← Book details Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 86

Sashe 67

Shuumar Masarauta Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lokacin da su Galadima suka samu labari sun matuƙar razana, sai kuma mamaki ya kama su duk da kowa ya san Fulani Umaima ba mai faran-faran da mutane ba ce, amma sun kaɗu da jin miyagun labaran da suke fitowa dangane da ita har zuwa kan mahafiyarsu. Kuma tun da gari ya waye suke sa ran ko Sarki Abdul'aziz zai neme su amma sai suka ji shiru, babu wani aike da suka samu daga fada. Don haka suka shirya shi da Ciroma suka wuce kai tsaye zuwa fadarsa, tamkar babu hassada ko ƙyashi a ransu haka suka shiga taya Sarki Abdul'aziz murna da jimanta masa game da abubuwa biyu da suka faru na farinciki da baƙinciki.

Kamar waɗansu sababbin hallitu haka waɗansu daga cikin bayi masu son ganin ƙwaƙwaƙƙwaf suka bi ta hanyar baya suka isa ɗakin duhu suna leƙen Fulani Umaima da Jakadiya. Tsoro ne ya kama su matuƙa da ganin halin da Fulani Umaima take ciki, ilahirin jikinta ya yi kace-kace da jini ta faɗi a gefe sai sauke numfashi take da ƙyar. Ita kuma Jakafiya gaban rigarta a yage ga mamanta ɗaya da ya gutsure wani irin ruwa da jini na zuba. Uwa-uba ga wani irin wari da yake tashi daga cikin ɗakin, don haka suka dinga toshe hancinsu. Sai da manyan Dogaran wurin suka fatattake su sannan kowa ya watse, kafin zuwa yammacin ranar tuni mabambamtan labarai suka dinga zaga ciki da wajen masarautar. Kowa da abin da yake faɗa, wasu su ce Sarki Abdul'aziz ne ya sa ake yi musu wannan horon na azaba, wasu kuma su ce aljanin da suka yi wa Fulani Umaima aiki ne reshe ya juye da mujiya suke dawowa gare ta. Wasu ma har ce wa suke fatalwar Fulani babba ce ta dawo take ɗaukan fansa. Tun safiyar ranar Ruƙayya ta dame shi da son ganin mahaifiyarta, kalaman da suka fara taɓa zuciyarsa yake jin tausayin yaran ya kama shi. Daga ƙarshe ma sai ya sa aka tura ta wurin Mai gado a can sashen Fulani babba domin ta ci gaba da kula da su, wunin da Kamalu ya yi tare da Takawa duk sai ya ji shi a takure don ya saba asubar fari suke fita kowa ya kama aiki gabansa amma tun da gari ya waye sai dai ya ci ya sha su yi hira da Takawa ya kwanta.

"Ranka shi daÉ—e ina son ganin su Inna wuro." Kamalu ya furta yana kallon yanayin Sarki Abdul'aziz.
"Mun samar maka Bayin da za su dinga taimaka maka su yi rakiya da duk wani abu da ya shafe ka. Su Inna wuro daban suke a wurinmu don haka za su yi maka rakiya zuwa wurinsu, amma daga yau ba ma son ku dinga yawan fita har sai mun sa an horar da ku É—abi'u da halayen 'ya'yan sarakuna." Sai da Kamalu ya russuna sannan ya furta. "Ina godiya da wannan karamcin ranka shi daÉ—e."
"Mun sa an fara gina wa su Inna wuro ɗakuna a bayan ɗakunan mahaifiyarka, muna so nan da ɗan wani lokaci mu keɓe su daga sahen Bayi." Sarki Abdul'aziz ya furta wa Kamalu. Farinciki ne ya mamaye shi ya sake zubewa ƙasa ya yi masa godiya, har sarki Abdul'aziz zai sa a kira bayin da za su fara yi masa hidima Kamalu ya ce. "Amma ranka shi daɗe idan babu damuwa zan iya zaɓar bayin da za su yi mini hidima?" Gyaɗa masa kai Takawa ya yi Kamalu ya yi godiya sannan ya faɗi sunan abokansa biyu da tun tasowarsu suke tare, kuma a ganinsa wannan ce hanyar da zai bi domin ya sauƙaƙa musu daga aikin bautar da suke yi suma su huta, tun da shi ma Allah ya 'yanta shi.

Kamar waɗanda suka ga baƙuwar hallita haka Bayi suka dinga bin Kamalu da kallo, duk hanyar da ya bi sai dai Bayi su dinga zubewa a ƙasa suna gaishe shi. Shi abin har mamaki yake ba shi, ko da ya shiga ɗakin Inna wuro suna ganinsa suka rungume shi cikin farinciki. Inna wuro ta shiga tattaɓa shi tana ƙare wa kayan jikinsa kallo.

"Kamaluna kai ne haka ka fito ka yi kyau?" Baffajo ya faɗa, yana taɓa rantsattsiyar rigar jikin Kamalu. "Baffa wallahi na yi kewarku." Kamar haɗin baki duka suka amsa masa. "Muma mun yi kewarku Kamalu." Jawahir ce ta shiga ɗakin hannunta ɗauke da ƙwaryar furar da Mai gado ta turo ta don ta kawo wa Inna wuro. Turus ta yi tana bin Kamalu da kallo, shi ɗin ma kallo yake bin ta da shi. Karamcin jiya da ta yi wa mahaifinsa ya sa ya fara ganin girma da ƙimarta. Taɓe baki ta yi kamar ba ta gan shi ba, ta miƙa wa Inna wuro furar sannan ta ce. "Inna wuro ga fura Inna ta ce na kawo miki kuma wai ku biyu kaɗai za ku sha." Jawahir ta yi maganar tana satar kallon Kamalu don da ta san yana ɗakin ba za ta yi wahalar dakan fura har ta dama ta kawo kuma ya sha ba.
"Inna zan sha fura." Kamalu ya faÉ—a saboda jin abin da Jawahir ta faÉ—a.

"Malam kar ka sake wallahi ka sha don ban daka fura don wani ƙato ya sha ba..." Daga bayanta Mai gado ta katse ta. "Dama rashin hankalin da kika zo yi kenan ko Jawahir? Kin manta matsayin Kamalu yanzu?" Jin haka ya sa Kamalu ya ɗan sake tsare gida, Jawahir ta ɓata rai baƙincikinta bai wuce a gaban Kamalu Mai gado ta dinga ce mata tana rashin hankali ba.
"Wallahi ni kam bai isa ba a wurina, ni kullin a kamalu nake kallonsa tun ba a taɓa sauyawa tuwo suna." Jawahir ta ƙarasa maganar tana ficewa daga ɗakin. Baki sake Mai gado ta bi ta da kallo, sannan ta rufa mata baya don kullin lamarin Jawahir ƙara gaba yake yi sai ta tashi tsaye a kanta. Wani murmushin ƙeta Kamalu ya saki don, ya fahimci hanyar da zai bi ya cusgunawa Jawahir don ya lura rainin da ke tsakaninsu ƙara yawa yake yi.

"Ban zaunar da ke domin ki yi mini kuka ba, tambayar ki nake cikin waye a jikin?" Mahaifiyar Fargi ta sake jefa mata tambayar.

"Na aikata babban zunubin da ya kasance babban hukunci ne ga duk wanda ya aikata makamancinsa a yankin nan, Inna aure na yi na sirri ba tare da kun sani da. Ki dubi girman tsafi kada ki fallasa wannan sirrin da na sanar da ke, wallahi ban san yadda aka yi na zunduma cikin kogin soyayyarsa ba. Dalilin haka ya sa muka yi aure a ɓoye, kuma ni kaina rannan bincike ya bayyana mini cikin da ke tare da ni." Ilahirin jikin mahaifiyarta rawa yake, ganin haka ya sa zuciyar Fargi ta sake karyewa. "Kuma shi bai kasance jinin zuri'ata ba, hasali ma Sarki ne a wata masarauta da ke nesa da yankin nan, sai dai masarautar ba ɓoyayya ba ce. Don girman tsafi da dogaron da muka yi akansa ki binne wannan sirrin, ke uwa ce za ki fahimci abin da nake faɗa. Ina nan zan ci gaba da binciko yadda zan yi da cikin jikina amma ba zan taɓa lalata shi ko na salwantar da shi ba."

"Me ya sa kika aikata haka Fargi bayan kin san zunubi ne yin soyayya da É—an wata zuri'ar, amma har ta kai ki ga aure?"
"Saboda ina son a dakatar da wannan mummunar ɗabi'ar da ke shiga haƙƙin zuƙata, an kashe 'yan mata da dama sanadin haka. Samari da dama sun kashe kawunansu saboda rasa masoyansu da ba sa cikin zuri'ar nan, shin ko kin san Lado, Tine, Wargu, zinne da Damiggu duk sun kashe kansu ne saboda sun san kashe su za a yi matuƙar tsafi ya san suna soyayya da waɗansu da ba sa cikin zuri'armu? Ta yaya za mu samu ci gaba har zuri'armu ta bunƙasa a doron ƙasa, na zaɓi hakan ne ko zan rasa raina a nan gaba ban damu ba matuƙar zai karya wannan alƙadarin da zuri'armu take kai tun iyaye da kakanni. Amma don matsayin da kika ba wa tsafi da sihiri kada ki tona asirina har sai bayan na sauke cikin da nake tare da shi." Ajiyr zuciya mahaifiyarta ta sauke sannan ta furta. "Ba na son na rasa ki Fargi, don haka zan taya ki rufe asirin halin da kike ciki. Amma ina tsoron abin da kaje ya zo a nan gaba."

A ranar kwana uku ciff da aika takardun da Sarki Abdul'aziz ya sa aka yi, Mai martaba da mahaifiyar Fulani babba suka yi wa Masarautar Huddam tsinke, ba a gama tarbarsu ba sai ga su Mahaifiyar Fulani Umaima sun ƙaraso. Lokaci ɗaya gidan ya hautsine da baki, Bayi suka shiga hidima da manyan baƙi aka sauke su a babban ɗakin saukar ɓakin Sarki Abdul'aziz, babu jimawa Sakina da Khadija suma suka ƙarasa cikin masarautar.

Wasu na ji suna mamakin Ruƙayya 'yar Fulani Umaima ba ta mutu ba, kun manta bayan ta haifi Basiru ta sake samun ciki ta haifi 'ya mace aka saka mata Ruƙayya. Ita waccan Ruƙayyan ai ita take bin Yarima Muhsin wannan kuma ita ce take bin Basiru.
*SHU'UMAR MASARAUTA*

*37*

*Littafin kuɗi ne 500 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.*

Boka Shaddas ya jima yana kai-kawo a cikin halwar tsafinsa yana bincike game da yadda zai ɗauko Basiru amma ko ɓurɓushin samun mafita bai gani ba.

"Tabbas Shugaba Zurufu ya kasance taƙadari kuma hatsabibi amma zan ji da shi, sai na yi masa kwantan ɓaunan da zan shamace shi a lokacin da bai za ta ba." Boka Shaddas ya furta cike da cin alwashi. Waɗansu tarkacan magunguna ya ɗebo ya fara watsawa jikinsa, ya shiga yin turarrika sannan ya zauna a gaban wutar tsafinsa yana tunanin hanyar da za bi don ya isa cikin Masarautar Huddam ya ɗauko Jawahir ɗin da Shugaba ya saka shi ko ya samu damar fanso Basiru da tasirin tsafin da ya dogara da shi.
Chapter 67 · 0% Book details