawo kanta ne?" Mai gari ya katse Umaru. Shiru Umaru ya yi yana tsoron kada ya ba da kai bori ya hau, yana cikin nazari ya tsinci kalaman Malam Malmo.

"Sanin kanka ne Umaru duk yankin nan babu wanda ya kai ni sanin sirrin tsafi da sihiri, na bincika kuma na gano waɗansu bayanai tun ranar da na ɗora ƙwayar idona a kan yarinyar nan. A zahiri ne kuke ganinta ƙanƙanuwa amma a baɗini basarakiya ce, shu'uma ce kuma tana ɗauke da rikitattun al'amura. Ita ba kamar kowa ba ce dalilin da ya sa mahafiyarta ta yo gudun fanfalaki da ita kenan daga cikin danginta, mukuma a ɓangarenmu na masu aikin tsubbace-tsubbace wannan yarinyar ta kasance tamkar taki ce da ke farfaɗo da shukar da ke cikin gona. Ya zama wajibi ka mallaka mana ita domin cikar muradinmu, a zahiri Mai gari zai karɓi riƙonta ta koma gidansa da zama. A baɗini kuma zan aiwatar da aikin da za ta kasance a ƙarƙashin ikona. Sharaɗi na biyu ya zama dole ka nuna mini daidai wurin da gawar mahaifiyar yarinyar nan take, idan ba haka ba wallahi sai na shayar da kai ruwan mamaki."

Gumin da ya shiga keto wa Umaru ne ya bankaɗa sirrin da ke cikin zuciyarsa, cikin matsanancin tsoro ya ɗago jiki na rawa ya furta. "Duk abin da kuka buƙata haka za a yi ranka shi daɗe, da kai da kaya duka mallakar wuya ne." Malam Malmo ya saki murmushi cikin jin daɗi don ya ga tsoro malale a saman fuskar Umaru don haka ya furta.

"Ba zan barka haka ba Umaru dole za mu aiwatar maka da naka tukwici mai tsoka." Umaru ya saki murmushin yaƙe yana godiya, sannan Mai gari ya sallame shi.

Kamar zai tashi sama haka ya ƙarasa gidan yana alla-alla ya ɗauko Jawahir ya kai musu ko ya yarda ƙwallon magwaro ya huta da ƙuda.

Masarautar Huddam

A ranar da aka kai Abubakar ɗakin da ke ɓangaren gidan ajiya da gyaran hali ko runtse Fulani babba ba ta runtse ba, baƙinciki da ɓacin rai ya mamaye zuciyarta. Sai gabannin asuba sannan ta samu hawaye ya zubo mata, zuciyarta cunkushe da ɓacin rai. Wani abu da ya so ɗaure mata kai ganin ta wayi gari lafiya ƙamas babu fitsari a shimfiɗarta, ba ta ankara da haka ba sai da aka kira sallar asuba da za ta yi wanka kamar yadda ta saba duk asuba sai ta wanke fitsarin jikinta. Amma wannan ranar da ta kwana idonta biyu sai ta ga babu komai a jiki, mamaki cike da zuciyarta ta yi alwala bayan ta gabatar da sallah a gurguje ta nufi sashen da Abubakar yake kwance ɗauke da kayan sawar da za ta sake masa kamar yadda ta saba tsaftace shi.

"Waye nan?" Aka furta mata cike da tsawa a lokacin da ta ƙarasa jikin babban ƙauren ƙofar. Baƙin ciki ya kama ta jin ƙasƙantaccan bawa na buga mata tsawa, da ace a sashen ta yake babu wanda ya... "Ina magana waye nan?" Kamalan Dogarin suka katse mata tunani. Sai da ta sauke ajiyar zuciya ta furta. "Fulani ce na zo wurin Abubakar." Cikin girmamawa Dogarawan suka zube. "A gafarce mu uwar gijiyarmu, muna neman afuwar saƙon da zai fito daga bakunanmu." Zuciyar Fulani ta fara azalzala kamar za ta hudo ƙirjinta, fargabarta ɗaya kada su ce mata wani abu game da Abubakar. "Allah ya taimake ki, ki yafe mu amma Takawa ya ja kunne da kada a sake buɗe ƙofar nan har sai hantsi ya ɗaga wurin ƙarfe tara." Da sauri ta dube su. "Yaushe ya bada wannan umarnin?"

"Ranki shi daÉ—e jiya da dare."

Sai da ta haɗiyi yawu mai ɗaci sannan ta miƙa musu kayan hannunta da akushin abincin da ta taho da shi.

"A gyara Abubakar da shi a tabbatar da an yi masa wanka, wannan abincinsa ne." Jim suka yi sannan ɗaya daga cikinsu ya furta. "Allah ya taimake ki koda mun karɓi kayan nan sai lokacin da Takawa ya zartar za mu buɗe ƙofar, amma a gafarce ni ranki shi daɗe." Wani irin kukan takaici ne ya taso mata, gudun kada ta bar abin faɗa ya sa ta juya da sauri ba tare da ta amsa musu ba. Fulani babba na zuwa sashenta ta fashe da matsanancin kuka, tana tsaka da kuka ta ji Khadija mai kimanin shekara goma sha shida ta dafa kafaɗarta. "Ummi me ya sa kullin cikin kuka kike? Ummi kin san idanun masarautar yana ko ina a lungu da saƙo don Allah kada ki bari a samu a bin faɗe, komai ya yi tsanani maganinsa Allah kamar yadda na ji kina faɗa. Wuya ba ta kisa na san a kan Sadiq kike wannan kukan don Allah ki kwantar da hankalinki na tabbata babu abin da zai faru da shi." Khadija yarinya ce mai nutsuwa da sanin ya kamata, idan tana magana kamar babbar mace, a hankali ta goge wa mahaifiyarta hawaye ta ci gaba da tausarta har damuwar da
take ciki ta yaye. Haka ta haƙurƙurtar da zuciyarta har lokacin da ya dace, sannan ta ɗauki kayan da kanta ita da Khadija suka nufi wurin Abubakar. Tun tasowar Abubakar ko da wasa Fulani ba ta taɓa yunƙurin ba wa wata baiwa hidimarsa ba, haka ta sawa ranta har zuwar ƙarshen rayuwarta za ta ci gaba da kulawa da shi ba tare da ta sare ba. A lokacin da suka ƙarasa ɗakin duk da kasancar safiya ce ƙudaje ne suka fara yi musu maraba, a kwance suka same shi kamar yadda Fulani ta bar shi da dare sai dai ya fitsari da kasaye duka kayan jikinsa. Ƙudajen da ke kai-kawo a kansa yake ɗaga kai yana cafko duk wanda ya zo hannunsa ya kai bakinsa ya cinye. A fakaice Khadija ta share hawayenta, sannan suka gyara masa jikinsa. Khadija ta kira Baiwa Salamatu ta damƙa mata kayan Abubakar don a wanke su, sannu a hankali Fulani babba take ba shi abinci wani ya karɓa wani ya zubar bayan sun gama suka tashi suka rufo shi suka fito daga sashen zuciyoyinsu babu daɗi.

Tsaye take hannunta ɗauke da wata irin sharɓeɓen tsafaffiyar takobin da Boka Bamaguje ya bata don kare kanta da shi, ta hango ƙurar ɗan matashin yaron ya tunkaro ta da bai fi sa'an Muhsin ɗin ta a shekaru ba, duk yadda ta so hana shi shiga cikin ƙofar Masarautar Huddan sai abu ya gagara. Ganin haka ya sa ta zaburo da sauri kafin ta aiwatar da abin da yake ranta ya sa hannuwansa biyu ya mauje ta, ta faɗi ƙasa warwasa. Ɗagowar da za ta yi ta hangi Baiwa Maimuna a bayansa tana sakar mata murmushin mugunta, sai wata inuwa da ta gagara tantance wace ce ita. "Ban yafe miki abin da kika yi mini ba kuma sai na ɗauki fansa a kanki." Rufe bakin Baiwa Maimuna ta sa hannu ta fara jan Fulani Umaina a ƙasa kanta sai kurjewa yake jini na zuba, ko da ta hango Bamaguje yana tsaye a gefe yana kallonsu cikin magiya da tashin hankali ta fara roƙonsa. "Da kai kaɗai na dogara Bamaguje ka taimaka mini za su kashe ni." Wata irin mahaukaciyar dariya ta ga ya bushe da ita, ya juya mata baya ya fara tafiya yana faɗin. "Na riga na gaya miki kin yi sake wannan yaron ba kamar ɗan uwansa yake ba."

Firgigit Fulani Umaima ta farka daga mummunan mafarkin da ta yi, a 'yan kwanakin nan ta rasa dalilin waɗannan miyagun mafarkai nata. Kusan kullin sai ta yi mafarkin wannan yaron yana barazana da rayuwarta. "Waye wannan da yake ƙoƙarin kutsowa cikin rayuwata har yake neman dagula lissafina?" Ta tambayi kanta ba tare da ta san amsar tambayarta ba. Ƙirjinta ya buga a lokacin da ta tuna jaririn da baiwa Maimuna ta fitar da shi yana nan a doron ƙasa, "Ƙarya ne ba shi ba ne! Ba zai taɓa razanar da ni ba." Fulani Umaima ta furta tana kai wa da kawowa.

*Littafin kuɗi ne 500 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*
*SHU'UMAR MASARAUTA*

©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga É—aukan tsattsauran mataki don haka a kiyaye.

*Masu ƙorafe-ƙorafe ta pc da groups zan rage 100 daga yau zuwa ranar da zan gama free pages. Free pages za su ƙare a page a 10 daga yanzu zuwa ranar duk mai son karanta littafin za ta turo 400*

SHAFI NA TARA
Chapter 14 · 0% Book details